← Book details Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki Local reading mode
READING PART 21 OF 31

Sashe 21

Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki · about 8 min read

Ammi ta ɗaga hannu tana share hawayenta, idonta cike da ƙarfi:
“Rehman! Karka sake yi min wannan magana. Ni na haife ka, kuma na san irin zuciyata. Wallahi sai na ga halin da amour ta ke ciki da kaina. Ba zan iya kwana cikin rashin sani ba.”

Mahek da ke gefe ya matso kusa yana goyon bayan Ammi:
“Boos, bari kawai mu tafi. Ka san halin Ammi idan ta dage. Idan har ta ji wani abu ya faru idan ba ta gani da idanunta ba, wallahi hakan zai iya cutar da ita. Gara ta ga gaskiya ta fuskance ta fiye da a ɓoye mata.”

Rehman ya zuba wa Mahek ido da wani irin kallo mai cike da jan kunne, kamar yana son ya ce ya rufe bakinsa. Amma daga ƙarshe ya yi shiru, ya juyo ya dubi Ammi da tausayi.

“Ammi… to shikenan. Bari mu tafi yanzu. Amma don Allah ki shirya zuciyarki. Kada ki nuna tsoro ko kuka a gaban Amour. Ki yi ƙoƙari ki ƙarfafa mata gwiwa.”

Ammi ta gyada kai, amma zuciyarta na rawa. Ta dafa ƙirjinta tana ambaton “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un… Ya Allah Ka bani ƙarfin guiwa.”

Rehman ya ɗauki makullin motarsa, suka fito daga falon tare da Mahek. Yayin da suke saukowa daga matakala, zuciyar Ammi na bugawa da sauri kamar zata fito daga kirjinta.

Sai dai Rehman kansa ba shi cikin nutsuwa. Duk motsin da yake yi yana jin wani nauyi a zuciya.

Yayin da suka fito daga falon, Ammi na gaba, Mahek a gefe, Chef Rehman kuwa yana takawa cikin sauri da jaruman maza.

Suna isa parlour kawai suka ci karo da Hajia Babba da ke zaune tare da Yasmeen suna fira. Da ta hango su a tare cikin hanzari, ta ɗago ido ta dubi Ammi da mamaki.

“Lafiya kuwa? Ina za ku haka cikin gaggawa?” Ta tambaya cikin murya mai ƙarfi.

Rehman bai tsaya ba, dan takaici ni ya rufesa, wai ina zaku? Sai kace wasu ƙananun yara. Ya mai maita kalmar a bakinsa, cikin ɓacin rai idan yace zai tsaya to rayuka ne zasu ɓaci. Dan haka kawai ya wuce zuciyarsa na tafasa, ya bar Ammi da Mahek tsaye kamar an dasa su.

Hajia Babba ta sake maimaita tambayarta, wannan karon da ɗan tsawa:
“Ammi, ki faɗa min, ina za ku haka?”

Ammi ta ɗago kai rai a ɓaci, karaf idonta ya shiga cikin na Hajia babba, sai ta ji kanta ya fara juyawa kawai sai jikinta ya ɗauki rawa kamar mai tsoro, ta ɗan tsaya, zuciyarta na bugawa. Ta ji bakinta ya mutu da amsa, ta kasa cewa uffan. Idanunta kawai suka sauka ƙasa.

Mahek kuwa ya kalli Ammi, ya kalli Hajia babba, sai ya yi shiru shima, bakinsa ya murɗe kamar wanda kalma ta makale masa.

Shiru ya ratsa parlourn. Sai kukan agogon bango kawai yake tashi. Hajia babba ta zaro ido tana kallon su biyun, ta ce cikin mamaki:
“Na rasa dalilin shiru na ku. Shin wani abu ya faru ne da kuke ɓoye min?”

Ammi ta runtse ido, hawaye na ƙoƙarin zubo mata. Ta san idan ta faɗa gaskiya, lamarin zai iya ƙara rikicewa. Amma kuma shiru ma ya isa ya nuna akwai wani abu.

Mahek ya yi ƙoƙarin buɗe baki ya ce:
“Hajia… mu… mu dai akwai ɗan abu da za mu je…”

Ammi ta yi saurin ɗaga hannu ta katse shi, tana girgiza masa kai alamar ya yi shiru.

Hajia babba ta kafe su da idanu, zuciyarta na cike da shakku:
“Hmm… ku na da wani sirri da kuke ɓoyewa. Amma wallahi ba zai daɗe ba sai na gano. Duk wanda yake ƙoƙarin ɓoye min abu a wannan gida, zai yi nadama.”

Ta faɗa a zuciyarta.
Ta miƙe tsaye tana kallon ƙofar da Rehman ya fita, idonta cike da zargi.

Ammi ta ɗan juya gefe tana share ƙwallar da ta fito a hankali, Mahek kuma ya sadda kai ƙasa.

Daga nan suka fita ba tare da sun ƙara cewa komai ba, zuciyoyinsu cike da nauyi.

Bayan fitarsu, Hajia Babba ta tsaya tsaye a tsakiyar parlour ɗin tana huci. Idonta ya ƙanƙance, zuciyarta cike da mamaki da kuma zargi.

Ta juya ta kalli Yasmeen da ke zaune tana binsu:
“san ina Ammi da Rehman suka nufa?
“A’a Hajia babba, ina zan san.
Yasmeen ta yi maganar cikin halin ko in kula.

Hajia Babba ta ɗan yi shiru tana nazari a harzuƙi. Ta furta a ranta:
“Ba al’ada ba ce a gidan nan su yi tafiya haka cikin gaggawa ba tare da sun sanar da ni ba. Akwai wani abu da suke ɓoyewa.”

Ta zauna ta jingina da kujera, tana jujjuya tunani.

Yasmeen ta dubeta da mamaki:
“wai Hajia babba me nine duk kika ɗaga hankalinki haka?”

Hajia Babba ta yi shiru na ɗan lokaci, sai kuma ta miƙe tsaye cikin ƙarfi, ta nufi ɗakin Ammi. Amma da ta kai ƙofar, sai ta tsaya cak ta saurari zuciyarta. Tana jin cewa wannan karon akwai wani babban abu da zai girgiza gidan gaba ɗaya.

Duk wacce ta ke son document ɗin littafin KURURUWAR SHAIƊAN daga farko ta min magana ta wannan number 07062701555

Please share like comment masoyana
KURURUWAR SHAIƊAN

*✨HAZIƘAN MARUBUTA✨*

*Book 1 free ne [2025]️*

Masoya littafin KURURUWAR SHAIƊAN kuzo ku shaƙata da sabon update ɗin da zai saka ku a cikin duniyar da ba zaku so ku fita ba.
Cike da ruɗani soyayya da asiri na san babu mai so ya rasa wannan kada ku bari a baku labari… Ku ka sance cikin masu karantawa na farko

Danna nan ku shiga link
HYPERLINK "https://chat.whatsapp.com/FuTlAsg7uedBXoMKiash4h?mode=ems_copy_thttps://whatsapp.com/channel/0029Vb6QGRg6WaKl7oWkqq30" https://chat.whatsapp.com/FuTlAsg7uedBXoMKiash4h?mode=ems_copy_thttps://whatsapp.com/channel/0029Vb6QGRg6WaKl7oWkqq30

Story & writing
By

ZULFA M. TUKUR

بسم الله الرحمن الرحيم

اللهم صل على محمد….

Page 22

Bangaren Tafiya – Ammi, Rehman da Mahek

Sun fito daga gidan cikin hanzari, zuciyoyin su a rikice. Rehman yana zaune, sai hucin ɓacin rai ya ke, ya kunna motarsa, ya buɗe wa Ammi ƙofa ta shiga. Mahek ya zauna a gaba, dukkanin su shiru, kowa cikin tunanin kansa.

Motar ta ɗauki hanya cikin nisan gari, iska na kadawa cikin shiru mai nauyi. Ammi ta dafa ƙirjinta tana ambaton kalmomin addu’a a hankali.

A zuciyarta ta furta:
“Ya Allah Ka bani ƙarfin guiwa, kar ka jarabce ni da abin da ba zan iya ɗauka ba.”

Rehman yana tukin cikin gaggawa, amma zuciyarsa ta fi gudun motar sauri. Yana jin kamar dukkan hanyoyin duniya sun takure masa.

Bangaren Hajia Babba

A cikin gida kuwa, Hajia Babba ta kasa zama. Tana ta yawo a parlour kamar mai neman wani abu da ya ɓace. Zuciyarta cike da shakku da rashin nutsuwa.

Ta dubi Yasmeen da ke zaune tana shan shayi, ta ce da murya mai ɗauke da izza:
“Yasmeen! Ki sani, akwai wani abu da ake ɓoyewa a gidan nan. Ni kuwa wallahi sai na gano. Ban yarda a raina ni cikin gidana ba.”

Yasmeen ta ɗan yi murmushi mai cike da nuna halin ko in kula, ta ce:
“Hajia babba, ko dai kawai kina son sa ido ne sosai? Wani lokacin fa rashin sani ya fi sani dadi.”

Hajia Babba ta harare ta da ido, ta ce:
“Ke! Ki rufe bakinki. Duk wanda ya raina ni a gidan nan, sai na nuna masa ko ni wace ce. Bari dai mu jira, gaskiya zata fito fili.”

Bangaren Zysha

A ɗaki, Zysha ta kasa samun nutsuwa. Duk kalaman Hamdiya, Rabi da Meena suna ta maimaituwa a kunnen ta. Ta ji zuciyarta tana nauyi, amma sai ta yi ƙoƙarin ɗaga kai.

Ta ɗauki Alqur’ani ta buɗe, ta jingina da bango tana karantawa da hawaye. A zuciyarta ta ce:
“Ko da kuwa kowa zai ƙi ni, na san kai Allah ba za ka taɓa ƙin ni ba.”

Sai ta rufe al Kur’ani da hannunta yana rawa, tana ƙara tabbatar da kanta cewa dole ta dage da addu’a domin tsira daga makircin su Hamdiya.

Bangaren Asibiti

Motar Rehman ta isa asibiti. Suna sauka, zuciyar Ammi ta buga sosai kamar zata fito daga ƙirjinta. Mahek ya dafa ta, yana ƙoƙarin kwantar mata da hankali.

Rehman ya jagorance su zuwa dakin jinya. A hankali ya tura ƙofar…

Ammi ta tsaya cak, numfashinta ya tsaya na ɗan lokaci. Idonta ya sauka kan Amour da take kwance, fuska fara kamar takarda, numfashinta ƙasa-ƙasa, hannunta riƙe da na’urar jini.

Ammi ta ɗauki numfashi mai nauyi, hawaye suka zubo mata, ta durƙusa kusa da gadon tana riƙe hannun Amour.

“Subhanallah! Ya Allah Ka sa wannan jarabawar ta zama rahama. Amour… ke ce mahaifiyar da ba ta haifa ni ba, amma na ɗauke ki kamar tawa kimmin komai aduniya. Kada ki bar ni yanzu.”

Rehman ya janye gefe zuciyarsa na karyewa, yayin da Mahek ya share hawayensa a ɓoye.

Shiru ya mamaye ɗakin – shiru mai nauyi da ya cika da addu’a da tsoro.

Ammi ta ci gaba da riƙe hannun Amour, zuciyarta na rawa kamar ba za ta iya tsayawa ba. Idonta ya cika da hawaye, amma ta ƙoƙarta ta yi murmushi a fuska, domin kada ta ƙara daga hankalin mara lafiyar.

“Amour… ki buɗe idonki ki kalle ni. Ki ji cewa muna tare da ke. Ki yi ƙoƙari don Allah.”

Amour ta ɗan motsa idanunta a hankali, kamar mai son yin magana amma kalmomi sun makale a leɓenta. Hannunta ya ɗan murɗa hannun Ammi, alamar ta ji kalamanta.

Wani sabon kuka ya cika zuciyar Ammi, amma ta riƙe shi a ƙirji, ta furta cikin zuciya:
“Ya Allah, kada ka ɗauke min wannan uwar.”

Rehman ya tsaya a gefe yana kallonsu, idonsa jajaye. Yana son ya yi magana amma muryarsa ta yi nauyi. Daga ƙarshe ya yi shiru yana binsu da ido.

Mahek ya gyada kai yana cewa:
“Amour tana jin ƙauna. Idan ta ga muna tare da ita, hakan zai sa ta yi ƙoƙari ta murmure.”

Ammi ta share hawaye, ta ce da ƙarfin guiwa:
“To, mu tsaya a nan tare da ita. Wallahi bazan bar ta ba har sai na ga ta dawo da murmushinta.”

Bangaren Hajia Babba Gida

A wannan lokaci kuwa, Hajia Babba ta shiga ɗakin Ammi tana bincike kamar mai neman sirri. Ta buɗe wardrobe, ta duba drawer, tana neman wata alama da zata nuna mata me Ammi da Rehman suke ɓoyewa.
Chapter 21 · 0% Book details