Sashe 17
Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki · about 8 min read
Rehman ya ɗaga kansa a hankali, idanunsa suka ƙanƙance. Ya ce cikin murya mai sanyi amma cike da nauyi:
“ita ce Amour… ita ce Granny na, ita ce kashin bayan zuciyata. Na faɗa maka ha ne dan karka sakimin wata tambar. Ku ceci ta… wallahi ku ceci ta! Idan har ta gaba ɗaya saina ɗaure dan ginka
Doctor ya yi shiru, yana mamakin chef Rehman da tsoro duk ya cika masa zuciya ya ce cikin taushin murya:
“za mu ceci ta, sai dai kuma idan lokacin ta ya yi to wannan bamu da yanda za mu yi
Rehman ya ja wani dogon numfashi, ya dafe bango, zuciyarsa ta rikice.
Duk wacce ta ke buƙatar document ɗin littafin KURURUWAR SHAIƊAN daga farko ta min magana ta wannan number 07062701555
KURURUWAR SHAIƊAN
*✨HAZIƘAN MARUBUTA✨*
*Book 1 free ne [2025]️*
Masoya littafin KURURUWAR SHAIƊAN kuzo ku shaƙata da sabon update ɗin da zai saka ku a cikin duniyar da ba zaku so ku fita ba.
Cike da ruɗani soyayya da asiri na san babu mai so ya rasa wannan kada ku bari a baku labari… Ku ka sance cikin masu karantawa na farko
Danna nan ku shiga link
HYPERLINK "https://chat.whatsapp.com/FuTlAsg7uedBXoMKiash4h?mode=ems_copy_thttps://whatsapp.com/channel/0029Vb6QGRg6WaKl7oWkqq30" https://chat.whatsapp.com/FuTlAsg7uedBXoMKiash4h?mode=ems_copy_thttps://whatsapp.com/channel/0029Vb6QGRg6WaKl7oWkqq30
Story & writing
By
ZULFA M. TUKUR
بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل على محمد….
Page 19
Bayan an kwantar da granny (AMOUR) likitoci suna ta zagaye suna duba numfashinta. Rehman ya shige ɗakin jinya da sauri, zuciyarsa na tafarfasa. Ya zauna gefenta, hannunsa na riƙe da nata idanunsa jaa suke har yanzu, alamar tashin hankali ya rinjaye shi.
Ya ɗaga kansa da ɓacin rai:
“ku faɗa min gaskiya, Doctor. Shin tana da rai ne? Ko kuwa…?”
Dr. Suleiman ya nisa kaɗan ya ce:
“Eh tana da rai. Amma zuciyarta tana fama da wani nauyi da ba kowane mutum zai iya ɗauka ba, ba zan iya tabbatar da tsawon lokacin da zata yi ba”.
Rehman ya kalli Dr. Suleiman da ido jajir kamar zai yi magana sai kuma ya kawar kansa gefe.
A kan gado granny ta kwanta, numfashinta na fita da ƙyar, oxygen a hancinta. Ta buɗe idanunta ƙalilan da ƙyar, ta ga Rehman a gefenta, hannunsa rike da nata sosai.
Cikin murya mai rauni, ta ce da ƙarfin hali:
“Reh…man… Zuciyarka kada ta cika da fushi. Ka tuna… idan zuciyarka ta sauya, kai kaɗai za ka iya tarwatsa komai. Ka… Ka tsare kanka daga ɓacin rai…”
“Granny…”ya furta cikin muryarsa mai sanyi.“ki yi haƙuri… Tsawon shekaru na kasa tsayawa na tsare ku ke da Ammi. Amma wallahi yanzu banzan bari komai ya sake shiga tsakanin mu ba. Na yi al’ƙawarin hakan. Ki dawo ki zauna tare da mu kamar yadda kika saba a baya”.
Ya yi maganar cikin wani mugun yanayi. Cikin wani hali granny ta fara magana:
“Rehman nima zan su hakan na kasance tare da ku har ƙarshen rayuwata, Amma sai dai nasan hakan bazai yiyu ba saboda….”
Maganarta ta tsaya saboda ƙarancin numfashi. Hannunta ya faɗi daga nashi a hankali, idanunta suka rufe.
Rehman ya riƙe yana girgiza shi cikin tashin hankali:
“Granny! Kada ki bar ni, don Allah! Granny!!!”
Ya juya a fusace ya dakawa wasu nurses da ke tsaye ya daka musu wata gigitacciyar tsawa.
Nurses suka ruga suka fara aikin gaggawa, da sauri ya yi waje ya tsaya a ƙofar ɗakin, idanunsa suka yi jaa, zuciyarsa kamar ta fashe.
*Ɓangaren familyn SALAHUDDEEN RANO*
Cikin gidan anyi masa wani irin ado da furen turare da kayan marmari. Ashraf kuwa shine kan gaba gurin ganin an ƙawata gidan, saboda shirye-shiyen walimar bazata da ya shiryawa Ammi, saboda murnar samun lafiyarta.
Zysha tana cikin kitchen tana taimakawa a shirye-shiryen, zuciyarta cike da farin ciki. Tunda ta shigo gidan, ta ji tana ƙwaunarta.
A falon, an jera kujeru da ballons masu ƙyalli, sai ƙamahi mai tsuma zuciya ya ke. Cikin ƙanƙanin lokaci su aunty asabe suka shirya lafiyayyun abinci kala-kala masu ƙayatarwa.
Ashraf ya shigo falon tare da Ammi ya rufe mata ido da hannunsa, ya saka kaya masu masifar kyau da murmushi a fuskarsa ya ɓuɗe mata fuska, Ammi na buɗe idonta taga wurin ya yi wani irin duhu.
“Surpriseeee!!!”
Ammi ta tsaya cak tana kallonsu da mamaki idanunta suka cicciko da hawaye na farin ciki.
Sai ta rungume Ashraf, shima ya rungume ta cikin annashuwa.
Wurin ya cika da ihun farin ciki, Ashraf ya buɗe wani ƙayataccin cake ya ɗebu wani a hannunsa yana dariya:
“Ammi wannan cake ɗin na musamman ne, aunty asabe da Zysha suka haɗa suka yi wa kitchen tsinke saboda su shirya miki”.
Ammi ta yi murmushi sosai tana share hawaye ta mayar da kallonta kan Zysha, Zysha ta yi murmushi tana gyara hijabinta. Sai kuwa Ashraf ya zubawa Ammi cream ɗin cake ɗin a goshi, falon ya kaure da tafi. Ammi ta ruga ta ɗauki cokali ta maida masa martani, su Abdul suka shiga ihu suna tafa hannu.
Bayan komai ya lafa Ammi ta zauna a kujera cike da nishaɗi tana kallon su Ashraf suna ta wasa da dariya, zuciyarta na cike da godiya ga Allah. Ta yi tunanin a zuciyarta ta ce:
“Allah ina godiya a gare ka da ka bani lafiya bayan tsawon shekarun da na ɗauka ina jinya.
Kuma wannan yarinyar, Zysha, kamar haske ce da Allah ya aiko cikin gidan nan”.
Ɓangaren Rehman da Granny
Rehman yana tsaye a bakin ƙofa, zuciyarsa na bugawa kamar ƙararrawa. Likitoci suna ta ƙoƙarin ceto Granny. Daga cikin kayan aikin da suke yi, yana iya jin ƙarar na’urar zuciya tana yin “beep… beep…” cikin rauni.
Sai wani ɗan likita ya fito ya dafa kafaɗarsa:
“Muna ƙoƙarin tsare rayuwarta, amma ba za mu iya ba tare da taimakon Allah ba. Ka yi addu’a sosai, dan saurayi.”
Rehman ya rufe idanunsa, idanunsa suka yi ja sosai, jikin sa ya fara girgiza saboda ɓacin rai. A zuciyarsa wani murya ta taso:
“Kar ka bari fushinka ya fito… ka bari su gane ƙarfin da kake ɗauke da shi… Ka ɗauki fansa akan duk wanda ya jawo mata wannan hali.”
Ya buɗe idanunsa da sauri, yana jin kamar zai yi magana Amma sai ya tuna da maganar Granny da ta furta a ƙarshe:
“Ka tsare kanka daga ɓacin rai, Rehman…”
Rehman ya dafe kansa, yana ƙoƙarin danne wannan wutar da ke ƙoƙarin tashi a jikinsa.
“Ba zan bari in zama abin da kuke so ba… ba yanzu… ba”
A dai-dai wannan lokacin, wata nurse ta fito ta ce da shi cikin gaggawa:
“Muna buƙatar jinin ka, domin jinin Granny ya ƙare. Shin kana shirye ka bayar yanzu?”
A hankali ya gyaɗa kansa ya bi bayan nurse aka gwada jininsa cikin Sa’a jinin yazo daidai ba ɓata lokaci suka ɗibi jininsa.
Da gaggawa aka fara saka mata jini, chef Rehman ya tsaya ya ɗura hannunsa a bango.
Sai wayarsa dake aljihu ta fara ture da ƙarfi. Sai ya ƙi ɗagawa saboda zuciyarsa ba a hayyacinta ta ke ba. Amma ganin kiran baya ƙarewa, sai ya fusata ya ɗaga cikin jin haushi:
“waye kai ne kuma ka ke damuna a wannan lokaci!”
Murya mai ciki da tsoro ta fito cikin wayar:
“Boos… Nine mahek. Ina ne ka tafi ne? Na je gidan amour… naga jini a ƙasa, kuma naga gat ɗin gidan a bude alamun wani ya fita da ita, amma banga kowa ba. Me ya faru ne?!”
Chef Rehman ya yi shiru idanunsa suka ƙara yin jaa, numfashinsa ya ɗauki nauyi. Ya ce da murya mai sanyi:
“me kake cewa, mahek? Ka je gidan granny? To me ya kai ka can?!”
Mahek ya buɗa baki muryarsa na rawa:
“na ji wani abu a zuciyata shi yasa na je gidan. Amma da na je kuma sai naga ba kowa ba jini alamun tashin hankali. Don Allah, boos ka faɗa min kada ka ɓuye min komai, ka faɗa min gaskiya. Ina amour ?!”
Chef Rehman ya rufe idonsa da ƙarfi, zuciyarsa ba daɗe ya yi tunanin kwai ba sai ya faɗa masa ba.
Chef Rehman ya daƙuna fuska kamar yana gabansa:
“mahek ka saurare ni da kyau! Kada ka sake zuwa gidan granny, yanzu ka bar gidan kafin wani abu ya same ka”.
Mahek ya yi shiru na ɗan wani daƙiƙu, kafin ya ce cikin rawar murya:
“amma boos… me yasa? Me ya faru da ita? Ka faɗa min gaskiya don Allah…”
Chef Rehman ya lumshi idanu, yana jin nauyin zuciya. Amma ya ƙi faɗa masa gaskiya ya ce cikin muryar tsawa:
“na ce kabar wurin! Wannan ba lokacin tambaya bane. Ka bar gidan yanzu, ka koma gida ka rufe gat, in akwai wani abu zan sanar da kai daga baya”.
Mahek cikin muryar fushi:
“boos… Kai kullum kana ɓuye min wasu abubuwa. Amma zanyi yadda ka ce… Zan bar gidan kamar yadda ka ce Allah ya kiyaye gaba”.
Ya katse wayar cikin ƙunar rai.
Chef Rehman ya dafe kansa da hannu biyu zuciyarsa na bugawa da ƙarfi, sai yaji ƙarar buɗe ƙofa a bayansa. Likitoci suka fito da gaggawa, ɗaya daga cikin su ya ce da shi:
“munyi iya ƙuƙarin mu, amma….” Maganarsa ce ta tsaya cak sakamakon shaƙar da chef Rehman ya kai masa yana huci kamar zaki idonsa ya yi jaa, sosai.
✨ Ɓangaren masarautar Egypt ✨
A tsakiyar daren nan, Afsana ta zabura daga bacci da wani ihu mai tsuma zuciya. Jikinta gaba ɗaya sanyi, gumi ya wanke goshinta, numfashinta na fita kamar wacce aka yi wa gudu.
Mamei ta tashi da firgici ta rungumeta, “Afsana! Afsana! Ki yi shiru, ni ce nan.”
Papa ya ruga ya ɗebo ruwan Zam-zam ya zauna a gefenta. Da muryar da take rawa kaɗan ya fara karantawa a hankali: Fātiha, Āyat al-Kursiyyu, Falaq da Nās, yana tofa mata shi uku-uku a cikin ruwan, ya mika mata.
Afsana ta sha a hankali. Da kyar ta iya furtawa cikin rawar murya:
“Papa… wata murya ta ce ni tawa ce uwar asirai… ta ce rabin jinina na su ne… ta ce in barta ta karɓi zuciyata zan zama sarauniya a duniyar su…”
Mamei ta matse hannunta, idonta ya cicciko da hawaye. “A’a, ke tamu ce. Babu mai rabani da ke.”
Papa ya share goshinta da tawul, ya kalli Mamei cikin natsuwa amma fargaba a ido: “Za mu yi kamar yadda Sheikh ya ce.”