← Book details Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki Local reading mode
READING PART 31 OF 31

Sashe 31

Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki · about 5 min read

Kalaman suka daki kunnuwan kowa tamkar saukar aradu. Gaba ɗayansu suka zaro idanu da tsananin razana. Falon ya cika da wani irin shiru mai nauyi na ɗan lokaci.

“Me kike faɗa, Zysha?!” Ashraf ya tambaya cikin rawar murya.

Amma kafin wani ya ƙara magana, Haeedar ya ruga gadan-gadan, zuciyarsa na harbawa kamar zai tsage ƙirjinsa. Ya kai hannunsa da nufin shaketa da fushi:

“Ke ce kika kashe Hajiya Babba?! Wallahi yau sai na…”

Sai kuwa kwatsam Zysha ta ɗago idanunta, idanun suka koma jaaa shuɗi mai firgitarwa kamar wuta. Jikinta ya fara karkarwa, yana saɓulewa da wani irin ƙara. Ƙashi da tsokarta na murɗewa.

Kafin idonsu ya rufe, jikinta ya fara rikidewa zuwa jibgegiyar macijiya mai launin baki da jan ɗigo, harshe na fita yana tsiyaya wani irin ruwa mai wari.

“Wayyo Allah na!!!” Haeedar ya ja baya da tsalle, jikinsa na kar-karwa kamar wanda ya kamu da ciwon sanyi. Ya nuna ta da yatsa yana rawar murya:

“Kuna ganin abin da nake gani kuwa?! Dama na faɗa muku… wannan ba mutum baceeee!!!”

Kafin ya kammala, sai Zysha ta yi wani irin nishi mai girgiza bango, tana juyawa da ƙarar tsinke-tsinke. Wannan kallo ya fi ƙarfin zuciya.

Haeedar ya juya gurin da gawar Hajiya babba ta ke, amma ba komai ya murza idonsa, yasa ki murzawa nam ma baiga komai ba.

A take gaba ɗayan su , Yasmeen, Hajiya Ƙarama, Aunty Asabe, Meena, Hamdiya, Rabi, Maryam — duk suka sume a wurin, falon ya rage mazan ne kawai, amma ko su numfashin su neman ɗauke yake.

A sama kuwa, Chef Rahman ya ɗan lumshe ido kamar wanda ke jiran wani abu da ya dade yana tsammani.

Kafin kowa ya motsa daga sume-sumen da suka yi, ƙwatsam sai aka ji ƙarar ƙafafu da ƙara a bakin ƙofa. Mutane uku suka shigo parlour ɗin da gaggawa, hannayensu na rawa, fuskar su cike da firgice. Da suka hango abin da ke gabansu, jikinsu ma ya fara kar-karwa, idanunsu na bin wurin tamkar zasu fito.

“Subhanallaaah… me ke faruwa anan?!” ɗaya daga cikinsu ya furta da rawar murya.

A wajen gidan kuwa masu gadi suna ta fama da ƴan jaridu da suka iso. Su na riƙe da kyamarori da microphones suna ƙoƙarin kutsawa cikin gidan. “Ku bari mu shigo! Ku bari mu shigo!” an kiramu anfaɗa mana, anyi kisan kai, suka faɗa suna tura juna

Al’amari ya rikice ta ko ina – babu sauƙi, babu tsari, babu nutsuwa. Gidan ya koma filin tashin hankali da kowa ke neman mafita.

A gidan Hajiya Ramlat…

Manisha tana zaune a garden tana lumshe ido saboda gajiya. Iskar da ta buso daga bayan kujerar ta ɗauke da wani irin sanyi mara daɗi. Ta ji jikinta ya yi sanyi, sai kwatsam ta ji ƙafarta ta zame ta faɗi ƙasa da mugun ƙara.

“Ahhh!!”

Ta yi saurin tashi tana shafar kanta, amma zuciyarta ta cika da wani irin tsoro. Kamar akwai wani abu da yake kiran ta daga cikin inuwa. Cikin rawar jiki ta juya ta nufi ƙofar gidan.

Amma kafin ta kai nesa, sai wata baƙar mota ta tsaya a gabanta da wani irin gadon-tsaye mai firgitarwa.

Tuni zuciyarta ta harba! Ta tsaya cak!

Kafin ta iya cewa uffan, mutane biyu cikin bakaken kaya suka fito da sauri, fuskokinsu a rufe da masks. Wata irin ƙarfi suka yi amfani da shi suka kama ta.

Manisha ta yi ƙoƙarin fasa ihu:

“Ku taimaka…!”

Sai dai kafin ta kammala kalmar, an rufe mata baki da kyalle. Wani daga cikinsu ya daga ta kamar jaririya, suka tura ta cikin motar da mugun ƙarfi.

Motar ta tashi da gudu mai ban razana, tana barin gidan Hajiya Ramlat cikin hayaniya da ƙura.

To fa masu karatu yau ake yinta….

ALHAMDULILLAH masu karatu Anan na kawo ƙarshen littafin KURURUWAR SHAIƊAN book 1 sai mun hadu a book 2

SHIN DA GASKE ZYSHA CE TA KASHE HAJIYA BABBA ⁉️ LALLAI AKWAI LAUJE CIKIN NADI WAYI KUMA YA KIRA ƳAN JARIDU ⁉️ SANNAN KUMA WAYE SUKA ƊAUKI MANISHA DA BAK’AR MOTA⁉️ SANNAN KUMA WAYE YA ƊAUKI GAWAR HAJIYA BABBA ⁉️ SHIN DA GASKE MA TA MUTU ⁉️SHIN DA GASKE ZYSHA MUTUM CE KO ALJANA ⁉️ SHIN WAI MA INA LABARIN UMMA (SUHANA) SANNAN KUMA SUWAYE SUKA SHIGO AWANNAN HALIN DA AKE CIKI ⁉️ SANNAN KUMA GA YASMEEN DA BURINTA NA SUN MALLAKAR CHEF REHMAN YANZU YA ZATAYI BAYAN WACCE TA KE ƊAURE MATA GINDI AN KASHE TA ⁉️ TO WAI MA ME NENE ALAƘARTA DA HAJIYA BABBA⁉️SANNAN KUMA GEFE ƊAYA GA HALIN DA AFSANA TA TSINCI KANTA NA SHIGA TARKON SARAUNIYA ALISHA SHIN ZASU KUƁUTA DAGA SHARRIN SARAUNIYA ALISHA ⁉️ YA KUMA RAYUWAR SU MAMEI PAPA ZATA KASANCE⁉️ ZASU RAYU KO ZASU MUTU ACIKIN WANNAN WUTAR KAMAR YADDA SARAUNIYA ALISHA TA SHIRYA⁉️ SANNAN KUMA WACCE MAMEI ⁉️ HMMM LALLAI AKWAI ƘURA DUK ZAKU SAMU WA’YANNAN AMSHU-SHIN ACIKIN BOOK 2 DAMA WASU TAMBAYOYIN DA SUKA SHIGE MUKU KAI DUMIN SHIGA PAID GROUP DAN MALLAKAR COMPLETE ƊIN LITTAFIN KURURUWAR SHAIƊAN ₦400 NE KACAL KISHA KARATUN KI KI MORE CIKIN KWANCIYAR HANKALI ZAKI TURA KUƊIN SHIGA TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 7062701555 OPAY ZULFAU TUKUR MUHAMMAD TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER 07062701555 IDAN KIN SHIRYA KIMIN MAGANA PLEASE IDAN KIN SAN BAKI SHIRYA BA KAR KARKIMIN MAGANA YAWWA

LALLAI IDAN BAKI KARANTA WANNAN BA AMBARKI A BAYA DAN KUWA AKWAI CHAKWA-KIYA AKACE BA’AYIBA YANZU AKE WASA FARIN GIRKI KUMUJE ZUWA YANZU AINIHIN WASAN ZAI FARA
Chapter 31 · 0% Book details