Sashe 16
Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki · about 8 min read
A nan wata murya ta sake bayyana:
“saboda ke ɗin tawa ce ke gaba ɗaya… Jinin ki rabin ɗan Adam ne, rabin kuwa na mu ne -- *zuciyar asirai!* Za ki zama sarauniya a duniyar mu, idan kika yarda ki ba su zuciyarki!”
Afsana ta faɗi ƙasa tana ihu, amma babu wanda ya ji ta.
Ɓangaren Zysha – Nigeria
Zysha na fitowa daga kitchen, tray a hannunta, zuciyarta na harbawa da sauri kamar zata fito daga kirjinta. Ta nufi part ɗin chef Rehman parlour shiru ba kowa, sai ta sauki ajiyar zuciya Bata yi zato ba, sai ta ji wani irin kallo mai nauyi ya sauka kanta tamkar nauyin dutse.
A hankali ta ɗago… idonta ya haɗu da idanun Chef Rehman da ya fito cikin shirin fita.
Green eyes ɗinsa suka cika da walƙiya mai haɗa jarumta da izza. Wannan kallo ya saka numfashinta ya tsaya cak, tamkar duk jinin jikinta ya tsaya gudu. Ta yi saurin runtse ido, amma hoton fuskarsa ya ci gaba da bayyana a cikin zuciyarta.
Tray ɗin da ke hannunta ya yi rauni, hannayenta suna rawa. Da kyar ta daidaita shi, amma duk jikinta ya yi sanyi. Sai ta fara tunanin goduwa kawai dan cetun kanta, a hankali ta fara baya² tray hannunta na rawa.
Chef Rehman ya matsa kusa, duk matakin da yake yi yana ji kamar ana girgiza dakin gaba ɗaya. Ya tsaya gabanta, ya ɗan kankance ido cikin ɓacin rai da natsuwa lokaci guda, sannan ya furta da murya mai kauri amma mai sanyi:
“ waye ya bakin ikon shigomin parlour!?Me yasa kuma kike ƙuƙarin gudu idan ba laifi kike da shi ba?”
Maganar ta tsaya mata a rai kamar ƙulle, zuciyarta ta dinga bugawa da ƙarfi. Ta kasa amsa, ta kasa motsi. Sai hawayen tsoro da suka yi ƙoƙarin taruwa a idanunta.
Kafin ta yi magana, chef Rehman cikin mugun ɓacin rai ya ɓarar da tray ɗin daga hannunta cikin kwanciyar hankali abincin da ke ciki duk suka tarwatse.
Zysha tai wani irin zabura tana kurma ihu chef Rehman ya daka mata tsawa:
”wallahi idan baki rufe min ɗan iskan bakin nan ba, sai na zubar da haƙwaran da ke cikinsa”.
Zysha ta yi saurin saka hannu a baki ta toshe duk ilahirin jikinta na rawa. Ya matsa kusan fuskarta, muryarsa ta ƙara yin natsuwa amma tana da nauyi:
“Na san baki zo gidan nan don aiki kawai ba… Asirinki zai bayyana da kanki.”
Zysha ta girgiza kai da sauri, hawayenta suka fara zuba, amma jikinta ya kasa motsi. Wannan kalmar ta shiga zuciyarta tamkar wuka.
A zuciyar Rehman kuwa, wani irin abu yake tafarfasa – “Idan hasashena gaskiya ne, wannan yarinya ce ta fara buɗe ƙofar da nake ta ƙoƙarin rufewa tsawon shekaru.”
Dakin ya yi shiru. Sai zuciyoyinsu biyu ne kawai suke tafka faɗa, babu wanda ya iya fassara shi.
Tsoron Zysha da rikicewarta ya bayyana.
Tun daga gefen parlour, Yasmeen ta tsaya cak tana bin duk abin da ya faru da kallo. Idonta ya ƙanƙance, zuciyarta ta cika da wani irin haushi mai haɗe da kishi.
Ta ga yadda Rehman ya tsaya gaban Zysha, ta ga yadda idanunsa suka nutse cikin nata, kuma ta ji kalamansa duk da cewa sun fito a hankali kuma ba masu daɗe ba ne.
Numfashinta ya rikice. Hannunta ya yi sanyi, sai ta rike kujerar da take kusa tamkar zata karye.
“Wallahi…! Ni Yasmeen, ban yarda wani ya raɓi Rehman ba. Ko da kuwa ita ce yarinyar da suke kallo kamar an hura wuta a jikinta, ba zan bari ta kwace min shi ba.”
Idonta ya cicciko da ƙwallar kishi. Sai ta yi tsaki tana huci, zuciyarta cike da ruɗani.
Chef Rehman ya ɗaga yatsansa ya nuna Zysha da shi alamar gargadi, ya ja tsaki bai bi takan Yasmeen ba ya bar sashen da ɓacin rai zuciyarsa a jagule.
Yasmeen ta ɗago ido da sauri, tana kallon bayansa.
Idon Yasmeen suka cika da wuta, ta ƙaraso kusa da Zysha a hankali, ta ce cikin wata irin murya mai ɗauke da izza:
“ke… Ki daina nuna kamar baki sanni ba idan kin iya nunawa mutanin cikin gidan ke wata salihar ce, to ni Yasmeen ƴar gidan Hajia Ramlat baki isa ki raina min hankali ba..!”
A rikice Zysha ta ɗago jajayen idonta tana kallon Yasmeen:
“me kike cewa ne haka? Ni wallahi ban sanki ba ban ma taɓa…. Ya’isaaa! “ki daina raina min hankali, me kike yi a cikin wannan gidan? Kin san gidan waye ne wannan kuwa?” kuma har ki saka ƙafa ki shigo part ɗin *mijina…!”*
Yasmeen ta ja dugun numfashi tana huci, Zysha na wani irin kuka:
“wallahi ni ba wacce ki ka sani bace, ni ƴar aikin gidan nan ce kuma aikin da aka ba ni shi nake yi, don Allah ki yarda da ni”.
Yasmeen ta ƙyalƙyale da dariyar raini:
“na yarda da ke? Ke? Hahaha! Wallahi kin yi kuskure babba. Wannan gida dai nawa ne, kuma matar gidan nan, sannan ina son ki sani saina tuna asirinki… *Banza ƴar ƙwauye kawai”.*
Zysha ta ƙwalalo ido kamar zasu faɗu, zuciyarta ta buga da ƙarfi. Amma sai ta yi shiru ta kasa cewa komai, zuciyarta ciki da tsoro da ruɗani.
Yasmeen ta matsa kusa sosai har sai da ta ji numfashin Zysha a fuskarta, ta ce cikin wata irin murya:
“ki saurare ni da kyau… Kada ki kuskura ki kusanci Rehman. Idan ma shine ki ka kawoma hari, hari domin shi ba naki bane. Shi nawa ne tun kafin nasan kaina, idan kika kuskura ki nuna masa murmushi ko kallo… Saboda kina tunanin ke wata mai kyau ce, to sai na tabbatar baki sake taka ƙafar ki a wannan gidan ba”.
Sai ta watsa mata wani mugun kallo, ta juya da izza ta bar parlourn.
Zysha ta durƙusa a ƙasa tana kuka mai tsuma zuciyar mai saurari tana rawar jiki. Ta rike ƙirjinta tana jin wani abu ya tasu daga ƙasan zuciyarta.
Ta furta cikin kuka:
“wayo Allah na shiga uku, ya Allah, me yasa kullum sai na shiga tsaka mai wuta? Me yasa Daddy baka biyo mu ba? Na tabbata da yanzu muna tare cikin farin ciki kamar yadda muka saba a kullum, ban taɓa tunanin wata rana zamu rabe kamar haka ba. Sai gashi komai ya sauya ya Allah…!”
Ta furta da ƙarfi tana sakin wani kukan na tausayin rayuwar su abin tausa ya duk fuskarta ta canja ta yi wani irin jaa idan ta ya kumbura lokaci guda.
Sai ta miƙe ta share hawayenta ta fara tattara kayan abinci da chef Rehman ya ɓarar ta juya zuwa kitchen domin ajiye kayan, bayan ta ajiye ta koma ta gyara ko ina fes ta kunna turari, ta fita ta je garden gidan kamar yadda ta saba a kullum.
Ɓangaren Yasmeen
Bayan komawarta ɗaki, Yasmeen ta rufe ƙofar ta jingina da ita tana huci. Zuciyarta tana tafarfasa da wuta, tana tunanin kalaman chef Rehman da kallon da ya ke wa Zysha.
Ƙwan-ƙwasa ƙofar aka yi kamar bazata amsa sai ta ji muryar Hajia babba da sauri ta buɗe, Hajia babba ta shigo tana mata kallon tuhuma.
Sai ta sunkuyar da kanta ƙasa Hajia ta zaro wayarta ta yi dailng wata number bugu goda aka ɗaga:
“ku shirya… Ina son ku kawo min duk wani labari game da wannan yarinyar ƴar aiki Zysha. Ina son sanin komai game da ita, asalin ta, iyayenta harma abin da ya kawo ta gidannan”.
Tana gama faɗar haka ta katse wayar, ta yi murmushi mai ɗauke da mugunta idonta suka canza suna ciki da makirci.
Yasmeen ta ɗagu kai tana mamakin yanda Hajia babba ta san abin da ke ranta,
“Wallahi, Hajia… ko da kuwa sai na zubar da jini, ba zan bari Manisha ta mallake shi ba. Sai dai ni ko ita!”
Ta furta cikin zuciya tana girgiza kai da alamar sharrin da zata ɓullo da shi nan gaba.
Ɓangaren Chef Rehman
Bayan barinsa parlour kai tsaye parking spot ya nufa batari da ya kula ma aikatan gidan ba ya shiga mota ya yi mata ƙey yabar estate ɗin su da wani irin gudu, ba ɓata lokaci ya yi parking a wani madaidaicin gida duk da ba wani girma ne, da shiba sosai gidan ya yi kyau.
Dau ki da sallama a bakinsa ya shiga parlour, amma shiru ba kowa a hankali ya suma jiƴu sautin nishi, cikin turawa ya suma takawa zuwa gurin da yake jiƴu sautin.
Karaf idonsa ya sauka a kanta jini na fita ta hanci da baki, da mugun ƙarfi ya zaru Green eyes ɗinsa lukaci ɗaya suka canza launin zuwa jaa, Da takun jarumta ya yi sauri ya ƙarasa yana kiran sunanta *GRANNY*(AMOUR).
Shiru ba amsa sai nishi ta ke numfashinta na fita da ƙyar kamar tana kokawa da shi, da sauri ya saɓata a kafaɗa kamar ƴar tsana, yasa kata a abaya ya kulle, ya je ya ɓuɗe gat ɗin gidan da ƙarfi ya shiga mota ya bar gidan da wani mungun gudu kamar zai tashi sama.
Motar na yin mugun gudu kamar za ta tashi sama, zuciyarsa na dukan ganguna. Numfashin Granny yana ƙara rauni, jini na fita daga hancinta da bakinta.
“Granny! Ki yi haƙuri… ba za ki mutu ki bar ni ba, kin ji na?”
Ya furta cikin murya mai ƙarfi amma idanunsa suka cika da ɓacin rai da ya daɗe bai bari ya bayyana ba.
Ya yi parking a gaban babban asibitin wanda ba kowa ya san shi ba, asibitin Ƙofar ta buɗe da sauri, nurses biyu suka fito, suka ɗauke Granny cikin stretcher.
Rehman ya bi bayansu da hanzari, ya na rike hannun Granny cikin rawar jiki. Green eyes ɗinsa sun cigaba da walƙiya jaa, alamar ba ƙaramin tashin hankali yake ciki ba.
A ka kwantar da ita a gado, doctors suka rufa mata jinya da oxygen. Rehman ya tsaya gefe, zuciyarsa na tafarfasa.
Sai wani doctor mai farin gashi ya fito, ya kalli Rehman da mamaki:
“bawan Allah… wannan matar—ba yau aka fara samun irin wannan matsalar ba. Yanzu dai gaskiya ya kamata ka faɗa min ko wanene ita gare ka.”