Sashe 30
Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki · about 8 min read
Ashraf ya juya gefe zuciyarsa na tafarfasa da tausayin ta, yana jin kamar a ransa shi ma yana ɗaukar zafin.
Nan take doctor ya yi mata allurar. Zysha ta saki wani irin kuka mai ƙarfi, kafin jikinta ya yi sanyi a hannun Aunty Asabe. Sai kawai ta rungume ta tana huci da wahala, idanunta suna cike da hawaye. Shiru sai ƙarar numfashin Zysha da yake fita da wahala. Jikinta ya fara rawa, hannayenta na kakkarwa cikin ɗumin gumi.
Ashraf ya riƙe hannunta da tashin hankali:
“Doctor! Me ke faruwa da ita haka? Ba dai illa ba ta jure allura bane?”
Doctor ya matsa kusa, yana duba zuciyarta da idanuwanta da suka fara lumshewa. Ya ce cikin nutsuwa:
“Ba komai bane. Jikinta kawai ya karɓi magani ne da ƙarfi saboda damuwarta da tsoro. Amma za ta huta. Ku kwantar da hankalinku.”
Aunty Asabe ta share hawayenta, ta zauna kusa da ita tana shafa kanta.
Zysha ta yi wani irin numfashi mai nauyi, ta lumshe idanu bacci ya ɗauke ta, su Ashraf suka sauki ajiyar zuciya aunty asabe ta ce:
“ Alhamdulillah, ta yi barce mubarta ta huta”.
Ashraf ya kaɗa kansa ya ce:
“hakane mubarta ta yi barcen” doctor ya bawa Ashraf takardar maganin da za’a siya mata, ya musu sallama, su Aunty Asabe suka bar ɗakin. An ɗan ɗauki lokaci kafin Zysha ta farka. Da ta buɗe idanu sai ta ji jikinta ya yi sauƙi kaɗan daga zazzabin da ya daure ta. Ta tashi a hankali ta shiga Bathroom, ta yi wanka da ruwa mai ɗumi. Bayan ta fito ta gabatar da sallah cikin nutsuwa, hawaye na zubo mata ba tare da ta sani ba.
Da ta idar, sai ta ji cikinta na kuka da ƙarfi – alamar yunwa. Ta fito daga ɗakin nata cikin sanyin jiki, ta nufi parlour.
A can kuwa, ta tarar da Hajiya Babba da Yasmeen suna hira suna dariya. Sai ta sunne kai ƙasa, suka hangota, sai Hajiya Babba ta daka mata tsawa:
“Ke kuma! Me kika fito nema??”
Zysha ta tsaya cak, jikinta ya yi sanyi. Bata yi ƙoƙarin cewa komai, amma muryarta ta makale.
Yasmeen ta dubeta sama da ƙasa cikin raini, ta ja tsaki ta ce:
“Ni dai ban san me yasa aka ɗauki wannan yarinyar aiki acikin gidan nan ba.”
Idanuwan Zysha suka cicciko da hawaye, amma ta daure ta mayar don kar ta nuna musu rauni.
Bayan sun gama yi mata wulakanci, sai Hajiya Babba ta juya da raini ta ce:
“Tashi ki kawo min black coffee daga kitchen. Kuma ki tabbatar kin kawo shi da tsafta, kar ki haɗa min shi da kazantarki… domin ni na san ku ‘yan aiki da kazanta kawai kuke.”
Zysha ta juya a hankali, zuciyarta kamar ta fashe.
Zysha ta nufi kitchen da ƙyar, zuciyarta a cike da hawaye da takaici. Ta ɗafa coffee ta zuba cikin kofi, ta gyara numfashinta tana mai cewa a ranta:
“Allah ka bani haƙuri… Allah ka bani ƙarfin jurewa.”
Da ta dawo parlour, ta yi ƙoƙarin ajiye kofin a gaban Hajiya Babba cikin natsuwa. Amma kafin ta kai kofin, Yasmeen ta yi wani ɗan harɗi da ƙafarta ta daki ƙafar Zysha.
Cup ɗin ya silmiyo daga hannun Zysha ya faɗi ƙasa ya tarwatse, black coffee ya watse a ƙasa.
Zysha ta tsaya a ruɗe, hawaye na ƙoƙarin zuba, amma bata ce uffan ba. Yasmeen kuwa ta maze kamar ba ita ta aikata hakan ba.
Hajiya Babba kuwa ta ɗaga murya cikin tsawa, zuciyarta cike da fushi:
“Kin fasa min kofi?! Kin sake bata min gida da kazantarki?!”
Ba tare da wata ja-in-ja ba sai ta kifa mata lafiyayyun maruka guda biyu a fuska. Ɗan ƙarfin marin ya sa jikin Zysha ya girgiza, ’yan-yatsun Hajiya Babba suka fito a fuskarta ruɗu-ruɗu, jikinta na kakkarwa, idanuwanta na zubar da hawaye.
Zysha ta tsaya cak, hawaye na bin fuskarta, zuciyarta cike da tsoro da takaici. Fuskar ta kumbura daga marukan Hajiya Babba, amma bata iya cewa uffan ba.
Hajiya Babba ta harare ta, ta ce cikin tsawa:
“Ki je ki sake kawo min wani black coffee, amma ki sani idan kika ƙara lalata min gida ko ki sake zubar da shi – sai na nuna miki waye ni! Kuma kafin ki dawo, ki tabbatar kin share gurin da kika bata yanzu.”
Kalmar ta ƙare kamar wuka mai kaifi a kunnuwan Zysha.
Da ƙyar ta tattara jikinta, tana ji kamar ƙafafunta sun yi nauyi. Ta ɗauki ragowar ƙarfinta ta juya zuwa kitchen, idanuwanta na zubar da hawaye masu zafi.
A ranta kuwa, tsanar Hajiya Babba ta yi mata ƙarfi fiye da zafin marin da ta sha.
Zysha ta goge hawayenta da bayan hannu, ta sake shiga kitchen cike da azaba da takaici. Hannayenta suna rawa, amma duk da haka ta dafa sabon black coffee kamar yadda Hajiya Babba ta umarta.
Da ta fito, sai ta taka a hankali, ta ajiye glass ɗin a kan centre table, zuciyarta na dukan uku-uku.
Hajiya Babba ta harare ta sannan ta ɗauki glass ɗin, ta sha coffee
Fuskar Hajiya Babba ta sauya! Hannunta ya fara karkarwa, sai ta rike cikinta da ƙarfi.
“Wayyo Allah na! Cikina… cikina yana ƙonewa!!”
Kafin su gane me ke faruwa, ta fara tari da ƙarfi, ruwan coffee ɗin da ta sha na zubewa daga bakin ta.
Yasmeen ta tashi da razana:
“Hajiya Babba! Subhanallah, me ke faruwa haka?”
Zysha kuwa ta tsaya a gefe, jikinta na rawa, idanunta na kallon ikon Allah. Zuciyarta na harbawa.
Sai parlourn ya cika da rudani, yayin da Hajiya Babba ta fara birgima a kasa, tana kururuwa cikin azaba.
Ta ɗaga hannayenta tana ƙoƙarin riƙe wuya, amma wani tarko mai ƙarfin gaske ya rufe ta gaba ɗaya.
Sai kawai jini ya fara tsiyaya daga hancinta da bakinta, yana zuba kamar an kunna famfo. Idanunta suka cika da firgici, tana birgima a ƙasa tana ƙoƙarin shaƙar iska.
Zysha ta tsaya cak a wurin, zuciyarta na dukan uku-uku, jikinta na karkarwa. Bata taɓa ganin irin wannan tashin hankali ba.
Yasmeen ta tsaya a gefe tana kallo da tsoro, kafin ta ruga kusa da ita tana girgiza ta:
“Hajiya Babba!! Ki tashi ki ce min ba haka bane!! Wayyo Allah na!”
Sai kawai numfashin Hajiya Babba ya tsaya cak. Hannayenta suka sulale gefe, idanunta suka zuba waje, suka kafe tamkar an ɗaure su da sarka.
Shiru ya rufe falon.
Zysha ta rungume jikinta tana rawar sanyi, idanunta sun cika da hawaye.
Amma Yasmeen ta fashe da ihun da ya cika duk gidan:
“Wayyo jama’a!!! Ta kashe ta!!! Hajiya babba mutane, ta mutu!! Ta mutu a gabana!!!”
Tana ƙwalla uban ƙara tana riƙe da gawar, zuciyarta na bugawa da tsoro, tamkar ita ce ta aikata.
Zysha kuwa ta durƙusa a gefe, zuciyarta tana wani irin ruɗe
Cikin gaggawa, ihun Yasmeen ya ratsa ko’ina cikin gidan.
Hajiya Ƙarama ta fara isowa da sauri tana ta ambaton “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Me ya faru haka?!”
Ashraf da Abdul da Haeedar suma suka fito cikin hanzari, fuskokinsu cike da tsananin tashin hankali.
Ƴan aikin gidan — Aunty Asabe, Hamdiya, Rabi, Meena da Maryam — suka ruga falon, kowacce tana neman jin me ke faruwa.
Suna isowa suka tsaya cak!
Idanunsu suka sauka kan Hajiya Babba da ke kwance ƙasa, jikinta sanye da jini daga hanci da baki, idanunta kafe a waje, babu numfashi.
Yasmeen kuwa tana birgima a ƙasa tana riƙe da hannunta tana ihu:
“Wayyo Allah na!!! Ashe ta mutu!! Ta!!Hajiya Babbaaaa!!”
Falon ya cika da ihu da ruɗani.
Zysha kuwa tana tsaye gefe jikinta na karkarwa, idanunta kumbure da hawaye, zuciyarta na ta ambaton “Subhanallah… wannan kuwa wane irin hali ne?!”
Ashraf ya ruga da sauri ya jijjiga Hajiya Babba yana ƙoƙarin gano numfashinta, amma shiru! Abdul da Haeedar suka tsaya kallon juna cike da firgici.
Aunty Asabe ta dafe ƙirjinta tana salati.
Dakin ya koma rikiciwa, ba a iya gane mai gaskiya da wanda ba shi ba.
Ashraf ya durƙusa kusa da Hajiya Babba yana jijjigata, amma babu alamar rai. Numfashinsa ya ɗauke, zuciyarsa ta tsaya cak. Ya ɗaga kansa cikin rawar murya:
“Subhanallah! Me ya same ta haka?! Wa ya yi mata haka?!”
Kafin wani ya ce komai, Yasmeen ta ɗaga hannunta da sauri, idanunta cike da hawaye da tsananin firgici. Ta nuna da yatsanta tana ƙwalla ihu:
“Wallahi! Gatanan! Itace ta kasheta!! ZYSHAAAA ce!!!”
Gaba ɗaya falon ya ɗauki shiru na ɗan lokaci. Kowa ya zuba wa Zysha ido da mamaki.
Zysha kuwa, idanunta suka ciko da hawaye, jikinta ya daina motsi, zuciyarta ta tsaya cak! Sai kawai ta furzar da numfashi mai nauyi, ta faɗi ƙasa sumammiya.
“ ZYSHAAA!!!” Ashraf ya ruga da sauri ya durƙusa ya rungumeta, yana jijjigata da tashin hankali.
“Ki tashi mana, don Allah ki tashi! Ki bude idanuwanki, Zysha!!”
A gefe kuwa, Hajiya Ƙarama ta ruga gadan-gadan ta finciki Yasmeen da ƙarfi, ta shaketa da hannu tana huci da fushi:
“Karya kike! Wallahi ƙarya kike!!! Zysha ba zata iya kashewa ba! Ku tsun-tsun ba zata iya kashe Hajiya Babba ba!”
Yasmeen ta fara fizge-fizge cikin tsananin firgici, idanunta suka firfito kamar zasu fado, ta na ƙwalla ihu:
“Wayyo Allah na! Za ta kashe ni! Ku ce ta sake ni! Wallahi gaskiya nake fada, itace!!”
Abdul da Aunty Asabe suka ruga cikin gaggawa suka finciko Hajiya Ƙarama daga kanta suna rokonta:
“Don Allah ki kyale ta, Hajiya! Kada ayi gawa biyu a cikin yini ɗaya!”
Falon ya koma wani irin rikici na ihu, kuka da salati. Ashraf yana rike da Zysha cikin hawaye, Yasmeen tana ihu tana neman taimako, Hajiya Ƙarama tana huci kamar maciji, sauran kuwa ba su san inda za su tsaya ba.
A gefe guda, Chef Rahman na tsaye ne kan bene, hannunsa a harde a kirji, idanunsa a zare yana kallo duk abin da ke faruwa, Fuskarshi a haɗe kamar ɓakin hadari.
A ƙasa kuwa, Ashraf har yanzu yana jijjiga Zysha tana kwance a jikinsa. Cikin gaggawa, sai ta fara motsi. Numfashinta ya fara nauyi, jikinta na rawa. Ta buɗe idonta da ƙyar, sannan ta fara sambatu da murya mai sosa rai:
“Eh… eh… Ni na kashe ta… Wallahi ni na kashe ta… Ni ce na kashe Hajiya Babba…”