← Book details Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki Local reading mode
READING PART 11 OF 31

Sashe 11

Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki · about 8 min read

“Ko da zan rasa rayuwata, sai na gano sirrin masarautarmu! Sai na nemo wanda zai tsayar da wannan muguwar halitta daga kora min iyali.”

Afsana ta sake kiran “Mamaaa… Papa… ku bar niiii….” Sai jikinta ya yi sanyi ta koma sumewa. Shiru ya mamaye ɗakin, sai huci da gumi a fuskar Papa da Mamie da kuka.

Ɓangaren Zysha – Nigeria

Da kyar ta tashi ta shiga kitchen bayi ta watsa hawaye suna zuba ta ɗaga hannunta sama cikin roƙo:
“Ya Allah, kai ka kare ni daga sharrin halittu, daga sharrin shaiɗan da kuma duk wanda ke neman hallakar da ni.”

Aunty Asabe ta shigo kitchen ɗin da mamaki ganin yanayinta:
“Zysha? Me ke damunki haka? Kin rame kwana ɗaya kacal. Wallahi kamar wadda ke ɗauke da wata cuta.”

Zysha ta ɗaga kai da hawaye suna zubo:
“Aunty, wallahi ba mafarki na yi jiya ba. Na ji inuwa ta tsaya bakin window, na ji hannunta ya taba ni. Na ji kamar ana son ɗauke ni! Aunty akwai wani abu a wannan gidan, akwai wani abu yana binaaa!”

Aunty Asabe ta tsaya cak, zuciyarta na bugawa. Ta girgiza kanta a hankali cikin ɗan ƙarfin hali:
“Zysha… ki kwantar da hankalinki. Shaidan ne ya zo ya firgita ki, amma ba zai taɓa cutar da ke ba idan kika dage da addu’a. Ki dage da karatu ki roƙi Allah, insha Allah za ki tsira.”

Zysha ta share hawayenta, amma a zuciyarta ta ce:
“Wallahi akwai alaka tsakanin abinda ke damuna da wani sirri da ba na fahimta ba. Amma sai na gano gaskiyar wannan lamari ko da zai sa zuciyata ta tarwatse.”

Ana haka sai hamdiya da rabi suka shigo kitchen ɗin idon su ya sauka kan Zysha suka watsa mata banzan kallo.
Aunty asabe ta kalli Zysha:
Ga breakfast ɗin uwar gida Ammi ki kai mata kar ki ɓata lokaci kinga akwai gyaran part ɗin yallaɓai Rehman.

Da to Zysha ta amsa ta ri da ɗaukar breakfast ɗin ta fita daga kitchen aunty asabe ma ta fita.

Ƙasaƙasa da murya hamdiya ta ce:
*”Wallahi wannan yarinyar idan muka yi wasa sai ta wace komai na gidan nan. Ki ga dai yadda aunty asabe ta ke kula da ita gobe ko jibi za ki ji Hajia ƙarama ma ta fara ɗaukarta fiye da mu*.

Rabi ta ɗaga gira, idonta ciki da ƙiyayya.
“Ni da kaina zan yi wani abu. Ba zan bari ta zauna ta yi dariya da mu ba. Duli sai mun zauna mun tsara yadda zamu *lalata ta* ba tari da wani ya gani mune ba”.

Hamdiya ta yi dariyar shiƙiyanci:
“Ai kuwa kin kawo shawara mai amfani gaskiya rabi kan ki yana jaa”.

Suka saki fashewa da dariya.

Rabi ta ƙara matsawa kusa da hamdiya ta furta a hankali.

“Kin tuna ruwan juice da aka ajiye a fridge?”.

“Eh… Eh na tuna. “ To sai mu saka wani ɗan gishiri ko barkono mu saka a breakfast ɗin da Zysha zata kaiwa yallaɓai Rehman daga nan kuma sai dai mujira muga hukuncin da yallaɓai Rehman zai mata”.

Rabi tai maganar tana sakin maƙirin murmushi.

Hamdiya ta tafa hannu da murna:
“Wannan shawarar ta yi kyau wallahi idan mu ka yi haka sai mu ji daɗin ganin yadda yallaɓai Rehman zai koreta daga gidan gaba daya.

Suka yi dariya mai tsa yi, suka ci gaba da tsara dabarun su, zuciyuyin su ciki da mugunta da kishi.

Bayan wani lokaci Zysha ta shigo kitchen ta ajjiye trayn da ta gama ciyar da uwar gida Ammi ta ɗauki breakfast ɗin Chef Rehman tana shirin fita rabi ta dakatar da ita:
“Wai ke ce aka baiwa aikin kai wa yallaɓai Rehman abinci ko? To wallahi ki sani kina taƙama da wani abu da ba ke ki ka chanchanta ba”.

Hamdiya tay ƙwafa, ta ɗan yi ɗariya mai ciki da raini,
“Dan aikin banza sai ki zace surukar gidan zaki zama”.

Zysha ta ɗago idonta da suka fara tara hawaye ba tari da ta yi magana ba sai kwai ta fita daga kitchen ɗin.

Maryam wadda shigowar ta kenam ta girgiza kai tana kallon su .

“ Ku dai bako gajiya da gulma ita Zysha ai ba ita ta tsarawa kanta aikin ba amma ɗan mugunta kun manta kowa yana da *ƙaddararsa*.”

Rabi ta ja tsaki ta juya amma a zuciyarta ciki da haushi hamdiya kuwa mai ƙayatarwa, ta ce. Ai ba zamu fasa ba. Gaba daya sai mun nuna mata bata isa ta ƙwace mana abin da muka daɗe muna nema ba.

Ɓangaren Yasmeen – Birthday Party

Gidan abokiyar Yasmeen ya kaure da haske, kida da dariya. Fitilu masu walƙiya na rawa a bango, kida na ta ruruwa, yara da manya suna rawa suna dariya. Yasmeen ta shigo cikin rigar gown ɗinta mai kyalli kamar sarauniya, ta tako cikin izza. Duk idanu sun tsaya a kanta.

“Woooow Yasmeen! Queen of the night!” suka yi ihu suna dariya.

Kawayenta suka fara ta zuga:
“Idan da gaske ke yarinya ce mai wayewa, sai ki sha giya. Idan ba ki sha ba, to karfin kawai kike yi.”

Yasmeen ta yi dariya tana girgiza gashinta mai walƙiya:
“Ni kuwa? Sai ku gani!”

Ta karɓi kwalban giya ta ɗaga ta sha a gaban kowa. Suka yi ihu suna ta dariya. Ta sake ɗaya, suka yi ihu:
“Another one! Another one!”

Da ta ƙara sha jikinta ya fara yin sanyi, numfashinta ya fara raguwa. Idonta ya rufe, jikinta ya yi rauni, ta koma gefe tana tari.

Ɗaya daga cikin kawayenta – saurayi ya bita da wani ɗan iskan kallo da ke can gefe – ya matsa kusa da ita yana murmushin mugunta. Ya ja hannunta a hankali cikin duhu, ya ce:
“Zo mu huta ki da ni. Kina da kyau baby Yasmeen, yau rana ce taki…”

Yasmeen ba ta a hayyacinta da ƙarfi, jikinta ya yi rauni. Kafin wani ya ankara, ya ja ta zuwa parking inda ya aji motarsa ya ɓuɗe mata gidan gaba tana layi ta yi ƙuƙarin shiga, amma ta kasa. Da kansa ya taimaka mata tashiga ya rufe ƙufar ya zagaya ya shiga mazaunin drive ya tada motar suka bar Hull ɗin.

Cikin wani ƙanƙanin lokaci suka isu wani matsa kai cin gida ya fito ya kama hannunta suka shiga bedroom nasa ya biya buƙatarsa da ita.

Bayan lokaci, Yasmeen ta fito daga ɗakin tana rawar jiki, zuciyarta cike da tsoro tunawa da dad. Ta ji kamar duniya ta rufe mata, ta rasa me zata ce.

A ranta ta ce cikin hawaye:
“Na shiga tarkon da ban zata ba… yanzu ya zan yi da dad? Me zan faɗa wa mommy? Wa zai ƙwace ni daga hannun dad?”

Gyefe goda Hajiya Ramlat sai zagayen ɗaki ta ke hannunta rike da wayarta tana kiran wayar yasmeen amma ba a ɗaga wayar.

Fuskarta duk ta jiƙe da gumi duk da sanyin a.c dake ɗakin:
“Haba lovely daughter ki ɗaga wayar na shiga uku”.

Hajiya Ramlat ta yi maganar cikin tashin hankali dan duk da kasancewar ta maci mai izza da kishi tana tsoron hukuncin abban yasmeen.

Please sh1. “Duk wanda ya tsira daga shaiɗan, sai da addu’a… amma shin addu’ar Mamie za ta isa ta ceci Afsana?” 2. “Kishi da mugunta sun fara cin zuciyar Rabi da Hamdiya – shin su ne za su hallaka Zysha?” 3. “A cikin dariya da rawar birthday, Yasmeen ta yi kuskuren farko… kuma shi ne ya jefa ta cikin haɗari.” 4. 🩸 “Alƙawarin da aka karya tun zamanin kakanni ya dawo yana bibiyar zuriyarsu – shin Papa zai iya tsayawa?” 5. ️ “Gidan ya cika da tsoro da hargitsi, amma zuciyar Afsana ta fara bada sirri… wacece ita a zahiri?” 6. “Sirrin masarautar Egypt ya fara bayyana – amma ba tare da tsadar rayuka ba.” 7. “Addu’a ita ce makami mafi ƙarfi, amma idan zuciya ta fara karkata ga shaiɗan, me zai iya tsayawa?. Duk waƴannan amsu shin suna cikin littafin KURURUWAR SHAIƊANn

KURURUWAR SHAIƊAN

*BOOK 1 free ne [2025] NOVEL ️*

Masoya littafin KURURUWAR SHAIƊAN kuzo ku shaƙata da sabon update ɗin da zai saka ku cikin duniyar da ba zaku so ku fita ba.
Cike da ruɗani soyayya da asiri na san babu mai so ya rasa wannan! Kada ku bari a baku labari… Ku kasance cikin masu farko da suka karanta !

Danna nan ku shiga link
HYPERLINK "https://chat.whatsapp.com/FuTlAsg7uedBXoMKiash4h?mode=ems_copy_thttps://whatsapp.com/channel/0029Vb6QGRg6WaKl7oWkqq30" https://chat.whatsapp.com/FuTlAsg7uedBXoMKiash4h?mode=ems_copy_thttps://whatsapp.com/channel/0029Vb6QGRg6WaKl7oWkqq30

Story & writing
By
ZULFA M. TUKUR

بسم الله الرحمان الرحيم
اللهم صل على محمد.....

Page 15

Hajia Ramlat tana tsaye sai zagayi zuciyarta na harbawa kamar ana danna ganga. Ta ƙarasa jikin taga ta ɗaga labule ta leƙa waje amma ba ta ga komai ba sai duhun dare da iska mai kaɗawa. Wayarta ce ta yi ƙara da sauri jikinta na rawa ta duba dan duk atunaninta yasmeen ce. Sai taga sunan abban yasmeen ya bayyana.

Tashin hankali saura ƙiris numfashinta ya ɗauki har wayar ta tsinke bata ɗaga ba wani ringing ya sake shigowa.

“subhanallah! Allah kada ya zama abin da nake tuna ni. Na shiga uku….“

Ta ɗauki wayar cikin rawar jiki, ta amsa da sauri:
“Hello, Alhaji“

Muryar abban ta fito cikin tsawa:
“Ramlat! Ina Yasmeen? Na kira wayarta sau goma sha biyu bata ɗauka ba! Kina ɓoye min cewa ta je birthday ko?“

Hajia Ramlat ta rike kanta da hannu biyu idonta ya yi jaa fuskarta ta cika da gumi.
“A’a…. Wallahi bana ɓoye maka komai…. Yasmeen ɗin fa tun fitarka ta ke kwance zazzaɓi ya rufe ta.“

Murmushi mai sauti abban yasmeen ya yi muryarsa ta ƙara yin nauyi, kamar ana tsoma dutse cikin ruwa:
“Ramlat ke nam ai nafi kowa sanin wacece ke ki saurare ni sosai…idan har Yasmeen ta je gurin birthday wallahi ku duka saina hukunta ku“.

Yana gama faɗar haka ya tsinke wayar. Hajia Ramlat ta durƙushe tana huci. Ta rafka uban tagumi kamar wacce ta rasa wani nata.

A lokacin ne aka turo ƙofar ɗakin ta buɗe a hankali Yasmeen ta shigo jiki a sanya ganin halinda mahaifiyata ta shiga jikinta a rude Kamar an yi masa dukan ƙwayar rai.

Da sauri Hajia Ramlat ta nufe ta ta rungume ta.
“yasmeen ina ki ka tsaya har dare ya ye haka!?”
Chapter 11 · 0% Book details