← Book details Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 42

Sashe 2

Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kuwa ba zata ce ta ga na bayan motan ba, bayan wucewansu ta cigaba da tafiyanta da gayunta yadda ta saba na maza kuma 'yan daba kaman yadda take'yar daba itama, cikin unguwar su ne don basu yi tafiya mai nisa ba suka isa wani gida matsakaici, gini ne na block amma babu plaster haka babu penti sai dai akwai gate mai girma da ƙarfi kalar Ja, karamin kyauren ta tura babu wuta solar ne kunne hakan ya haska mata tsakar gidan da kaman rana ne maza ne kala kala a ciki ana shaye shaye da cha-cha.

"Barka DIVA! Barka KWARUWA!"
Kalaman da ke ta tashi kenan bakunansu cikin yanayin tsantsar dabanci.

Hannu ta É—aga tayi crossing suka amsa
"Chauchauuu... Eeeyyy mana"
Tayi murmushi ta juya ga gayunta
"Sai Allah ya kai mu"
"Mu kwana lafiya Diva"
Suka haÉ—a baki wurin faÉ—a don sun san ba sake fitowa zata yi ba kenan, ta nufi karamin barandar ta haye ta tura kofar parlorn ta kutsa kai babu ruwanta da sallama.

"Baaba"
"Ƴar Baba!"
Wani rikakken murya ya amsata ta riga ta ga abinda yake ɓoye wa don haka dariya kawai tayi.
"Babana na kaina... A cigaba da sana'a"
Tana kai nan ta wuce su don zaune yake da wasu mutane biyu diloli ne da suke zuwa karbar kwaya wurinshi, É—akinta ta tura ta shige bata damu da rufewa ba don ko kuda ne Jagaban ba ya bari ya sauka kanta bare ita kanta hatsari ce.

Ba rayuwar da ya so zaɓa mata ba kenan amma bahaushe ya ce barewa ba zata yi gudu ɗanta yayi rarrafe ba.

Gado ta faÉ—a ko boots na kafafunta bata cire ba ta shiga bacci irin na maye.

****

Allah ne ya kawo su gida lafiya don Malam Bala ko uffan bai sake cewa ba yana ji Imam da Ammar suna tattauna batun wacce aka kira da Divaa amma ya kasa furta ko A shi da ya gama ganin mutuwa ganin idanunshi.

Irshad Al-Noor kuma dama sun san ba tankawa zai yi ba shiyasa Ammar ya kama Imam suke ta maganan, Horn nasu shi ya tado mai gadi ya zo ya buÉ—e tamfatsatsen kyauren gidan na Alhj Omar Al-farouq mai kamfanin Twins Enterprises, gida ne mai Girman gaske, gida ne da kallo daya zaka mishi ka fahimci daÉ—É—aÉ—den kuÉ—i ne ciki ba sababbin arziki ba, an zuba kayan alatu iya ganin ido.

Yana da gine gine manya manya kuma hakan bai tare faɗi da girman gidan ba, gaban wani building suka yi parking Imam ya fito da sauri ya buɗewa Shehi kofa, sai da ya ɗan ɓata lokaci kadan yana kamalla Adu'a kan ya zura kafafunshi dake cikin simple shoe na maza na kamfanin Gucci da ya bayyana kyaun kafafunshi da kaman baya taka ƙasa ya sauƙa, sai da ya tsaya da kyau ya gyara jubba ɗin jikinshi kan ya taka cikin natsuwa ya isa wurin Malam Bala da ya fito yake shan Iska Ammar kuma na kallon barnar da suka yi musu.

"Malam Bala kana lafiya dai?"
Muryarshi mai cike da natsuwa ya fita cikin kulawa.

"Ba dai ƙalau ba Shehi yau na ga abin da ya fi ƙarfin kakata"
Cikin jimami da tsoro yayi magana don Allah ya gani ya ji tsoro, cikinshi wani irin ƙugi yake ba zai manta da mutuwar da ya ga gilmawarta kan idansa ba, 'yan daban nan zare musu imani ake don ta kashe sa da wannan kaifaffen wuƙar ba komai ba ne.

"Tsoro halal ne! Amma karka manta da ambaton Allah a yayin da wannan tsoro na abokin hilitta ya É—arsu a ranka"
Ya faɗa yana kokarin wucewa don shiga ɓangaren shi.
"In shaa Allahu Allah gafarta malam, Mu kwana lafiya"

Ammar ma ya iso yana ce mishi
"Sai Allah ya kaimu Shehi"
Kai kawai ya gyaÉ—a, Imam ya bi shi da abubuwanshi.

Malam Bala fita yayi ya nufi gidanshi dake nan cikin Layin, Ammar kuwa ciki ya wuce don anan sashenshi yake kasancewar shi Cousin kuma amini na kut da kut da Irshad Al-Noor.

Imam kuwa bayan ya zube mishi abubuwan daga parlor ya juyo ya fito, shima waje yayi yana yin sallama da mai gadin don gidansu na dalibai na nan gefen gidan wanda akwai su dayawa daliban ilimin Shehi da kan zo daga garuruwa daban daban saboda ɗaukan karatu, nauyin su da komai a wuyan Shehi yake zama bai taɓa bari sun shiga yanayi ba, kuma suna kwasan ilimi daidai gwargwado ya kan ce musu yana hidimta musu ne saboda kanshi ba don su ba saboda duk wani ilimi da suka koya daga gareshi muddin sun isar to ladan shi a wurin ubangiji ya fi abin da ya basu suka ci a cikinsu har bayan ranshi.

Bai zauna a parlorn ba ya wuce sama, wani parlorn da ya fi yanayi da study room saboda tarin littatafan addini da kuma qur'anai Dukda yana da study room amma ya fi gane parlorn saman tunda shi kaÉ—ai yake rayuwa sai hidimtawa addini da ubangijinsa.

Kai tsaye É—aki ya wuce da sallama kan lips É—inshi, a hankali yake zame komai na jikinshi sai da ya saura doguwar farar cotton wando da farar singlet kan ya nufi toilet.
Ya jima ciki kan ya fito a kimtse cikin fararen kayan bacci masu fadi kan dresser ya je ya fesa turarukanshi na Oud masu sanyi da nauyi wurin shaka.

Parlorn ƙasa ya koma ya ɗauko laptop ɗinshi ya dawo saman a kan gado ya zauna tare da saka glasses ɗinshi ya buɗe ya fara nazarin wani littafin addini, komai nashi cikin natsuwa da kamala yake yinsu, ya san idan da zai duba parlor akwai abinci da Maamah zata aiko amma babu abin da zai iya ci a yanzu don haka dabino da ruwa ya sha bayan tsawon lokaci yana duba littafin da harshen larabci kan ya rufe.

Suratul Mulk da Rahman ya karanto da kai cikin wani irin Muryar qira'arsa mai sanya natsuwa da tada tsikar jiki kan yayi sauran adu'o'in bacci ya kwanta ta hannunshi na dama, dama ba wutan É—akin ya kunna ba dim light ce ya barta kunne kasancewar ba daidai ba ne kwana cikin duhu mai tsanani da ba'a iya kallon tafin hannu.
Babu bata lokaci yayi bacci don kwakwalarsa babu space na wani tunani a lokacin tsantsar gajiya ce da jiki kan yi bayan doguwar hidima na yau da kullum barin ma irin nashi.

********

Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi....

DAÆŠIN ZAMA BY SEEMAHWRITES
JODA BY SADI-SAKHNA
ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH

*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*

*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*

Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin

Sai a tura shaidar biya ta
09039206763

🖤Gureenjoh🖤

ƘARFE ƊAYA BA YA AMO

✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN
(GUREENJOH)

@Gureenjo on Arewapen
@Gureenjih6763 on Wattpad

ADABI WRITERS ASSOCIATION

#THE TRIO OF TALES
(THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY)

TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne.

GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba.

NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k.

*SHAFI NA BIYU*

Ƙarfe uku da rabi ya buɗe idanunsa, a hankali lips ɗinsa ke furta
"Alhamdulillahil lazi ahyana ba'ada ma amatana wa ilaihin nushur"
Cikin natsuwa ya miƙe zaune ya ɗan jima a zaunen kaman yadda sunna ya nusar akan samun cikakken natsuwa bayan farkawa daga bacci kan miƙewa.
Ya zura kafafunsa ƙasa ya sauƙa ya nufi toilet, wanka yayi tare da alwala, ko da ya fito sai da ya shirya tsaf cikin farar thob da baƙar jubba mai gold a aikin hannu da kuma gaban daga wuya zuwa ƙasa, ya saka oil perfumes nashi na Oud da har sun kama jikinshi ba kayanshi kaɗai ba, duk kuma inda zai zauna ya tashi sai ya bar kamshin na lokaci mai tsawo, don shi ɗin ma'abocin son kamshi ne kwarai da gaske musamman turaruka irin na Larabawa, ya ɗora farar Ghutra a kanshi ba tare da ya nemi Agal ba don ba buƙata, a natse yake ajiye kafafunsa cikin tattausan rug ɗin ɗakin har zuwa wurin sallarshi, burner ya kunna sai da yayi zafi sossai ya kashe sai ya ɗora turaren wutanshi a kai, a kan sallaya ya daidaita natsuwarshi kan ya fara ganawa da ubangiji cikin kankantar da kai da sallamawa.

Sai da ya jima yana nafilfili kan ya zauna ya ɗan yi wasu zikirori anan ya ji an fara ƙiran Sallar farko bai motsa ba, ya karanta shafuka biyu daga cikin qur'ani kan ya miƙe yana gyara Ghutra ɗin shi har wurin fuska ya nufi ƙasa, wata farar mage da bata yi yanayi da na ƙasar Nigeria ba ta taho da gudu ya duƙa ya ɗaga ta zuwa jikinshi fuskarshi na sakewa a hankali daga a kame zuwa murmushi mai sanyi har fararen hakwaranshi na bayyana yana shafata a hankali ya furta.

"Sabahulkhairrr yaa humayrah!"
Tayi miyauuu ya saki murmushi, ya duƙa ya ajiyeta ya nufi wani locker ya fitarda canfood ta bi shi da gudu zuwa gefen dining inda anan yake saka mata abinci ya juye mata a kwanon ta shiga ci shi kuma ya fice, sai da yayi rakatanil fajir kan ya isa matsayar limami babban masallacin nashi mai suna Al-Noor Mosque ya shiga gabatar da Sallar asuba duka unguwar ya ɗauki tattausan muryarsa mai tsuma zuciya da sanya salama ya kuma tada tsikar jikin duk mai saurare.

Bayan sun idar bai motsa ba yana nan zaune yana adu'o'i da azkar har bayan mintuna talatin kan ya juyo gabaÉ—aya, duk wasu mamun da suka bi Sallar tashi sun fice ya saura dalibanshi ne na kusa su wurin Ashirin da biyar, matso wa suka yi suka yi musabaha kaman yadda yayi musu nuni da hakan suna kuma gaishe shi da Fatan ya tashi lafiya.
Chapter 2 · 0% Book details