← Book details Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki Local reading mode
READING PART 23 OF 31

Sashe 23

Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki · about 8 min read

Zysha ta rungumi addu’a da Alƙur’ani – kuke ganin addu’arta zata ceci ta daga makircin Hamdiya da Rabi?

A Egypt kuwa, Afsana ta zama wakiliya a gasar ƙasa – shin Elena zata bari ta yi fice ko kuma zata yi nasarar makircinta?

Ku bar mana amsoshinku a comment, domin ra’ayinku shi ke ƙara wa littafin armashi!

Duk wacce ta ke son document ɗin littafin KURURUWAR SHAIƊAN daga farko ta min magana ta wannan number 07062701555

Please share like & comment masoyana

KURURUWAR SHAIƊAN

*✨HAZIƘAN MARUBUTA✨*

*Book 1 free ne [2025]️*

Masoya littafin KURURUWAR SHAIƊAN kuzo ku shaƙata da sabon update ɗin da zai saka ku a cikin duniyar da ba zaku so ku fita ba.
Cike da ruɗani soyayya da asiri na san babu mai so ya rasa wannan kada ku bari a baku labari… Ku ka sance cikin masu karantawa na farko

Danna nan ku shiga link
HYPERLINK "https://chat.whatsapp.com/FuTlAsg7uedBXoMKiash4h?mode=ems_copy_thttps://whatsapp.com/channel/0029Vb6QGRg6WaKl7oWkqq30" https://chat.whatsapp.com/FuTlAsg7uedBXoMKiash4h?mode=ems_copy_thttps://whatsapp.com/channel/0029Vb6QGRg6WaKl7oWkqq30

Story & writing
By

ZULFA M. TUKUR

بسم الله الرحمن الرحيم

اللهم صل على محمد….

Page 23

Bangaren Gasar Jiha

Ranar gasar ta iso. An tattaro manyan makarantu daga sassa daban-daban na jiha a babban dakin taro da aka kawata da tutoci da kujeru masu kyau. Dalibai suna cikin farin ciki, kowa na sanye da kayan makarantar su cikin tsari.

Afsana da Sabiya suka shiga da tawagar makarantar su, dukkan idanu suka biyo su saboda yadda suka fito cikin tsabta da annuri. Shugaban makaranta ya yi musu nasiha kafin su hau:
“Ku tuna, wannan dama ce ta nuna hazakar ku. Ku tsaya da gaskiya, ku nuna ilimi da tarbiya.”

An fara gasar da tambayoyin gaggawa. Malamai masu shari’a suna taɗa ƙararrawa suna fitar da tambayoyi cikin sauri.

Tambaya ta farko aka buga kan tarihin duniya. Afsana ta ɗaga hannu da kwarin gwiwa ta bada amsa cikin daidai.

Na biyu aka yi kan lissafi. Wannan karon Sabiya ce ta ceto makarantar, ta bada amsa cikin sauri har malamai suka yi mamaki.

Mutane suka fara jin daɗi, suna tafi. Makarantar su Afsana ta fara ɗaga kai.

Bangaren Elena

Elena tana cikin tawagar makarantar su ma, tana zaune tana kallon Afsana. Ta ji haushi ganin yadda ta ke haskakawa a gaban jama’a.

Sai ta ce a zuciyarta:
“Ba za ki gama da farin ciki ba, Afsana. Zan nemo hanya da za ta ɓata miki suna.”

Ta haɗa baki da wasu daga cikin dalibai a ɓoye, suna shirin yi mata mummunar cikas kafin gasar ta ƙare.

Bangaren Ƙarshe Karatun Rubutun Jama’a

Shirin ƙarshe na gasar shi ne karatun rubutu a gaban taron jama’a. Kowace makaranta ta aika ɗalibi ɗaya. Shugabannin makaranta suka zaɓi Afsana ta wakilta saboda kyakkyawan furuci da nutsuwarta.

A lokacin da ta hau kan dandalin, dakin ya yi shiru. Idanunta cike da natsuwa, hannunta riƙe da rubutun da aka ba ta. Ta fara karantawa da muryarta mai taushi, tana bayyana kalmomi cikin salo mai ɗaukar hankali.

Ko da waɗanda suka yi niyyar tsanar ta sai suka tsinci kansu suna sauraro cikin shauƙi.

Wani daga cikin malamai ya ce a ransa:
“Wannan yarinya ba karamar baiwa gare ta ba.”

Bayan kammala karatun jama’a, malamai suka koma don lissafin maki. Dakin taro ya cika da hayaniya, dalibai na ta hasashen wane zai lashe gasar.

Afsana ta dawo kan kujerarta, zuciyarta tana bugawa da sauri, amma fuska cike da tawakkali. Sabiya ta riƙe hannunta tana murmushi:
“Afsana, ki kwantar da hankalinki. Na san ba za mu tafi hannu rabau ba.”

Elena kuwa tana gefe tana bin Afsana da kallo mai cike da kishi. A zuciyarta ta ce:
“Idan har kika ci wannan gasa, to sai na yi amfani da makircina na gaba. Wallahi ba za ki yi suna a gabana ba.”

Sakamakon Gasar

Shugaban malamai ya ɗago tsaye da takarda a hannunsa, ya fara sanar da sakamako cikin girmamawa:

Makarantar farko ta sami matsayi na uku.

Na biyu kuwa wata makaranta ce daga cikin birni.

Dakin ya ɗauki kiran suna da tafi. Sai ya ɗan yi shiru kafin ya ce:
“Wanda ya zo na ɗaya kuma ya lashe wannan gasa ta jiha… ita ce Afsana daga makarantar su!!!”

Wata ƙara ta tashi a dakin taro, dalibai suka tashi tsaye suna ta tafi. Sabiya ta rungume Afsana tana dariya hawaye na zuba a idonta saboda farin ciki.

Afsana ta tsaya cak tana jin kamar tana mafarki. Ta ɗora hannunta a ƙirjinta tana fadin:
“Alhamdulillah… na gode Allah.”

Elena

Duk da farin cikin da ya cika dakin, Elena ta zauna a kujerarta ba ta tafi ba. Ta matse yatsunta, idanunta sun kaɗa da ja.

“Wannan ba ƙarshe ba ne, Afsana. Na rantse da dukkan abinda nake da shi, sai na lalata farin cikin ki. Za ki gane wannan nasara ta zama bala’in ki.”

Ta haɗa baki da wasu daliban da suke da kishin ta, suka fara tsara cikas tun kafin Afsana ta koma makaranta.

Bangaren Mamie

A gida kuwa, Mamie ta samu wasiƙa daga Sarauniya Alisha wacce take mata barazana:

“Idan har baki rabu da ɗana Japheth ba, to ki shirya asarar komai da kike da shi.”

Mamie ta karanta wasiƙar, jikinta ya ɗauki rawa. Ta dafe ƙirji tana fadin:
“Ya Allah, wannan jarabawa ce mai nauyi… amma ba zan bar mijina ba ko da kuwa me zai faru.”

Hawayenta suka zubo, amma zuciyarta ta daure.

Washegari makarantar su Afsana ta shirya taron murna saboda nasarar da suka samu. An kawata harabar makaranta da tutoci, dalibai da malamai duk sun hallara.

Shugaban makarantar ya yi magana cikin farin ciki:
“Wannan nasara ta Afsana ba nata kaɗai bace, nasarar makaranta ce gaba ɗaya. Ta nuna mana cewa da dagewa da naci, za mu iya kaiwa duk inda muka nufa.”

Dalibai suka yi tafi, wasu suka ɗaga kwalaye masu rubutu “Congratulations Afsana!”

Afsana ta tsaya a gaban taro, tana murmushi cikin kunya, hawaye na farin ciki a idanunta. Ta ce:
“Na gode wa duk wanda ya goyi bayana. Wannan nasara ta kasance sakamakon addu’a da haɗin kai. Allah shi ne ya ba ni wannan damar.”

Bangaren Elena

Amma a gefe, Elena da ƙawayenta suna tsaye da mugun murmushi. Ɗaya daga cikinsu ta ce:
“Elena, ya kamata mu bari ta more farin cikinta kafin mu ɗauki mataki.”

Elena ta girgiza kai, idonta ya kaɗa da tsananin ƙiyayya:
“A’a! Wannan shi ne lokaci mafi dacewa don ɓata mata suna. Lokacin da kowa ya ɗora ta kan sama, sai mu jawo ta ƙasa. Ku jira, ku ga yadda zan yi.”

Da dare bayan taro, Elena ta shiga makaranta makarantar shiru ba kowa, amma ita ko tsoro bata ji ba ta shiga dakin aji litattafai ta ɗauki wasu takardu daga cikin files ɗin makaranta. Ta shirya yin amfani da su wajen zargin Afsana da laifi — wai tana satar bayanai domin ta ci gasar.

Ta haɗa dukkanin bayanan a cikin envelope, ta ce cikin dariya mai sauti:
“Da safe, duk duniya za ta ji cewa Afsana ba ‘yar gaskiya bace. Idan aka tabbatar da wannan zargi, nasararta za ta zama abin kunya.”

Bangaren Afsana da Mamie

A lokacin kuwa, Afsana ta koma gida tana farin ciki. Mamie ta rungume ta sosai, tana fadin:
“Na yi alfahari da ke, Afsana. Ki sani cewa nasararki tana da daraja fiye da zinariya.”

Papa ya ɗora hannu a kafaɗarta ya ce:
“Ki ci gaba da dagewa, karki bari wani ya rage miki ƙima.”

Afsana ta yi murmushi cikin hawaye:
“Ina godiya da addu’ar ku, da yardar Allah zan ci gaba da kasancewa abin alfahari gare ku.”

Amma Mamie har yanzu zuciyarta na ɗauke da wasiƙar Sarauniya Alisha. Duk da tana farin ciki da Afsana, a zuciyarta tana fargaba cewa barazanar da ake yi mata kan Japheth za ta iya ƙara tsananta.

Papa ya kalli afsana ya ce:
“Sweetheart gobe na shirya mana zuwa gidan wasa mai ƙayatarwa” afsana ta saki ihun farin ciki tare da rungume shi:

“wayyo daɗi papa I love you so much” tai maganar tana sakin dariyar farin ciki, shima papa ya rungumeta cikin so da kyauna, mamei kuwa sai kallon su take gwanin birgewa.

Da safe, bayan sun gama shiri, Papa ya fito cikin farar riga da hula mai kyau, Mamei kuma ta saka doguwar riga mai ɗauke da ƙayatarwa. Afsana kuwa ta saka riga mai ruwan pink, ta sha ɗan kwalliya mai sauƙi, fuskarta ta ƙara haske kamar furannin da ke buɗe a lokacin asuba.

Suka nufi mota tare da dariya da nishadi. Papa ya kunna motar, sai suka kama hanyar zuwa wani gurin wasa da aka fi sani da Paradise Garden wurin da yara da manya ke samun annashuwa iri-iri.

Lokacin da suka isa, Afsana ta ruga kamar wacce aka ɗaure aka sake. Ta fara gudu zuwa wurin roller coaster, tana dariya tana faɗin:
“Papa! Mamei! Ku hanzarta mana… ku yi sauri kafin a gama ticket!”

Mamei ta yi dariya sosai har sai da ta riƙe ciki.
“Ke dai Afsana, babu wanda ya fi ki sauri wajen jin daɗi.”

Papa ya bi bayanta yana dariya, ya biya kuɗin shiga, sannan ya rakata har cikin.

Sai aka fara zagaye na farko, Afsana ta kurma ihu saboda tsoro, amma daga baya sai dariya ta mamaye ta. Mama ta riƙe hannunta tana murmushi, shi kuwa Papa ya ci gaba da ɗaukar hotu.

Daga nan suka wuce wurin carousel, inda Afsana ta hau kan dokin roba mai juyawa, tana ta dariya tana daga musu hannu.

Wurin cike da yara da manya, kowa da farin cikin kansa. Wani yaro ƙarami ya zo ya miƙa mata balloon, ta amsa tana murna. Sai ta gudu zuwa ga Mamanta ta rungume ta:
“Mamei, yau na ji kamar ba zan taɓa yin kuka ba har abada.”

Mama ta share hawayen farin ciki, zuciyarta ta cika da godiya.

Papa ya tsaya gefe yana kallon su biyu, zuciyarsa ta furta da ƙasa-ƙasa:
“Ya Allah, idan wannan farin cikin nasu zai dawwama, to babu abin da nake nema a duniya sai hakan.”

Bayan sun shafe rana gaba ɗaya a Paradise Garden suna dariya da nishaɗi, sai da dare ya yi sannan suka bar wurin cikin gajiya mai daɗi.
Chapter 23 · 0% Book details