Sashe 11
Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Nasiha ne zan miki ba tare da kin roƙa ba idan kin ɗauka ruwanki, kina yawo da jahilci da rashin wayo a dole ke kin waye. Bari ki ji Allah babu ruwanshi da wannan dole ne kowani matashi ya san addininsa, me addininsa ya koya masa? Menene dalilin halittarsa? Wallahi da addini ne ake gamuwa da Allah ba wannan haukar banzar ta dabancin da kika ɗora wa kanki ba, da a ce za ki fita wannan haukar a kasheki sai kin gayawa Allah dalilin fitarki da kuma dalilin kisanki, kuma sai kin faɗi akan me kika mutu a sannan ne Allah zai kalli abin da zai miki hisabi a kai, idan mutuwarki ta Allah ce ko ta Manzon Allah ko wurin kare hakkin addininki to Allah zai tambayeki kuma zai miki shari'a amma idan kika mutu kan wannan fa? Kina tunanin za ki tsira daga azabarsa?"
Da yatsa ya nuna ta, Muryarsa na sake zama deep don haka yake idan yana ɓacin rai da wuya ka ji ma Muryar na fita.
"Duk sai Allah ya tambayi me kike yi ki ci abinci da nemawa kai tufafi, zalunci ne? Sata ne? Fashi ne? Duk sai kin yi wa Allah bayani, baki isa ki ce za ki zo duniya ki daka tsalle ki zagi uban kowa ki zalunci wanda kika ga dama ki kwana lafiya kuma ki ce za ki shiga lahira lafiya ba wane ke."
"Wallahil azeem ba ki da wani abu mafi munin tarnaki a rayuwa kaman laifukan da kike aikatawa, Allah ya ce in da kun yi imani kun kiyaye dokokin Allah da mun kankare musu laifukansu kuma da mun shigar da su gidajen Al'janna na ni'ima. Imani na tsoron Allah imani na bin dokokin Allah...ko duk don saboda samun duniya ne kike wannan haukar?
Kina ganin in kin bi Allah ba za ki samu duniyar ba ne? ubangiji ya ba wa waenda ma basu bi shi ba bare ke da kika amsa sunan musulma? Kalmar Mutuwa kaÉ—ai Aya ce mai girma!"
Tsaki ya ja, ya juya ya kama Malam Bala da har lokacin jikinshi na rawa ya buÉ—e bayan mota ya sanyashi, ya kalli Ammar cikin kaushin murya ya ce
"Drive"
Da sauri Ammar ya shiga mazaunin driver imamu ya zaga da sauri ya buÉ—e mishi mota ya shiga ya rufe kan shima ya shiga Ammar ya ja suka barta kafe a wurin har lokacin kamar wacce aka dasa.
Hannayenta ta dunkule da ƙarfin gaske, wani zafi ya ziyarce ta a wanda ya murɗe ɗin ta runtse ido da karfin gaske wani irin tafasa da bata taɓa ji ba zuciyarta ke yi, idanunta sun rine kwarai da gaske ga shi bata iya kuka ba, wani irin rawa jikinta ya ɗauka numfashinta na fita da ƙarfi da ƙarfi, cikin wani irin sauri ta je ta shiga motar ta ja da karfin gaske ko kallon gabanta bata yi tayi gida.
Wani irin Horn da take dannawa da karfin gaske shi ya fito da mai gadin su da gudu kan ya buɗe ta sauƙa ta turo karamin kyauren da sauri, daka tsalle yayi amma ganin bata kula shi ba sai wani huci da take kanta babu dankwali iska na kaɗa gashin kanta tamkar sabon shigar kamun hauka tayi hanyar parlor, akwai Matasa masu ɗan dama a tsakar gidan yadda suka kalleta ya sa duk suka mimmike tsaye suna bin bayanta da kallo, babu wanda zai ce ya taɓa ganinta haka kowa ya rasa abin cewa.
Jagaban na zaune kawai ya ga shigarta a haka tamkar wacce aka jefo daga sama, da sauri ya tashi ya tare ta don ta nufi É—akinta ne.
"Ke! Sohana!! Menene?? Me haka? Wa ya taɓa ki?"
Wani irin jan numfashi tayi tana ƙoƙarin zagaye shi ta wuce ya sake tare ta yana ɗago fuskarta.
"Sohana me ya sameki? Ke da wa?" Idanun da ya sauƙe kan fuskarta ya sa ya zabura yana sake riƙota, Jagaban namijin gaske ne Dukda shekaru sun ja amma tsaye yake kyamm ga tsawo ga ƙira, bashi da imani bai san haƙuri a dukkan lamarinsa ba bare abin da ya shafi ɗiyarshi da duk duniya babu abu da yake ji da shi kamarta...
Muryarshi ta sake kaurara
"Mari? Uban wa ya mareki haka? Wa ya mareki???"
Da wani irin tsawa ya ƙarasa maganar daidai shigowan yaranta, tambayar kuma ya motsa mata irin kalaman bakinsa da suka fi marin zafi a zuciyarta.
Bata san ta yi wani irin ihu ba tana kokawa da numfashi, rungumeta jagaban yayi ta sake sakin ihu tana kuka irin mai jijjiga haÉ—e da ihu.
Daga shi har yaran hankalinsu ya ɗaga, basu taɓa ganinta haka ba, janta yayi ɗaki amma suna jin Muryar ihu da kukanta daga inda suke jikinsu na tsuma.
Da Jagaban ya ga ba zai iya jurewa ba ya haÉ—a wata allurar bugarwa ya yi mata da kanshi daga haka ta faÉ—i sai bacci.
Waje ya fito suka yi cirko cirko.
"Mari??"
Ya faÉ—a yana kai kawo cikin parlorn hannayensa dunkule idanunsa jajazir.
Skipo ya ce
"Na rantse da Assamadu yau Kano babu zaman lafiya an taɓa DIVA?? Wallahi babu mai bacci cikin daaɗin rai daga yanzu har gobe"
"Faɗa ma ɓata baki ne ai Skipo...aiki da cikawa ya kamata a gani mu jeeee"
Pablo yayi maganan yana zaro addarshi Tuni su Bravo sun fice sun yi kira, Jagaban bai hana su ba, don shi nashi ba a kan jama'ar gari ba ne ya tabbatar duk wanda ya iya ɗaga hannu ya mari Sohana har ta yi irin wannan kukan to ba ƙarami ba ne, faɗar su su biyu ne kuma ko waye yayi alkawari sai ya cire hannun, shi da marin wani halitta kuma har Abada..
Kaman yadda su Pablo suka yi alkawari, ƙira kawai suka dinga yi suna sanar da an taɓa DIVA a take gungun 'yan daba suka haɗu tun daga unguwar suka fara kan mai uwa da wabi suna shara... Har arear kasuwa da abin ya faru sai rufe kasuwa aka yi lokacin tashi bai yi ba.
Tashin hankalin da ya janyo dole polisawa suka kama fiye da rabinsu ciki har da su Pabloo don su ne gaba gaba, gari gabaÉ—aya ya rikice.
Shaly ce kawai da Skipo ne ba'a kama ba amma an kama Obo, Pabloo da kuma Zee, Zubash tana chan asibiti bata san me ke going ba.
***
A lokacin Shehi na zaune a reception na kyakyawar private hospital da ya sa Ammar kawo Malam Bala don duba kafarsa da ke ta jini, tapping kafarsa ɗaya yake a ƙasa yana ambaton Allah amma har lokacin zuciyarsa ta kasa sanyi.
Bai yi wa kowa magana ba su Ammar ma duk cikin sanyin jiki suke tsaitsaye, kowa ya san Shehi kallo daya za ka mishi ka san an kai shi makura a yau.
Abiey Ammar ya ƙira ya sanar mishi abin da ke faruwa anan Abiey ɗin ke sanar da shi shima yanzu ya fito daga office kenan za shi gida yanzu haka 'yan daba sun tsatsare hanyoyi suna ta barna.
Da sauri Ammar ya kalli Shehi, sai ya ce
"Abiey yanzu kuna ina? Babu abin da ya same ku?"
"Mun samu dai mun fita babu abin da ya same mu, akwai hukumomi a wurin Dukda su ma abin ya fi karfinsu ashe ku kam har da illata Malam Bala suka yi?"
"Toh Alhamdulillah, da sauƙi shima dressing ne yanzu za mu taho gidan gabaɗaya ba sai kun zo ba"
"Toh Allah ya kiyaye gaba a cigaba da kula Ammar, Allah ya kawo ku lafiya ya tsare mana imaninmu ya shirya mana yaranmu"
Ya amsa da Ameen kan ya katse ƙiran ya kalli Shehi.
"Irshad!"
Idanunsa da suke lumshe ya buÉ—e har lokacin a rine.
"Ka kuwa san abin da action É—in ka ya haifar?"
Bakinsa ya É—an taune bai ce komai ba.
Ammar ya buɗe wayarsa ya shiga Facebook ya miƙa masa videos ne na abin da 'yan daba suka yi yau babu wani shugaba da zai ce yayi maganinsu.
Ransa ya sake ɓaci, wato ma ɓata miyaun bakinsa ya yi ba za ta taɓa chanzawa ba? Meyasa shi da yayi mata bata yi masa ba sai waenda basu ji ba basu gani ba?
Commissioner of police ya ƙira
"Last time na tura maka hoton yarinyar nan da abin da suke aikawa ban ga ka yi wani hobbasa ba, hasali ma cigaba da yawo ta yi freely yau ta jagoranci mummunar hari irin wannan na zalunci haka za ka bari ta tafi Scott free again?"
Commissioner da ba zai so shiga bad list na Shehi ba don ya san ja da shi ba daaÉ—i ya ce
"Wannan karo ba ita ba ce! Amma ina maka albishir da cewa mun samu nasarar kama yaran kuma za mu gurfanar da su gaban court cikin gaggawa don a yanke musu hukunci daidai da abin da suka aikata"
ÆŠan shiru Shehi yayi kan ya ce
"Zan cigaba da bibiyar wannan case har sai na ga ka yi abin da ka ce É—in, ka kula da gaskiya a kan aikinka ka sani duk abin da ka yi Allah na nan yana kallo mala'iku suna rubutawa sai an tambayeka ranar gobe"
Yana kai nan ya katse wayan tare da damketa a hannunsa da ƙarfi kaman ita ce ta masa laifi.
Daidai nan Malam Bala ya fito yana ɗingisa ƙafa, Imam ya riƙe shi suka yi mota yana yi wa Shehi godiya.
Sai da suka zauna Ammar na driving Irshad ya ce
"Malam Bala ina roƙon ka da ka yi haƙuri da abin da ya faru, ka yafemin"
"Baka yi min komai ba Shehi, ita ma da tayi ina mata Fatan shiriya da samun rabauta don tabbas ina mata tsoron mutuwa a haka"
Shehi bai sake cewa komai ba suna isa gida kuma suka samu duk ahalin gidan a waje ana jiran isowarsu shi kam sannu da gida kawai ya musu ya wuce sashenshi don ko a ƙalau ma bashi da wani abin mayar da magana bare har lokacin yana jin zuciyarshi na zafi, idanunshi na hasko mishi marin da ta sauƙe wa malam bala haƙiƙa ya ji zafin marin nan wane Abbiey ɗinshi aka mara, ya san darajar mutum ya san darajar duk wani dake zagaye da shi.