Sashe 24
Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki · about 8 min read
Afsana ta kwanta a bayan motar tana rike da ƙaramin teddy bear ɗinta, idanunta suna rufewa a hankali. Mamei ta saki lallausan murmushi. Papa kuwa yana tukin mota cikin natsuwa, zuciyarsa na ta godewa Allah da ya mayar musu farin ciki bayan dogon damuwa.
Da suka isa gida, ba a ɓata lokaci ba, kowannensu ya yi wanka ya kwanta. Afsana ta yi bacci cikin nutsuwa, murmushi a fuskarta kamar tana mafarkin farin ciki.
Washegari
Da safe, karar agogo ya tashe ta. Mamei ta zo ta ɗago blanket:
“Afsana, tashi ki shirya, yau makaranta ce.”
Afsana ta tashi tana goge idonta da hannayenta:
“Mamei, ban gama bacci ba fa…”
Mamei ta yi dariya ta ce:
“Idan ba ki tashi ba, sai ki makara.”
Da sauri Afsana ta miƙe, ta je ta yi brush, ta watsa ruwa ta saka uniform ɗinta mai tsabta. Mamei ta shirya mata break-fast, sannan Papa ya fito yana rike da makullin mota.
“Zo mu tafi, Afsana.”
Ta ɗauki jakar makaranta da teddy bear ɗinta tana gudu zuwa ga Papa.
Bayan sun shiga mota, aka fara tafiya. Afsana ta zauna a baya tana kallon titi, zuciyarta cike da nishaɗi.
Da suka iso makaranta, yara da yawa suna shigowa suna dariya da wasa. Afsana ta sauka ta ruga cikin makaranta da murmushi, tana tafiya cikin sahun dalibai.
Da Afsana ta shiga makaranta ranar, kowa na kallonta da sabuwar girmamawa. Dalibai na ta yi mata taya murna, wasu ma suna kiran sunanta cikin farin ciki.
Amma a gefe guda, Elena ta na nan tsaye haushi kamar zai kashe ta.
Malamin makaranta ya kira Afsana zuwa ofis:
“Afsana, ki zo ɗauki takardar sakamakon gasar. Wannan zai shiga tarihi na makarantar mu.”
Bangaren Mamie
A gida kuwa, Mamie ta na zaune tana tunanin barazanar da Sarauniya Alisha ta yi mata. Kwana biyu kenan ba ta iya bacci da kyau ba. Ta ji zuciyarta tana ce mata akwai wani abu mai girma da zai faru.
Sai kawai ta ji kiran waya. Ta ɗaga cikin rawar murya.
“Hello…”
Muryar Sarauniya Alisha ta fito daga ɗayan ɓangaren:
“Na gaya miki ko? Idan baki rabu da Japheth ba, zan sa rayuwar ki da ta ‘yarki ta zama tamkar dabba. Ki jira kawai.”
Nigeria
A asibiti, Ammi tana zaune kan gadon jinya, Mahek na gefenta yana rik’e da hannunta. Chef Rehman ya tsaya kusa da taga, hannunsa ɗauke da takardar sakamako, fuskar sa cike da miskilanci. Bai ce uffan ba, sai dai idanunsa suna nuna akwai damuwa.
Mahek ya yi ƙoƙarin murmushi yana cewa da Ammi:
“Ki kwantar da hankalinki… komai zai wuce da yardar Allah.”
Ammi ta share hawayen da ke neman zuba mata, tana jin zuciyarta na cike da tambayoyi. Amma tana tsoron ta sake matsa wa da tambaya.
Chef Rehman ya juyo daga wajen taga, ya ajiye….kan tebur cikin natsuwa. Ya ce da sanyi:
“Abinda ya kamata ku sani kawai shi ne… akwai abu da ba za a iya ɓoyewa ba har abada.”
Ya ɗauki phone ɗinsa ya bar ɗakin asibitin ba tare da ƙarin magana ba.
Bangaren Hajia babba
Bayan fitar ta ɗakin Ammi bataga wata alama ba, sai ta koma part nata. Bata zauna ba, kai tsaye ta nufi ɗakin sirrinta.
A can ta ɗauki wayarta ta kira wata lamba da ta daɗe tana tsaye a sirri.
Bayan ƙarar wayar ta ɗauki lokaci, sai aka daga. Murya mai sanyi ta fito daga cikin lasifika:
“Na jima ina jira wannan kiran.”
Hajia Babba ta ce:
“Ina son jin dalilin fitar Ammi daga gida tare da Mahek da wannan Chef Rehman. Kina da bayanin?”
Sai murya ta amsa, amma fuskar ba ta bayyana ba — ana jin kamar mace ce a sanye da fararen kaya tana zaune a ɗaki mai ɗauke da turaren ƙanshi.
“Komai zan fayyace miki Hajia… amma ki shirya zuciyarki, domin abinda zan gaya miki ba ƙaramin girgiza ki zai yi ba.”
Hajia Babba ta matse wayar a kunnenta, idonta ya rufe da damuwa.
Muryar matar ta ci gaba:
“Abin da zan gaya miki zai buƙaci ki yi haƙuri, kuma ki shirya zuciyarki sosai…”
Sai ta ɗan yi shiru, kamar tana nazari.
“Zan zo da kaina, na fuskanci ki a ido-na-ido. Domin idan na faɗa miki ta waya, wataƙila ba za ki gaskata ba.”
Hajia Babba ta lumshe idanu, zuciyarta na bugawa da sauri.
Sai kawai aka kashe wayar.
Duk wadda ke son document ɗin littafin KURURUWAR SHAIƊAN daga farko ta magana ta wannan number 07062701555
Please share like comment masoyana
KURURUWAR SHAIƊAN
*✨HAZIƘAN MARUBUTA✨*
*Book 1 free ne [2025]️*
Masoya littafin KURURUWAR SHAIƊAN kuzo ku shaƙata da sabon update ɗin da zai saka ku a cikin duniyar da ba zaku so ku fita ba.
Cike da ruɗani soyayya da asiri na san babu mai so ya rasa wannan kada ku bari a baku labari… Ku ka sance cikin masu karantawa na farko
Danna nan ku shiga link
HYPERLINK "https://chat.whatsapp.com/FuTlAsg7uedBXoMKiash4h?mode=ems_copy_thttps://whatsapp.com/channel/0029Vb6QGRg6WaKl7oWkqq30" https://chat.whatsapp.com/FuTlAsg7uedBXoMKiash4h?mode=ems_copy_thttps://whatsapp.com/channel/0029Vb6QGRg6WaKl7oWkqq30
Story & writing
By
ZULFA M. TUKUR
بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل على محمد….
Page 24
Hajia Babba ta zauna da matar da ta zo mata. Matar ta cire mayafin da ke rufe fuska — kwatsam! Idanun Hajia Babba suka faɗa cikin tsananin mamaki.
“Ke ce?!” ta furta da tsananin razana.
Matar ta yi murmushi mai ɗauke da sanyi:
“Eh ni ce…”
Hajia Babba ta zuba idanu cikin tsananin razana, zuciyarta ta yi wani irin dokawa da bata taɓa ji ba.
Matar ta ɗan saki murmushi mai ɗauke da sanyi, ta zauna a gaban Hajia Babba tana kallonta kai tsaye.
“Na san kin yi mamaki… amma gaskiyar da na zo da ita yau, ita ce za ta girgiza rayuwarki gaba ɗaya.”
Hajia Babba ta daure fuska, ta haɗe hannaye a ƙirji, duk da tashin hankalin zuciyarta ta nuna ƙarfin hali.
Sai ta matsa kusa da kunnen Hajia Babba ta fara magana da ƙasa sosai.
Kamar daga nesa, muryarta ta ratsa kunnuwan Hajia Babba har cikin zuciyarta. Idanun Hajia Babba suka yi ja, jikinta ya ɗan karkarwa.
Bayan ta gama magana, sai ta jingina da kujera ta yi shiru.
Hajia Babba kuwa ta dafe ƙirji, numfashinta ya yi nauyi.
Bangaren Afsana
Daliban makaranta suka zagaye Afsana suna yi mata taya murna. Wasu suna ɗaga kwalaye, wasu kuma suna ta ɗaukar hotuna da ita. Farin ciki ya lullube harabar makarantar gaba ɗaya.
Afsana tana murmushi cikin jin kunya, zuciyarta cike da godiya ga Allah. Sabiyya ta riƙe hannunta tana faɗin:
“Afsana, yau makarantar mu ta samu tarihi saboda ke. Kin cancanci wannan girmamawa.
Bangaren Chef Rehman
Bayan ya fita daga asibitin, Chef Rehman ya kama hanya kai tsaye zuwa gida. Fuskar sa cike da natsuwa, amma a zuciya akwai wani abu mai nauyi da yake ɓoye.
Da ya shiga bedroom, ya ɗaure towel a kugu, ya nufi bathroom domin yin wanka.
Amma kafin ya shige, sai ya lura bathroom ɗin ba komai, an ji ƙarar ruwa yana gudana, Ya ɗan ɗaga gira.
A hankali ya buɗe ƙofar bathroom ɗin — nan take idanunsa suka faɗa kan Zysha da take tsaye cikin ruwa tana wanka.
Zysha ta kalli ƙofar a ruɗe, idonta ya faɗa akan Chef Rehman da towel ɗin sa. Ta rikice, ta shiga firgice kamar wacce aka zuba ruwa mai zafi:
“Ya… ya…yallaɓai!!”
Ta rufe jikinta da hannayenta cikin tsananin kunya da tsoro.
Chef Rehman kuwa ya tsaya cak, idanunsa suka kaɗa da wani irin yanayi mai rikitarwa.
Zysha ta zube a bango tana kakkarwa, hannunta na neman rufe jikinta gaba ɗaya. Ruwa na zuba a kanta, zuciyarta na dukan uku-uku.
Chef Rehman ya ja numfashi a hankali, ya ɗan ɗauke idanunsa gefe yana ƙoƙarin kaucewa kallon ta.
Zysha ta lumshe ido kunya duk tabi ta addabeta, tana jin yadda zuciyarta ke tsalle kamar zata fito. Bata taɓa tsammanin za ta haɗu da shi a wannan yanayi ba.
Chef Rehman ya fito daga bathroom ɗin fuskarsa a ɗaure, towel ɗin jikinsa har yana matsewa saboda yadda ya daure tsukewar hannunsa, zuciyarsa na bugawa da wani irin abu da shi kansa bai iya fassara ba.
“Ƴar aikin nan…” ya furta a hankali, idanunsa na cike da ƙyama. “Ta iya raina ni har ta shigo bathroom ɗina? Wannan rainin da ba zan taɓa lamunta ba.”
Ya watsa towel ɗin ya ɗauko rigar barci mai sauƙi ya saka, sai ya ɗauki wayarsa ya jingina a kujera. Duk da ya ƙi yarda da shi, hoton yadda ya hangi yarinyar a cikin ru”an wanka bai bar kwakwalwarsa ba.
Cikin zuciyarsa ya yi ƙwafa da tsawa:
“Na tsane ki, har sunanki ban san shi ba. Amma zan tabbatar da cewa kin gane bambanci tsakanin mu. Zan nuna miki irin hukuncin da bai kamata ki taɓa mantawa da shi ba.”
A gefe guda kuwa, Zysha har yanzu tana cikin bathroom ɗin tana kuka, zuciyarta cike da fargaba. Tana ta maimaitawa a ranta:
“Me zai yi min? Ya Allah, na shiga uku…”
Ni ko na ce idan ba kauɗi ba kima miya kai ki.
Zysha ta fito daga bathroom ɗin jikinta duk a takure, tana bin bango kamar wata munafuka. Idanunta sun cika da tsoro, jikinta na rawa kamar za ta nutse cikin kasa.
“Ke!” muryar Chef Rehman ta daka mata tsawa mai firgitarwa, har sai da zuciyarta ta tsalle ta kusa zubewa a ƙasa.
Ta shiga jijjiga kai tana neman magana amma murya taƙi fitowa.
“tsaya daga nan ki fara tsallin kwado.
Zysha ta yi saurin tsallin kwado, jikinta na rawa kamar ta shiga cikin sanyi mai tsanani.
Shi kuma ya shige bathroom domin yin wanka.
Zysha ta fara gumi, hawaye da majina suna zubo mata duk da sanyin A.C mai ƙarfi da ke gudana a ɗakin.
Bayan ƴan mintuna, Chef Rehman ya fito daure da towel, jikinsa na ɗauke da wani irin sanyi mai ratsa zuciya. Bai ma kalleta ba balle ya damu da halin da take ciki. Kai tsaye ya shige dressing room.
Ba da jimawa ba ya fito cikin ƙananun kaya masu matuƙar kyau, fuskar sa a ɗaure. Ya ɗauki laptop ya zauna ya fara dannawa cikin sakainar kashi.
Can sai ya ɗago idanunsa masu tsananin haske, ya lura da ita a durƙushe a ƙasa, ta rigaya ta suma saboda tsoro da kuka.