Sashe 20
Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki · about 8 min read
Ammi kuwa tana zaune a falon ta, zuciyarta cike da damuwa. Rana ɗaya kenan bata ga Chef Rehman ba, wanda kullum yake zuwa ya ga halinta.
Ta dubi Mahek cikin damuwa:
“Mahek, ko ka ga Rehman yau? Ban ji labarinsa ba, hakan yasa nake cikin rashin nutsuwa.”
Mahek ya girgiza kai:
“Wallahi Ammi, ni ma ban gan shi ba. Ban ma san inda ya shiga ba tun jiya. Ni ma zuciyata ba ta daɗi.”
Ammi ta runtse ido, ba tare da ta sake magana ba, amma azuciyarta sam ba daɗe.
Bangaren Chef Rehman da Amour
A dakin jinya kuwa, bayan dogon lokaci, Amour ta samu ta farfaɗo, sai dai ba ta iya magana sosai. Ta rufe idanunta ta koma bacci mai sanyi.
Chef Rehman ya zauna gefenta yana kallonta, zuciyarsa cike da tausayawa. Ya riƙe hannunta yana furta cikin murya mai sanyi:
“Amour, ki kwanta ki huta. Ni zan tsaya a tare da ke har sai kin murmure.”
Sai dai zuciyarsa bata samun nutsuwa gaba ɗaya. Duk da ta farfaɗo, yana jin wani irin nauyi a ransa, musamman ma ganin ba ta iya magana kamar yadda ya saba jin ta ba.
Bayan lokaci ya miƙe tsaye, ya sumbaci goshinta ya fita harabar ajjiye motuci, ya shiga mota kai tsaye gida ya huci.
Yana shigowa parlour gidan ba tare da ya kula su Ammi da ke zaune ba, ya huci part ɗinsa. Wani irin san yi da ƙamshi mai saka nutsuwa suka dirar masa a hanci, ya lumshi jajayen idunsa a hankali ya ji wata irin nutsuwa. Bai tsaya komai ba ya ajiye phone ɗinsa kan bedside drawers ya shiga bathroom.
Sai da ya ɗauki tsawon lokaci, a bathroom, kana ya fito sumar kansa na ɗiɗɗigar da ruwa. A gaggauci ya shirya cikin ƙananun kaya, duk da baya cikin kwanciyar hankali, amma ya yi wani irin kyau mai ɗaukar hankali. Yana shirin fita mahek ya shigo ɗakin.
“boos! Ka daina ɓuyemin na san komai, jiya naga lokacin da ka fita…”
Chef Rehman ya tsaya cak, ya ɗan ƙanƙance idanunsa, ya ce:
“Mahek yau shi ka zama ɗan sa ido haka”.
Mahek ya yi murmushi mai ɗaci ya ce:
“kai fa jinina ne dole idan wani abu na faruwa ba daidai ba saina ji a jikina, amma please boos na roƙeka ka faɗamin halin da amour ta ke ciki”.
Yay maganar yana marai-raice fuskarsa, chef Rehman ya taɓe bakinsa ya juya da nufin barin parlour, karaf idonsa ya sauka kan Ammi da ke tsaye idonta sun cicciko da ƙwallah, sai ya yi saurin runtse idonsa, dan ya tabbatar ta ji maganar duba da ganin yanayin fuskarta.
A hankali Ammi ta tako cikin parlourn idonta na kan chef Rehman.
Ammi ta tsaya cak a gaban chef Rehman, tana kallonsa ido cikin ido. Murya na rawa ta ce:
“Rehman… gaskiya ina so ka faɗa min dukkan abin da ke faruwa, me ya samu amour ɗin, don Allah ka gaya min, bai kamata ka ɓoye min ba. Na ji da kunnena abin da Mahek ya faɗa yanzu.”
Chef Rehman ya sunkuyar da kai, zuciyarsa tana bugawa da ƙarfi. Bai san yadda zai fara ba. Ya lumshe ido kafin ya buɗe a hankali ya ce:
“Ammi… gaskiya abubuwa sun yi nauyi a kaina. Ban san ta yaya zan fara gaya miki ba…”
Ammi ta matso kusa, ta ɗora hannunta a kafaɗarsa cikin tausayawa:
“Rehman, ku kaɗai ne abin alfaharina. Idan wani abu ya dame ka, ka gaya min, ko da kuwa zai ɓata min rai, zan fi so na ji daga bakinka fiye da na ji daga bakin wasu.”
Rehman ya yi shiru na ɗan lokaci, sai ya sauke wani dogon ajiyar zuciya ya furta:
“Ammi…” sai kuma ya yi shiru.
Idon Ammi ya cicciko da ƙwalla, zuciyarta ta cika da damuwa. Ta yi shiru tana kallon ɗanta kamar tana karanta zuciyarsa.
Mahek ya matsu kusa da ita, sai ya dafa kafaɗarta:
“Ammi ki kwantar da hankalinki ba wata matsala ba….” Sai Ammi ta katsi shi ta hanyar ɗaga masa hannu.
“Mahek kar ka ce komai, na ji da kunne na kaima baka san halin da ake ciki ba”.
Ammi ta yi maganar a hankali hawaye na sauƙo mata. Chef Rehman ya yi saurin rintsi idonsa dan ko kaɗan baya sun yaga hawayenta.
Matsuwa ya yi, ya kai hannunsa ya share mata ƙwallar, yana girgiza kansa ya maa kasa magana.
Ammi ta tsaya tana kallon ɗanta, zuciyarta na rawa. Tana jin kamar akwai wani abu da yake ƙoƙarin ɓoye mata, wanda ya fi ƙarfin zaton ta.
Ta dafa hannunsa da ƙarfi, tana hawaye:
“Rehman, duk abin da zai faru ka gaya min. Ni uwarka ce, ban zan ji daɗi idan ka boye min damuwa ba. Na san akwai wani abu mai girma da kake ɓoyewa.”
Chef Rehman ya runtse ido ya lumshe, yana jin kalamanta suna huda zuciyarsa. Murya na rawa ya furta:
“Ammi… Amour ba ta cikin koshin lafiya. Likita ya ce tana buƙatar kulawa ta musamman… akwai wasu abubuwa da ba su dace in faɗa ba tukuna. Amma ina roƙonki ki yi haƙuri ki ba ni lokaci.”
Ammi ta ɗan girgiza kai cikin kuka:
“Lokaci kuma, Rehman? Lokaci na nufin rai da mutuwa ne! Kada ka bari wani abu ya faru da ita kana shiru. Wallahi idan wani abu ya same ta, ni ba zan iya jure maka ba.”
Ya riƙe hannunta yana share hawayenta:
“Ammi ki kwantar da hankalinki. Zan yi iya ƙoƙarina don ceton ta. Ki roƙi Allah kawai ya tsare mu daga abin da muke tsoro.”
A haka suka rungume juna, zuciyoyinsu cike da damuwa.
Bangaren Hamdiya da Rabi
A ɗayan ɓangaren kuwa, Hamdiya ta ɗaga kai tana magana cikin muryar ɓacin rai:
“Kin ji labari kuwa? Ammi ta fara nuna kulawa sosai ga Zysha. Haka kawai ta fi mu daraja.”
Rabi ta ce cikin tsanar zuciya:
“Wannan ba za mu bar shi haka ya wuce ba. Dole mu nuna mata cewa ita ba ta da wata ƙima a wannan gida. Ko da Ammi tana goyon bayanta, za mu sa ta daina jin daɗi.”
Hamdiya ta gyara zaman ta, idonta ya ɗauki wani irin kallo:
“Na shirya tsaf don tsara mata wani abu. Sai ta gane wannan gidan ba wurin wasa ba ne. Ni dai sai na ga karshe, ko ita za ta yi nasara a wajen Ammi, ko mu da muka girma cikin gidan nan.”
Rabi ta yi murmushi mai ɗaci, ta ce:
“To, mu fara tsara komai cikin hikima. Wannan faƙari zai nuna mata da gaske ba ta da matsayi a wajenmu.”
Zuciyoyinsu suka cika da makirci da ƙiyayya.
Bangaren Zysha
Zysha kuwa tana ɗaki, tana kallon madubi. Tana jin kalaman Ammi da suka ƙara mata ƙarfin gwiwa. Amma zuciyarta na cike da tsoro – ba ta san dalilin da yasa wasu daga cikin ‘yan gidan ke ƙin ta haka ba.
Ta jingina da kujera tana furta a ranta:
“Allah kai ne ka kawo ni gidan nan… ka tsare ni daga duk wani sharri. Na lura akwai wanda ba so na a cikin gidan nan”.
Ta share hawayenta, ta daure fuska, tana shirin fuskantar duk abin da zai taso.
Zysha ta miƙe ta fito daga ɗakin fuskarta ɗauke da damu na halin da take ciki. Duk da cewa tana cikin farin cikin samun kulawa daga Ammi, zuciyarta har yanzu cike take da tsoro da damuwa.
Ta nufi kitchen don taimaka wa su aunty asabe aiki. A lokacin Hamdiya da Rabi na tsaye a can suna ta hira. Suka yi shiru suka yi wani irin murmushi mai ɗaci.
Hamdiya ta jefa mata wani kallo daga sama zuwa ƙasa tana cewa cikin raini:
“Lallai wannan yarinyar tana jin kanta yanzu. Wai saboda Ammi ta ɗauke ta kamar ƴarta kenan, ta fara shiga wuraren da ba nata ba.”
Rabi ta ɗan gyara murya ta ce da wata annuri amma zuciya cike da ƙiyayya:
“Ki dai yi hattara, Zysha. Wannan gidan ba wurin wasa ba ne. Kowa ya san matsayinsa.”
Zysha ta tsaya cak, ta ɗauki numfashi a hankali, ta kalle su cikin ladabi ta ce:
“Ni dai ban zo nan da niyyar yin faɗa da kowa ba. Na zo ne kawai domin abin da ya kawo ni. Idan na ɓata muku rai, ku yafe min.”
Meena da ta shigo yanzu ta yi dariya mai cike da raini:
“Zaman lafiya kuwa? Ai ya riga ya ƙare, tun da har kin samu wani matsayi da Ammi, hakan ya isa ya nuna mana ba zaman lafiya za a yi ba. Mu dai za mu ga yadda za a kare.”
Hamdiya ta matso kusa da ita sosai, tana wani kallo mai cike da ƙiyayya, ta furta da ƙaramin murya:
“Ki kula da kanki, Zysha. Gidan nan akwai abubuwa da ba za ki iya jurewa ba idan kika tsaya kan hanya da ba taki ba.”
Zysha ta girgiza kai kawai ta juya jikinta yana rawa, ta bar kitchen ɗin tana hawaye.
Da ta koma ɗaki, ta faɗa kan gado ta rungume pillow tana kuka. Sai dai cikin ranta ta furta:
“Allah kai tsare ni daga sharri da makircinsu. Ni ba ni da kowa sai kai.”
Bangaren Chef Rehman, Mahek da Ammi
“Rehman, ba zan iya zama haka ina sauraron magana ba tare da na ga da idanuna ba. Tun da har ka shirya yanzu ka kaini wurin Amour. Idan ba haka ba, wallahi zuciyata ba zata taɓa samun nutsuwa ba.”
Chef Rehman ya yi shiru, ya sunkuyar da kai. Bai son Ammi ta ga halin da Amour ke ciki saboda tsananin yanayin da ta shiga. Amma ya san halin mahaifiyarsa, idan ta matsa ba zai taɓa iya ƙin biye mata ba.
Ya ɗan ja numfashi dan gaba ɗaya ya gaji, da duguwar maganar nan da ya ke, wallahi idan ba Ammi ba ce ba zai iya ba. Da sanyin murya mai ciki da gajiya ya ce:
“Ammi… ai ba dole ne ki gan ta yanzu ba. Likitoci sun ce tana bukatar hutu sosai. Idan kika je yanzu kina iya dagula mata lamarin.”