Sashe 22
Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki · about 8 min read
A zuciyarta ta furta:
“Ni kam, ban yarda da tafiyar nan ba. Ina jin akwai babban abu da suke ɓoye min. Amma wallahi sai na gano komai.”
Yasmeen ta leƙo daga ƙofa ta ce da dariya:
“Hajia babba, ai idan kika ci gaba da wannan binciken sai kace wata ‘yar leƙen asiri ce.”
Hajia Babba ta harare ta:
“Ke baki san komai ba. Wannan gida ba wasa ba ne. Ni dai na rantse, duk wanda ya ɓoye gaskiya a gabana, sai ya yi nadama.”
Bangaren Zysha Ɗaki
A ɗaki kuwa, Zysha ta kwanta tana tunani. Har yanzu kalaman Hamdiya da Rabi suna ratsa zuciyarta. Sai ta janye
Ta sake janye Alqur’ani ta karanta surar Yasin a hankali, hawayenta na zuba, tana jin ƙaramin ƙarfin guiwa yana komawa cikin ranta.
Bangaren Asibiti
Ammi tana riƙe da hannun Amour, zuciyarta na rawa. Cikin ɗan lokaci, Amour ta motsa leɓenta kamar mai son yin magana. Ammi ta matsa kusa sosai tana sauraro.
“Am… m…” ta furta da ƙyar, muryarta ƙasa sosai har sai da Ammi ta saita kunnenta.
Mahek ya matsa da sauri, zuciyarsa na tsalle da fargaba.
“Amour! Ki yi ƙoƙari, me kike so ki faɗa?”
Amour ta buɗe idanunta a hankali, hawaye na taruwa a gefen su. Ta yi ƙoƙari ta motsa hannunta amma ƙarfinta ya ƙare. Kalma ɗaya ce ta fito daga bakinta:
“…sirri…”
Nan take, zuciyar Ammi ta buga da ƙarfi. Rehman ya runtse ido, zuciyarsa kamar zata fashe. Mahek kuwa ya tsaya cak, jikinsa ya yi sanyi.
Ammi ta ce cikin rawar murya:
“Wane sirri ne, Amour? Don Allah ki gaya min, kada ki barni cikin duhu.”
Sai kawai na’urar dake a gefen gadon ta yi ƙara, tana nuna alamun numfashinta ya sauka ƙasa. Likita ya shigo da sauri tare da nas, suka rufe su daga dakin.
Ammi ta tsaya a bakin ƙofa tana kuka, hannunta na rawa. Rehman ya dafa goshinsa yana tafiya a hankali cikin damuwa. Mahek kuwa ya jingina da bango, idonsa cike da tsoro da tambayoyi.
Likitan ya dubi su daga nesa, ya ce da muryar dake ɗauke da nauyin gaskiya:
“Dole mu yi iya ƙoƙarinmu, amma ku shirya zuciyoyinku. Jikinta na fama da rauni mai tsanani… ta yi ƙoƙari saboda wata ƙauna ce da ke rike ta. Amma idan ta sake, ba zai zama da sauƙi ba.”
Kalmar likita ta fado a zuciyar Ammi kamar dutse. Ta rufe fuskarta da hannaye tana roƙon Allah cikin kuka:
“Ya Allah, kada Ka ɗauke min ita yanzu…”
Masarautar Egypt
Bangaren Afsana da Papa da Mamie
A gefe guda kuwa, rayuwar Afsana ta cika da annashuwa da farin ciki tare da iyayenta. Papa kullum cikin dariya da raha ya ke saka su.
Mamie ta kasance mace mai kirki da salo na musamman wajen kula da gida. Komai cikin tsafta da kwalliya, haka kuma kullum tana nuna ƙauna ga Afsana kamar ƙawarta.
Afsana kuwa ta fi samun kwanciyar hankali a gidan. Kullum tana tare da Mamie tana koyon girki, da sauran ayyuka na mata. Saboda mamei ta ce ita bata buƙatar ko wace kuyanga. Sai dai duk da haka, Papa baya barinta da aiki mai wahala. Idan ya dawo gida ya tarar da ita cikin aiki sai ya yi dariya ya ce:
“Ke fa masoyiya, ba ke kadai bace a gidan nan, ki bari kuyanga ta taimaka miki, kin dai zama fara’a a cikin gidan nan.”
Mamie ta yi murmushi tana ce masa cikin wasa:
“Papa, ni fa ina jin daɗi idan na yi aiki.
Bangaren Maranta
Yau kuma Afsana ta shirya zata fita zuwa maranta da sabuwar kawarta, Sabiya, domin Afsana na samun farin ciki da nutsuwa idan ta je can.
Da suka isa, aka tarbe su cikin farin ciki. Maranta suka zagaye Afsana suna mata sannu da zuwa, fuskar su ɗauke da murmushi.
Sabiya kuwa ta tsaya a gefe tana kallon ikon Allah – yadda yaran ke mugun ƙaunar Afsana, kamar wata haske ce ke yawo tare da ita.
Daga can gefe, wata tsohuwa daga cikin maranta ta yi addu’a tana duban Afsana da mamaki:
“Allah ya tsare ki yarinya, kina da wani haske daban. Kin fi kowa ɗaukar hankali a wajenmu.”
Afsana ta yi murmushi ta durƙusa cikin ladabi ta ce:
“Amin, Baba. Allah ya saka da alheri.”
Sabiya ta kalle ta cikin farin ciki ta ce:
“Wallahi Afsana, idan na zo tare da ke, ina jin kamar duniya ta sauya min. Kin kasance kamar wata gata da Allah ya yi wa maranta.”
Tun daga wannan rana, Sabiya ta kara jin daɗin kasancewa tare da Afsana.
Rayuwa a makaranta ta kasance wata sabuwar tafiya ga Afsana da Sabiya. Duk da kasancewarsu ƙawaye na kusa, sun kasance ‘yan gaban goshi wajen karatu. Malamai suna sha’awar yadda suke dagewa, musamman Afsana wadda ta kasance daliba mai hazaka fiye da zato.
Wani lokaci idan malamai suka yi tambaya, kafin kowa ya ɗaga hannu, sai Afsana ta riga kowa da amsa. Wannan ya sa wasu ɗalibai suka fara jin kishin ta. Amma Sabiya kullum tana tare da ita tana ƙarfafa ta:
“Ki ci gaba da yin haka Afsana. Kada ki damu da masu kishi, ilimi fa bai da abokin gaba.”
Wata rana, Malamin Turanci ya kira Afsana da Sabiya gaban aji ya ce:
“Ku biyun kun zama abin koyi. Idan kuka ci gaba da dagewa haka, wallahi makarantar nan zata yi alfahari da ku.”
Sai duk aji suka ɗau tafa musu, Afsana da Sabiya suka yi dariya suna kallon juna cikin farin ciki. Ka
A gefe guda, Papa da Mamie suna cike da farin ciki da ganin yadda ‘yarsu ke kwashewa a makaranta. Kowanne daren Lahadi, Afsana kan zauna a parlour tana nuna musu sakamakon test ɗinta.
“Kin fi ƙarfin yabonmu ‘yata,” inji Papa yana shafa kanta.
Mamie kuma ta ce da murmushi:
“Allah ya ƙara miki basira, Afsana. Kin zama haskenmu.”
Afsana ta sunkuyar da kanta cikin ladabi ta ce:
“Amin Mamie, amin Papa. Zan dage har sai kun yi alfahari da ni fiye da yau.”
Bangaren Makaranta – Sabuwar Jarabawa
Bayan makonni da dama suna cikin annashuwar karatu, wata sabuwar jarabawa ta taso ga Afsana da Sabiya. Wannan jarabawar kuwa ba daga malamai bace, sai dai daga wasu dalibai da ke jin kishin su.
A cikin ajin su akwai wata yarinya mai suna Elena, wadda ta sha fama da zama abar yabo kafin zuwan Afsana. Tunda Afsana ta fara yin fice, sai ta ji kamar an yi mata katsalandan a wurin da take da iko.
“Ni Elena ce mai wayo a wannan aji. Amma yanzu, wannan Afsana tana son ta kwace min komai,” ta fada wa ƙawayenta cikin ɓacin rai.
Sai suka shirya makirci – su sa a yi jarabawa tsakanin Afsana da Elena a bainar jama’a, domin a ga wacce ta fi ƙwarewa.
Wata rana, Malamin Turanci ya shigo da wani babban littafi. Ya kalli daliban aji ya ce:
“Mun sami damar shiga gasar karatu ta matakin ƙasa. Kuma daga wannan aji, za a zaɓi wakilai. Na ga akwai hazikai biyu – Elena da Afsana. Za mu gwada ku a gaban aji domin mu ga wacce tafi dacewa.”
Ajin ya kaure da hayaniya. Wasu na goyon bayan Elena a, wasu kuma na fadin suna Afsana.
Sabiya ta damƙi hannun Afsana tana cewa:
“Ki kwantar da hankalinki. Kin shirya, Allah zai taimake ki.
An fara tambayoyi masu zurfi kan Turanci da kuma ɗan nazarin adabi. Elena ta yi ƙoƙari sosai, amma Afsana ta fito dabam. Kowane amsa da ta bayar ta kasance mai natsuwa da fahimta, har malamai suka fara kiran sunanta da yabo.
A ƙarshe, Malami ya ce:
“Mun yanke shawara. Afsana za ta wakilci ajin nan a gasar ƙasa. Amma Elena, kin yi ƙoƙari sosai, za mu buƙaci gudunmawarki wajen shirin gasar.”
Ajin ya tafa da farin ciki, wasu suna murna, wasu kuma sun yi shiru.
Bangaren Elena
Elena ta yi murmushi a waje amma zuciyarta cike da haushin Afsana.
“Wallahi sai na nuna miki, Afsana. Kin ɗauke min suna, amma ba za ki ɗauke min zuciya ba.”
Tun daga ranar da aka zaɓi Afsana, makaranta ta shiga cikin shirye-shirye na gasar jiha. Malamai suna daɗa ƙarfafa ta, suna mata horo na musamman a kowane fanni – daga rubutu zuwa karatun zauren jama’a.
Sabiya ta kasance a gefenta kullum, tana taimaka mata da shirye-shiryen da ake buƙata. Duk lokacin da Afsana ta gaji, Sabiya tana ce mata:
“Ki tuna Afsana, ba kawai kanki kike wakilta ba. Ni, makaranta, har da iyayenki suna tare da ke.”
Afsana ta yi murmushi tana dubanta cikin idanu:
“Sabiya, ke ce ƙarfina. Da ke nake jin komai zai yiwu.”
Malamai suna mamakin yadda Afsana ta ke haɗa ilimi da ladabi. Malamin Turanci ya sha faɗi cikin ajin:
“Ba wai kawai ta iya amsa tambayoyi bane. Yadda take gabatarwa da kwarin gwiwa, shi ne abin mamaki. Wannan yarinya tana da kyakkyawar makoma.”
Har ma shugaban makaranta ya kira Afsana a ofishinsa ya ce:
“Mun ba ki amanar makarantar mu, duk da ƙarancin shekarun ki. Ki tabbatar kin yi abin da zai sa makarantar ta yi alfahari. Amma kada ki ji tsoro, muna tare da ke.”
Da ta dawo gida ta faɗa musu za a tafi gasar ƙasa, Papa ya rungume ta da farin ciki.
“Kin zama abin alfahari ga mu, Afsana. Allah ya ba ki nasara.”
Mamie kuma ta ce da hawaye a idanuwanta:
“Na dade ina addu’a Allah ya ba ki abin da zai yi haske a rayuwarki. Wannan shi ne farkon alheri. Amma ki dage da sallah da addu’a kafin ki fita.”
Afsana ta sunkuyar da kai cikin ladabi:
“Insha Allah Mamie. Zan dogara da Allah.”
Amma a gefe guda, Elena ta kasa jurewa ganin Afsana na samun wannan dama. Tana haɗa baki da wasu daga cikin dalibai, suna cewa:
“Mu dai ba za mu bari ta yi fice a gasar nan ba. Za mu tabbatar ta kasa.”
Haka aka fara ɗaga labule na sabon rikici mai girma, wanda zai kasance gwajin ƙarshe ga Afsana a makaranta.
❓ Tambayoyin Masoya littafin KURURUWAR SHAIƊAN
Amour ta furta kalmar “sirri” kafin ta rasa ƙarfin magana… wace irin asiri kuke tunanin take so ta faɗa?
Hajia Babba ta fara bincike cikin ɗakin Ammi – shin zata gano wani abu kafin lokaci?