← Book details Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki Local reading mode
READING PART 15 OF 31

Sashe 15

Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki · about 8 min read

Rehman bai ma kalli kowa ba ya zauna kusa da Ammi yana sumbatar hannunta Zysha kuwa ta ɗan ja baya cikin sanyin jiki, zuciyarta ta buga da sauri, tana jin wani irin farin-ciki da tsoro lokaci guda.

Ashraf ya jingina da kujera yana kallon Zysha da wani irin kallo.

Shiru ya ratsa parlourn sai kukan spoon da plate kwai ake ji.

Chef Rehman sai dannar waya ya ke ya ji kamar ana kallonsa a hankali ya ɗago sai ya ƙanƙance ido cikin ɓacin rai idonsa ya sauka kan Yasmeen da ke masa kallon kurilla.

Yasmeen ta ji kamar a zuciyarta an zuba mata wuta. Rehman ya ja tsaki ya miƙe tsiya, ya tura kujerarsa da ƙarin tsiya ya bar parlourn da sauri.

Yasmeen ta tsaya tana bin bayansa da kallo kamar zata bishi, amma sai ta tsaya cak ta juya ta dubi Zysha da ke tsaye gyefe a makore.

Sai ta ja tsaki ta bar dining Hajiya baba ta bi bayan ta suma su Abdul duk suka bar dining, su Hamdiya kam tun fitowar chef Rehman suka zame jiki suka bar gurin.ya rage daga Ammi sai Ashraf Hajia ƙarama Zysha.

Cikin damuwa Ammi ta sunkuyar da kai tana hawaye Ashraf ya matso kusa da ita shima fuskarsa ta nuna damuwa.

Ba tare da ya yi magana ba ya share mata ƙwallar ya ɗebu abinci ya bata a baki yana ɗan murmusawa.

Ashraf ya share wa Ammi hawayenta cikin tausayi, ya ce da ita da muryar da ta cika da natsuwa:

“Ammi, ki kwantar da hankalinki. Ki bar komai a hannun Allah, komai zai daidaita. Don Allah kar ki bari maganar wasu ta shiga miki rai.”

Hajia ƙarama ta yi ƙoƙarin murmushi, amma zuciyarta ta cika da damuwa. Idonta ya sauka kan Zysha wadda ke tsaye gefe kamar wacce aka ɗaura da sarka. Cikin tausayi ta kira sunanta:

“Zysha, zo nan.”

Da rawar jiki ta ƙaraso, kanta ƙasa, hawayenta na taruwa a idanuwanta. Ammi ta kamo hannunta, ta zaunar da ita kusa da ita Hajia ƙarama ta ce:

“Kar ki damu, yarinya. Duk wanda Allah ya nufa da alheri, akwai jarabawa a hanyarsa. Ki yi haƙuri, ki zama mai tawakkali. Gidan nan naki ne kamar yadda nake so.”

Zysha ta ɗaga kai a hankali, ta kalli Ammi, hawayen farin ciki suka zubo. Tana so ta buɗe baki ta yi magana, amma muryarta ta tsaya cak saboda tsananin tashin hankali.

Ashraf ya ci gaba da kallonta da wani irin yanayi Zuciyarsa na tafasa.

“Wacece wannan yarinya a zahiri? Me yasa ta yi kama da wacce na taɓa gani a baya? Kuma me yasa zuciyata ke tafarfasa idan na kalleta?”

Hajia ƙarama ta gyara zama tana duban Ashraf:

“Ashraf, kai ma ka kwantar da hankalinka. Ka sani, duk mai nisan jifa ƙasa zai faɗo. Kada zuciyarka ta rikice da abin da baka tabbatar da shi ba tukuna.”

Shiru ya sake mamaye wurin. Sai sautukan zuciyoyin su suka cika dakin.

A waje kuwa, Yasmeen na tafiya cikin hanzari tana cije lebenta. Zuciyarta ta karye, ta cika da tsananin haushi da kishin da ba ta iya ɓoyewa.

“Wallahi, idan har wannan yarinya ce da nake zato, to sai na tabbatar da cewa ba zata taɓa samun farin-ciki a wannan gidan ba. Zan tona mata asiri har sai ta gudu da kanta!”

Ta furta hakan a zuciyarta tana rike da hannun kujera da ƙarfi, idonta ya cika da ƙiyayya.

”wallahi babu wanda ya isa ya rabani da kai, Rehman.ko da kuwa zan rasa raina, sai na tabbatar babu wata mace da zata mallake ka”.

Tai maganar tana huci, Hajia babba ta dafa kafaɗarta tana wani irin makirin murmushi. Sai kuma ta sake ta ta fara jagayen ɗakin idonta suka fara chanza launi zuwa ja.

”yasmeen kin san dai abin da ya kawo ki cikin gidan nan tun farkon zuwan ki kin fara ɓata mana aiki saboda rawar kanki, Rehman ba irin samarin da ki ke tunani bane. Sannan kuma iina sun ki faɗamin me ce ce alaƙarki da waccan yarinya?”.

Yasmeen ta zaro ido tana kallon yanda idon hajia babban ya sauya lokaci guda:
”ni bana da alaƙa da ita kwai dai nasu na ruɗe ne, sabo wallahi tana min kama da ƴar aikin gidan mu”.

A can part ɗin chef Rehman kuwa, yana ta yawo sama da ƙasa. Zuciyarsa ciki da haushi da ɓacin rai kamar gangar rawa. Ya dafe kansa ya ce cikin zuciya:

“Na tabbata ba baƙuwa bace. Idan har hasashena gaskiya ne… to lamarin zai yi muni fiye da yadda ake zato.”

Ya tsaya cak, idonsa ya ƙanƙance, ya furta cikin tsananin ɓacin rai:

Masautar Egypt

Sheikh ya gyara muryarsa ya ce:

“… babu wanda zai iya kuɓutar da Afsana sai idan an gano asalin sirrin da aka ɓoye tun ƙarni da suka wuce…”

Wani irin shiru ya ratsa ɗakin, kowa ya zuba masa ido, zuciyoyi na bugawa da tsoro da fargaba.

Sarauniya ALISHA ta shigo ɗakin a birkice sauri, ta ce da murya mai cike da iko:
“Sheikh! Wane irin sirri ne wannan da kake nufi? Mun sha jin tatsuniyoyi, amma ka san fadar nan ba ta yi wasa da jita-jita. Ka fadi gaskiya ko kuma ka fuskanci hukunci.”

”haƙeƙa Japheth ka kusa fuskantar hukunci daga gare ne, bayan lai fin da ubanka ya aikata ya aura maka musulma kaima ka koma musulmi. Yanzu kuma gashi ka ƙara aikata wani laifi, ka kawo Sheikh ya matsayinsa na musulmi kuma babban malami”.

Sheikh ya sunkuyar da kansa:
“Ya Sarauniya, sirrin nan ya shafi jinin masarautar. Idan ba a gano shi ba, to cikin shekara bakwai masu zuwa, za a sami ruɗani mai girma wanda ba kowa zai iya tsira daga cikinsa ba. Kuma…” ya tsaya cak, idonsa na kallon kowa.

“…wadda ke ɗauke da mafita tana nan cikin gidan nan, amma kuma tabbas zata bayyana zata zama ne mabuɗin.”

Duk su mamei suka zuba masa ido ciki da rashin fahimta suka dinga kallon juna da mamaki.

Sarauniya ALISHA kuwa dai ta ɗaga murya tana cewa:
“Wacece ko wanene wannan mabuɗin?!” koma dai waye bamasun jin komai ka tashi ku bar masarautar nan tunkafin insa a kulle ku”.

Amma kafin wani ya sake magana, aka ji wata ƙarar iska mai ƙarfi ta shigo cikin zauren, fitilun zinariya suka yi ƙararrawa kamar za su karye. Sarauniya ALISHA ta rikice ta koma kujerar, zuciyarta na harbawa da tsoro.

A gefe kuwa, Afsana wacce ake magana akanta ta yi wani irin firgigit kamar wacce aka shafa da wuta. Idonta ya sauya launi, zuciyarta na bugawa da sauri.

Sheikh ya ɗaga hannunsa sama ya ce da ƙarfi:
“Gare ta ne! Jinin da aka ɓoye ya fara bayyana. Wannan ne farkon gargadi!

Mamei ta fashe da kuka, Amma sai sarauniya ALISHA ta daka mata tsawa:
”ke ki mana shiru duk Waye ya ja wannan!? Idan ba ke ba…”

Kuyi hakuri da wannan ba yawa please share like comment masoyana

Duk wacce ta ke buƙatar document ɗin littafin KURURUWAR SHAIƊAN daga farko ta min magana ta wannan number 07062701555

KURURUWAR SHAIƊAN

✨ HAZIƘAN MARUBUTA ✨

*Book 1 free ne [2025] ️*

Masoya littafin KURURUWAR SHAIƊAN kuzo ku shaƙata da sabon update ɗin da zai saka a cikin duniyar da ba zaku so ku fita ba.
Cike da ruɗani soyayya da asiri na san babu mai so ya rasa wannan kada ku bari a baku labari… Ku ka sance cikin masu karantawa na farko

Danna nan ku shiga link
HYPERLINK "https://chat.whatsapp.com/FuTlAsg7uedBXoMKiash4h?mode=ems_copy_thttps://whatsapp.com/channel/0029Vb6QGRg6WaKl7oWkqq30" https://chat.whatsapp.com/FuTlAsg7uedBXoMKiash4h?mode=ems_copy_thttps://whatsapp.com/channel/0029Vb6QGRg6WaKl7oWkqq30

Story & writing
By

ZULFA M. TUKUR

بسم الله الرحمن الرحيم

اللهم صل على محمد…..

Page 18

Papa ya yi ƙukarin magana, amma ta dakatar da shi ta hanyar ɗaga masa hannu:
”japheth na yi rantsuwa da shikarun kakana a wannan lokacin bazan saurareka ba, dole saina ɗau mataki akan ku”.

Sarauniya ALISHA tay maganar da mugun ɓacin rai ta fice daga ɗakin. Mamei ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya, papa kuwa ya yi laƙwas duk jikinsa ya yi sanyi.

Sheikh Addurraman ya yi gyaran murya ya ce:
”YUSIF (papa Japheth) mu zamu tafi ga wannan ruwan zam-zam ne arinka bata ta na sha, amma idan za’a bata arinka karanta mata addu’o’I ciki sai abata ta sha idan da wata matsala ka kirani Allah ya kawo karshen wannan Al’amarin”.

Papa ya amsa da Ameen ya raka su har parking spot Yana godiya sosai ya koma cikin gida ya same mamei har yanzu kuka ta ke Afsana na kwance sai bacci ta ke, shima ya samu guri ya zauna ba tare da ya ce uffan ba, ya rafka uban ta gumi.

Bayan wani lokaci papa ya meƙi da ƙyar ya shiga bathroom ya yi wanka ya ɗauro alwala ya yi salla ya daɗe zauni yana addu’a, kana ya mayar da kallon sa kan mamei da ke zaune baccin wahala na neman ɗauke ta, sai ya girgiza kansa zuciyarsa ta yi wani irin rauni na tausayinta.

Haƙeƙa kowani bawa da irin ƙaddararsa tabbas su wannan ita ce tasu jarabawar. Har dare ya ye Afsana bata farka daga barci ba tunsu mamei na jiran farkawar har suma baccin ya ɗauke su.

Dare ya ye sosai, Afsana ta farka daga dugun bacci, amma wannan karon ta ji kanta a wani wuri daban. Ba ɗakin papanta bane, ba kuma ɗakin mamei ba. Ta ganta a wani fili mai duhu,duhun da bai da iyaka, sai hayaniyar tsuntsaye da kurar iska mai sanyi.

A hankali ta fara tafia,ƙafafuwanta suna shan ƙasa kamar an ɗaure su. Can gaba ta ji wata murya na kiranta cikin zurfin filin:

”Afsanaaaa… Ki taho gare ni…Ni ce uwar ki ta gaskiya… Ki bar su, ki biyo ni, domin ni kaɗai zan baki farin ciki, har ƙarshen rayuwar ki..”

Afsana zuciyarta ta fara bugawa. Ta kalli kanta a ruwan tabki kusa da ita, sai ta ga hoton wata tsohuwa mai kyawun ido amma cike da tsoro tana tsaye a bayan ta. Ta yi saurin juyawa, amma ba kowa.

Afsana ta fashe da kuka:
”ni ban sanki ba papa da mamie suna sona… Me yasa ki ke sun ki rabani da su? Ke wacece…!?”
Chapter 15 · 0% Book details