← Book details Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki Local reading mode
READING PART 8 OF 31

Sashe 8

Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki · about 8 min read

Ƙyalƙyalewa da dariya hamdiya ta yi”. Kema ke nam ai ne in faɗa miki daidai da shafin mai sai-dai ayimin wanka kawai na cire”.

Shewa rabi ta yi”. Ashe dai ba ƴar, iskar bace na ɗauka shi kansa wankan sai am-miki”.

Suka saki ƙyalƙyalewa da dariya
Haka dai suka cigaba da tsara mafarkin su cikin fatan mafarkin nasu ya kasance gaski.

Hmmm babbar magana kuna da aiki babba ma a gabanku.

**Chef Rehman**

Batari da yace abin cin da Hajiya ƙarama ta zuba masa ba ya miƙe tsayi zai bar dining area.

“Ah babana ina kuma zaka je naga ko abin cikin baka ci ba?”.

Batari da ya ɗagu ya kalleta ba ya cigaba da tafiya.

“Na ƙushi”.
Ya faɗa yana cigaba da ta fiyarsa.

Girgiza kai Hajia ƙarama ta yi tace”. Ikon Allah Mai hali dai baya fasa halinsa lallai Mahek kana ƙukarin zama da shi”.

Ƙyalƙyalewa da dariya Mahek ya yi yace”. Wllh kowa ai kaɗan ma ki ka gani indai wannan boos ɗin ne.

Chef Rehman direct part ɗin Ammi ya nufa sallama ya yi iya samun laɓɓansa an yi sa’a kowa Ammin bacci ta ke.

Ƙarasawa ya yi bakin bed ɗin ya kama hannunta guda daya yana ɗan murza shi ta rida lumshi kyawawan Eyes ɗin nasa ya saki buɗe su sun yi jajir kamar jan gauta.

Motsi idon nata ya fara kana ta buɗe su gaba daya kai tsaye sai cikin na chef Rehman.

Zaro idon ta yi alamar wanda ya kaɗu kaɗa mata kansa ya yi alamar da gaske she ɗin ne.

Duk da haka dai har yanzu zuciyarta ta kasa aminta da she ɗin ne.

Zafa-fan hawaye ne suka zubu mata a kunce ya yi saurin guge mata hawayin da suka zubu mata.

A hankali kamar wanda aka ɗaurewa harshe yace”. No please Ammi ki daina bana sun ganin wannan yay maganar yana share mata ƙwallar da ta saki zuba mata.

Girgiza kanta ta yi hawayi na cigaba da zubu mata Allah ne kaɗai yasan farin-cikin da take ji amma bata nuna hakan a fuskarta ba.

Sai da ya tabbatar da ta daina hawayin kana ya miƙe tsayi ya ɗakko mata ruwa a ƴar ƙaramar firizar da ke ɗakin ya kafa mata a baki kaɗan ta sha ta kyauda kanta.

Karku manta na faɗa muku kanta ne kawai take iya motsawa a jikinta.

Ya ɗade sosai a part ɗin Ammi duk da shi ba ma’abucin surutu bani amma ya ɗan ƙuƙarta ya saka Ammin nashi farin-ciki ganin ana kirayi-kirayin sallar magrib ya saka shi me ƙewa ya ɗan sumbaci gushinta ya mata sai da safi ya fice daga shashin.

Sai da ya wuce part ɗinsa ya ɗauro alwala
Kai tsaye masallacin da ke estate ɗin su ya huce achan ya haɗu da su Mahek sai da ya yi sallar isha sannan ya dawo.

Bai zarce ko ina ba sai bathroom dan yin wanka kosan 40mnt ya ɗauka a bathroom kana ya fito ɗauri da bathrobe da wani karamin towel yana gugi kansa ya tsaya gaban mirror cikin nutsiwa yake shafa oil ya gyara sumar kanshi sai ƙyalli take cikin ƙan-ƙanin lkc ya gama shiri cikin tsadaddin kayan barcinsa farare ne tas riga da wando ya ɗakko laptop ɗinsa da ke bedside drawers ya koma saman bed ɗinsa ya fara ayin dannata.

A haka dai Mahek ya zo ya samesa ya zauna gyefinsa.

“Boos agogo sarkin aiki ai sai ka aji aikin ga abinci na kawo maka ina ji ɗazu kacewa Hajia ƙarama ka ƙushi alhanin nasan komai baka ci ba.

“Uhhm kwai ya ce ya cigaba da aikin sa.

“Boos ka ajjiye aikin mana ka ci abincin”.

Ɗan ƙaramin tsaki chef Rehman ya yi yace”. To tunda harka kawo ai saika tafi ka bani guri na cigaba da aikina”.

“Amma dai wllh ɗan rainin wayo ne boos daga abin arziki sai ya koma na tsiya”.

Mahek yay maganar yana ɗan hararar shi.

“Ai ba sai ka koreni ba zan tafi tunda kai ba’a taɓa ye maka gwaninta”.

Ɗage kafadarsa ya yi tare da nuna masa ƙofa alamar ya tafi ɗin.

Girgiza kansa Mahek ya yi ba tare da ya damu da maganar chef Rehman dan shi abin dariya maa ya basa dan indan da sabu ai ya saba da halin ɗan-uwannsa koma amininsa ogansa.

Lallai kam duli sai hakuri su yallaɓai mahek.

Mahek yana futa ya ture laptop ɗin gyefe ya jawo laidar da ya shigo da ita ajiyewa ya meƙi tsayi ya nufi kitchen ya ɗafa coffee ya juyi a gilas cup ya dawo bedroom.

Buɗe laidar nan ya yi shawarma kaɗai ya ci sai black coffee ɗin da ya haɗa bayan ya kammala ya tattara ledar ya kai kitchen ya dawo ya ɗauki laptop ya cigaba da aikin nasa sai da ya kai kusan 12:00 kana ya ajjiye laptop ɗin saman bedside drawers.

Kwanta wa ya yi ya rage haskin ɗakin ya ja blanket bai daɗe bacci yay awon gaba da shi.

Kiran asuban farko a kunnin shi ya yunƙura ya meƙi ya shiga bathroom ya ɗaura alwala ya chanza kayan baccin da jikinsa zuwa blue ɗin jallabiya ya ya sauko upstairs.

A babban parlour gidan ya haɗu da Mahek Ashraf da kuma abdul buɗa bakinsa ya yi a hankali yace”. Ina haeedar ko shi bazai tafi masallacin bane?.

“Big bro yana bedroom nasa”.

Abdul ya yi maganar.

“Ok jeka kira shi so kar ku ɓata mana lkc”.

Jiki na rawa Abdul ya amsa da”to ya nufi bedroom ɗin haeedar kwance sai sharar barcinsa ya ke ko takalmin da ya saka bai samu damar ciresu ba da gani kasan bai shiriyawa baccin ba ya ɗauke shi.

Cikin mugunta Abdul ya saka hannunsa ya danne masa hanci a firgice haeedar ya meƙi zauni idonsa ya yi jajir dan bacci.

“Dallah ka tashi mutafi masallaci ga yaya Rehman chan a parlour ka dai san baya sun jira ko?”.

Haeedar yana ƙun-ƙuni ya shige bathroom ya ɗauro alwala suka tafi masallaci.

Zysha

Kiran sallar asuba ne ya tashi Zysha daga barci tay wanka ta ɗauro alwala bayan ta idar da Sallah tayi azkar da karatun Alqur’ani kamar dai yan da ta saba sai kusan 6:20 ta meƙi ta zura uniform ɗinta ta nufi kitchen tana gaf da zata shiga suka haɗu da aunty asabe.

“Yawwa Zysha dama yanzu nake shrin zuwa bedroom ɗin nake sai kuma gashi kin fitu”.

“Eh ina kwana aunty asabe?”.

“Lafiya qalau Zysha muƙarasa kitchen ɗin ga breakfast ɗin yallaɓai Rehman ki kai masa part ɗinsa dan shi baya fitowa dining area”.

A zaburi Zysha ta ɗago ta zubawa aunty asabe ido.

“Lafiya dai Zysha?”.

Aunty asabe ta maganar cikin tuhuma da sauri ta girgiza kanta zuciyarta na harbawa.

“Bab.. babu komai aunty asabe bari na ɗakko breakfast ɗin saina kai masa”.

Zysha tai maganar cikin rawar murya ta yi sauri wof ta shige kitchen ta ɗakko breakfast ɗin ta nufi part ɗinsa.

A parlour suka haɗu da chef Rehman ya fito daga geme rom razanannin ihu! Zysha ta fasa ta rida sakin madaidaicin tray ɗin da ke hannunta.

Gaba daya breakfast ɗin ya tarwatsi.

A mugun fusace ya dago rinannun idonsa ya daka mata tsawar da taje numfashinta na neman ɗaukewa.

“K! Wace irin banza ce ko bakya gani kin makance ne?....

Please share & like

KURURUWAR SHAIƊAN

*Book 1 free ne [2025]️*

HYPERLINK "https://whatsapp.com/channel/0029Vb6QGRg6WaKl7oWkqq30https://chat.whatsapp.com/GMguONdwRnw5KiIfxpKquJ" https://whatsapp.com/channel/0029Vb6QGRg6WaKl7oWkqq30https://chat.whatsapp.com/GMguONdwRnw5KiIfxpKquJ

Story & writing
By

*ZULFA M TUKUR

(Zufee baby shalelen momma)

Ƙarƙashin jagurancin ƙungiyar….

بسم الله الرحمن الرحيم

اللهم صل على محمد....

Page 12

Chef Rehman ya bita da kallon da ya fi ƙarfin tsawa.

Idanusa suka ƙara yin jajir, sai, azuciyarsa ya fara cewa.

“Amma me yasa yarinyar-nan take rawar jiki haka idan ta ganni? Tsoro ne ko wani abu daban?”

A zahiri kuwa ya buɗa murya cikin ɗace:

“Idan baki iya aiki ba ki faɗa musu su cireki kafin ki tarwa tsa mana gida!”.

Jikin Zysha na ɓari ta durƙusa tana ɗaukar fir-fesun abincin da ya zube hannunta na rawa kukan da take dannewa ne ya suɓuce mata.

“Yi….yi hakuri don Allah ranka ya daɗe wllhi ba da gan-gan na zubar ba….”

Shiru ne ya biyo baya Rehman ya janyi idonsa daga kanta amma zuciyarsa ta wani irin doka.

Ba sabu bani a wajensa ya tsawaita amma irin wannan yanayin na Zysha ya bashi mamaki lkc ɗaya ya ji tsanarta ta ɗarsu azuciyarsa dan shi ya tsani mutane matsorata

A hankali ya jiyo ya kalli Zysha wacce ta ke shari karyayun tray da kuma abinci ya ɗan tauna laɓɓansa cikin tsawa.

“Ki gyara wajen nan sosai bana sun ƙazanta da sakarci”.

Amma kafin tace wani abu, kiran wayarsa sai ya katse su bai jira amsarta ba ya shige bedroom ya barta durƙushi a gurin tana tattara ɓangarorin tray ɗin da ya far-fashe zuciyarta na ɗaci da al-amarin wllh gaba ɗaya ta tsani shigowa part ɗin yallaɓai Rehman.

*A ɓangaren aunty asabe*

Tana jiran dawowar Zysha dan gaba daya ta fara damuwa da halin da Zysha take ciki kwana biyu.

*Ɓangaren Zysha*

Bayan tabar parlour zuciyar Zysha ta kasa kwanciya tana tafiya cikin dugun corridor ɗin gidan, hannunta na kyarma ta shiga kitchen.

Aunty asabe ta tsaya tana kallonta.

“Zysha lafiya? Me ya faru? Naga kamar kin firgita”.

Zysha ta girgiza kai da sauri.

Aunty asabe ta tsaya tana kallonta.
“Zysha ki gayamin gaskiya wani abu ne ya faru tsakaninki da yallaɓai Rehman?”

Zysha ta yi shiru, ta kasa cewa komai sai hawaye kawai suka cika idonta. Ta san idan ta buɗe baki zata iya faɗar abin da ke ranta na tsoro, amma zuciyarta ta ce”idan na yi magana ko ni zasu ce ban da hankali”.

Don haka kwai tayi saurin girgiza kanta ta share hawayen da ya silalo a fuskarta.
“A’a babu komai aunty asabe…. Wallahi babu komai”.

Aunty asabe ba dan ta gamsu da maganarta ba kawai dai bata sun takurata bata dan haka kwai ta ce”to shikinam ki je ɗaki ki huta”.

Da sauri Zysha ta bar kitchen ɗin.

ƁANGAREN CHEF REHMAN
Chapter 8 · 0% Book details