← Book details Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki Local reading mode
READING PART 12 OF 31

Sashe 12

Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki · about 8 min read

Da sauri ta girgiza kanta tana turo baki:
“haba mommy sabo da haka ki ka shiga damuwa? Ni fa ba yarinya bace. Sai kace biki san gurin da na je ba.

“Shhhh…ki yi shiru ki bari mu nemi mafita kafin abbanki ya gano yan zunnan ya kira ya tambaya ya kira wayarki har sau goma sha biyu ba ki ɗaga ba kuma ni ma na kira baki ɗaga ba shi yasa hankalina ya tashi“.

Yasmeen ta rike hannun mamanta tana rawar jiki:
“Wayyo Allah Me kika faɗa masa to mommy?“

Hajiya Ramlat ta sakar mata murmushi tana rike haɓarta:
“haba ki ko lovely daughter ki kwantar da hankalinki ai tun da kin dawo shi kenam na faɗa masa zazzaɓi ya rufe ki“.

Da tsantsar farin-ciki Yasmeen ta ƙanƙameta:
“gaskiya mommy ke ta dabance ina Matuƙar ƙaunarki“.

*Ɓangaren Hajiya babba*

Ta shiya ta yi shiga ta alfarma rantsatsin material coffee da ratsin milk sai zuba sihirtaccin ƙamshi ta. Fuskarta ɗauki da ƙayataccin murmushi duk abin da matar nan mai fafarin kaya ta gaya mata ya ƙara mata ƙarfin zuciya.

Kai tsaye part ɗin Hajiya ƙarama ta nufa.
A parlour ta sami Hajiya ƙarama tana kallo A tafkekiyar TV. A firgice ta mai da hankalnta kanta cikin mamaki.

Hajiya babba ta ɗan murmusa ciki da mugunt:
“wata sabuwar hanya ta buɗe min lokacin ramuwar gayya ya kusa. Duk wanda ya ke tunanin zai tsira da nasara…zai gani munfi ƙarfinsa“.

Cikin rashin fahimta Hajiya ƙarama ta kalleta:
“fatima me kike nufi da ramuwar gayya?“.

Hajiya ƙarama ta yi tambar cikin ruɗewa.

Hajiya babba ta zauna a kan kujera tana lumshi ido tayi shiru na ɗan wani lokaci. A hankali ta ce“na shirya Lubna zata zama *hadaya* ta farko”.

Lokacin da ta furta Lubna saura ƙiris zuciyarta ta buga jikinta na rawa zuciyarta na wani irin bugu ta miƙe tsaye.

“mim…me ki ke nufi Fatima!? Kina nufin da gaske ne zargin da nake miki! Ke ce sanadiyyar ciwon Lubna!?

Hajiya babba ta yi murmushi, idonta ya rine ya yi jajir:
“salamatu ai na huci nam duk wanda ya san sirrina kuma ya shiga gunata bana taɓa barin shi ke ma bazan barki ba “.

Cikin mamaki da kuma al’ajabi Hajiya ƙarama ta ke girgiza kanta tana hawayi ta tushe kunninta da ƙarfin tsiya.

“inallalillahi wa’innah ilaihi raji’un. Allahumma ajirni fe musibate wa’aklihini kairan minhaa….“

Hajiya babba ta meƙi tsayi, ta ɗaga hannuta sama tana dariya cikin shaiɗanci:
“wallahi tun da ban samu abin da nake so ba gaba ɗayan ku sai naga bayan ku!

Tana gama faɗar haka fitilun ɗakin suka ƙarye aka barta cikin duhu. Hajiya ƙarama ta firgice tana neman taimako.

*Ɓangaren Ammi*

Bayan Zysha ta gama ciyar da ita tana kwance sai zuciyarta ta fara bugawa da sauri sai ɗan yatsun ƙafarta ya fara mutsawa. A rude ta daga hannunta nanma ta ga gaba ɗaya jikinta ya saki sai ta miƙe tsaye a kan ƙafafunta. Wata irin ƙasala ta lulluɓe jikinta, kamar wacce aka shafa mata wani nauhi. Ta dafa ƙirjinta tana kallon kanta cikin mirror.

A hankali taga fuskarta tana rabewa kamar mutum biyu ne ke bayyana ta cikin maduben. Ita da kuma baƙar fata, ido jajaye baki ciki da haƙora kamar na macijiya.

Ammi ta firgita da sauri runtse idonta. Lokacin da ta buɗe komai ya koma daidai. Sai dai ta jiyo wani kallo ta bayanta a madubin wani inuwa mai tsaye ta na kallonta.

“wayeee ne!? Ta faɗa tana juyawa da sauri, amma ba bu kowa.

Wata murya mai sanyi ta ratsata:
“lubnaaa…kin riga kin zama hadaya jininki ya zama kofa. Ki shirya”.

Ammi ta rike kanta tana kururuwa. A wannan halin Hajiya babba ta shigo ɗakin fuskarta ciki da murmushin mugunta, idonta na ɗauki da wani haske mara ƙyan gani.

Sai dai da ta shigo komai ya koma daidai inuwar da Ammi ta ke gani ta ɓace, komai ya dawo normal.

Ammi ta zube ƙasa tana kuka tana faɗin:
“Wallahi fatima Allah bazai taɓa barin ku ba“.

Hajia babba ta ɗurƙusa kusa da ita, zuciyarta ciki da murna.

“ki kwantar da hankalinki Lubna wannan ne na biyun bayyanar ki zuwa ga *ƙaddararki* kin zama cikakkiyar hadaya“.

Ta furta kalmomin cikin nishaɗi tana dariya ta fita daga ɗakin wani ɓangare daga cikin gidan ta nufa gurin shiru baka jin kumai sai kukan tsuntsaye.

Ƙasar gurin ta girgiza tamkar ana buɗe wani ɓoye-ɓoyen wuri. Ta durƙusa ƙasa ta zaru wata kwalba wadda ta ke da wani jajayen ruwa kamar jini ta ɗan ɗiga karun farko a ƙasa, tana furta wasu kalmomi da ban fahimta ba.

Nan take ƙasar gurin ta tsage kamar rame daga ciki wani hayaƙe ya fito da ƙananan murya masu kuka.

Muryar da ba ta da fuska ta bayyana daga cikin ramin:
*“fatimaaa…(Hajia babba) lokaci ya kusa. Hadayar ki tana shirye, amma sai kin cika wasu sharuɗɗanmu. Jinin yarinyar zai buɗe mana ƙofa“.*

Hajiya babba ta sunkuyar da kanta cikin nuna tsantsar biyayya na ƙarya.

“na shirya Lubna zata zamu cikakkiyar sadaka a gare ku. *Amma ku tabbatar da dukiyar da nake nema na mallake ta da ɗaukaka su tabbata a hannuna.”*

Sai muryar ta yi dariya mai sanyi, wadda ta saka jikin Hajiya babba rawa.
“zaa tabbatar amma dole sai kin ƙawar da matsalolin da suke tunkaro ki“.

Da sauri ta rufe ramin zuciyarta na harbawa sai ta koma cikin gida tana shirya muguwar hanya.

Tana shiga bedroom ta ɗauki phone ɗinta da ke kan bed ta yi dailng wata number bugu goda ta ɗauka:
“hello Hajia babba. “yawwa Ramlat ki yi sauri ki gayawa Yasmeen ta haɗa kayanta ta zo gube familyn SALAHUDDEEN RANO Rehman ya dawo “.

Yasmeen da ke kwance kan ƙafafun Hajia Ramlat sai shaɓa ta ke zubawa ta ji maganar da Hajia babba ta faɗa ai kamar wadda aka yewa albishir da gidan aljanna ta zabura ta miƙe ta buga uban tsalle tana ihun murna.

* ZYSHA *

Ta fiya ta ke amma sam zuciyarta babu nutsuwa saboda irin abubuwan da ta gani darin jiya.

Daidai ta ƙarasa part ɗin chef Rehman a hankali ta buɗe door ɗin parlour bakinta ɗauki da sallama sai ta tarar da shi a zauni kan kujira yana aiki a laptop gashin kansa ya zubu har wajen wuyansa idonsa kuwa sun cika da irin ƙyalli mai ɗaukar hankali.

Zysha ta ɗan yi shiru na ɗan wani lokaci zuciyarta na harbawa ta ajiye tray ɗin a saman ɗ’ dining area.

Rihman ya ɗago a hankali idunsa suka sauka a kanta. Ya jefa mata wani mugun kallon da yasa jikin ta ya ɗau rawa.

Sai ya kawar da kallon sa daga gareta ya mayar kan aikin da ya ke a hankali kamar wanda ya ke magana da kansa:
“gidan ku ba a koya miki gaishe da manya ba“.

Harga Allah ko kaɗan bata ji maganar sa. Ya saki ɗago shayyun eyes ɗinsa ya wasa mata yana jan tsaki ya daka mata tsawar da ba ita ba har Ashraf da ya ke shigowa yanzu sai da ya firgita.

Ai kawai sai ta fashe da kuka dukkan ilahirin jikinta ya ɗauki rawa. Rihman ya yi saurin tushi kunninsa yana jin mugun ɓacin rai dan ya tsani ƙara ko ya ya ne. Ya ja dugun tsaki ya ɗauki laptop ɗinsa ya bar parlourn.

Da sauri Ashraf ya ƙarasu gurinta zai yi magana sai idansa Ya sauka kan goshinta da ya kumbura gurin ya yi jaa sosai kasancewar ta farar fata.

“subhanallah Zysha me ya same ki? Yay maganar yana ƙuƙarin kai hannunsa kan goshin. Cak kukanta tsaya ta fara ja da baya.

Ashraf ya murmusa dan tasu ta bashi dariya sai kwai ya girgiza kansa shi ba da wata manufa yay hakan ba. Sai ya sake sakin murmushin da ba ta fahimta ba.

“na gode Zysha da tunatarwa n yi hakan ne ba da wata manufa ba na ɗauke ki ne a matsayin ƙanwata ba ƴar aiki ba sorry kin ji?”

Yay maganar yana hade hannayinsa alamar ban haƙuri wata irin kunya ce ta kamata ta yi saurin girgiza:
“A’a ba bu komai ka yi haƙuri yaya Ashraf. Tai maganar cikin sanyin murya….

*Masarautar Egypt*

Mamie ta kwanta gyefin gadun afsana, idonta sun kumbura da kuka da rashin bacci.
Papa kuwa ya zauna kan kujerar da ke gyefin gadun, yana rike da charbi yana maimaita.
“astaghfirullah, La ilaha illa Allah“. Ba tari da tsayawa ba.

Afsana ta fara motse a hankali. Ta buɗe idanunta waɗanda suka koma yana yinsu na halitta, amma fuskarta ta nuna rauni sosai.

Ta dubi mamie da ta tafi tunanin duniya ƙasa-ƙasa muryarta bata fita sosai:

“mamie ki taimaka min in tashi jikina ciyu ya ki min. Mamie tamkar a mafarki haka ta ji maganar afsana da ƙarfi kamar ba dare ba dan kusan karfe 2:2 na dare.

“afsana…Afsana! My baby, kin tashi da gaske ke ce!?.

Cikin ruɗewa ta ke tambar ta papa ma ya ƙarasu da rawar jiki:
*“soweet… Sweetheart ke ce?“.* Shiru kawai afsana ta yi sai sauki numfashi ta ke mamie ta rungume ta da ƙarfi tana sakin marayan kuka papa kuwa sai fadin.
“Alhamdulillah“ ya ke.

Da siririyar muryarta da bata fita sosai ta ce:
“mamie papa me nine ku ke kuka “.

Da sauri mamie ta guge hawayenta tai murmushin da yafi kuka ciyu.
“A’a afsana ki daina magana nasan yanzu kina jin yunwa bari na haɗa miki Black tea“.

Tai maganar tana nufar kitchen. Ba a wani ɓata lokaci ba ta shigo hannunta ɗauki da ɗan ƙaramin cup ta zauna kusa da afsana ta bata a baki Kaɗan ta sha ta ɗauke kanta mamie ta shafa bakin gashinta. Papa ya ce:

“Sweetheart ki ƙara ko kaɗan ne zaki ji ƙarfin jikin ki”.
Afsana ta girgiza kanta alamar ta ƙushi basu wani takura mata ba mamie ta mayar da cup kitchen ko da ta dawo afsana ta yi barce.

Mamei ta kalli papa da alamun tambaya ya ce mata ta yi bacci sai, ta sauki ajiyar zuciya ta kwanta gyefinta tana kallonta kamar yau ta fara ganinta. Papa ma ya kwanta ɗaya ɓangaren suka sakata tsakiya.

Afsana lokacin da bacci ya ɗauki ke ta wani irin ƙaƙƙarfan mafarki ya lulluɓe ta.
Chapter 12 · 0% Book details