Sashe 28
Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki · about 8 min read
Sai ga Sarauniya alisha ta shigo cikin ƙasaita, da rawanin zinariya a kanta, fuskar ta lullube da murmushi. Duk suka miƙe da girmamawa, domin a idonsu ita ce Sarauniya Nufureya wacce suka sani da nuna ƙauna da tausayi gare su. Basu taɓa zargin komai ba, don kuwa Sarauniya Nufureya ce kaɗai take a tare da su da kulawa.
Papa ya yi murmushi ya ce:
“Lallai yau mun samu girmamawa. Sarauniya Nufureya da kanta ta kawo mana ziyara!”
Mamie kuma ta ce cikin murna:
“Bismillah ranki ya daɗe, yau ba zaki fita nan ba sai na kawo miki girki mai ɗanɗano da abin sha masu daɗi.”
Nan take ta wuce ɗaki, ta kawo mata daddadan girki da abubuwan marmari.
Sarauniya Alisha ta zauna cikin annashuwa tana murmushi, idonta na haske da mugunta a ɓoye. Da suka kawo girkin sai ta ɗauko wani ƙaramin kwalba daga aljihu, ta zuba a cikin abincin dukan su basu lura ba.
Cikin murmushin mugunta ta ce;
“Yau rana ta musamman ce,” ta faɗa cikin taushin murya. “Ina so mu zauna tare mu ci abinci, mu yi dariya, mu ji daɗi.”
Papa ya ce cikin farinciki:
“Gaskiya wannan abin alfahari ne. Ba mu taɓa samun irin wannan rana ba.”
Afsana ta ce tana tsalle:
“Yauwa! Yau rana ce ta farin ciki!”
Suka zauna gaba ɗaya suka ci abincin cikin farin ciki. Bayan wani lokaci suka ji bacci mai nauyi na shirin ɗaukar su, Amma kafin su ankara, kowa ya fara jin wani irin kasala, idanu suka rufe.
Ƙaramin murmushi ya bayyana a fuskar Sarauniya Alisha wacce ta yi nasara.
“Eh, haka nake so,” ta faɗa a hankali.
Da kowa ya faɗi bacci ya ɗauke shi, sai ta miƙe ta nufi dakin mamei inda ta ke tunanin zata samu wannan ruwan, cikin sa’a kuwa idonta ya sauka inda kwalbar ruwan zam-zam take.
Wani irin dariya ta fashe da shi, sai da ɗakin ya girgiza. Ta ɗaga kwalban ta yi dariya mai sanyi, ta ajiye ruwan tsafi a maimakon ruwan su na zam-zam.
“Daga yau babu tsarkinsu a cikinsu. Abin da zai gudana daga nan, ni ce na tsara shi.”
Nigeria
Ɓangaren Zysha Washegari
Da safe,Zysha ta tashi daga bacci amma jikinta ya fi jiya rauni. Idanunta sun kumbura saboda kuka, jikinta kuma har yanzu yana rawa da zazzaɓi.
Tana zaune kan gado tana ƙoƙarin tashi zuwa bathroom, amma ƙafafunta suka kasa ɗaukar ta. Ta jingina da bango tana numfashi da kyar.
A wannan lokacin ƙarar ƙofar ɗakin ta buga kunnuwanta. Kafin ta iya cewa komai, ƙofar ta buɗe — aunty asabe ta shigo ɗakin.
Idonta ya sauka kan Zysha da sauri ta ƙarasu har gurin da take.
“Me yake damunki ne?” ta faɗa cikin muryar mai sanyi da tausayi.
Zysha ta yi ƙoƙarin murmushi don ta ɓoye halinta, ta ce cikin rauni:
“Ba komai… kawai ciwon kai ne.”
Aunty asabe ta ɗan tsaya tana kallonta, sannan ta ce:
“zysha kamar wani abu yana damun ki?”
Kafin Zysha ta yi magana ƙarar wayar aunty asabe ta ratsa kunnuwan su, aunty asabe ta ɗaga wayar ta ce:
“yallaɓai Ashraf, wannan abokiyar taka ba ta da lafiya sosai. Yanzu da na zo kawo mata kayar, amma sai naga bata cikin ƙushin Lafiya.”
Da ya ji maganar aunty asabe, zuciyarsa ta buga da ƙarfi. Ya ɗora hannu a goshi yana jin wani irin ɗaci da ba zai iya bayyana ba.
Ashraf ya miƙe da sauri ya bar ofis ɗin, Zuciyarsa na bugawa, ya nemi da ta bata wayar su yi magana.
Aunty asabe ta bata wayar,
Zysha ta dafa ƙirjinta da hannunta mai rawa, zuciyarta na ta bugawa. Ta karɓi wayar daga hannun Aunty Asabe da ƙyar, ta ɗora a kunnenta.
Muryar Ashraf ta cika da tashin hankali da damuwa:
“Zysha…Aunty Asabe ta faɗa min baƙya jin dadi? Me ke damunki ne? Ki faɗa min don Allah.”
Zysha ta yi ƙoƙarin yin murmushi, amma muryarta ta fito da rauni kamar mai shirin fashewa da kuka:
“Ba komai yallaɓai Ashraf… zan warke. Kar ka damu.”
Ashraf ya ɗaga murya cikin damuwa:
“Kar ki yi min haka! Ki bar ɓoye gaskiya, kin san bana jure ganin kina cikin raɗaɗi. Ina zuwa yanzu-yanzu… ki jira ni!”
Kafin ta iya cewa komai, wayar ta katse. Hannunta ya saki wayar ta faɗi kan gado, idanunta suka cicciko da hawaye.
Aunty Asabe ta zauna kusa da ita tana shafa bayanta:
“Ki kwantar da hankalinki, komai zai yi kyau.”
Zysha ta yi shiru, hawaye na gangarowa. Ta kasa amsawa.
Bangaren Ashraf
A cikin mota, zuciyar Ashraf kamar ta fasa kirji. Hannunsa na rawar juyawa a kan sitiyari, ya dinga sauke numfashi mai nauyi.
“Zysha ba lafiya… kuma tace ‘ba komai’…ya furta cikin zuciya, idonsa na cika da hawayen da ya ƙi zuba.
Da ya iso gida, bai tsaya a ko’ina ba, kai tsaye ya nufi part ɗin Zysha.
Bangaren Masarautar Egypt
Sai dare suka fara farkawa ɗaya bayan ɗaya. Papa ya miƙe da jinkirin da bai fahimta ba, ya dafa kansa yana kallon Mamie da Afsana.
“Subhanallah… wai me ya same mu ne?” ya furta da mamaki.
Mamie ta riƙe kanta itama, tana kallon Afsana wacce ta rarrafo kusa da ita:
“Nima ban gane komai ba. Na tuna muna zaune tare da Sarauniya Nufureya muna cin abinci… daga nan sai kawai bacci ya ɗauke mu.”
Afsana ta runtse ido tana ƙoƙarin tunawa. Amma duk yadda ta yi, hoton abin da ya faru ya ɓace daga kwakwalwarta. Ta ce cikin ruɗani:
“Amma ban tuna da komai sosai ba… kamar mafarki.”
Papa ya jinjina kai yana kallon su gaba ɗaya:
“Wannan abin ba daidai ba ne. Amma ko da me ya faru, dole mu yi addu’a. Allah shi kaɗai yasan gaskiyar abin da ya jefa mu cikin wannan yanayi.”
Sun tashi gaba ɗaya suka yi alwala, suka tsaya suka yi sallar dare da addu’o’i. Amma ba wanda ya lura cewa a cikin ɗakin, kwalbar ruwan zam-zam ta canja — yanzu ruwan tsafi ne da Sarauniya Alisha ta bari a maimakon asalin ruwan.
A gefe kuwa, a cikin masarauta, Sarauniya Alisha ta tsaya a gaban tagar ɗakinta tana kallon sama, murmushi na bayyana a fuskarta. Yelena ta shigo da girmamawa ta durƙusa.
“Uwar masarauta, duk abin da kika tsara ya fara aiki. Sun farka ba tare da sun tuna komai ba.”
Sarauniya Alisha ta yi dariya mai cike da mugunta, ta ɗaga kwalbar ruwan zam-zam ɗin asali wacce ta kwashe:
“Da wannan a hannuna, sun rasa tsarkinsu. Komai daga yanzu, ni ce zan tsara makomarsu. Zasu sha wahala ba tare da sun san daga inda take fitowa ba.”
Ta ɗaga rawaninta sama cikin izza:
“Lokaci ya yi da muneka zata san ni ba wai ita kadai ce ba — ni ce Sarauniya Alisha!”
Muryarta ta daki bango ta haɗu da daren da ya lullube masarauta, har ƙasa ta girgiza da ƙarfin maganganunta.
Ta zauna kan gadon sarauta tana riƙe da kwalbar asalin ruwan zam-zam da ta kwaso daga gidan Papa. Idonta yana walƙiya da annurin mugunta.
“Wannan ruwa… shi ne sirrin ƙarfin su. Yanzu kuwa na mallake shi! Hahaha!”
Yelena ta durƙusa a gabanta tana sauraro cikin biyayya.
“Uwar masarauta, menene mataki na gaba?”
Alisha ta miƙe, rigar sarauta ta biyo bayanta tana walƙiya da zinariya. Ta taka zuwa gaban wata madubi babba da aka ƙera da duwatsu masu daraja. Ta ɗora hannunta a jikin madubin, nan take madubin ya fara haskawa, yana nuna hoton gidan Papa.
Ta yi murmushi mai sanyi:
“Za su ci gaba da rayuwa ba tare da sun tuna abin da ya faru ba. Amma ruwan tsafi da suka fara sha shi zai rikide a jikin su — zai dusashe soyayya daga zuciyoyinsu, zai rikita hankalinsu, har su fara fada da juna.”
Yelena ta ɗaga kai cikin mamaki:
“Amma uwar masarauta, ba zai yiwu su gane da wuri ba?”
Sarauniya Alisha ta yi dariya taɗiɗi, kamar macijiya mai wasa da ganima:
“Ba zasu gane ba, ko kin manta ke kika ce tasirin ruwan yana shiga ne a hankali, kamar guba mai salo. Zasu fara da mantuwa, daga nan rikici, daga nan kuma lalacewa. Ni kuma zan zauna ina kallon su suna rushewa da hannunsu.”
Ta ɗaga hannunta sama tana rera wasu kalmomin tsafi. Nan take kwalbar ruwan zam-zam ɗin da ta mallaka ta fara walƙiya da haske mai ƙarfi, ta cika ɗakin da wani irin ƙamshi na ban tsoro.
“Da wannan ruwa, zan shanye karfin su, in mallaki duniyar su. Kuma duk wanda ya tsaya a gabana… zai rushe kamar ƙura!”
A wannan lokacin iska mai sanyi ta shigo fadar, fitilun suka fara walƙiya.
Washe gari
Da asuba, kiran sallah ya ratsa ko’ina cikin masarautar. Mamie ta shigo ɗakin Afsana da nufin ta tashe ta domin makaranta.
“Afsana, ƴata, ki tashi.”
Ta taɓa kafadarta. Amma da Afsana ta buɗe idonta, sai Mamie ta zaro ido. Idanun Afsana sun ɗauki wani irin duhu na baƙi kamar ƙwalla ta taru a cikinsu. Nan take kuma sun dawo yadda aka saba.
Mamie ta ja da baya cikin firgici.
“Afsana… kina lafiya kuwa?”
Afsana ta miƙe da ɗan wahala, jikinta yana rawa. Ta riƙe kansa:
“Mamie, ban san me yake damuna ba. Ina jin jikina yana da nauyi, kuma zuciyata tana bugu kamar zan faɗi.”
Ta kalli hannayenta, sai ta ga wani ƙaramin ɗan ja a jiki kamar alamomin hatsi na duhu. Ta goge da sauri, amma sai ya ɓace kamar bai taɓa kasancewa ba.
“Mamie, kin gani kuwa?”
Mamie ta kasa magana, kawai ta rungume ta cikin tsoro, zuciyarta na bugawa da sauri.
“Allah Ya tsare ki, ƴata. Allah Ka tsare mana Afsana.”
Papa ya shigo cikin ɗakin da sauri, ya tambaye su cikin damuwa:
“Me ke faruwa?”
Mamie ta nuna masa Afsana:
“Tana jin jikinta ya sauya. Kuma idanunta sun… sun yi wani abu ba na al’ada.”
Papa ya tsaya cak, ya tuna da ruwan da suka sha da daddare. Ya duba kwalbar da ta rage a gefe, zuciyarsa ta shiga bugawa.
“Akwai wani abu a nan…” ya furta a hankali, idonsa ya cika da damuwa.
Afsana kuwa ta tsaya tana kallon su, hawaye na taruwa a idonta:
“Papa, me yake faruwa da ni? Me yasa nake jin abubuwan da ba kowa yake gani ba?”