← Book details Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki Local reading mode
READING PART 2 OF 31

Sashe 2

Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki · about 8 min read

Ɗaguwa Manisha tayi taga kowa ya zubu mata ido”. ɗan kami kami ta fara tana turo baki ita tsoron ta kar ace a fili ta faɗi maganar harara umma ta jifu mata tace”. Wllh Manisha ki kiyaye ne”. kiyi sauri ki bata hakuri ko ranki ya ɓace.

A ɗaƙili Manisha ta bata hakuri tana turo baki kallon matar umma tayi tace”. Dan Allah kiyi hakuri”. Haba dai wllh ba komai nasan ai ƙuruciya ce taki damun ta so karki damu.

Harara Manisha tabi matar dashi cikin ɓacin rai aranta tace”. Lallai ma matar nan ne ce ƙuruciya ke damu?”. Zysha dake rakuɓi gife ta yi shiru ba abin da taki sai tunani ta kalla dan danan taji kwallah ta ceko mata ido.

Tafiya sosai sukayi sune basu sauka ba sai karfe 6:54 suka sauka sosai su Zysha suka jigata idanuwansu sunyi jajajir sabu da gajiyar mota ga yunwar da ta addabi cikinsu.

Ciki da rashin sanin inda zasu nufa suka sauƙu daga motar dabara ce ta faɗuwa umma kallon matar nan tayi tace”. Baiwar Allah ina zamu samu gidan haya?”. Mu baƙi ne bamu san ko ina ba A nan garin.

Murmushi matar tayi tace”. Aikowa faɗuwa tazu daidai da zama inada wani ɗan karamin gida na haya wasu ne a ciki basu daɗi da tashi daga gidan ba”. Muji sai kuga gidan idan yayi muku sai ku karɓi hayar she.

Cikin jin daɗi umma tace “. Mun gode sosai Allah ya saka da alheri ta tar mai nafif matar suka shiga basu daɗi ba suka sauka matar ta biya mai nafif kuɗinsa ƙey ɗin gidan matar ta ciro a jakar ta ta bude gidan suka shiga.

Bin gidan da kallo Manisha tayi ɗakuna ne guda uku sai ban ɗaki da Kuma kitchen sai kuma tsakar gida ta ɓuda baka”. Zatayi magana umma tayi mata wani mugun kallo shisu tayi ta zubawa sarautar Allah ido.

Yawwa balarabiya ga gidan nan ku ɗuba ku gani idan yayi muku”. E gidan yayi sosai umma ta faɗa”. Yar dariya matar tayi tace”. Saidai har,yanzu ban san sunayen ku ba.

Murmushi umma tayi tace”. Sunana suhana sai Kuma ƴaƴana Zysha da Manisha ƴan biyu ne ta faɗa tana nuna su Zysha”. Masha Allah ai kam ba sai kin faɗa ba idanuwana ma sun faɗa min tun a motar

Ne sunana Hajiya Turai gidana ya nan jikin wannan gidan “. Ne zan tafe kar na cika ku da surotu kuma ga gajiyar mota insha allah gobe zan leƙu sallama ta musu ta huce.

Kamar jira Manisha take Hajiya Turai ta tafi tace”. Wai umma a wannan kur,kukun gidan zamu zauna?”. Cikin daka tsawa umma tace”. Stop talking nonsense!”. Ko yanzu ranki yayi mugun ɓaci “. Haba dami ki kiso inji da tashin hankalin da muke ciki kuda banza yin maganar ki.

Jikin Manisha ne yayi sanyi tace”. Umma dan Allah ki yi hakuri kin ji?”. Insha Allahu bazan saki makamancin wannan ba.

Sallama aka musu wani yaro ne ya shigo hannun sa riƙi da kula gaida Umma yaron yayi ya ce”. Gashi wai inji Hajiya Turai ta ce na kawo kar ɓar kular Umma tayi”. Kace mata an gode”. Da to yaron ya amsa yayi tafiyar sa.

AMERICA

Wani katafarin parlour ne wanda ya ji, kayan furniture manya manyan sofa set purple ne tsakiyar kujirun a kwai wani haɗaɗɗin sofa table.

Zau ne yaki akan sofa mai cin mutun biyu ya ɗaura laptop akan cinyarsa sai aikin danna ta ya ke da gani kasan aiki mai matukar muhimmanci ne duba da yanda ya mai da hankali kan aikin sosai.

Sanyi yaki da farar t-shirt dap
Baƙin wandon 3 kwata wani matashin kyakkyawan saurayi ne ya kalli shi cikin harshen English ya ce”. REHMAN Ar you mad at me?”. At least listen to me.

Ya yi maganar yana marai-raice fuskarsa.

Shiru yayi ba tare da ya ɗagoba ya cigaba da aikin sa nisawa kaɗan saurayin yayi ya samu gure ya zauna yana mamakin hali irin na aminin nasa.

Yallaɓai Chef Rehman!”. Yallaɓai ɗaguwa chef Rehman yayi ya zuba musu kyawawan eye ɗin sa yayi ba tare da ya amsa ba.

Yallaɓai several soldier were killed, others Injured”. What!?”. Ya faɗa da mugun karfe yana miƙiwa tsayi cikin firgici da tashin hankali
Sojojin nan suka faɗi kasa duk jikinsu raunika ne.

Cikin mugun sauri ya hau stair kai tsaye bedroom nasa ya huce naushin bangon daki bedroom ɗin sa yayi ya ce”. A gobe nayi niyar zuwa Nijeriya amma yanzu komai ya lalace duli sai zuwa nan gaba dugun tsaki yaja tari da shigiwa bathroom dan ragiwa kansa zafi.

Shiguwa bedroom ɗin MAHEK yayi jin saukar ruwa ya tabbatar masa da ya shiga bathroom ya kusan futuwar sa ba yanzu ba tunawa da halin da sojoji suke ciki ya sashi saurin barin ɗakin.

*NIJERIA*

ASHRAF

“Brothers wllh go nan yana”. Matuƙar birgi ne sosai da ace a kasar Nijeriya yaki ai da baza asamu ƴan ta adda ba ashraf ya faɗa yana nuna musu wani vedeo na wani matashin kyakkyawan saurayi.

“E wllh kuma kasan abin da yaki bani mamaki kowa?”.shi ne ba wani wanda ya san she ko gurin da yaki da zama saidai ƴan uwansa sojoji”.

Abdul ya faɗa cikin mamaki

“Ne kun san abin da nake gani kuwa a face ɗin sa kuwa?.”A’a suka haɗa baki suka faɗa”. Wllh idon sa ya na min kama dana yaya Rehman da yanayin jikin su ashraf ya faɗa yana nuna musu.

Saurin wafce wayar haidar yayi ƙurawa vedeon ido sosai yayi yana sun ya tabbatar da abin da ashraf ya faɗa cikin mamaki ya ce”. Tabbas nema naga hakan ya faɗa tari da miƙawa ashraf phone ɗin sa.

Miƙiwa tsayi ya ce “lokacin cikin abin cen Ammi yayi ne zan ji, na bata gyaɗa masa kai kwai sukayi kwalawa shugabar yar ai kin gidan kira yayi.
KURURUWAR SHAIƊAN

*Book 1 [2025] Nobel ️*

*NA ZULFA M TUKUR*

ZUFEE BABY SHALELEN MOMMA

MY Channel link
HYPERLINK "https://whatsapp.com/channel/0029Vb6QGRg6WaKl7oWkqq30" https://whatsapp.com/channel/0029Vb6QGRg6WaKl7oWkqq30

INA GODIYA GA ALLAH DA YA BANI IKON RUBUTA MUKU WANNAN LITTAFIN MAI TAFI DA DARUSSA KALA KALA MASU ILIMANTARWAR DA KUMA NISHADAN TARWA WANNAN SHINE LITTFINA NA FARKO KAR KUBARI AYI TAFIYAR NAN BA KU

بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل على محمد وآل على محمد كما صليت على ابراهيم وعلى آل إبراهيم إنك حميد مجيد وبارك على محمد وآل على محمد إنك حميد مجيد

Page 4

“Meƙiwa tsaye Ashraf ya yi ya ce”. Lokacin cin abincen Ammi ya yi ne zan ji na bata”. Ya faɗa yana kallon tsadaddin agogon dake hannunsa.

Gyaɗa masa kai kwai sukayi”. Kwala kiran aunty asabe shugabar ƴan ai kin gidan ya yi”. Na’am yallaɓai Ashraf”.
Ga abin cin na haɗa mata kai kwai yake jira aunty asabe ta faɗa fuskarta da murmushi.

Martanin murmushi shima ya mayar mata karɓar madaidaicin farantin dake hannunta ya yi “. Sannu da ƙuƙari aunty asabe”. Murmushi kawai aunty asabe tayi sosai take jin daɗin yan da Ashraf ya ke girma mata ba kamar sauran ƴan gidan ba yana da kyakkyawar zuciya.

Hucewa Ashraf ya yi dumin kaiwa Ammi abin centa itama Aunty asabe komawa kitchen ta yi dan cigaba da abin da ke gabanta.

Da sallama ɗauki A bakinsa ya shigo bedroom ɗin Ammi fuskarsa ɗauke da ƙayataccin murmushi ya ƙarasa bakin bed ɗin ya zauna tare da daura farantin dake dau ki da lafiyayyin abinci.

“Sannu da hutawa Ammi yaya karfin jikin naki?.” Girgiza kanta kwai tayi ɗumin kuwa shi kaɗai ne abin da take iya mutsawa ajikinta.

Dagata zaune ya yi tare da yimata matashi da pillow ya fara ciyar da ita yana mata fira mai dadi sosai Ammi take jin daɗin firar da yake mata.

“inama ace inada lafiya da na nuna maka kulawa ɗana feyi da wacce kake nuna min amma hakan ba zai taɓa faruwa ba”. Ammi ta faɗa cikin ranta idanunta suna cicciko da kwallah sosai take jin zafin abin amma ba yan da ta iya.

“Subah’anallah!”. Ammi me nine kuma ya faru?”. Ashraf ya faɗa cikin tashin hankali”. Ganin yan da duk yabi ya ruɗi ya sa Ammi saurin shanye kwallar da ke shirin zubu mata.

Kama hannunta guda daya ya yi cikin nuna kulawa da sanyin murya ya ce”. Please Ammi ki daina saka damuwa aranki bana sun ganinki cikin damuwa nafi sun na gan ki cikin farin ciki kin ji ko Ammi?.” Gyaɗa masa kanta ta yi alamar eh.

ZYSHA

Daƙir Umma ta sakata ta ce Abinci sabi da ita wllh kwata kwata bata jin yunwa to yama zata iya cin abinci bayan bata san inda Daddynta ya ki ba ya mutu ko yana rayi.

Dare ya yi sosai yayin duk wata halitta mai rai take sun bacci amma saidai wasu suke ganin tamkar rana ce ba dare ba kamar dai yan da ta kasance agurin Zysha.

Zaune take ta haɗa kanta da guiwar kafarta A hankali take rira kukanta”. Dafa kafaɗarta taji anyi afirgice ta ɗagu fuskarta da ta yi jajir sabi da kukan da tasha

Sauki ajiyar zuciya Umma tayi ta ce”. Dama nayi tunanin cewa bakiyi bacci ba ashi kuwa hakani”. Cikin Muryar lallashe Umma ta ce”. Kiyi hakuri Zysha ki dauki wannan jarabawar da Allah ya mana insha allah komai yayi farko yana da karshi.

“Umma na saba da rayuwa tare da Daddy lokaci daya na rasashi wllh bazan iya jurewa ba zuciya ta zata iya bugawa”. Zysha ta faɗa cikin muryar kuka zuciyarta na mata zafi.

“Haba Zysha ya kike sun nayi da raina?”. Idan na rasaki ku kaɗai ne yanzu ku ka rage min kuma ku kaɗai ne zan kallah naji sanyi araina ya kike ganin idan na rasa daya daga cikinku?.” Dafa kafaɗarta Umma tayi cikin raunin murya ta ce”. Zysha nasan ki mai hakuri ce ako da yaushe ki yi hakuri da wannan jarabawar kin ji Zysha na?.” Umma ta faɗa tana shari mata hawayin fuskarta amma kamar ƙara turo su ake.

Manisha da ke tsayi kusa da su itama kukan take ɗumin kuwa taji duk abin da suka faɗa sosai take jin tausayin kansu na sabuwar rayuwar da suka shiga.
Chapter 2 · 0% Book details