Sashe 19
Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki · about 8 min read
Ammi ta zauna tana kallon ’ya’yanta da farin ciki, zuciyarta na cike da godiya ga Allah. Ta dubi Ashraf ta ce cikin muryar da ta nuna ƙauna:
“Ashraf, kai da gaske ka bani mamaki yau. Ban taɓa zato ka shirya min irin wannan walima ba.”
Ashraf ya sosa kai yana murmushi:
“Ammi, ai ke ce komai a wurinmu. Babu wani abu da zan iya yi da zai daidaita girman ƙaunar ki gare mu. Wannan ƙaramin abu ne kawai.”
Sai Abdul ya tashi yana dariya ya ce:
“Ammi, ki ga yadda Ashraf ya kashe kudi yau saboda ke. Wallahi ya yiwa kitchen tsinke saboda cake ɗin kawai!”
Kowa ya fashe da dariya. Zysha ta duƙar da kai tana murmushi, zuciyarta cike da wani natsuwa da ta dade bata ji ba.
A lokacin, aunty Asabe ta kawo wani tray ɗin abinci mai ƙamshi, ta ce:
“Ammi ki ɗan ci abinci, kar ki tsaya da dariya kawai.”
Ammi ta ɗauki cokali, ta ɗan ɗiba, sannan ta dubi Zysha ta ce da murmushi:
“Ke kuma, yarinya, na gode da taimakonki yau. Wallahi na ji daɗin kasancewarki tare da mu.”
Zysha ta ɗaga kai da ladabi ta ce:
“Ammi, ai wannan ƙanƙanin abu ne. Ina fata zan ci gaba da kasancewa kusa da ku.”
Ashraf ya dubeta da wani irin kallo na musamman, wanda ya sa zuciyarta ta buga da sauri. Ta kawar da idonta cikin kunya, tana wasa da mayafinta.
Sai Abdul ya lura da kallon da Ashraf ya yi mata, ya saki murmushi a hankali yana cewa a zuciyarsa:
“Hmm, akwai wani abu a nan…”
Bayan kowa ya ci abinci, suka zauna a falon suna ta hira da dariya. Ashraf ya jingina a kujera yana kallon Ammi da murmushi, zuciyarsa cike da godiya ga Allah da ya ba ta lafiya.
Ammi ta yi shiru na ɗan lokaci, tana kallon Zysha da kyau. Sannan ta ce cikin natsuwa:
“Zysha…”
Zysha ta ɗaga kai cikin ladabi:
“Naam, Ammi.”
Ammi ta dafa kirjinta ta ce:
“Allah ya sani, tun da na fara ganin ki, zuciyata ta amince da ke. Yau da na ga irin yadda kika taimaka wajen shirya min wannan walima, sai na ji kamar kina da alaƙa ta musamman da ni. Ina jin kamar na dade da saninki.”
Zysha ta runtse ido, hawaye ya cicciko a gefen idanunta. Ta yi murmushi tana girgiza kai.
Ammi ta matso kusa da ita ta rungume ta a jikinta. Tana share mata hawaye da hannunta, ta ce cikin muryar ƙauna:
“Idan har kina son haka, to daga yau ni zan ɗauke ki a matsayin ɗiyata. Ke ɗiyata ce, Zysha.”
Ashraf ya tsaya kallonsu, zuciyarsa ta buga da sauri. Abdul ya fashe da dariya ya ce:
“Wai, kai Ashraf! Ka ga yanzu kana da ’yar uwa kenan!”
Zysha ta yi dariya tana share hawayenta, amma idonta ya haɗu da na Ashraf na ɗan daƙiƙa. Sai ta yi murmushi, cikin kunya ta kawar da kanta.
Ammi ta yi addu’a tana cewa:
“Ya Allah, ka sa wannan yarinya ta zama albarka a cikin gidanmu, ka tsareta daga sharri da fitina.”
Sai kuma suka ci gaba da walima da nishadi har dare ya yi.
Washegari da safe gidan Ammi ya cika da nishadi. Ammi na zaune a falo tana shan shayi, Ashraf na gefenta yana karanta jarida, Abdul kuma ya shiga kitchen yana ta dariya da Zysha wacce take taimakawa girki.
Ammi ta juyo da murmushi tana kiran Zysha:
“Zysha, ki bar aikin nan ga su hamdiya zasu yi. Ke dai zo kusa da ni mu yi hira.”
Zysha ta goge hannunta cikin mayafi ta nufi wurin Ammi da ladabi. Ashraf ya ɗago idanunsa daga jarida ya kalleta a hankali, sannan ya kawar da kai yana danne murmushi.
Sai Yasmeen ta shigo falon cikin shigar alfarma, fuskarta cike da murmushi amma zuciyarta na cike da haushi. Ta ce:
“Ammi, ina kwana?”
Ammi ta dubeta da murmushi:
“Lafiya lau Yasmeen. Kin yi kyau sosai yau. Masha Allah.”
Yasmeen ta yi murmushi mai ƙarfin gaske sannan ta zauna kusa da Ammi. Sai kuma ta juyo ta kalli Zysha da wani irin kallo na harin zuciya, ta ce cikin salo da sunan da taji ana kiranta:
“Zysha, da alama kin saba da gidan nan da wuri sosai. Kina iya komai… har da girki.”
Zysha ta kalli ta da mamaki. Sai ta ce:
“Eh na ɗan iya ba duka ba, Kuma ina jin daɗin taimakawa Ammi.”
Yasmeen ta taɓe baki ta ce:
“To ai hakan yana da kyau. Allah ya saka da alheri. Amma ki tuna… wannan gida akwai iyakokinsa. Ba duk abin da kike gani za ki iya yi a cikinmu ba.”
Ashraf ya ɗago kai cikin ɗan ɓacin rai, amma kafin ya yi magana, Ammi ta katse shi da cewa:
“Haba Yasmeen, me yasa ki yi wannan magana? Ai Zysha kamar ’yar gidanmu ce yanzu.”
Zysha ta sunkuyar da kai tana jin wani irin sanyi a zuciyarta, amma a lokaci guda kuma tana jin tsoron kalaman Yasmeen.
Yasmeen ta yi murmushi na ƙarya ta ce:
“Ammi, ai ba komai bane. Na yi magana ne kawai saboda ina son ta san yadda gidanmu yake.”
Ammi ta kalle ta da ido mai tsauri:
“Yasmeen, ina roƙonki ki daina wani abu da zai ɓata wa kowa rai. Wannan gida ya kamata mu zauna lafiya.”
Yasmeen ta yi shiru, amma a zuciyarta tana cewa:
“Kin fara samun ƙarfin hali, Manisha. Amma wallahi ni da ke sai dai ɗaya ya zauna lafiya a wannan gidan.”
Sai ta yi murmushi tana ƙara ɓoye zuciyarta, ta miƙe ta bar falon.
Ashraf ya kalli Zysha ya ce da sanyi:
“Kada ki damu da maganarta. Ki yi kamar ba ki ji ba.”
Zysha ta ɗan yi murmushin yaƙe tana kallon ƙasa, ranta ciki da damuwa.
A ɗakin jinya kuwa, Chef Rehman yana ta kai-komo a tsakar ɗakin kamar wanda ya rasa nutsuwa. Idanunsa jajir, hannunsa na kakkarwa, zuciyarsa na bugawa kamar ana danna ƙararrawa.
Ya dinga duba agogon hannunsa, ya yi tsaye, ya zauna, sannan ya sake miƙewa. Har dare ya yi amour bata farfaɗu ba.
Likitan ya nisa yana mai kallon yadda idanun Rehman suka yi jaa na tashin hankali.
“Mun yi iya ƙoƙarinmu. Amma zuciyarta tana da rauni mai tsanani. Dole ne ta huta sosai kafin ta sake magana. Idan ta ci gaba da magana da yawa, zai iya zama haɗari.”
Chef Rehman ya riƙe kansa da hannu biyu yana ƙoƙarin danne wannan zafin da ke taso masa. Amma zuciyarsa ta kasa samun natsuwa.
Masarautar Egypt
Da suka dawo gida bayan yawo, Afsana ta kwanta kan cinyar Mamei tana shaƙar ƙamshin uwarta. Fuskarta cike da annuri, idanunta suna lumshewa cikin natsuwa.
Papa ya zauna kusa da su yana kallon su cikin ƙauna, ya ce da muryar kwanciyar hankali:
“Abin da ya fi muhimmanci shi ne farin cikin mu tare. Wannan gidan ba zai sake zama gidan kuka ba, sai gidan dariya da soyayya.”
Mamei ta yi murmushi, ta ce:
“Ameen. Allah ya kare mana wannan farin ciki.”
Afsana ta ɗaga hannunta sama kamar yarinya mai addu’a, ta ce:
“Ameen.”
Sai ta lumshe ido cikin natsuwa, ta fara bacci mai sanyi da kwanciyar hankali.
Mamei ta lullube ta da blanket, Papa ya kashe fitila, suka bar ta tana bacci cikin nutsuwa.
Da safe, rana mai daɗi ta fito, Afsana ta shirya cikin sabuwar uniform ɗinta.
Mamei ta gyara mata ribbon ɗin gashinta ta ce:
“Baby, yau fa za ki fara makaranta. Ki je ki yi dariya, ki yi wasa da sabbin abokai.”
Papa ya kawo mata jaka mai ɗauke da zane-zane masu kyau, ya ce:
“Ga jakar ki, ni da kaina na zaɓa miki.”
Afsana ta rungume su duka biyu, sannan suka raka ta makaranta.
Afsana ta shiga cikin aji, bayan gama darasi.
Yaran makaranta suna ta gudu-gudu da dariya. Afsana ta tsaya a gefe tana kallonsu.
Sai wata yarinya mai fara’a ta matso ta ce:
“hello, sunana SABIYA. Ke fa?”
Afsana ta yi murmushi ta ce a hankali:
“Ni Afsana.”
Sabiya ta ce da dariya:
“Zo mu je mu hau slide tare! Na ji daɗin samun sabuwar ƙawa.”
Hakan ya sa Afsana ta fara yin wasa a hankali, tana dariya. A hankali ta fara mantawa da duhun da ya ratsa rayuwarta a baya.
Da aka tashi makaranta, Papa ya zo ya ɗauke ta da mota. Afsana ta yi tsalle ta rungume shi tana cewa:
“Papa! Na samu sabuwar ƙawa a makaranta. Sunanta SABIYA.”
Papa ya yi dariya ya ce:
“Wannan fa abin farin ciki ne sosai. Kin ga ai ba ke kaɗai ba ce yanzu.”
Mamei da ta saurara daga baya ta yi murmushi, zuciyarta ta cika da farin ciki ganin yadda Afsana ke komawa yanayi na da.
Duk wacce ta ke son document ɗin littafin KURURUWAR da ta min magana ta wannan number 07062701555
Please share like comment masoyana
KURURUWAR SHAIƊAN
*✨HAZIƘAN MARUBUTA✨*
*Book 1 free ne [2025]️*
Masoya littafin KURURUWAR SHAIƊAN kuzo ku shaƙata da sabon update ɗin da zai saka ku a cikin duniyar da ba zaku so ku fita ba.
Cike da ruɗani soyayya da asiri na san babu mai so ya rasa wannan kada ku bari a baku labari… Ku ka sance cikin masu karantawa na farko
Danna nan ku shiga link
HYPERLINK "https://chat.whatsapp.com/FuTlAsg7uedBXoMKiash4h?mode=ems_copy_thttps://whatsapp.com/channel/0029Vb6QGRg6WaKl7oWkqq30" https://chat.whatsapp.com/FuTlAsg7uedBXoMKiash4h?mode=ems_copy_thttps://whatsapp.com/channel/0029Vb6QGRg6WaKl7oWkqq30
Story & writing
By
ZULFA M. TUKUR
بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل على محمد….
Page 21
Bangaren Hamdiya da Rabi – gidan salahuddeen rano
A gefe guda, kuwa, Hamdiya da Rabi sun kasa boye bakin cikinsu. Zuwan Yasmeen cikin gidan ya sa su ji tsoro da kuma haushi, domin sun san halinta da kuma abin da ya kawota gidan.
Hamdiya ta dubi Rabi tana cewa da ɓacin rai:
“Kin ga ko? Yanzu Ammi ta fara nuna soyayya ga wannan yarinyar, Zysha. Wai har tana cewa ta mayar da ita ƴarta, me kike tunanin zai faru a nan gaba?”
Rabi ta yi dugun tsaki, rai ɓaci:
“Wallahi ni kuwa tsanarta nake ji. Ashe za ta maye gurbin mu wajen Ammi? Wannan ai rashin adalci ne. Mu da muka daɗe a cikin gidan nan bata nuna mana
Haka ba sai wata ƴar aikin da ta zo shekaran jiya.”
Haka suka ɗaura karan tsana akan Zysha, zuciyoyinsu cike da hassada da ƙiyayya.
Bangaren Ammi