Sashe 29
Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki · about 8 min read
A cikin masarauta, Sarauniya Alisha ta sake kallo ta madubi. Tana murmushi tana cewa:
“Hakan yake, jaririya. Kullum da safe za ki farka da sabon alamu. Wannan ne farkon mallakar ruhinki.”
Yelena ta ce:
“Wannan ba wasa ba ne. Idan aka bar hakan, za ta iya zama cikin ikonmu gaba ɗaya.”
Alisha ta ɗaga hannu cikin ƙasaita:
“Shi ne dai burina. Sai dai in gani wane ne zai iya tsallake wannan sihiri nawa.”
To masu karatu kuyi hakuri da wannan ba yawa yau bana jin daɗin jikina. Book 1 free ya kusa ƙarewa masoya littafin KURURUWAR SHAIƊAN duk wacce ta ke son shiga paid group dan mallakar complete ɗin littafin zata turo kuɗin shiga ₦400 ne zaku tura kuɗin ta wannan number 7062701555 OPAY ZULFAU TUKUR MUHAMMAD shaidar biya a wannan number 07062701555 duk wacce ta shirya ta min magana please idan kin san baki shirya ba karki min magana
Duk wacce ta ke son document ɗin littafin KURURUWAR SHAIƊAN daga farko ta min magana ta wannan number 07062701555
Please share like comment masoyana
KURURUWAR SHAIƊAN
*✨HAZIƘAN MARUBUTA✨*
*Book 1 free ne [2025]️*
Masoya littafin KURURUWAR SHAIƊAN kuzo ku shaƙata da sabon update ɗin da zai saka ku a cikin duniyar da ba zaku so ku fita ba.
Cike da ruɗani soyayya da asiri na san babu mai so ya rasa wannan kada ku bari a baku labari… Ku ka sance cikin masu karantawa na farko
Danna nan ku shiga link
HYPERLINK "https://chat.whatsapp.com/FuTlAsg7uedBXoMKiash4h?mode=ems_copy_thttps://whatsapp.com/channel/0029Vb6QGRg6WaKl7oWkqq30" https://chat.whatsapp.com/FuTlAsg7uedBXoMKiash4h?mode=ems_copy_thttps://whatsapp.com/channel/0029Vb6QGRg6WaKl7oWkqq30
Story & writing
By
ZULFA M. TUKUR
بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل على محمد….
Page 27&28
Afsana ta zauna a gefen gado tana riƙe da kanta. Idanunta suna haskawa da wani irin duhu da sai a lokaci-lokaci yake ɓacewa. Hannunta na rawa, zuciyarta kuma tana bugawa kamar ana ƙwanƙwasa ganga.
Mamie ta riƙe ta tana kuka:
“Allah Ya tsare ki, ƴata. Na shiga uku, Papa! Wannan ba al’ada ba ce.”
Papa ya kasa magana, zuciyarsa ta haɗe da zafi. Sai ya tuna da kwalbar ruwan zam-zam da suke sha kullum. Ya ɗauko kwalbar daga ɗakin.
Ya zauna ƙasa yana riƙe da kwalbar, ya bawa afsana.
E|Afsana ta fara girgiza kai da sauri, ta ce cikin kuka:
“Papa… ina jin kamar akwai wani abu yana magana da ni. Wani muryar mace… tana cewa ‘Na riga na mallake ki’.”
Kafin su kai ga wani abu, Afsana ta fasa ihu mai ƙarfi, tagogin ɗakin suka yi ƙara kamar za su tarwatse. Tana jefa hannunta a sama, fitila ta fashe.
Papa ya rungume ta da ƙarfi yana karanta:
“A’uzu billahi minash-shaiɗanir-rajim…”
Amma Afsana ta ƙara ihu, idanunta suka koma jajaye, tana kallon Papa cikin wani hali dabam.
Sarauniya Alisha kuwa, tana cikin parlour masarauta tana kallon su ta madubi, tana dariya mai sanyi.
“Eh, haka nake so. Ruwan tsafi ya fara aiki. Ƙaramar Afsana zata zama hanyar lalata rayuwar su, yanzu muneka zata fara sanin *KO WACECE SARAUNIYA ALISHA*.”
Bangaren Afsana
Wata irin iska ta ɗauko ta cikin ɗakin, labulen ɗaki ya fara girgiza da sauti mai ban razana. Idanun Afsana sun canza launi suka yi duhu, tamkar gawayi mai kyalli.
Sai kawai ta riƙi kujerar Mamei ta yi sama da ita kamar ba ta da nauyi, ta fatattaka ƙasa sai ta tarwatse gunduwa-gunduwa.
Papa ya yi saurin miƙewa ya rungume Mamie yana furta addu’a, amma kafin ya rufe baki Afsana ta tsalle da sauri ta ɗauko wata bulala da ba a san daga inda ta fito ba. Bulalar tana haske kamar ƙarfe mai zafi, tana fitar da wuta idan ta motsa.
Ta fara jibgarsu da ita ba tare da jin tausayin su ba. Kowane duka da bulalar ya kama jikinsu sai su ji tamkar ana ƙonawa da wuta.
“Ahhh! Afsanaaa!!!” Mamie ta fasa ihu, ta yi ƙoƙarin rike hannunta amma bulalar ta buga kanta da ƙarfin da ta jawo ta a kasa, tana birgima da azaba.
Papa ya ƙoƙarta ya tsaya a gaban Afsana, hawaye na tsiyaya daga idanunsa, ya ce cikin murya mai rauni:
“Ya Allah, wannan ba ‘yar tawa bace! Ka dawo min da ƴata!”
Amma Afsana ta fuskance shi, tana dariya mai razana wacce ta cika dakin da wani irin sauti da babu daɗi.
“Papa… yanzu ni ce jikinka, ni ce ƙarfin iko. Ba za ku taɓa kuɓuta ba”.
Bulalar da ke hannun Afsana ta sake yin ƙara kamar ana ƙonawa da wuta. Duk lokacin da ta daga ta, ana jin karar ƙararrawar tsafi a cikin ɗakin.
Papa ya tsaya a gabanta da ƙarfin hali duk da tsananin tsoro da azabar da suka sha. Ya rufe Mamie a bayansa, yana furta addu’a cikin hanzari.
“Bismillahir Rahmanir Rahim… Hasbiyallahu la ilaha illa Huwa, alaihi tawakkaltu wa Huwa Rabbul-‘Arshil-‘Azim!”
Sai kawai bulalar ta tsaya a tsaye tana rawa a hannun Afsana, kamar wani abu yana ƙoƙarin ƙwace iko daga gare ta. Idanunta suka yi duhu sosai, amma a hankali wani irin haske ya fara walƙiya a cikin su – tamkar Afsana na ƙoƙarin dawowa.
Mamie cikin kuka ta rungume Papa ta ce:
“Ka ji, Papa… kamar tana dawowa… Allah Ka taimake mu!”
Amma kafin su ƙara furta wani abu, sai wata murya ta sake cika ɗakin daga nesa:
“Kar ku yi tsammani za ku tsere min. Afsana ta zama tasa, ku kuma za ku zama gurbatattu saboda ita!”
Sai kawai tagogin suka karye gaba ɗaya, iska mai ƙarfi ta shigo. Fitilu suka yi ƙarar fashewa.
Afsana ta fadi ƙasa tana jijjiga kamar ana ƙoƙarin tsage jikinta gida biyu. Wani lokaci idanunta na komawa launin ja, wani lokaci kuma su dawo farare suna zubar da hawaye.
Papa ya durƙusa kusa da ita yana roƙon Allah:
“Ya Allah, idan wannan jarabawa ce, Ka ba mu ikon jimrewa. Kada Ka bari shaidan ya mallake ta!”
Afsana ta daka ihu mai tsananin ƙarfi, hannunta ya kama wuyan Papa da ƙarfin da ba ta da shi a al’ada. Mamie ta rarrafa cikin tsananin kuka tana kiran:
“Afsanaaa! Ki tuna ni ce Mamie ɗinki, ni ce nake rike da ke tun kina jaririya!”
Wani irin ƙara ta sake, sannan hannunta ya saki Papa. Sai ta rufe kunnuwanta tana kuka da murya mai sanyi, tamkar tana magana da kanta.
Amma nan take, wata murya mai sanyi da duhu ta fito daga bakinta ba tare da ta buɗe idanu ba:
“Mun riga mun kafa gindinmu a jikinki, Afsana. Ba za mu tafi ba…”
Sai ƙasa ta girgiza ƙasa da ƙasa, labule suka ɗauki wuta da kansu. Papa da Mamie suka rike juna suna kiran sunan Allah cikin tsoro.
Wutar da ta kama labulen ta bazu da sauri cikin ɗakin, tana cinye kowane kusurwa. Kaya da gado suka fara hargitsewa da ƙura, hayaki ya lullube su gaba ɗaya.
Papa ya yi ƙoƙarin rufe Afsana da jikinsa, amma wutar ta ci gaba da ƙone musu kaya da fatar jikinsu. Mamie ta tsaya tsakar ɗaki tana ihu tana kiran taimako:
“Wayyo Allah! Wayyo jama’a! Ku taimaka mana, ɗakinmu ya kama da wuta!”
Amma babu wanda ya shigo. Babu wanda ya ji muryar su, kamar duk wani abu a waje ya kulle kunne da idanu.
Afsana kuwa tana kwance a ƙasa tana dariya cikin muryar da ba ta kanta ba:
“Na gaya muku ba za ku tsira ba… wannan wuta ce ta tsafin da zata kone ku gaba ɗaya, ku zama ƙura!”
Dakin ya cika da hayaki mai baki, su Papa suka kasa ganin juna da kyau. Sai ihu kawai ake ji, ihu mai cike da tsoro da azaba.
Papa ya rungume Mamie yana fadin:
“Allah ka tsare mu! Allah ka tsare Afsana!”
Amma wutar ta mamaye su gaba ɗaya. Ganuwar ɗakin ta fara karyewa, tagogi suka narke tamkar su gilashin zafi.
Ihun su Papa da Mamie suka ci gaba da tashi, amma babu wanda ya kawo ɗauke. Su kaɗai ne cikin wannan masifa, yayin da wutar ta cigaba da cinye su kamar ƙonannun ganyaye.
Afsana ta taso tsaye tsakiya cikin harshen wutar, jikinta gaba ɗaya yana haske kamar wuta ta zama tufafinta. Idanunta na walƙiya ja, tana kallon su da murmushin da ya cika tsoro:
“Ku gama da kuka… domin wannan shi ne ƙarshenku.”
Shiru ya rufe komai.
Hayaki mai baki ya lullube ɗakin, harshen wuta na ci gaba da tsalle-tsalle, amma babu ƙarar Papa, babu ƙarar Mamie. Babu motsin komai.
Afsana kuwa ta tsaya cak a tsakiya, jikinta yana karkarwa kamar mai suma. Idanunta sun rufe gaba ɗaya, hannayenta sun rataye gefe.
Sai shiru… shiru mai nauyi, tamkar an tsayar da lokaci.
Duk abin da ya faru, ya ɓace cikin duhu.
A Nigeria kuwa
Lokacin da Ashraf ya shiga ɗakin zysha ya ga halin da ta ke ciki, ba ɓata lokaci ya kira doctor ɗin gida. Ba’a wani daɗi ba sai ga doctor ya shigo ɗakin da sallama, suka amsa masa ya fara duba jikin zysha ya ce tana bukatar ayi mata allora, cikin firgice zysha ta ɗago kanta dan-danan idonta suka fara tara kwallah, tana girgiza kanta alamar bata su
Zysha ta durƙusa a gefen gadon, ta rungume Aunty Asabe da ƙarfi kamar wacce za a raba da duniya. Hawaye suna tsiyaya daga idanuwanta, jikinta yana karkarwa.
“Don Allah Aunty… kar ku bari ya yi min allura. Bana so! Wallahi bana so… kar ku yarda,” ta faɗa tana rawar murya.
Ashraf ya durƙusa a gefenta, ya kama hannunta yana shafa bayanta cikin lallashi:
“Zysha… ki saurare ni, wannan ba don cutar da ke bane. Don lafiyar ki ne. Ki yarda, zan tsaya a nan har sai an gama. Ki daina kuka, ki yi haƙuri.”
Amma Zysha ta girgiza kai da ƙarfi, ta ƙara riƙe Aunty Asabe sosai kamar zata shige jikinta gaba ɗaya. “Aunty, ki ce musu su bar ni! Bana soooo! Na rantse bana so!”
Duk suka tsaya kallon ta da tausaya, musamman ganin yadda take ƙemadagewa kamar ƙaramar yarinya.
Aunty Asabe ta lumshe idanu tana shafa kanta da tausayawa, amma a ƙarshe ta ce cikin murya mai ƙarfi:
“Zysha, ki daina. Wannan dole ne. Ba zan bari ki cutu ba saboda tsoron ki.”
Da ƙarfi ta riƙe hannunta, tana tsayar da ita yayin da doctor ɗin ya miƙo allura. Zysha ta ƙwalla ihu tana ƙoƙarin fizgewa, amma Aunty Asabe ta ƙara matse ta.
“Yi sauri kafin ta ƙara rikicewa,” Aunty ta furta.