Sashe 26
Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki · about 8 min read
Manisha kuwa tana tsaye hankali kwance, ta ɗan ɗora hannu bisa ƙugu, fuskar ta ɗaure ba tare da wata fargaba ba. Sai ta ce da sanyi, cikin izza:
“Hajia ki rike wuƙar da kyau, kada ki cutar da kanki kafin ki kuskure.”
Hajia Ramlat ta ƙara ihu, ta ɗaga wuƙar sama tana ƙuƙarin chakawa Manisha.
“Zan nuna miki ni ce Hajia Ramlat! Na rantse da Allah sai kin bar gidan nan da gawa ko da rai!”
Kafin ta kai ga Manisha, Abban Yasmeen ya yi tsalle da ƙarfi ya riƙe hannunta. Wuƙar ta kusa soke shi, ya ƙwace da ƙarfi har suka yi jujjuya kamar masu faɗa.
“Ramlat! Kina hauka ne? Wuƙa kike ɗauka akan kishin banza? Ki san me kike yi kuwa?! Ki zubar da mutuncinki a haka a gabana?”
Hajia Ramlat tana ihu tana ƙoƙarin kwace wuƙar:
“Ka barni na kashe ta! Wallahi idan ba ta bar gidan nan ba yau, sai na kashe ta!!”
Manisha ta tsaya gefe, fuskar ta ɗaure, ta ce cikin ɗan murmushi mai cike da izza:
“Hajia, idan kishi ya rikide ya zama hauka, sai ya zama bala’i. Amma ki sani, duk da wuƙar hannunki, ba za ki iya kore ni daga nan ba. Ko da na fita daga gidan nan, ba da fushinki zan fita ba, sai da ƙaddara ta rubuta hakan.”
Abban Yasmeen ya ƙwace wuƙar da ƙarfin tsiya, ya jefa ta gefe da ƙara. Sai ya kama hannun Hajia Ramlat, yana jijjigata da ƙarfi:
“Ramlat, ki dubi kanki! Wannan haukan kishin zai hallaka ki! Idan kika sake ɗaga hannu da wuƙa a cikin gidana, wallahi sai na ɗauki mataki da baki taɓa tsammani ba.”
Hajia Ramlat ta fashe da kuka, tana bubbuga ƙirji, tana fadin:
“ka ci amanata….”
To jama’a yau fa ake yinta, muhaɗu ranar Alhamis idan Allah ya kaimu hmmm kada ku bari abaku labari. Book 1 free ya kusa ƙarewa masoya littafin KURURUWAR SHAIƊAN duk wacce ta ke son shiga paid group dan mallakar complete ɗin littafin zata turo kuɗin shiga ₦400 ne zaku tura kuɗin ta wannan account number 7062701555 OPAY ZULFAU TUKUR MUHAMMAD shaidar biya a wannan number 07062701555 duk wacce ta shirya ta min magana please idan kin san baki shirya ba karki min magana.
Duk wacce ta ke son document ɗin littafin KURURUWAR SHAIƊAN daga farko ta min magana ta wannan number 07062701555
Please share like comment masoyana
KURURUWAR SHAIƊAN
*✨HAZIƘAN MARUBUTA✨*
*Book 1 free ne [2025]️*
Masoya littafin KURURUWAR SHAIƊAN kuzo ku shaƙata da sabon update ɗin da zai saka ku a cikin duniyar da ba zaku so ku fita ba.
Cike da ruɗani soyayya da asiri na san babu mai so ya rasa wannan kada ku bari a baku labari… Ku ka sance cikin masu karantawa na farko
Danna nan ku shiga link
HYPERLINK "https://chat.whatsapp.com/FuTlAsg7uedBXoMKiash4h?mode=ems_copy_thttps://whatsapp.com/channel/0029Vb6QGRg6WaKl7oWkqq30" https://chat.whatsapp.com/FuTlAsg7uedBXoMKiash4h?mode=ems_copy_thttps://whatsapp.com/channel/0029Vb6QGRg6WaKl7oWkqq30
Story & writing
By
ZULFA M. TUKUR
بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل على محمد….
Page 25
Hajia Ramlat ta ɗaga wuƙar sama cikin hauka, idonta jajaye kamar ta rasa hankali. Amma kafin ta kai ga Manisha, Abban Yasmeen ya yi saurin tsalle da ƙarfi ya ƙwace hannunta — wuƙar ta faɗo ƙasa da ƙarar soke. Hajia Ramlat kuwa, ganin an ɗauke mata abin da ta riƙe, ta yi tsalle sai kasan ta tsakure kamar wacce aka yi mata duka; ta faɗi zauni kamar yar buri, hannayenta na rungume kirji, fuskarta cikakke da ƙuncin rai da nadama.
Abban Yasmeen ya tsaya a gabanta ya ɗaga muryarsa cike da ɓacin rai, yana murmusawa da ƙoƙarin rike fushinsa: “Ramlat! Me kike yi haka? Ki kalli kanki! Wannan ba dabi’a bace — me ya sa za ki ɗauki wuƙa a cikin gidan nan? Ki daina haka! Ki zauna ki yi tunani! Ina so ki koyi zama da hankali ba da tashin hankali ba.”
Hajia Ramlat ta fashe da kuka, tana juyawa cikin kasala, tana zagayawa da kai kamar wacce ta rasa matsayin kanta. Abban Yasmeen ya ci gaba da faɗa mata amma a zuciyarsa akwai tausayi da mamaki.
A gefe, Manisha ta ɗaga hannunta ta ja ƙaramin tsaki — tana jin tsanar mummunar halin Hajia Ramlat — sai ta juya ta bar parlour ɗin a hankali. Tafiyarta cike da natsuwa amma fuskar ta bayyana takaici da tsanar wulaƙan cikin da aka nuna mata ya sa ta yi nisa kafin ta zauna a wani ɓangare na gidan.
Abban Yasmeen kuwa lokacin da ta fita, ya tsaya kallon Manisha daga inda take cirewa, idonsa na bin ta har sai ta ɓace. A fuskar sa ya bayyana mamaki, ƙarfin hali da a izza.
Bangaren Zysha
Da ƙyar ta iya ficewa daga ɗakin Chef Rehman, zuciyarta na tsalle-tsalle, jikinta yana kakkarwa kamar maraƙi. Ta riƙe bango tana tafiya a hankali har ta ƙarasa bedroom ɗinta.
Da ta faɗa kan gadon sai zazzaɓi ya kama, jikinta ya yi zafi fiye da kullum. Hannunta na rawa ta ja bargo ta lullube kanta, amma bugun zuciya da ƙarar muryar Chef Rehman a zuciyarta sun hana ta samun natsuwa.
Hawayen da ta dade tana riƙewa suka sulale suka gangaro a fuskarta. Ta dafe kanta tana faɗin cikin ƙanƙanuwar murya:
“Ya Allah… me yasa rayuwa ta take cike da tsoro da rudani haka?”
Idanunta suka lumshe, jikinta ya yi sanyi gaba ɗaya, zuciyarta tana neman yin tsaye-tsaye.
Bangaren Chef Rehman
Yana tsaye a bakin taga yana kallon sararin sama, hannunsa rike da gilashin ruwa. Fuskar sa cike da nutsuwa amma idanunsa sun nuna akwai abu mai nauyi a zuciyarsa.
Ya yi wani ɗan murmushi mara daɗi sannan ya furta da ƙasa-ƙasa:
“wannan ƴar aikin…”
Sai yaɗanyi tsaki ya juya ya fice daga ɗakin zuwa wani wuri da ba kowa.
Bangaren Asibiti (Ammi & Mahek)
Ammi ta jingina da gadonta, fuskar ta ba da ƙarfi sosai. Mahek ya riƙe hannunta yana ƙoƙarin kwantar mata da hankali:
“Ammi ki yi haƙuri, komai zai daidaita… kar ki manta Allah baya barin bayinsa haka kawai.”
Ammi ta kalle shi da idanunta masu cike da hawayen da ta riƙe, ta ce da ƙanƙanuwar murya:
“Mahek, akwai abubuwa da nake ji a zuciya.”
Mahek ya girgiza kansa cikin tausayawa:
“Ammi ki kwantar da hankalin ki insha Allahu komai zai wuce”.
Ammi ta share hawayenta zuciyarta sam babu daɗe.
Bangaren Sarauniya Alisha masarautar Egypt
A cikin fadarta mai cike da hasken fitilu da ƙanshin turaren oud, Sarauniya Alisha tana zaune a kujerarta ta zinariya. A gabanta akwai manyan dattawa da ministoci biyu, amma ta fi karkata kunnenta ga wata tsohuwar bokanya da ake kira Madame Yelena, wadda aka fi sani da muguwar tsafi wajen amfani da sihiri.
Alisha ta ce cikin muguwar murya:
“Na gaji da jiran wannan muneka. Na ce sai ta bar Japhet, amma ta ƙi. Idan ba ta rabu da shi ba, to ni zan raba su da kaina. Ban damu ko da yarinyar nan Afsana za ta sha wahala ba, burina kawai a karya zuciyarta.”
Madame Yelena ta murmusa tana kaɗa zobenta:
“Sarauniya, wannan lamari a hannuna yake. Zan haɗa wani tsafi da zai fara da Afsana, saboda ita ce ɗauri tsakanin muneka da Japhet. Idan ta fara fuskantar wahala, zuciyarsu za ta karye, su rabu da juna da kansu.”
Sarauniya Alisha ta gyara zaman ta, ta ce da ƙarfin hali:
“Na amince. Ki shirya wannan tsafin nan da nan. Zan ba ki duk abin da kike buƙata. Amma ina so wannan yarinya ta fara ganin abin tsoro a cikin mafarkinta har ta kasa kwanciyar hankali.”
Madame Yelena ta ɗaga kwanon tsafi mai ɗauke da ƙura da ganyayyaki, ta yi wasu surkulle cikin harshen da babu wanda ya fahimta. Wata iska mai duhu ta ratsa cikin dakin, fitilu suka yi walƙiya kamar ana son su mutu.
Alisha ta yi murmushi cikin mugunta:
“Zan ga yadda Afsana za ta jure wannan. Kuma idan iyayenta suka ce suna da Allah, to mu kuma muna da ƙarfarmu.”
Bangaren Afsana
Daren nan bayan ta kwanta, Afsana ta shiga cikin bacci mai nauyi. Amma kafin dogon lokaci, ta fara ganin mafarki mai ban tsoro.
A cikin mafarkin, ta tsinci kanta cikin daji mai duhu, iska tana hura ganyayyaki, ana jin ƙarar tsuntsaye masu ihu. Kamar daga nesa, ta ga wata mata mai dogon rigar baki wacce fuskarta take ɓoye da mayafi.
Matar ta yi mata magana cikin sauti mai sanyi amma mai firgitarwa:
“me yasa ƴata baki dawo gare ni ba, na faɗa miki iyayenki basa sunki.”
Afsana ta fara kakkarwa, ta ce da ƙarfin hali:
“Ni ba zan bar iyayena ba! Allah ne mai kare mu. Duk wanda ya yi niyyar cutar da mu, zai sha wuya.”
Mummunar Halitta
Nan take mayafin matar ya ɗaga, fuskarta ta bayyana da wani idanuwa biyu ja kamar wuta. Afsana ta firgita ta fara gudu, amma ƙasa ta fara nutsewa a ƙafafunta. Ta ɗaga hannayenta sama tana kuka:
“Mamie! Papa! Ku taimaka min!”
Sai ta farka cikin ihu, jikinta duk gumi, zuciyarta na bugawa da sauri.
Mamie ta shigo da sauri ta rungume ta, papa ya biyo bayanta da damuwa.
“Afsana, me ya same ki?” suka tambaya a tare.
Afsana tana huci ta fashe da kuka, mamei ta fara lallashinta tana tausayin rayuwar su.
Afsana ta kwanta a cinyar Mamie tana kuka tana bada labarin mafarkinta, zuciyar papa ta cika da tashin hankali. Amma duk da haka ya tuna da abu mai muhimmanci da ba ya mantawa.
Ya nufi ƙaramin bedroom nasa ya ɗauko ruwan Zam-Zam, wanda Sheikh Abdurrahman, ya bashi.
Papa ya shigo ya kalli Mamie da Afsana, zuciyarsa cike da imani da ƙarfin hali.
“Yau na fahimci dalilin da yasa Sheikh ya bani wannan ruwa. Wannan ita ce jarabawarmu.”
Ya ɗebo ɗan ruwa cikin kofin ƙarfe, ya mika wa Mamie da Afsana su sha. Daga nan ya ɗebo ya shafa a goshinsu yana fadin:
“Allah ka kare mu daga sharrin duk wani mai nufin sharri. Ka tsare mana Afsana.”
Afsana ta rufe idanuwanta, zuciyarta ta samu natsuwa. Mamie kuma ta fashe da kuka cikin farin ciki:
“Japhet, ka tuna da wannan ruwa ne? Lallai Allah baya barin bayinsa.”
A wannan dare gidan ya samu nutsuwa bayan kowa ya sha daga ruwan Zam-Zam. Amma a gefe guda, Sarauniya Alisha da bokanyarta suna cigaba da shirya sabbin makirci, suna mamakin dalilin da yasa tsafinsu bai yi nasara a kan Afsana ba.
Bangaren Bokanya Yelena