← Book details Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki Local reading mode
READING PART 27 OF 31

Sashe 27

Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki · about 8 min read

A cikin ɗaki mai ɗauke da ƙura da turaren wuta, Bokanya Yelena ta zauna tana kallon madubin sihirinta. Ta yi ƙoƙari ta kira sunan Afsana a cikin tsafi, amma duk lokacin da ta kawo hoton yarinyar a cikin madubi, sai haske fari ya bayyana ya kore duk wani inuwa.

Ta fashe da ihu:
“Wannan ba al’ada bace! Wata kariya mai ƙarfi tana kewaye da yarinyar. Wannan ba ƙaramin abu bane.”

Sarauniya Alisha ta matso kusa da ita da fuskar damuwa:
“Yelena, kina nufin tsafinmu bai isa ya karya ƙaramin zuciyar yarinya ba? Me ke tsare ta?”

Yelena ta rufe idanu, ta shafa hannunta a saman zobenta mai duhu, ta ce:
“Na ji ƙamshin wasu ruwan … wani babban malami ne ya ba ku wannan kariya. Idan har suna amfani da shi, to dole mu samo tsafi mafi ƙarfi wanda zai iya karya kowane nau’in addu’a da kariya.”

Sarauniya Alisha ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta ce da muguwar murya:
“ina tabbatar miki zan san du yanda zan yi na chanza wannan ruwan da kika faɗa. Zan yi duk abin da ya dace. Ko da kuwa zai cinye dukiya ta, dole ne in ga muneka ta rabu da Japhet. Kuma Afsana—yarinyar nan—dole ta sha wahala kafin wannan ya tabbata.”

Yelena ta yi murmushi mai ban tsoro:
“Ki shirya, Sarauniya. Zan yi amfani da tsafin da ba a taɓa yin irinsa ba. Amma ki sani, wannan zai buƙaci hadaya mai tsada.”

Sarauniya ta ɗaga kai cikin ƙuduri:
“Babu abin da ya fi burina muhimmanci. Ko da kuwa hadayar ta zame jini, zan bayar.”

Madubin sihiri ya sake yin walƙiya, an nuna hoton Afsana tana bacci cikin nutsuwa, amma inuwar duhu na zagaye da ita a nesa, tamkar ruwan guguwa da ke neman huda ƙarfinta.

Wannan harshen wuta mai duhu da Yelena ta saki ya yi ƙoƙarin shiga cikin gidan Afsana kamar guguwa. Ya zagaye taga, ya buga ƙofa, ya shiga ta saman rufin. Amma duk inda ya nufa, sai ya tarar da wani haske mai ƙarfi yana kare gidan.

Harshen wutan ya yi ihu, ya koma ya sake kai hari kan Afsana kai tsaye a gadonta. Amma da zarar ya kusanci jikinta, sai wani haske fari ya fantsama daga kan goshinta kamar rana ta faɗo cikin daki.

Mamie ta firgigit ta tashi daga inda take kwance. Ita kanta ta ga hasken ya ratsa ɗakin, ya kare Afsana gaba ɗaya. Japhet ma ya yi mamaki, ya furta da rawar murya:
“Lallai, wannan shi ne ikon Allah. Wannan ba karfin mu bane.”

Bangaren Yelena

A cikin dajin, Yelena ta fadi kasa tana tari kamar wacce aka buge. Idanunta suka zazzaro suka cike da tsoro:
“Ba zai yiwu ba! Na aika da tsafi mafi ƙarfi amma haske ya kore shi. Wata zuciya ce mai tsabta ke rufe wannan yarinya… wani abu da ya fi tsafinmu ƙarfi.”

Sarauniya Alisha ta yi tsaki da fushi:
“Yelena, kar ki gaya min kin kasa! Kin ce wannan tsafi ya fi dukkan kariya ƙarfi!”

Yelena ta yi shiru, sai jan hawaye suka zubo daga idanunta na tsufa:
“Na kasa, Sarauniya. Amma dole in nemo wani hanya. Sai dai wannan karon, dole a yi amfani da hadaya ta jini mai tsarki.”

A gefe guda, papa da Mamie ya sake cika da nutsuwa. Amma Sarauniya Alisha da bokanyarta sun fara shirin sabon hari wanda ya fi na farko hatsari.

Bangaren Yelena da Sarauniya Alisha

Wani duhun hayaƙi ya lullube ɗakin tsafi na Alisha. Fitila mai launin ja kawai ke ta walƙiya a tsakiyar dakin, yayin da Yelena ke kwance a gaban Sarauniya tana tari da wahala.

Sarauniya Alisha ta yi tsalle ta tsaya gaban girmamiyar tabarmarta, ta ɗaga hannuwanta cikin fushi:
“Yelena! Kin ce min wannan tsafi zai rusa yarinyar, amma me na gani? Haske ya kore shi kamar iska ta kore hayaƙi!”

Yelena ta lumshe idanu, murya na rawa:
“Sarauniya, wannan yarinya ba karamar halitta bace. Wani abu yana cikinta wanda ke ƙarfafa ta. Na gano cewa hasken da ke rufeta yana da alaƙa da wannan ruwan da Sheikh Addurrahman ya bata. Wannan ruwa yana da tsarkin da tsafinmu ba zai iya kaiwa ba.”

Sarauniya ta ɗan ja numfashi tana riƙe sarƙarta ta tsafi.
“To, menene mafita?”

Yelena ta ɗaga hannayenta da rawar jiki, idanunta suka haske da ja:
“Mafita ɗaya tilo ita ce ki sauya wannan ruwan, idan kuma hakan bai samu ba zaki bada hadayar jini mai tsarki. Jinin mai alaƙa da ke, wannan hadaya, za ta saka, tsafinmu ya yi nasara.”

Sarauniya Alisha ta yi murmushi mai sanyi, idonta cike da mugunta:
“chanza ruwa? Hmm… wannan abu ya zama mai sauƙi. Zan gano inda suke, ajiye shi.”

Bangaren Mamie da papa

A can gida kuwa, Mamie ta tashi da daddare tana jin tsoron abinda ya faru da Afsana. Ta dubi papa da yake zaune a gefen gadon yana karanta addu’a.

Mamie ta furta cikin kuka:
“Japhet, ba zan iya jurewa ba. Kowanne dare tsafi ke zuwa kan yarinyarmu. Shin har yaushe haka zai wuce?”

Papa ya ɗan janye Qur’an daga hannunsa ya kalleta cikin tausayawa:
“Ki kwantar da hankalinki Mamie. Sheikh Addurrahman ya ce ruwan Zam-Zam da addu’o’I sune garkuwarta. Kuma har yanzu kariyarta tana nan daram. Amma dole mu ƙara dagewa, domin waɗanda ke binmu sun shaƙu da zuciyar mugunta.”

Mamie ta share hawayenta, ta ce:
“To, yaushe za mu sake tuntubar Sheikh? Ina jin kamar akwai wani sabon abu da suke shiryawa. Idanuwana suna bani labari, zuciyata na tabbatar min.”

Japhet ya ɗaga ruwan Zam-Zam da aka kawo musu ya dube shi sosai. Ya furta cikin tsantsar damuwa:
“Wannan shi ne garkuwa a garemu. Amma dole na je wajen Sheikh gobe. Ina jin wani sabon hatsari na shirin tasowa. Sai mun ɗauki mataki kafin su sake kai hari.”

Mamie ta jingina kanta bisa kafaɗarsa, zuciyarta cike da tsoro amma kuma da ɗan ƙarfin gwiwa.

Bangaren Sarauniya Alisha

Alisha ta ɗaga hannunta ta ce da muguwar murya:
“Idan wannan ruwa ne garkuwarsu, to sai mun chanza shi da namu. Na san hanyar da za ta kai mu kusa da su zuwa wajen su da kyauta – amma cikin kyautar akwai ruwanmu na duhu wanda zai maye gurbin ruwa ɗin su.”

Yelena ta yi dariya mai sauti:
“Haka ake so! Da zarar sun sha daga wannan ruwa, kariyarsu ta kare. Kuma daga nan ne tsafinmu zai yi nasara.”

Bokanya Yelena ta kalli madubinta mai sihiri, ta ga hoton papa da Mamie. Fuskar ta ta ɗauki muguwar annuri:
“Wannan lokacin, babu wanda zai tsere. Afsana dole ta fadi cikin tarkonmu.”

To masu karatu me kuke tunanin zai faru hmmm. Muhaɗu ranar assabar idan Allah ya kaimu kada kubari abaku labari yanzu wasan zai fara.
Book 1 free ya kusa ƙarewa masoya littafin KURURUWAR SHAIƊAN duk wacce ta ke son shiga paid group dan mallakar complete ɗin littafin zata turo kuɗin shiga ₦400 ne zaku tura kuɗin ta wannan number 7062701555 Opay ZULFAU TUKUR MUHAMMAD shaidar biya a wannan number 07062701555 duk wacce ta shirya ta min magana please idan kin san baki shirya ba karki min magana

Duk wacce ta ke son document ɗin littafin KURURUWAR SHAIƊAN daga farko ta min magana ta wannan number 07062701555

Please share like comment masoyana

KURURUWAR SHAIƊAN

*✨HAZIƘAN MARUBUTA✨*

*Book 1 free ne [2025]️*

Masoya littafin KURURUWAR SHAIƊAN kuzo ku shaƙata da sabon update ɗin da zai saka ku a cikin duniyar da ba zaku so ku fita ba.
Cike da ruɗani soyayya da asiri na san babu mai so ya rasa wannan kada ku bari a baku labari… Ku ka sance cikin masu karantawa na farko

Danna nan ku shiga link
HYPERLINK "https://chat.whatsapp.com/FuTlAsg7uedBXoMKiash4h?mode=ems_copy_thttps://whatsapp.com/channel/0029Vb6QGRg6WaKl7oWkqq30" https://chat.whatsapp.com/FuTlAsg7uedBXoMKiash4h?mode=ems_copy_thttps://whatsapp.com/channel/0029Vb6QGRg6WaKl7oWkqq30

Story & writing
By

ZULFA M. TUKUR

بسم الله الرحمن الرحيم

اللهم صل على محمد….

Page 26

Washegari da safe, rana ta fito da haske mai kyau. Afsana ta farka da fara’a duk da mafarkin da ta yi jiya. Ta shirya cikin uniform mai tsafta, ta ɗauki jakar makaranta.

Mamie ta zo ta duba ta, ta taɓa goshinta:
“Kin kwana lafiya yau, ƴata?”

Afsana ta murmusa:
“Na kwana lafiya Mamie. Zan yi ƙoƙari a makaranta yau.”

Papa ya fito da motarsa ya kira ta:
“Afsana, mu tafi makaranta.”

Ta rungume Mamie kafin ta fita, sai ta bi bayan papa da fara’a.

A cikin mota, papa ya kalle ta ta madubi ya ce cikin kulawa:
“Ƴata, kar ki ji tsoro da komai. Allah yana tare da mu. Ki dage da karatu, ki yi addu’a a duk lokacin da kika samu dama.”

Afsana ta gyada kai, ta ce da murmushi:
“Insha Allah papa.”

Sun isa makaranta, Afsana ta shiga aji da murmushi. Abokanta sun zagaye ta suna ta tambaya da wasanni.
Malamin ajinsu ya kira ta ya ce:
“Afsana, kin yi babban ci gaba a gwajin baya. Ina alfahari da ke.”

Elena, wacce ta ke kallo ta da kishin ta, ta taɓe baki ta juya:
“Hmm… ai ba wai ta iya bane. Wani abu ne kawai yake ba ta sa’a.”

Afsana ta ji maganarta, amma ta yi shiru. Ta tuna da maganar papa: “Allah yana tare da mu.”

Bangaren Sarauniya Alisha

A cikin masarautar Egypt, Sarauniya Alisha ta tsaya a gaban madubi tana kallon kanta, tana murmushi cikin mugunta.
“Lokaci ya yi. Ban yarda wani bawa ya yi kuskure ba. Ni da kaina zan shiga cikin gidan su muneka, a matsayin Sarauniya NUFUREYA. Zan kawo musu kyaututtuka, ciki har da ruwan tsafi da zai maye gurbin wannan ruwan. Ba za su taɓa gane ba.”

Yelena ta duƙa ƙasa cikin girmamawa ta ce:
“Uwar masarauta, wannan dabara taki zata karya su daga ciki. Zasu sha abin da suka ɗauka da tsarki, alhali kuwa guba ce mai tafiyar da jini.”

Alisha ta yi tsaki tana gyara rawanin kanta:
“Na fi kowa sanin dabarun. Wannan ita ce hanyar da zan ruguza iyalansu kafin su fahimci ko daɗi ko zafi.”

Ɓangaren mamei

Da yamma, lokacin da papa ya dawo da Afsana daga makaranta suka zauna a parlour, Mamie tana musu sannu da zuwa.
Chapter 27 · 0% Book details