Sashe 14
Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki · about 8 min read
Sai kwai ta watsa da gudu ba tare da tana gani ba a wannan duhun ta ji ta yi karu da mutum ba. Tari da sanin waye ba ta ƙan-ƙamishe shi kuwa ya tsaya cak ya waro ido ba rida ya san wace. Yana jin yanda ƙyerjinta ke sama da ƙasa.
Bayan wani lokaci haski ya haska ko ina Zysha sai ajiyar zuciya ta ke saukewa kamar wacce ta yi tsare ɗagowa ya yi sai, ya zuba mata shayyatun idonsa masu haske.
Ganin abin nata ba mai ƙarewa bani:
“ɗaga ni. Ya yi maganar a hankali, da sauri Zysha ta ɗago idonta sai cikin idon chef Rehman. Gaban ta ya yi wani irin bugu, ba bu ɓata lokaci ta sakesa Zysha ta ɗauki idonta, daga cikin nasa hawayen tsoro suka gangaro a fuskarta. Bakinta na rawa:
“yallaɓai… Sorry wllhi ba da gan-gan na faɗo maka ba… Bansan kai bani na ji tsoron duhun ne“.
Chef Rehman ya watsa mata banzan kallo yana kwauda idonsa:
“me ya kawo ki wannan wajen da dare haka?“
Yay maganar ba daga bakinsa ta fito ba.
“bab babu komai kwai dai…” sai kuma ta yi shiru, chef Rehman ya ja dugun tsaki ya huci ta.
Da sauri Zysha ta dafe ƙirjinta:
“wai shi wannan wani irin mutum ne duk lokacin da na hadu da shi sai ransa ya ɓaci“.
Jiki a sanya ye ta nufi cikin gida.
*ƁANGAREN YASMEEN*
Kamar dai yanda suka tsara ita da Hajiya Ramlat hakance ta kasance ko da abban yasmeen ya dawo Yasmeen ta yi baccin ƙarya da ya tambaye Hajia Ramlat sai ta ce tasha magani bacci ya ɗauke ta ba dan ya gamsu ba ya girgiza kansa ya huci bedroom nasa.
Yasmeen kuwa tana bedroom nata sai juyi ta ke saman bed gaba ɗaya ta kasa bacci. Zuciyarta tana tuna maganar Hajia babba:
Rehman ya dawo..“
Zuciyarta na rawa da sha’awa. Ta rufe idonta, hoton Rehman ya cika mata zuciya.
“wayyo Allah! Wani irin so na ke maka Rehman?“ ta furta tana dariya zuciyarta ta cika da farin-ciki.
Washi gari da farin-ciki Yasmeen ta ta shi bata wani ɓata lokaci ta shiga bathroom ta yi wanka lokacin da ta fito daga wanka ɗauri da towel iya ƙugunta ta hangu Manisha da ke karkaɗi gadunta sai ta ja tsaki ciki da tsanarta.
“ki zo nan“ Manisha ta yi kamar bata ji ta ba. Sai ta ci gaba da aikinta:
“ki bakya je ina magana zo ki shafa min oil. Manisha ta ɗago ta kalli ta sheƙiƙe.
Cikin mugun ɓacin rai Yasmeen ta ƙasu:
“ki dan iyayen ki baki ji ba ke ƴar gidan uban waye ina magana ki yi min irin wannan, banzan kallo“ ta ɗaga hannuta zata mareta.
Charaf Manisha ta rike hannun ta zabga mata uwar harara:
“kar ki kuskura… Ko a mafarki ki saki yunkurin marina. Domin ni ba irin ƴan aikin da ku ka wulaƙantawa bani!“.
Sai ta yarfa hannun ta fice daga ɗakin Yasmeen ta bita da kallo tana mamakin tsaurin idon Manisha yarinya, sai uban izza sai ka ce ɗiyar wani shige. Yasmeen ta yi ƙwafa cikin mugun ɓacin rai.
“wallahi kin ci albarkacin yau ina farin cikin ganin masoyena, bada ban haka ba wallahi saina koya miki hankali“.
Sai ta ja tsaki ta nufi gaban mirror cikin lukacin ta fito daga bedroom ɗin nata cikin shiga mai ɗaukar hankali sai da ta tabbatar abbanta ya fita saita huci bedroom ɗin Hajiya Ramlat tana tako cikin izza.
Ta cikin mirror Hajia Ramlat ta hango ta itama ta ci uban kwalliya. Da murmushi ta ƙasu:
“mommy good morning“morning lovely daughter kin ga yanda ki ka yi kyau kowa? Masha Allah“.
Sai Yasmeen ta yi murmushin jin daɗi:
“Allah mommy? ”Allah kuwa lovely”.
Yasmeen ta rungumet ita ta rungumeta tana fara kewar ƴar ta ta. “lovely ki saurare ni da kyau… Kinsan dai Rehman baya sun hayaniya shi wani irin bauɗaɗɗin mutum ne. sai kinbi a hankali dan kar shirin mu wargaje“.
Yasmeen ta yi wani makirin murmushi:
“haba mommy sai kace baki san wacece ƴar Ramlat ba ai idan ban mallaki Rehman ba wallahi babu macin da zata aure shi, koda kuwa zan rasa raina ne!”
Hajiya Ramlat ta yi murmushi ciki da alfahari ta ke saurarenta.
“amma lovely daughter zaki tsaya ki yi breakfast?”A’a gaskiya mommy idan naga Rehman na yi”.
Yasmeen ta yi maganar tana turo baki da shagwaɓa Hajia Ramlat ta yi dariya suka fito parlour, Hajia Ramlat ta ƙwalawa zainab ƴar aiki kira ba ɓata lokaci zainab ta zo ta durƙusa ƙasa.
”Hajia gani”. Hajia Ramlat ta ce ”ki ɗauki akwatin Yasmeen ki kaima parking spot da to ta amsa ta ɗauki akwatin.
Hajia Ramlat har parking spot ta rakota, sai suga wata motar black jeep parki a harabar ajjiye motuci. Direban Hajia babba ne ya buɗe motar ƙofa yana gaishe, su suka sama sama kana Hajia Ramlat ta rungume Yasmeen idonta na tara kwallah na kewar ƴarta.
Yasmeen tana hura hanci ta shi motar tana ɗagawa Hajia Ramlat hannu direba ya tada mota mai gadi ya buɗe musu gat suka bar gidan.
Direba na gaba parking Yasmeen ta ta fito ta tsakiya a daular harabar gidan SALAHUDDEEN RANO cikin yanga, wani matsatsin murmushi ta yi ta ɗaga wayarta ta shiga gidan camera ta fara bidiyo ta tura Instagram da facebook TikTok.
Ba daɗewa aka fara mata ruwan comment da like ta duba wani sharhi ta lumshi ido da izza tana ƙara cije leɓenta.
Bayan ta shiga babban parlour gidan, kallon farko idonta ya sauka kan wata yarinya da ta ke huciwa da tray a hannu. Zuciyarta ta yi wani irin bugu.
”what?!” ta furta da murya da ba kowa ne ya ji ba.
Please share like comment masoyana
KURURUWAR SHAIƊAN
✨HAZIƘAN MARUBUTA ✨
*Book 1 free ne [2025]️*
Masoya littafin KURURUWAR SHAIƊAN kuzo ku shaƙata da sabon update ɗin da zai saka ku acikin duniyar da ba zaku so ku fita ba.
Cike da ruɗani soyayya da asiri na san babu mai so ya rasa wannan kada ku bari a baku labari… ku kasance cikin masu karantawa na farko
Danna nan ku shiga link
HYPERLINK "https://chat.whatsapp.com/FuTlAsg7uedBXoMKiash4h?mode=ems_copy_thttps://whatsapp.com/channel/0029Vb6QGRg6WaKl7oWkqq30" https://chat.whatsapp.com/FuTlAsg7uedBXoMKiash4h?mode=ems_copy_thttps://whatsapp.com/channel/0029Vb6QGRg6WaKl7oWkqq30
Story & writing
By
ZULFA M. TUKUR
بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل على محمد....
Page 17
Yasmeen ta tsaya cak tana bin Zysha da kallo, zuciyarta na harbawa da sauri ciki da tambayoyi.
A gefe kuwa, Zysha ce ta fito daga kitchen. Ganin Yasmeen ya sa zuciyarta ta buga, sai ta ɗauke kai tana wucewa.
Yasmeen ta kasa ɓoye mamaki ta furta a hankali:
”wayyo Allah! Wa nake gani haka? Ko dai idona ya samu matsala ne” tai maganar tana mutsike idonta.
“me yasa fuskar nan ta yi daidai da fuskar MANISHA ko dai na rikice ne?”.
Zysha kuwa, tana hucewa a labce, dauke da tray tana nufar dining.
Hajia babba da ta lura da Yasmeen tsaye sai bin Zysha da kallo ta ke:
“Ke kuma ya kika tsaya a nan?” Jin maganarta yasa gaba ɗaya duk suka mayar da kallon su kanta.
Sai kwai ta yi murmushin yaƙe ta ƙarasa dining area ta ja kujerar kusa da Hajia babba ta ɗaura kanta a shoulder ɗin Hajia babba.
”good morning Hajia babba”who are you doing today my daughter?”.
”Alhamdulillah “ok,
Sai ta kalli aunty asabe:
“asabe ki yi serving nata”.
”no… Hijia babba sai naga bab… Hajia ta yi mata banzan kallo ba shiri ta yi shiru.
Zysha ta ƙarasa babban dining ta ajjiye trayn kusa da Ammi cikin ladabi, ta gaisheta Ammi ta yi murmushi ta ɗaga kanta, alamar amsawa.
Ba ɓata lokaci ta yi serving nata, ta miƙe tsaye zata bar gurin Ammi ta rike hanunta, Zysha ta ɗago da mamaki ta kalleta da alamar tambaya.
Sai ta nuna mata kujirar kusa da ita, cikin rashin fahimta Zysha ta ɗago ta kalleta. Ashraf da ke kusa da kujirar Ammi ya yi ƴar ƙaramar dariya:
”tana nufin ki zauna ayi breakfast tare da ke“.
Hajia babba ta tsaya cak da cin abincin da ta ke, da sauri Zysha ta girgiza kanta sai Ashraf ya haɗe fuska ya ɗan harareta. Cikin rawar baki ta ce:
”don Allah… Uwar gida Ammi yallaɓai Ashraf… Ku yi haƙuri wallahi ban zan, iya breakfast tare da ku ba amma”.
Zysha ta ja hannunta daga riƙon Ammi cikin ladabi, sai hawayen da ta ƙi bari sun fara taruwa a idonta.ta sunkuyar da kai, tana wasa da yatsun hannunta kamar wacce aka kama da laifi.
Yasmeen kuwa ta kasa ɗauki idonta daga fuskar Zysha. Cikin zuciyarta wani irin hausi ya harɗeta tuna da abin da Manisha ta yi mata ɗazu.
Ashraf ya ƙara ƙura mata ido, zuciyarsa na bugawa da wani irin abu da ba ya iya fassara wa. ”me yasa kike ba zaki iya zama kusa damu? Ya faɗa yana sakin wani ɗan ƙaramin murmushi mai sa ɓacin rai.
Sai ta ƙara yin ƙasa da kanta:
”yallaɓai Ashraf ni fa mai aiki ce ba na da wani incin zama tare da ku”.
Kafin Ashraf ya yi magana sai Hajia babba ta ɗan yi gyaran murya tana kallon Zysha sama da ƙasa:
”ke ƴar aiki, ina kika taɓa gani a rayuwarki kafin ki shigo gidan nan ƴan aiki na zama tare da masu gida!?”
Ta yi tambayar ta faɗa da ƙarfi kamar ƙarar wanƙiya. Dukan su suka juyo suna kalllonta.
Zysha ta tsaya cak! Jikinta ya ɗau rawa, laɓaɓanta na motsi amma babu kalma da ta fito
Su Hamdiya suna daga gyefe sai murmushin jin daɗi suke.
Cikin hanzari Hajia ƙarama ta ƙatse maganar da wata irin murya mai sanyi.
”Hajia babba, wannan ai ba lokacin irin waɗannan magana ba ne. Ita fa baƙuwa ce, ba komai ta sani ba“.
Kafin wani ya yi magana dadda ɗan kamshin chef ya cika kunnin su, shiru ya ratsa parlourn. Kowa ya sunkuyar da kai.
Ba ƙaramin firgita Yasmeen ta yi da kyakkyawar hallitar da Allah ya yewa chef Rehman ba, gaba ɗaya ta bi ta ruɗe zuciyarta kamar zata yi tsalle, ta yi murmushin jin daɗin ganinsa sai kallonsa ta ke uwa zata cinye shi.
Ciki da zumuɗi ta miƙe tsaye, Hajia babba ta muntsi neta Yasmeen ba shiri ta koma ta zauna tana turo baki.