Sashe 10
Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki · about 8 min read
“Kuyita gwagwarmaya, Japheth, duk yadda ku ka yi afsana ta zama ƴata! Kamar yadda nake shaƙar rayuwar ku haka zan shaƙi wannan ɗan ƙaramin numfashinta har sai na mallaketa da dukkan jikinta dan ƙarfafa *tukunyar tsafin mu….*”
Dariya ta karaɗe ɗakin kafin komai ya ɗauke.
Mamie ta sake ruɗewa da hawaye ta rinka karantu addu’o’i. Papa kuwa ya riƙe gushinsa ya tabbatar akwai wani abu da ya faru a masarautar.
A ransa ya ce:
“Dole ne na bincika tarihin masarautar mu. Na tabbata akwai wani ɓoyayyin al’amari da yake ɓoye tun shekarun baya. Ni kuma sai tuna shi ko da zan fuskanci mutuwa!”
*NIGERIA ƁANGAREN ZYSHA*
Bayan ta gama karanto addu’o’I ta daina jin wannan motsin na ɗan wani lokaci duk da ta daina jin motsin amma zuciyarta ta kasa samun natsowa sai ƙara duƙunƙini bargun take.
Ta rufe idonta da niyar bacci amma kwasam ta fara jin ƙarar iska a cikin ɗakin. Fitilar ɗakin ta yi *dummm!* Tayi ƙasa ta koma duhu.
Zysha ba karamin firgita ta yi ba kamar zata haɗi zuciyarta ta haɗe wani mugun yawu ji kake kutt! Kutt!. Kokawa ta shiga yi da numfashinta da ƙyar ta samu ta fara karatu addu’a.
*A’uzubillahi minash shaiɗanir rajim….*
*Bismillahir rahamanir rahim….*”
Sai kawai ta ji kamar an taka ƙafafu gyefin gadunta.
Hannunta ya yi wani irin sanyi jikinta ya ɗauki rawa ta buɗe idonta a hankali sai ta hangu *inuwa* ta tsaya bakin window tana kallonta.
Wata murya mai kauri ta yi dariya”Zysha ki bakuwata ce….”
Zysha a firgice ta ruga da gudu tana neman hanyar fita ɗakin ya yi wani irin duhu a haka taci gaba da neman hanyar fita bata ankara ba taji ta ƙume da bangon ɗakin ta kurma wani gigitaccin ihu!!!.
Aunty asabe dake shirin wanciya ta jiyu wannan ihu kasancewar ɗakin su yana jeri ne bakinta na rawa ta furta”Zysha?”.
“Tabbas wannan Muryar Zysha ce”.
Fita ta yi daga ɗakin ta nufi ɗakin Zysha da sassarfa hannunta na rawa ta murɗa kofar ta shiga ɗakin.
Chan ta hango Zysha kwance numfashinta na fita sama-sama goshinta ya kumbura sumtum.
Cikin tashin hankali aunty asabe ta dafe ƙirjinta.
“Subahanallah! Zysha me ya sameki?
Da ƙyar ta buɗe bakinta ta ce”wallahi aunty asabe, akwai wani abu a ɗakin nan! Akwai wani abu yana binaaa!”.
Cak ta muryarta ta ɗauke da alama sumewa ta yi.
Cin ruɗani da ban mamaki aunty asabe ta fara girgizata tana kiran sunanta”Zysha! Zysha! Shiru ko alamun mutsi bata yi ba. “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”.
Hankalin aunty asabe yay mugun tashi aguji ta ɗebu ruwa ta shafawa fuskarta, Zysha ta ja wani numfashi hamdala aunty asabe ta yi muryarta na rawa ta ce”sannu Zysha zo ko kwanta gobu da safi sai muyi magana dan wannan yanayin naka ya bani mamaki”.
Da sauri ta girgiza kanta jikinta na rawa.
“Don Allah aunty asabe kar ki barni a ɗakin nan wallahi tsoro nake ji”.
Tai maganar cikin tsananin kuka. “Zysha ki kwantar da hankalinki ki kwanta ki yi addu’a wata ƙila maa mafarki ki ka yi kin ji ko?”
“Wallahi aunty asabe ba mafarki bane. “Zysha ki yi haquri ki kwantar da hankalinki a dokar gidan nan ba a yar da wata ƴar aiki ta kwana a dakin yar uwarta ba dole ki yi haquri ki kwanta ki yi addu’a, insha Allahu ba abin da zai sa meki”.
Jikin sanyin jiki Zysha ta kaɗa kanka amma a ƙasan zuciyarta tsoro fal aunty asabe ta taimaka mata ta kwanta saman bed aunty asabe ta mata sallama ta koma ɗakinta.
Da fargaba Zysha ta kwanta tana karanta addu’a dakyar ta samu bacci ya yi awon gaba da ita.
*Washi gari*
Zysha ta farka da mugun zazzaɓi a jikinta ta ɓude rinannun idonta da suka kumbura gushinta ya kumbura saboda ƙumewar da ta yi darin jiya.
Da ƙyar ta samu ta miƙe ta dafa bango ta shiga bathroom ta yi wanka ta ɗauro alwala tay sallah.
Tana idarwa ta ɗaga hannuta sama ta farawa Allah kirari kana ta roƙi Allah ya kareta daga wannan masifar da ta kunnuta aranta ta raya tabbas akwai matsala a wannan gidan.
Darin jiya da ya gabata ya matukar bata tsoro da gigicewa.idonta sunyi jajir fuskarta ta rame, kamar wadda ke ɗauki da cuta a cikin dare guda.
*Ɓangaren yasmeen*
Kamar yadda ta ƙudiri niyar zuwa gurin birthdayn friend ɗinta haka kuwa ta kasance.
Mahaifinta na fita wani ɗan iskan murmushi ya bayyana a fuskarta, alamar bata yi watsi da zuwa gurin birthdayn ba duk da kowa mahaifinta ya gar-gaɗeta.
“Mommy na faɗa miki ko? Ba wanda zai hana ni zuwa. Wannan Birthday ɗin ni ba kamar sauran bace dole na je”.
Ta faɗa tana ɗaura kanta a shoulder ɗin Hajiya Ramlat cikin shagwaɓa.
Hajiya Ramlat ta sumbaci gushinta ta ce:
Ki shirya lovely daughter. Ki nuna musu cewa ki ƴar Ramlat ce.
“Yawwa mommy ki turon wannan ƴar aikin mai tsaurin idon nan”.
Tai maganar tana yatsini fuska.
“Ki dai bar shigiyar yarinyar nan sai na yi maganinta. Tai kwafa
Cikin ɗakinta yasmeen ta shige sai taga kaya saman gado da zumuɗi ta ƙarasa dan ta san wannan aikin mommynta ce.
Kayan rigunan alfarma, takalma masu danƙarin kyau da tsada kwalabin turare masu matukar ƙamshi. Ta fara jerasu gaban mirror.
Cikin ƙan-ƙanin lkc ta shirya cikin riga gown mai walƙiya da duwatsu na ƙyalli, kamar da zinari aka ƙyera su.
Ta ɗaura dugun *heel shos,* mai sheƙi, ta ɗauko jakar hannu ƙarama ta designer, sannan ta ratayi sarka da ɗan kunne masu walƙiya.
Bayan ta gama shiryawa ta ja ɗugun gashin da ta ƙarawa kanta ta lulluɓeshi da curly style mai walƙiya, ta ɗauki turarin Gucci Bloom ta feshe jikinta.
Ta tsaya gaban madubi tana juyi kamar wata sabun kamu haka take kallon madubin tana jinta tamkar sarauniya.
“Birthday yau zai zama namu. Saina birge kowa”.
Ta faɗa da wani ƙayataccin murmushi. Ta fita daga ɗakin tana tako cikin izza Mommy ɗinta ta hangota tana kiran kalllonta cikin alfahari. Ta ce” lovely daughter yau kin kyau tamkar sarauniya, ki tafi ki more abunki lovely.
Yasmeen ta yi murmushi ta sumbaceta sannan ta fice.
Da haka zance muhadu daku ranar Laraba idan Allah ya kaimu dumin ganin cakwakiyar da zata gudana a birthday party sannan gyefe daya Egypt…. Hmmm kar ku bari a baku labari
Kuna sun labarai masu matukar ɗadi ko biyu tashar ZULFA M TUKUR HAUSA NOVEL ka
daihttps://linkfly.to/70627Qedmw6
✨Labarin soyayya mai ƙayatarwa
✨ Firgice ruɗani
✨ Darasi nishaɗi duk acin littafin KURURUWAR SHAIƊAN kar ku bari a baku labari
Like & share comment please
KURURUWAR SHAIƊAN
*Book 1 free ne [2025] novel ️*
My channel Link
HYPERLINK "https://whatsapp.com/channel/0029Vb6QGRg6WaKl7oWkqq30https://chat.whatsapp.com/GMguONdwRnw5KiIfxpKquJ" https://whatsapp.com/channel/0029Vb6QGRg6WaKl7oWkqq30https://chat.whatsapp.com/GMguONdwRnw5KiIfxpKquJ
Story & writing
By
ZULFA M. TUKUR
Page 14
*Masarautar Egypt*
A darin nana bayan komai ya lafa, papa ya kwantar da afsana a gadunta. Duk da cewa ta dawo da numfashi, jikinta ya yi sanyi kamar an jawo rai da rai.
Mamie ta zauna gyefinta tana karantu addu’o’I cikin harshen Hausa da larabci, hawayen ta baya tsayawa. Papa ya fita daga ɗakin, zuciyarsa na cike da damuwa.
Ya nufi babban parlour masarautar inda aka zuba fitilu masu walƙiya, ya zauna cikin ɗaya daga cikin sofa set ɗin parlourn.
Bai jima da zama ba sai ya ga wata tsuntsuwa mai girma kamar kurciya, wadda ta ke da idanu jajayi Kamar wuta. A hankali ta rikiɗe ta koma maci mai tsayin gaske, fuskarta baƙe ce tamkar an gasata da wuta, idanunta kuwa sai walƙiya su ke. Hannayinta masu tsayi ƙafafunta suma haka.
Cikin murya ɗauki da tsoro papa ya ce:
“Wacece ke? Sannan me ki ke nema a tari da mu!?”
Dariya ta fashe da shi mai ban razana.
“Japheth kana sun kasan asalin wacece ni? Ni ce *lamiya*,ɗaya daga cikin halittun da aka haifa tun kafin mulkin kakaninka. Mun rantse ba zamu yarda wani musulmi ya zauna mana masarautarmu ba. Ubanka ya karya alƙawari. Ya ɗauki abokantaka da Musulmi. Shiyasa nake jin amanar jininka har zuwa yau”.
Papa ya yi shiru jikinsa na ƙarƙarwa.
Ta ƙarasa da murya mai ciki da nuna tsantsar ƙiyayya:
“Jinin da zai fitu daga tsatsunka sadaukarwa ne domin in hana ko wani ɗa ɗaya daga jinin ku ya rayu muddin akwai musulmi a cikin gidan nan. Ita afsana ta zama abin cina. Ko da kun hana ni yau zan dawo gobe. Har sai na tsotse jininta gaba ɗaya”.
Papa bai gama dawowa daga shiga firgice ba tsohuwar ta rikiɗa zuwa wani ƙatun maciji mai kan maci.
Macijin ya yi irin kukansa na mai ban tsoro, sannan ya shige cikin bango ya bace.
Tashin hankali.
Papa durƙushewa ya yi idonsa na zubar da hawayi ya tuna maganarta:
“Jinin musulmi bazai ci gadon masarauta ba”.
Ciki da rashin mafita ya fita daga parlour ya koma bedroom ɗin afsana. Mamie ta yi bacci kusa da ita, amma ba baccin nutsuwa ba zuciyarta na ciki da tsoro.
Afsana ta motsa a hankali, numfashinta na fita sama-sama. Idonta ya buɗe a hankali, sai kawai suka koma ja kamar ana ƙona wuta a cikinsu. Muryarta ta fito da tsoro, tana haɗa maganar ƙaramin yaro da tsohuwa:
“Papa… Mama… ku bar ni… ni ba ƴa na ku ba ne… na riga na zama nata… nataaaa!”
Mamie ta fashe da kuka mai tsuma zuciya ta rungume ta da ƙarfi tana ihu:
“Wallahi ba zan bari su kwace min yarinyata ba! Ya Allah ka taimaka min!”
Papa ya matso da gaggawa yana girgiza afsana:
“A’a Afsana! Ki tuna mu ne iyayenki! Ke jininmu ce! Kada ki bari wani abu ya sarrafa ki!”
Kwatsam bangon ɗakin ya fara yin ƙara, fitilun suka fara yin ƙift-ƙift, sai wata iska mai ƙarfi ta kaɗa labulen taga. Murya ta fito daga cikin bango tana dariya mai ban razana:
“Ku iya ihu, ku iya kuka… amma duk da haka Afsana ta zama tawa. Jinin ku ya zubar da sirrinmu tun farko. Japheth, kai da zuriyarka ba za ku tsere ba! Duk wanda ya fito daga jinin ku, sai ya zama na tukunyar tsafinmu… sai ya mutu ko ya zama bawa na har abada!”
Mamie ta ruɗe ta fara karanta addu’o’I da kyar, jikinta yana rawa. Papa kuwa ya rike kansa zuciyarsa na harbawa kamar zata fashe, amma ya ɗauki alƙawari a ransa: