← Book details Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 42

Sashe 13

Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Me Jagaban yake yi basu fita ba?"
Key ta É—auka zata fita Shaly zata bita tace
"Don't!! Don't you dare Follow me don a yanzu ban yarda da ke ba!"

Tana fita harabar ta ɗauki mota bata kula da gaisuwar da kowa ke miƙa mata ba ma ta fice daidai nan kiran Jagaban ya shigo alamun Shaly ce ta kirashi don ba ya gida, amma tana jin kalaman da ya fara ta katse call din bata ce komai ba.
Police station ɗin da suke tayi parking harabar ta fito ta taka ta shiga cikin police station ɗin sanye da wasu baƙaken hoodie riga da wando bata gama jan zip ɗin ba don ta gaba ana hangar farin vest ɗinta, facing cap ne kanta haka idanunta da baƙar space saboda yanayinsu na kwanakin rashin daaɗin rai da ta yi.

"Ina son ganin IPO na case É—in su Pabloo"
Ta Yi maganar ba tare da ta kalli kowa ba ma.

"Waye hakan? Ya za ki shigo mana wuri da gadara?"

"Kai!! ba ni da lokacin batawa a kanku ka faÉ—a min ina zan ga IPO?"
Ta ƙarasa tana matso wa tare da cire glasses ɗin idanunta suka bayyana.

Police É—in kasa sake magana yayi sai hanya ya nuna mata, ko da ta je da zafin ranta IPO É—in ya nuna dole za'a yi musu hukunci kai tsaye ta kira Jagaban
"Baaba! Waennan kwalawar suna neman rigima da ni, duk wanda zaka kira ka kira a sakar mini su Pabloo dukkansu tun kan in kunce musu zaren hauka na rantse"

"Ki yi haƙuri! Ban ma so kika je da kanki ba Sohana bari na yi ƙira"
Wayan ya saukar ya shiga kiran Commissioner da kanshi don connections da yake da shi alfarmar dabanci da sayar da kwayoyi baya tunanin wani Chairman ko member ma na da irinshi.

"Jagaban hakan ba zai yiwu ba a yanzu, don Allah ka ba 'yarka shawara ta É—an dakata tukuna su kwana biyu case É—in yayi sanyi sai a sake su"
Cewar Commissioner É—in

"Me kake cewa ne? Jiya haka ka sanar da ni amma ka ƙi faɗa min dalili, Toh saboda mene?"
"Ko na faɗa ba zaka gane ba amma ka ƙira Excellency zai maka bayani.
Kittt ya katse ƙiran.

Excellency ɗin ya ƙira
"Alhaji Bashir Dantani!"

"Jagaban! Ya aka yi kake kirana a irin wannan lokacin? Akwai wani matsala ne?"
Babban ɗan siyasan Alhj Bashir da kowa ke yi wa ganin mutumin kirki saboda tarin kyautatawarsa da taimako na ganin idanu ya faɗa cikin Muryar sanayya mai ƙarfi tsakaninsa da Jagaban ɗin.

"Akwai wasu Yarana da aka kama na kira Commissioner da kaina yake sanar da ni dole sai na tuntubeka don shi ma faÉ—an ya fi karfinsa"
Jagaban ya faɗa Muryarsa babu wasa don ba zai so a sake baƙantawa diyarsa rai bayan wanda ta sha ba.

"Oh tun shekaranjiyan da aka kama yaran ya sanar da ni yaranka ne amma wannan karon bana tunanin zan iya maka ko wani irin ƙoƙari cikin gaggawa don akwai wanda yayi kane kane ciki da taɓashi daidai yake da lalata siyasata"

"Wanene shi? Meyasa ya fi karfinka?"

"Shi ɗin idon Al'umma ne, ya fi ƙarfina ne saboda ya fi ni kusanci da al'umma magana marar daaɗi ɗaya a kaina zai iya rusa duk wata gwagwarmayana, bari ka ji Irshad ba mutumin da zan yi over looking bane Dukda na tsane sa with passion saboda na sha nuna son sayarsa ta hanyar kudi da sauransu yayi min campaing ta wurin al'umma yana turning ɗina down, ka ga kuwa ya kira Commissioner sau biyu a kan Yarinyarka Diva muddin ya ga ba'a ɗauki mataki ba zai iya bin diddigi kuma zai samu hannuna dumu dumu so ka ga za mun ɓata goma ne biyar bata gyaru ba"

"Irshad!"
Jagaban ya faÉ—a cikin nazari kan ya sake cewa
"Wannan malamin addinin? Irshad Al-Noor É—an masu Twins Enterprises?"
"Kwarai da gaske!"

Jagaban ya ce
"To me zai hana a ɓarar maka da shi idan zai hana mu rawan gaban hantsi kowa ma ya huta?"

"Jagaban! Ka bar wanda ya riƙe Allah ka ji, amma dai yanzu ka yi haƙuri a bar yaran nan a rufe zuwa kwana biyu i promise you za su fito kuma za'a kula da su ba za su rasa komai ba, ai na san kalar amfaninsu a wurina bare ma nan da lokaci kankani zan bukace su"

Sallama suka yi, sai sunan Irshad Jagaban ke nanatawa.
Miƙewa yayi ya ɗauki motarsa ya fita, tafiyar mintuna ya kai shi police station ɗin, shiga ciki yayi ya samu Sohana tana zaune ya kama hannunta suka fito waje har jikin motarsa.

"Baaba ya kake fitar da ni ba tare na ga su Pabloo sun zama free ba?"
Ta Yi tambayar hannayenta duka cikin aljihu.

"Akwai babban dalilin hakan, amma ina so ki kwantar da hankalinki mu je gida zan miki bayani"

Ta haÉ—e gira
"Ban gane ba? Kana nufin an fi karfinka a wannan É—an karamin case É—in?"

A ranshi ya ce ba za ki gane ba Sohana a fili ya furta
"A'a ai babu abin da zai fi ƙarfina muddin abin ya shafe yaran nan, mu je gida zan miki bayani"

Ba don ta so ba ta nufi motarta ta ja tayi gaba ya bi ta a baya har gida, a parlor ya sameta tana kai kawo har ya shigo ciki.

"Me kake nufi Baaba?"

Wayanshi ya zaro ya shiga media yayi searching sunan Irshad Al-Noor sai ga hotunanshi iri iri sun fito duk cikin shigar kamala irin ta Larabawa wasu yana kan mimbari wasu yana zaune yana wa'azi wasu yana zaune kawai wuraren taruka da dai sauransu.

Idanunta ta sauƙar kan fuskar wayar daidai wani bugawa da zuciyarta ta yi, hannu ta ɗaga ta nuna shi da yatsa muryarta na rawa ta ce

"Baaba a ina ka...san shi? Wanene shi a garin nan? Kuma a ina ka san zan sameshi?"

"Kin sanshi ne Sohana?"

"Shi ne!"

"Shi ne wa?"

"Wanda ya..."
Sai ta shafa kuncinta tana runtse ido

"shi ya mareki?"
Gira ta É—aga don kalmar yayi mata mugun nauyi a harshe ba zata iya fitarwa ba idan ta fitar tana jin kaman zuciyarta zai babbake don bacin rai da tafasa.

Hannunta ya kama suka zauna.

"Then wannan malamin shi zai zama makiyinmu na farko a wannan gaɓar, ba zai fito daga No where yayi ta dasa miki baƙin ciki ba Sohana ba zan zuba ido in kalleshi ba! Shi ya sa aka kama su Pabloo a yanzu daga sama kowa na tsoron tsoma baki don kar ya lalata musu siyasa saboda karfin ikonshi cikin al'umma amma idan sun san wata ai basu san wata ba".

Ta riƙe hannunshi.
"Ka bar ni da shi Baba"
Ya girgiza kai
"No! Ki bar ma batun sanya kanki a lamarinshi ni zan ji da komai"
Ta Yi shiru kawai ba don ta ji maganan baban ba, a ranta tana nanata sunan Irshad.

****

Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi....

DAÆŠIN ZAMA BY SEEMAHWRITES
JODA BY SADI-SAKHNA
ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH

*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*

*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*

Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin

Sai a tura shaidar biya ta
09039206763

🖤Gureenjoh🖤

ƘARFE ƊAYA BA YA AMO

✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN
(GUREENJOH)

@Gureenjo on Arewapen
@Gureenjih6763 on Wattpad

ADABI WRITERS ASSOCIATION

TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne.

GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba.

NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k.

*SHAFI NA GOMA*

Daren ranar da abin ya faru ko sau ɗaya bai runtsa ba gabaɗaya bacci ya kauracewa idanunsa, duk tsarinsa na dare ya gama har Adu'a yayi ya kwanta amma da ya rufe idanu sautin sauƙar hannunsa kan fuskarta ke dawo mishi.

Bai taɓa yin abin da yake jin damuwa a kanshi ba sai wannan bayan ya natsu sossai da alqur'ani sai ya fahimci bai kyauta ba dukda laifinta ne amma yana ganin bai kamata ta haka ya ɗauki mataki ba, despite his anger he was raised to respect women don ko ɗaga murya wa iyayensu mata basu taɓa ji mazan na yi ba wannan tarbiyar gidan ne, sannan beside that addini ma bai yarda da duka a fuska ba saboda irin darajar da Allah yayi wa fuskar dan adam. That guilt eats him alive.

Tsam ya bar gadon ya fita balcony ya tsaya hannunayensa duk biyu zube a aljihun kayan baccin jikinsa idanunsa a lumshe yana shakar iskar da ke kadawa kaɗan kaɗan, lips ɗinshi kuma na ambaton Astagfirullah! Har sai da ya ji sassauci kan ya dawo ko da ya duba time biyu har yayi kawai ya je yayi alwala ya zo ya fara nafila sai da yayi ra'aka shidda ya zauna ya buɗe alqur'ani ya shiga karatu, yana yi ɗin amma har lokacin chan ƙasan ranshi guiltness ɗin na nan, hoton jinin lips ɗinta da kuma idanunta na dawo mishi ya san dole ne suka sake crossing path ya bata haƙuri ba wai don ya ramawa Malam Bala mari ba sai don ya san ya ketare iyakar ubangiji a kanta.

Sai da ya ja Sallar asuba kan ya cewa dalibanshi yau babu karatun safe, gida ya dawo ya É—an kwanta bacci saboda headache da ya matsa masa.

Ƙarfe tara ma ya farka saboda rashin sabo da baccin safe ya sake wanka ya sauƙo ya karya da abincin Maamah, yana so ya shiga cikin gidan ya gaishe su amma sai wayanshi ya shiga ringing, ko da ya duba Malaminsa ne daga chan saudia.
Chapter 13 · 0% Book details