← Book details Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 42

Sashe 7

Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan gama duk wani nazari ya É—auki wayarsa ta pixel ya kunna data, Page É—inshi ya fara dubawa ko yana da tarin tambayoyi wanda idan akwai dole zai yi live da dare saboda amsawa duk tambayoyin da aka yi mishi, ya kuwa same su birjik dole imamu zai zauna yayi sorting masu muhimmanci sossai.

Kiran azahar ya sa ya miƙe ya shirya ya fice, bayan ya gabatar da sallah da imamu suka shigo ya karɓi sauran aikin Shehi ɗin shi kuma ya shiga don bacci saboda a irin waennan ranakun ya kan huta da rana, ƙarfe uku ya tashi ya sake wanka ya shirya cikin Midnight blue thob da White Jubba sai White Ghutra da Agal ɗinshi baƙi sama.

Cikin tsantsar kamala ya fito a dining ya zauna ya zuba abincin da ya tabbatar daga wurin Maamah ne ya zuba kaɗan ya ci kan ya miƙe ana kiraye kirayen sallah ya fita, bayan gabatar da Asr aka shirya mishi wurin zama da zai gabatar da karatun littafi da suke yi da yamma, masallacin ya cika da gidajen television na Musulunci kaman su Sunnah Tv, Africa Tv3 da su Manara su Wisal duka sun saita camerori, shi ya zauna akan kujerar gabanshi coffee ne a wani kyakyawar mug da Imam ya kawo ya ajiye, duk ya buɗe mishi system ɗinshi ga littafin ma a buɗe nan ya fara gabatar da wa'azin Magana ya gangaro da shi kan tuba da neman gafara.

"Darasin anan shi ne idan an ce a yawaita Istigfari ba sai mai budadden laifi kaman zina, da saura su ba ne a'a asalin bayin Allah na ƙwarai ba sa rabo da Istigfari, da tuba saboda yanayin halittar da Allah ya yi mana. Dama a halittar ɗan Adam akwai wani nau'in kasawa da ubangiji ya yi mana duk ƙoƙarinka bahaushe ya ce tara kake baka cika goma ba, idan ka amince da wannan za ka samu sauƙi a ranka... Mafhumm?"

Suka amsa da
"Na'am"
Ya ce
"Dayyib"
Kan ya cigaba cikin kamalarsa

"Wasu su kan sakankance su ce ai laifukansu ya fi karfin tuba ko sun yi ma a banza don suna da yakinin Allah ba zai karɓa ba Lalala ku sani shi shaidan ba wai yana son ka cigaba da laifi ba ne kawai yana so ne ka yanke kauna daga rahamar ubangiji"

An natsu sossai ana sauraronsa wasu na ta tuna ayyukansu.

"Idan da fa Allah yana so ya halaka ka saboda zunubinka...da ba zai taɓa buɗe maka kofar tuba ba, kada ku kuskura ku bari wani zunubi ya sa ku ji ba ku chanchanci komawa ga Allah S.W.T ba"
Yana kai nan ya ce anan za'a dakata za su cigaba gobe da yardar Allah.

Tambayoyi ya amsa Imam na karantawa yana amsawa kan suka tashi daga karatun, sai da ya fita kan kowa ya shiga ficewa daya bayan daya a lokacin karfe biyar, gida ya shiga sai sannan ma yake tuna yana da taron Matasa na awa guda a masallaci don haka Ammar ya kira a waya ya tabbatar mishi yana zuwa, mintuna kadan sai ga shi sanye da dakakkiyar jumpa, musabaha suka yi kan suka koma masallacin ya gabatar da taron cikin ilimi da Allah yayi mishi.

Wani abu da Irshad Al-Noor muddin yayi wa'azi to sai ya je viral, mata dayawa ya zama crush É—insu kowacce tana son kallonshi don yana da tsafta, natsuwa, kamala da izza irin mai tasiri É—in nan, yana da taushi amma idan ya murde yana da karfin da babu mai iya tankwara shi, hakan ya sa dayawa daga cikin wasu malaman ya zama kaman makiyi ko abokin gabansu.

Wasu yana sane yayinda wasu bai ma san suna yi ba duk ya tarkatasu ya watsar abin da ke gabanshi kawai yake da kuma wanda ya san zai amfani al'umma.

Sun idar da Magrib yayi karatu har aka kira isha yana zaune a inda yake saboda kwaɗayin samun wannan ladar na zama tsakanin Magrib zuwa isha, ko da aka kira isha'i suka gabatar, Ammar da Imam da kuma malam Bala suka take mishi baya har zuwa baƙar motarsa da Malam balan ya janyo suka nufi inda yake lecturen dare.

A hanya ne Ammar ke ce masa
"Shehi wai ka ga abin da wannan yarinya Diva da mukarrabanta suka aikata a garin nan yau?"

Hotunanta da irin barna da suka yi ya miƙa mishi wayanshi ya shiga dubawa, bai jima yana kallo ba yayi tsaki kadan tare da miƙa wayar ga Ammar ɗin.

Kaman zai basar kuma sai ya É—auki wayanshi ya shiga contact list É—inshi ya duba commissioner of police ya kira shi.

Ringing na kusan karshe ya yi picking
"Allah ya gafarta Shehi barka da warhaka"

"Barka dai yallaɓai ya aiki?"
"Alhamdulillah ya hidima da jama'a"
Ya É—an lumshe ido ya buÉ—e kan ya amsa da
"Alhamdulillah"

"Na ƙira ka ne in yi maka tuni don na san ka sani sai dai tuni ɗin yana da kyau wasu lokutan, a kan Haƙƙin al'ummar da ya rataya wuyanku, abin da waennan 'yan daban suka aikata ina fata ba za ku bari ya tafi haka nan ba! Alhakin gyaran al'umma ba akan iyaye kaɗai ya rataya ba, ya rataya a hannayenmu maluma, har da ku hukumomi da shugabanni da kuma duk wani mai faɗa a ji, idan ana barinsu Scott free shi yake ƙara basu daman maimaita same laifi..."
Ya ƙarasa fuskarta na sake dawo mishi, shi mamaki da kyankyaminta ne ke rufe shi a duk sadda ya tuna irin magananta zuwa abin da suka riska tana sha a jiyan da kalar irin dressing ɗinta wa'iyazubillah! Ya ambata a saman lips ɗinshi.

"Kwarai da gaske haka yake Ya Sheikh, Na gode kwarai da tunatarwa yanzu haka muna kan bincike ne kan su idan suka shiga hannu kuma za mu tabbatar sun dandani kudarsu daidai da abin da suka aikata"
Kai ya gyaÉ—a kan suka sake tattauna tabarbarewar tarbiya kan suka yi sallama.

Ammar bai yi mamaki ba don ya san idan da zai iya ba da gudumawa wurin ganin duk sun shiryu kuma basu lalata matasanmu masu tasowa ba tsaff zai bayar.
Ya É—an kalli Shehi yana sake mayar da kanshi kan wayan yana scrolling yayi murmushi

"wa'azin da ka yi É—azu É—in nan? Ga Ustaz khalid na sukar ka a media yanzu haka"

Karamin murmushi kawai yayi bai tanka ba.
Imam ya ce
"Ni na rasa irin Ustaz Khalid wallahi, ga tarin ilimi ga shi haziki sai dai ya fi girmama Spotlight akan da'awa da yake yi kuma hakan ba daidai ba ne"

Ammar ya ce
"Kuma sukar shi ba ya tashi sai Irshad ya yi wa'azi abin shin akwai daure kai.. Addinin ya zama gasa ne?"

Malam Bala ya ce
"Irin wannan yana jin haushin yadda mutane suke girmama Shehi ba tare da yana nuna hakan ma ya damesa ba don bai taɓa ɗaga murya don a ji sa ba..."

"Ammar! Imam Ku sani shi mutum mai tsoron Allah ba ya buƙatar ɗaga murya domin a ji nauyin kalamansa, maganan Ustaz khalid kuma a bar ta haka kila yana da hujjar sukar kalaman nawa matuƙar na kuskurewa fahimta"

Daga nan bai sake magana ba su ma basu sake ba don sun sanshi tunda ya ce a barta barinta ya zama dole ba ya son maganan wani a tare da shi sai ya zama dole.

Sun isa ya ba da lectures yadda ya saba, Imam ya koma yana nunawa Ammar yadda lectures na daren da mata ne ma ya yiwa ya dusashe sukar da É—azu Ustaz khalid ke mishi tun kafin ma a farga da shi wanda sun san sai ya kusa kwana da bakin ciki tunda abinda ya É—ora wa kanshi kenan wanda yake da shi bai ma nuna ya sani.

Daga nan gida suka dawo kowa ya nufi wurin kwanciyarshi, shi kam Irshad Al-Noor live video yayi ya amsa tambayoyi ya ba da ilimi sossai har karfe sha biyu kan ya sauka yayi wanka ya zo ya kwanta kaman kullum.

****

Ƙarfe sha ɗaya da rabi na dare ta farka, wanka ta sake ta jiƙa har gashinta saboda kanta da ke ciwo tsabar ta sha abubuwa sun yi yawa, da towel blue ta fito daure a kirjinta ta busar da gashinta ta yi sallar isha, ta shirya akwai birthday party da aka gayyaceta wani CLUB, ta shirya kuwa cikin wasu ja da farin riga da wando ta saka hill shoe ta rufe gashinta da scarf red ta fito tana baza kamshi hannunta riƙe da car key.

Jagaban yana ganawa da mutane kaman koyaushe don koyaushe yana busy ne ko solving manyan rigima da ya gagari yara ko sayar da kwayoyi yana kirga kuÉ—i.

Ficewa ta yi da Pablo, Obafiya da Zee baby.
Chasu ne da ko da suka je an yi nisa da farawa wuri ta samu ta zauna tana kallon masu raye-raye, ana shaye shaye ana rawa.

Idanu ta zubawa samari biyu da ta ga sun fara rigima kan wata figaggiyar budurwa, tsaki ta ja tana gyara zama ta san ƙarshen night club ɗin ne ya zo Dukda babban night club ne na manya kuma akwai bouncers dayawa hakan ba ya hana faɗa a lokuta dayawa.
Suna cikin jayayyar ta ga kaman an zo ana ƙoƙarin sasanta faɗar ji ta yi ana yi mata magana a ka...

"Fine gurl ya dai kike zaune ke É—aya?"
Ta mayar da idanunta kansa ta zuba masa su kawai bata ce komai ba.

Karkada ƙafa take har ya zauna gangarta ya kai hannu zai ɗora kan cinyarta cikin rashin zato ko tsammani ya ji wani lafiyayyiyar azaba ya ratsa shi har kwanya, ihu ya tsala yana riƙe hannunshi da ta yiwa wani yanka da wukar da bai ma kula da lokacin da ta zare shi ba, ta miƙe tana kallonshi cikin ido...
Chapter 7 · 0% Book details