← Book details Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki Local reading mode
READING PART 25 OF 31

Sashe 25

Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki · about 8 min read

Cikin halin ko in kula ya miƙe, ya ɗauko robar ruwa mai ɗan ƙaran sanyi, Kai tsaye ya zuba mata a jiki.

Zysha ta yi firgigit ta farfaɗo, jikinta duk na rawa, ta shiga kiran:
“Ummaaa! Manisha!!!”

Muryarta ta cika ɗakin cikin kuka da firgici.

Chef Rehman ya tsaya cak yana kallon ta da idanunsa masu sanyi amma masu tsananin firgitarwa. Ya ɗaga yatsa ɗaya, muryarsa ta fito da kaushi:

“Idan na kirga uku baki bar bedroom ɗina ba… wallahi saina karai-raya ki a nan ɗin.”

Zysha ta ji jikinta ya mutu da tsoro, numfashinta na kasa fita yadda ya kamata.

“Ɗaya…” ya furta da sanyi, yana ƙara matsowa kusa.

Ta ja baya da sauri tana shesheƙar kuka, jikinta na rawa kamar ganyen bishiya.

“Biyu…” ya ƙara da ɗaga muryar, idonsa ya ƙanƙance kamar zai cinye ta.

Zysha ta rarrafa har bakin ƙofa, zuciyarta na neman tsagewa saboda bugawa.

“Kada ka ce uku don Allah… don Allah…” ta rinka maimaitawa cikin rawar murya.

“Uku!” ya daka da ƙarfi har sai da ta faɗi ƙasa tana rawar jiki.

Da ƙyar ta miƙe ta ɗora hannunta kan zan kafa, ta fice da gudu daga bedroom ɗin tana kuka kamar za a sare mata kai.

Chef Rehman ya tsaya yana kallonta da idanu masu cike da raini, sai ya yi ƙwafa ya janye kansa cikin izza.
“Ƴar aiki kenan…” ya furta cikin zuciya. “Sai kin gane matsayinki.”

ƁANGAREN GIDAN HAJIYA RAMLAT

Bayan tafiyar Yasmeen, gidan ya ɗan yi shiru, sai ka ce wani abu ya ɗauke da shi. Hajiya Ramlat ta zauna a kan kujera tana juyawa a zuciyarta yadda zata tabbatar shirin su bai lalace ba.

Manisha ce ta shigo falon da tray ɗin shayi, ta ajiye a gaban Hajia Ramlat cikin yatsini fuska. Kallon banza ta watsa mata, domin ta tuna da kalaman da gayawa Yasmeen da safe.

Manisha bayan ta ajiye tray ɗin gaban Hajia Ramlat, ta tsaya gefe ba tare da ta ɗaga kai ba. Hajia Ramlat ta kalle ta daga sama har ƙasa ta yi ƙwafa, tana murza zobenta.

“Ke!” ta furta da murya mai ɗauke da izza.
“Tun da zainab ta tafi, ke ce za ki riƙa gyara bedroom ɗina da sauran abubuwan ta. Ba na so in ga wani abu ya lalace a ɗakin nan. Kuma ki sani, ke ɗin ba komai bace face yar aiki, kar ki kuskura ki manta matsayinki.”

Manisha ta ɗan matse baki. Ta ji kamar ta amsa mata, amma ta riƙe harshenta. Duk da haka idonta ya nuna ƙarfin hali.

Ta ce a hankali amma da ƙarfin zuciya:
“Na ji Hajia. Amma ki sani ban yi aikin nan domin in zama kamar baiwa ba. Aikin da aka ɗora min shi zan yi, ba kuma zan bari ki wulaƙanta ni ba saboda girman kai.”

Hajia Ramlat ta miƙe tsaye da sauri, ta ɗago idonta cikin bacin rai:
“Ke wa kika ɗauke kanki? Ƴar iska! Ni zan yi magana da ke sai ki yi min gardama? Ashe kin manta da inda na fito? Ashe baki san ni ba? Na san irin mutanenku!”

Sai ta taka a hankali ta ƙaraso inda Manisha take tsaye, ta ɗan sunkuya da fuska a kusa da fuskarta, ta ce cikin kasala amma da mugun dariya:
“Kin dai yi sa’ar zama a hannuna ne. Wallahi da na samu dama sai na nuna miki banbancin da ke tsakanin mai gida da ƙaramar yar aiki.”

Manisha ta ja numfashi ta ɗan janye baya, ta ce:
“Hajia, ban yi sa’ar zama a hannunki ba. Allah ne ya ƙaddara haka. Kuma ki sani, ko wace mace uwace, ba ta da ikon raina ‘yar aiki saboda ta fi ta kuɗi ko izza. Allah ne kawai mai ɗaukaka da ƙasƙantarwa.”

Hajia Ramlat ta fashe da dariyar raini:
“kutumar uban chan! Ke yarinya mai aiki, kina yi min huduba kenan? Wallahi sai kin gane irin uwar da kika hadu da ita. Ki jira, ba yanzu ba. Zan koya miki yadda ake girmama manya idan a gida ba’a koya miki ba.”

Ta juya da izza ta zauna kan kujera, tana jijjiga ƙafarta cikin huci.

Manisha kuwa ta ɗaga idonta sama tana furta a ranta:
“Ya Allah kai ka sani, ban tsani wannan matar saboda komai ba, face don zalunci da girman kai da take nunawa. Allah kai ne masani mai adalci.”

Daga nan ta ɗauki tray ɗin ta fita daga falon cikin natsuwa, duk da zuciyarta na cike da tsanar Hajia Ramlat.

Bayan Manisha ta fita da tray ɗin, zuciyar Hajia Ramlat ta ci gaba da tafarfasa da ƙiyayya. Ta dafe ƙirji ta ce da kanta:

“Wannan yarinya za ta fara raina ni? Wallahi sai na koya mata darasi da ba zata taɓa mantawa ba. Ba wai saboda ta yi kyau ko kuma ta iya aiki ba. Ina tsoron irin ƙarfin zuciyar ta – irin waɗannan yaran idan aka bar su sai su rikide su zama barazana ga gidanka.”

Bayan ƴan mintuna, Manisha ta dawo da ragowar kayan shayi. Kafin ta ajiye sai Hajia Ramlat ta ce:
“Ke tsaya.”

Manisha ta tsaya a tsaye, hannayenta rike da tray.

Hajia Ramlat ta kalle ta da wulaƙanci:
“Me yasa kike yawan ɗaga kai idan ana magana da ke?”

Manisha ta taɓi baki ta ce cikin izza amma da ƙarfin zuciya:
“Hajia, ba na gardama. Ina dai faɗin gaskiya. Kullum kina wulaƙanta ni kamar ba mutum ba. Amma ki sani, ni ƴar Adam ce kamar kowa. Babu komai tsakaninmu face aikin gidan nan, ki tsaya a haka, kada ki raina ni.”

Cikin ɓacin rai Hajia Ramlat ta miƙe tsaye, ta fisge tray ɗin daga hannunta ta jefa shi a ƙasa. Gilashi ya tarwatse ƙasa da ƙara!

“Ban taɓa ganin yar aiki marar kunya irin ki ba! Wallahi sai kin gane ni mace ce mai mulki a gidan nan!”

Manisha ta yi tsaye tana kallon ta, zuciyarta na harbawa. Sai ta ce da murya mai ƙarfi:
“Hajia, ki ci gaba da zalunci. Amma ki sani, Allah na kallonmu.”

Hajia Ramlat ta tsaya tana huci, tana kallon ta cikin ƙiyayya.
“Wallahi sai na kawo ƙarshen rainin wayon nan yarinyar. Idan na bari haka ya ci gaba, zata iya karya min burin da na dade ina ginawa.”

Abban Yasmeen wanda yake a falo na gaba yana sauraron wayar kasuwanci, sai ya ji muryar Hajia Ramlat cikin tsawa da hayaniya.

Ya fito da sauri, fuskar sa a ɗaure. Da ya isa ƙofar falo, sai idonsa ya sauka kan gilashin da ya tarwatse a ƙasa da kuma Hajia Ramlat da ke tsaye tana huci kamar wacce ta yi faɗa.

A gefe kuma, Manisha tana tsaye bakin ƙofa, fuskarta a tamke kamar bakin hadari.

Cikin ƙarfi Abban Yasmeen ya ce:
“Subhanallah! Me nake gani a cikin gidana haka? Me ya faru ne Ramlat?”

Hajia Ramlat ta yi saurin juyawa ta ce da sauri tana nuna Manisha:
“Ka ga yarinyar nan kuwa? Ita ce ta fara yi min gardama! Ni matar gidan nan, sai yar aiki ta fara ɗaga min murya kamar muna daidai!”

Manisha ta ɗan matsa gaba, ta ce cikin murya mai ciki da ƙarfin zuciya:
“Hajia, ki faɗi gaskiya. Na shigo kawai na kawo kayan breakfast, amma kika fara wulaƙantani, sannan kika jefar da tray a ƙasa.”

Abban Yasmeen ya kalli Manisha, ya dubi Hajia Ramlat, sannan ya daka musu tsawa:
“Ku daina wannan hayaniya a gidana! Gidan nan ba kasuwa bace! Ina da isashen matsaloli a wajen aiki, bana buƙatar rigima tsakanin mai gida da yar aiki a nan cikin gida.”

Hajia Ramlat ta yi shiru amma tana huci, ta juya ta zauna bisa kujera da izza tana cije lebenta.

Abban Yasmeen ya ɗan yi shiru sannan ya ce cikin natsuwa amma da faɗa:
“Ramlat, ki sani, ba zan taɓa lamunta wulaƙanci ga yar aiki ba. Ko da kuwa tana ƙarƙashin ki, ita ma ɗan Adam ce. Ki guji irin wannan rainin. Idan kuma ta yi kuskure, akwai hanya na gyara ba tare da hayaniya irin wannan ba.”

Hajia Ramlat ta ɗago kai da sauri, ta ce da murya mai cike da izza:
“Toh kai yanzu kana goyon bayan ta ne?”

Abban Yasmeen ya ɗauke kai cikin takaici, ya ce:
“Ni ba zan ɗauki ɓangaren kowa ba. Abin da nake so kawai shi ne zaman lafiya a cikin gida. Amma zan gargade ki Ramlat: ki rinka dafa magana da hikima, kada ki zubar da mutuncin ki saboda fushi.”

Da Abban Yasmeen ya gama faɗa, Hajia Ramlat ta daka tsalle tana ihu kamar wacce ta sha tsuntsuwar hauka:

“WALLAHI ƙarya ne!ka fara nuna min baka son ganin idona! Yar aikin nan ce kake ɗauka ka fi bani daraja?”

Sai ta durƙusa ƙasa ta kwashe da uban ashar, tana watsa musu kamar ruwan sama:
“Uban uban ku, ubanni dukansu, shegu! Wawaye! Tattabaƙa! Ai na faɗa tun farko, yarinyar nan ba rani bace sai wata asiri ce ta kawo maka a gida!”

Ta ɗaga hannu tana buge ƙirji, idonta jajur saboda kishin zuciya.

Manisha ta yi saurin zaro ido, tana kallon haukar Hajia Ramlat take, ta juya tana nufar ƙofa zata fita.

Amma kafin ta kai bakin ƙofa, Abban Yasmeen ya dakatar da ita ya juya kan Hajia Ramlat.

Abban Yasmeen ya dubeta da idanu masu zafi, ya ce cikin kashedi:
“Ramlat, ki nutsu kafin ki zubar da mutuncinki gaba ɗaya. Wallahi wannan haukan kishi naki zai zama bala’I gare ki. Ki sani ba za ki iya kore ƴar aiki daga gidan nan ba, kuma ni ba zan bari hakan ya faru ba. Idan kina ganin ba za ki iya jurewa ba, sai dai ki ɗauki shawarar da kanki, amma ni ban taɓa korar marar laifi.”

Jin wannan magana yasa Hajia Ramlat ta ɗan yi tsalle ta daka ƙafa kamar yar karamar yarinya, tana ihu tana cizon yatsa:
“Abban Yasmeen ka ci amanata! Ashe yau yar aiki ta fi ni daraja! Wallahi sai na nuna maka waye ni!”

A haukace ta shiga kitchen tana wani irin huci.

Hajia Ramlat ta fito daga kitchen da wani irin ihu, idonta jajaye kamar ta sha ruwan barkono. Hannunta riƙe da babbar wuƙar girki tana karkarwa, gashinta ya warwatse.

Ta daka tsalle ta nufi Manisha gadan-gadan tana ihu kamar wacce ta yi hauka:

“Wallahi yau sai na yanka ki! Ki bar gidan nan da gangan!”
Chapter 25 · 0% Book details