← Book details Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki Local reading mode
READING PART 13 OF 31

Sashe 13

Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki · about 8 min read

Ta tsinci kanta a cikin wani guri mai duhu, irin wanda ba a san iyakarsa ba. Gaba daya ba bu wani haske saina ɗan kaɗan na wani ƴar ƙamar ƙyanɗir da ke rawa a tsakiyar filin.

Afsana sai ta matso kusa zuciyarta na tsinkewa. Sai taga wata yarinya tsaye a ɗaya ɓangaren na duhun, tana kuka da hawaye, jikinta yana rawa.

Afsana ta furta cikin fargaba:
*“ke wacece… Ki?Me ya kawo ki a wannan duhun!?“.*

Amma kafin ta gama tambar sai wani hazo ya lulluɓe filin gyandir ɗin ya mutu da kanta, sai kawai ta ji muryar yarinyar ta ratsa filin zuciyarta ta yi wani irin bugu kamar zata fasu ƙirjinta ta fito.

Wallahi wannan sabon update ɗin da ya sauka… Idan baka karanta shi ba, kai ka rasa labarin da kwayenka za su taɓa yi maka ba’a da shi
KURURUWAR SHAIƊAN

*Book 1 free ne [2025] novel ️*

Masoya littafin KURURUWAR SHAIƊAN kuzo ku shaƙata da sabon update ɗin da zai saka ku acikin duniyar da zaku so ku fita ba.
Cike da ruɗani soyayya da asiri na san babu mai so ya rasa wannan kada ku bari a baku labari…ku kasance cikin masu karantawa na farko

Danna nan ku shiga link
HYPERLINK "https://chat.whatsapp.com/FuTlAsg7uedBXoMKiash4h?mode=ems_copy_thttps://whatsapp.com/channel/0029Vb6QGRg6WaKl7oWkqq30" https://chat.whatsapp.com/FuTlAsg7uedBXoMKiash4h?mode=ems_copy_thttps://whatsapp.com/channel/0029Vb6QGRg6WaKl7oWkqq30

Story & writing
By
ZULFA M. TUKUR

بسم الله الرحمن الرحيم

اللهم صل على محمد....

Page 16

Yarinyar ta ɗago kanta a hankali, fuskarta ta bayyana kamar anyi kwafin Afsana amma idonta sunyi jajaye, bakinta yana zubar da ɗan jini.

Muryarta ta fito kaɗan kamar daga ƙasa:
“ni… Sunana ZUHURA“.

Afsana ta ja baya da tsoro.
“zuhura? Ni ban san ki ba!“

Zuhura ta yi murmushi mai susa rai, sannan ta nuna hannunta ga wani gini mai kama da gida mai duhu.
“za ki san ni, saboda sirrin gidan ku na cikin jikina sirrin jikina yana cikin zuciyarki“.

Kafin Afsana ta fahimci abinda ta ke nufi sai ta ji wani ƙara mai ban tsoro, kamar kururuwar maci daga nesa, tana ƙaratowa da sauri. Dukan duhun ya motsa, ƙasa ta tsage, wani hazo baƙi ya taso ya lullɓe su dukan su.

Afsana ta yi ƙuƙarin gudu, amma ƙafafuwanta sun maƙale a ƙasa. Ta yi ihu cikin tsoro:
“wayyo Allah naaa…!“

Nan take ta farka daga mafarkin da ihu, duk jikinta ya jiƙe da zufa. Tana kallon sama, tana daga rawar jiki. Idonta sun cika da hawaye, zuciyarta na bugawa da ƙarfi.

A rikice mamie ta shigo ɗakin hannunta ɗauki da ƙaramin tray ta ajiye shi a ƙasan carpet ta haura saman bed ɗin ta rungume ta. Afsana ta fashe da kuka a rude mamie take tambayarta.
“baby me faru ki ke kuka…¡? Ko wani abin tsoro ki ka gani…!?“.

Afsana ta sake fashewa da kuka jikinta ya ɗaukI ƙarƙarwa haƙwaranta na sama da ƙasa na haɗewa. Mamie ta fashe da kukan tausayen ɗiyarta:
“inna’lillahi wa’innah ilaihi raji’un… Afsana baby kina jina? Don Allah ki dawo hayyacin ki…!“

Mamie tai maganar tana ɗan motsa kumatunta Afsana ta ja wani dugun numfashi idonta ya yi jaa sosai. Mamie ta ƙara rungumeta sosai tana kuka.

Aka turo ƙofar ɗakin papa ne da wasu manyan mutane suna sanye da farar jallabiya da hirami kamar suka fito asalin larabawa.

Zuciyar papa ta yi wani irin salle da sassarfa ya ƙarasu yana tambar mamie me ke faruwa. Sai kawai mamie ta fashe da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.

Papa ya tsaya tsaye yana rawar jiki, jikinsa na kyarma. Afsana ta fara ihu kamar za a tsaga ƙirjinta, tana jijjiga gado. Idonta na chanzawa daga ja zuwa baƙi.

Malamai biyu da suka shigo suka tsaya suna karanto addu’o’I da ƙarfi.
Ɗaya daga cikin su ya ɗaga hannunsa sama:
“ya Allah mai iko da komai ka sauƙaƙa mana wannan lamarin“.

Afsana ta yi ihu mai tsuma zuciya, tana jijjiga jiki kamar ana ɗaura mata wuta. Sai wata halitta mai girman gaske ta bayyana saman gadon tana dariya mai ban tsoro.

“ina gaya muku wannan yarinyar ba ta ku bace kun ƙi ganewa saina hallakata da gaba ɗaya abin da ku ka haifa“.

Malamin ya ja baya baya da tsoro, yana kallo idonsa a firfice.
Papa kuwa ya kasa tsayawa ya duƙusa ƙasa yana kuka da hawaye zuciyarsa na so ta buga.

Malam na biyu ya bude murya da ƙarfi ya na karanta:

“A’uzubillah minash shaiɗanir rajim… Bissimillahir rahamanir rahim…“

Kalmomin na fita daga bakinsa muguwar halittar nan tay dariya mai tsuma zuciya. Idon Afsana suka ƙara baki sosai, jikinta ya fara jujjuyawa kamar tana shin karya ƙasusuwan jikinta.

Mamie ta rike hanunta tana kuka sosai:
“ya Allah ka kare min ɗiyata kar ka barta a hannun wannan shaidaniyar“.

Halittar nan ta yi dariya:

“Afsana! Ke ce jinin da ya rage. Kin kasance tsatson da ya hadu tsakanin Musulma da
Sarauta. Wannan haɗin shi zai rusa duk wani tsafi idan na barki. Amma ba zan bari haka ta faru ba! Zaki koma ga abin da ya dace da ke“.

Papa ya meƙi tsayi da ƙarfi, jikinsa na ruwa, ya daka mata tsawa:
“leave her alone!! Shi is my daughter, and I won’t let you harm her“.

Amma halittar ta yi dariya mai firgitarwa, tana kallon Afsana da ke kwance tana numfashi.
*“kai ka manta, Japheth wannan jinin nata ba ɗaya ba ne. Ita ba cikakkiyar ƴar masarautar Egypt bace, jinin muslma ke gudana a jikinta…kuma wannan shi ne laifin ubanka“.*

Da wannan kalaman halittar ta fara chanzawa zuwa wata halittar mai mutum da jini da ƙaho, idonta na walƙiya da ja ba ƙyan gani.

Su papa suka fasa ihu suna rungume juna shi da mamie ɗaya daga cikin malaman nan ya hade wasu irin yawu masu wuyar hucewa a maƙugaro ya ji cikinsa ya murɗa sai ya saki futsari a wando jikinsa na ƙarƙarwa.

Ɗaya malamin kuma ya fara karatun Alqur’ani cikin suratul jinni da ƙarfi.
Nan take fitilun ɗakin suka yi walƙiya gilashi ya fashe.

“aahhh!! Wannan ƙarfi… wannan ƙarfi yana ƙunani!“

Karatu ya ci gaba. Muryar Sheikh Addurraman tana ƙarfi kamar ana kaɗa ƙararrawa.

Ya ƙara ɗauri tsohuwa Lamiya da ayoyin Alkur’ani Afsana ta fara ƙarƙarwa, jikinta ya ɗaukar rawa mai ban tsoro, idonta ya koma baƙi hannayinta suka fara ƙarkacewa kamar suna so su fashe.

Aljana Lamiya ta fara dariya mai ban tsoro:
“sheihk Addurraman kar ka kus kura ka shiga cikin wannan lamari don ba kada wata alaƙa da masarauta ka gani idan kace zaka ƙuna ni to tari da Afsana zamu mutu!“.

Sheikh Addurraman bai saurare ta ba ya cigaba.
“la hawla wa la quwwata illa billah! Ki shaiɗaniya ke ba mai iko ba ce Allah ne mai iko!p ki fita daga jikinta domin Allah bai halicce ki domin zaluntar wannan yarinyar ba!“

Karatun ya tsananta.
Afsana ta faɗi daga kan gado, tana ihu mai taɓa zuciya.
Sai wani baƙin hayaƙe ya fara fita daga bakinta yana zagayi cikin ɗakin.

Mamie ta ƙara rungume papa kamar zasu koma mutum ɗaya.

Sheikh Addurraman ya ƙara ɗaga muryar yana karatu:

“wa qul jaa al-haqqu wa zahaqqal-baatilu… innal baatilu kana zahoooqa…“

Sai hayaƙin ya yi ƙara kamar ana ƙuna shi, kuma inuwa mai kama da maci tana kurma ihu:
“zan dawo ku baza ku rabani da ita ba har abada tawa ce! Tun kafin tazo duniya!“.

Sheikh ya ci gaba da katun qur’ani har sai da inuwar nan ta ɓace ɓatt. Afsana ta yi kwanci laƙwas Sheikh ya sharci gumi ya ce da muryar gajiya:
“na kori wannan shaiɗaniyar na ɗan wani lokaci. Amma ta yi rantsuwa sai ta dawo wannan yarinyar tana bukatar kulawa da addu’a kullum ku rinka mata sallah da karatun Alqur’ani, da istghfari, idan ku ka yi sakaci zata iya dawowa cikin ƙanƙanin lokaci“.

Papa ya ruga ya rike hannunta yana kuka:
“sweetheart ki bude ido don Allah karki barni“.

Wani irin numfashi Afsana ta sauki ta saki wata duguwar ƙara sai ta buɗe idonta da ƙyar amma ba irin na da ba yanzu sun koma normal.

Da ƙarfi mamie ta ce“Alhamdulillah Afsana ta dawo dai sai ta rungume tana sakin kukan farin-ciki papa ma ya shari hawa yinsa yana godiya ga Allah.

Shiei ya dube su da fuskar damuwa ya ce:
“Allah shi ne abin godiya, amma ku sani wannan al’amarin ba mai ƙarewa a nan kusa bani. Wannan yarinya ta shiga babban haɗari. Sai dai ku dage da addu’a da neman kariya, saboda wannan ba ƙaramar shaiɗanir bace. Mai alaƙa da zuriyar ku tun shekaru da yawa da suka huci“.

Papa da mamie suka suka zaro ido suna kallonsa cikin firgice.

“zuriyar mu? Me ka ke nufi Sheikh?“ papa ya tambaya cikin rawar murya.

Sheikh ya gyara muryarsa ya ce:
“babu wanda zai iya kuɓutar da Afsana sai idan an gano asalin sirrin wannan masarautar da aka ɓuye tun ƙarni da suka wuce…“

*NIGERIA*

FAMILYN SALAHUDDEEN RANO a yau sun cika da farin-ciki da samun lafiyar Ammi duk da cewa bata iya magana sai dai ta bi kowa da ido Zysha ma ta yi murna da samun lafiyarta saɓanin su Hamdiya.

Dari na yi Gaba ɗayan su sun haɗu a dining area harda chef Rehman da baya dining tari da su Ashraf kuwa ya fi kowa murna sai nan nan take da ita jiyake tamkar a mafarki ya ke.

Ɓangaren Zysha

Zysha ta fita garden gidan ta zauna a kujera da ke kusa da wata flowers. Wannan guri ne kaɗai da ta ke samun natsuwa.

Ta ɗaga kanta sama, ta ce a ranta:
“ya Allah ka bani hakuri da juriya zama a wannan gidan“ hawayen ta ya zubu, amma ta yi sauri ta share.

Sai kuma ta yi murmushi tunawa chef Rehman dazu da safe lokacin da ya daka mata tsawa ya ja tsaki ya shige bedroom. Sai kuma ta tabe baki.

“ mutum sai bakin hali Allah wannan yallaɓai Rehman ya fiye tsawa, kowa idan ka kalli fuskarsa da murmushi amma shi ban taɓa ganin haka a fuskarsa ba“.

Haka dai ta ci gaba da tunanin ta har bacci ya suma ɗaukar ta, ƙwatsam haskin garden ya ɗauki gurin ya yi duhu a gigice Zysha ta miƙe tsaye jikinta na rawa.
Chapter 13 · 0% Book details