← Book details Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 42

Sashe 9

Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A waje yau ta yi parking suka bubbude kofofin motar suka zazzauna baki baki suna ta hira tsakaninsu ita dai kujera plastic aka dauko mata ta zauna.

Wannan zama da su kan yi ba karamin rikita 'yan unguwar suke ba don duk wanda ya doso idan ya gansu sai ya koma da baya saboda abu kadan za ka yi su zalunceka.

Cikin rawar jiki ya taho don wallahi bai so zuwa ba amma Malam Iro ya rantse mishi idan suka bari wani abu ya samu khadija to wlh duk sai sun yabawa aya zaƙinta gwara ya zo ya nemi Zubash ɗin.

A rikice yake gabaÉ—aya haka ya zo ya tsaya kyammm kan su ya rasa me zai fara cewa saboda tsoro.

Idanu ta É—aga ta kalleshi ta watsar..

"Obo.."
Obafiya ya diro ta kalleshi
"Wannan bai iya gaisuwa ba ne?"
Sarai ta gane shi shima kuma a rikice yake ya sa bai gaishe su ba, kan yayi wani yunkurin Obafiya ya faska mishi mari sai da ya kusa faÉ—uwa ya gyara tsayuwa yana dafe kunci idanunshi falll hawaye a zuciyarshi kuwa ya tsinewa kafafun da suka biye wa Malam Iro suka kawo shi gaban Diva.

"Babu manya ne a gidanku? Ko gaisuwar ce ba'a koya maka ba"
Hannayenshi biyu kan kumatun ya zube jiki na rawa ya shiga cewa
"Wallahi an koya min...Na rikice ne ya sa na manta..ina yini... Ammm ahh ina kwana? Ina gajiya?"

Babu wanda ya saki fuska a cikinsu Dukda dariyar da ya ba wasu.

"Mu aljanu ne dole mu rikitaka ko?"
Divaa ta faÉ—a tana zukar tabar hannunta.

"A'aa ki yi haƙuri Diva...kiyi haƙuri"

"Me ya kawo ka?"
Diva ta tambaya.

"Khadija ce tana dawowa makaranta mota ta kaÉ—eta kuma ta bugu sossai shine...shi ne baba ya ce in zo in duba Zubaidah a kaita asibiti kar wani abu ya sameta"

Idanu Diva ta zuba mishi wato duk gidan babu mai iya kaita asibiti sai Zubaida ta zo? Sun mayar da ita saniyar tatsa shiyasa jikinta baya taɓa hutawa da maza, tsaki mai ƙarfin gaske ta ja cikin wani irin takaici don alamu sun nuna tun jiya Zubash ɗin bata tare da su kuma bata gida.

"Obo...mu tafi mu kai yarinyar nan asibiti"

Ta miƙe da sauri suka shiga mota ta ja zuwa kofar gidan su Zubash ɗin suna parking sai gata tana sauƙa a machine, cikin mamaki take tambayar su me ya faru.

Diva bata ce komai ba sai tsayuwar da ta gyara tana wasa da dankwalinta Bakinta na taunar chewing gum a hankali.

"Shiga ki duba ƙanwarki"

Wani irin tashin hankali ne ya bayyana a fuskarta da gudu ta shiga cikin gidan, yadda ta samu Nana sai da ya sa ta kusa faÉ—uwa, haka suka daukota sai asibiti.

Da taimakon Allah dai babu abin da ya faru, an kula da ita sossai kan suka baro asibitin yamma ne don haka Diva wanka tayi har ta ma kwanta ta tuna akwai abubuwan da take son saya a kasuwa don turarukanta sun yi ƙasa.

Key ta zara tana gyara trench coat na jikinta, wasu irin takalma hills ta saka ta fito.

"Hajjo!"

Da sauri hajjo ta zo
"Na'am uwar É—akina"

"Idan su Obo sun shigo ki ce musu su jirani ina zuwa yanzu"

"Toh Sohana amma yau ke kaÉ—ai za ki fita?"

Ta ɗan kalleta sai ta duƙar da kai bata ce komai ba don ba'a yi mata tambayar iskanci ita kanta hajjon ta sani subutar baki ne.

Fitowa tayi ta shiga mota ta kunna tare da juyawa ta isa gate É—in sai dai bata ga alamun Bilya ba.

Horn ta yi sau ɗaya bai fito ba ta sauƙa a harzuke, daidai yana fitowa daga bayi da gudu, kafa ta sa ta kwashe shi ya zube timmmm a ƙasa.

"Ki yi haƙuri Diva...!"

"A karo na karshe da zaka kira sunana, aikin me aka daukeka da za ka barni ina ta Horn shiru??"

"Cikina ne ya ruÉ—e shine na je ba..."

"Ka buɗe gate ɗin nan ko sai na ɓurma cikinka in ya so abubuwan su zube nan ƙasa ka huta da zuwa bayin?"

Da gudu ya je ya shiga buÉ—e gate É—in ta doka tsaki ta koma motar watarana sai ta cirewa Bilya hannaye in bai kiyayeta da sokanci ba.

Da gudu ta fice daga gidan jiki na rawa ya zube yana sauƙe numfashi.
Allah ya gani ba yadda ya iya ne yake gadin wannan gida, idan ya bar nan É—in bai san ta inda zai fara neman wata sana'ar da zai ci da kanshi da matarshi ba kuma ya kula da lafiyar yaron su in ba don haka ba da ya bari da jimawa, a haka É—in sun yi masu gadi sama da goma sha wani abu duk basa iya jure halin Diva don yau za ta iya yi maka kirki gobe ta karta maka rashin mutunci ba damuwarta ba ne, Musamman idan tana Buge kaman yanzu.

Kasuwa ta nufa music na tashi a motar kaman zai É—aga sama, chewing gum take ci tana gyaÉ—a kai cikin reckless driving da sai dai a bata hanya ba dai ta bayar ba.

********

Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi....

DAÆŠIN ZAMA BY SEEMAHWRITES
JODA BY SADI-SAKHNA
ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH

*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*

*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*

Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin

Sai a tura shaidar biya ta
09039206763

🖤Gureenjoh🖤

ƘARFE ƊAYA BA YA AMO

✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN
(GUREENJOH)

@Gureenjo on Arewapen
@Gureenjoh6763 on Wattpad

ADABI WRITERS ASSOCIATION

TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne.

GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba.

NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k.

*SHAFI NA BAKWAI*

Kasuwar cike yake da hayaniya, masu sayar da kaya na yi hada hada ko ta ina haka ta ratso da motarta inda yayi mata tayi parking, sai da ta ɓata lokaci ta sauƙo wearing all Black hannayenta cikin aljihu, fito ma take yi da Bakinta.

Cikin seconds ta É—auki hankalin mutane dayawa ta inda take duk an yi shiru kawai an zuba mata ido.
Wani matashi ya taɓa na gefenshi da suke sayar da kayan dan kunne da sarka

"Wallahi ita ce! DIVA ce! Wannan da kake gani
Ko manyan maza suna tsoron shiga komarta"

"Ita ce wa? Ni ta burgeni"
"kambala'i na rantse idan kana son kanka da lafiya ka kama bakinka tun kan ta ji ka, ka santa kuwa? To wannan da kake gani idan ta yanke hukunci kanka babu wanda ya isa ya É—aga mata yatsa kaff zuri'ar ku"

"Meyasa ake kiranta DIVA kaman wata shugaban 'yan dabar indiyawa"
Ya faÉ—a yana dariya har da sake karkacewa don kallonta da kyau.

ÆŠayan ya ce
"Ai duk ɗaya, babu macen da tayi kaurin suna a dabanci irinta, kuma fa har da ma ɗaurin gindi daga wasu 'yan siyasar garin nan saboda ubanta shi ke tafiyar musu da siyasa yadda suke so idan lokaci ya yi. Sunan DIVA kuma na taɓa ji daga wani dan daba wai tun tana shekaru takwas a duniya ta samu sunan, a lokacin farkon riƙe wukarta ta cire yatsar wani da ya nuna babanta da yatsa...DIVA na nufin mai kwarjini, kyau, da kuma confidence na tarar duk wani aradu da ka, irin waennan boss ladies ɗin ake kira DIVA to daga yanayinta ne aka sa mata sunan ga ta da son gayu kuma Ubanta na kashe mata, ta haɗa kyau, iko ga izza irin na duk wani ɗan daba mai ban tsor..."

Wuce su ta zo yi hakan ya sa duk suka yi shiru har ta wuce ta É—an kallesu kaÉ—an don ta tsinci maganan da su ke É—in amma bata yi niyyar kula su ba ne ta shiga shagon turare tana shiga ta zare glasses na idanunta ta tsaya kikam kan ta ce cikin muryarta

"Duk ku fita waje...!"

Ta yiwa costumers da suke wurin umurni, dayawa tsoron ta da suka ji ya sa suka fita amma wasu Matasa na nan tsaye.

"Akan me za ki ce mu fita? Na ga abin da kika zo saya shi mu...."
Wukar da ta zaro shi ya datse maganar ta nufe shi tana juya tsinin wukar a fuskarshi.

"Ban ji da kyau ba maimaita..."
Jikinshi rawa ya kama, yana mamaki.
"Naa fyeÉ—e fatar fuskarka idan na rufe ido na buÉ—e na ganka tsaye a gabana....."
Kaman walkiya haka suka yi waje da gudu.

Ta cigaba da riƙe wukar.

****

"Nana"

Zubash ta kira ƙanwartata da ta buɗe ido ta kalleta ta sake lumshewa.

"Yaya Zubaidah ke ce? Kin dawo?"

"Eh Nana ya jikin? Fatan kin ji sauƙi?"

"Da sauƙi yaya Zubaida"
Kallonta ta cigaba da yi har Zubaidar ta tsargu

"Menene kike kallona haka Nana? Na chanza ne?"
Nana ta girgiza kai tamkar za tayi kuka ta ce

"Yaya Zubaidah don Allah ki daina irin wannan rayuwar, bana jin daaɗin ganinki haka... Yaya Zubaida mu gudu mu koma wurin Abbanmu na tabbatar zai riƙe mu...ba na so ki mutu akan wannan tafarkin, yaya Zubaida a makarantarmu har kwatance ake da ke da Diva, idan na shiga mutane a tsarge nake ni karan kaina dayawa kyamata suke, wasu ma cewa suke tare muke yawon iskanc..."
Kuka ne ya sarƙe ta.

"Dalilin da kika hau hanya kenan ki kashe kanki ki huta?"
Zubash ta faÉ—a cikin sanyin murya.

"Ko É—aya, na san duk wanda ya kashe kanshi wuta za shi Yaya Zubaida ba zan fara ba, wasu seniors ne suka yi bullying É—ina akan ki na fito ina tunanin wani irin rayuwa muke ciki ban kula da na zo hanya ba mota ta kaÉ—e ni. Don Allah ki amince Yaya Zubaida mu gudu Taraba"

Ta ƙarasa da wasu irin hawaye.
Chapter 9 · 0% Book details