← Book details Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 42

Sashe 23

Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Me hirar ya yi?"
Baki sake Ammar ke kallon sa.

"Haka ake hira tsakanin saurayi da budurwa? Ba kyau wulakanci ka sani kuma"

"wulakanci? Kai ma ka san ba halina ba ne, Ammar Ammiey cewa tayi in zo in ganta ba gashi kuma na gantan ba? Sai me kuma?"
Ya faÉ—a yana tsatsare Ammar din da idanunsa.

Ammar rasa ma abin cewa yayi don takaici.

"Allah ya sa a sake saka ka dawowa zan ga wanda zai biyo ka don ni ba da ni ba"

Ya juya yana kallon Ustaz Abdallah da ya fito yana cewa har sun fito ko ruwa basu sha ba inji Na'ima.

Shehi ya ce
"Yamma yana yi ne ina da karatu a masallaci kan magrib"

"Masha Allah, Allah ubangiji ya taimaka na gode sosai da sosai a gaishe da su Alhajin"

Ammar ya amsa suka yi musabaha kan suka shiga mota suka bar gidan.

Driving Ammar ke yi yana tuna wai hirar da Irshad yayi ya yi tsaki ya fi dubu, tattausan Murmushi mai kyau Irshad yake saukewa don shi dariya Ammar ke bashi kaman bai san halinsa ba? Shi dai harkar mata kam ba ya tunani yana da wannan baiwar. Ko ya ce lokacin dogon magana da su ne bashi da shi amma bai kushe ta ba tana da natsuwa kuma tana da ilmi ga kyau daidai gwargwado kuma ta fito daga gidan tarbiya wannan qualities za su sa ya zubawa Ammiey idanu su yi duk abin da suka ga shi ne daidai.

Gida kai tsaye suka yi parking... Baƙin jallabiya ce jikin shi yau bai dora alkyabbar ba amma baki da farin gutra da kuma Agal suna kanshi, iska ke dan kada ɗankwalin yana komawa bayanshi yana kuma bayyana fari sol din fatar wuyanshi zuwa kunnuwasa, yana gama sa kafafunsa ƙasa suka jiyo salati da kuka.

Da É—an hanzari ya daga kai ga bangaren sai ya ga Sumayya ce tafe da sauri tana kuka.

Ammar yayi hanzarin tare ta Shehi na zagayowa bangarensu.

"Menene? Me ya faru?"

"Ya Ammar Daddah...! Daddah ce ta zame ta faÉ—i a toilet ta kasa tashi"

"Subhanallahi!"
Shehi ya furta yana nufan sashen, Ammar ya rufa mishi baya tun kan su fita su Maamah suka fice Wani Yayansu na aurar da 'ya akwai walima kuma duk Daddah ta saka su Goggo hindatu binsu sumayya ce kawai aka bari ta zauna da ita.

Sun same ta kam kafarta da kugunta ba karamin bugu wa suka yi ba.
Ammar da Irshad suka É—aga ta suna mata sannu har mota, sumayya ta shiga baya Ammar ya shiga mazaunin driver Shehi ya shiga seat na gaba suka fice daga gidan Baba Lawan na ta Allah ya kiyaye ya bata lafiya.

Asibiti suka yi wa tsinke, a kan wheelchair aka É—ora Daddah wasu nurses suka tura ta zuwa ciki.

Likitan da ke duty lokacin ya karɓi file din su, Ammar ne ke ba da umurnin a kai ta Amenity duk da sun sani nan din ne mutanen gidan suke kwanciya.

"Ranka ya dade Amenity din nan ya zama out of bond, mun samu wani patient da ake tunani lassa fever ce da shi hakan ya sa mun dakatar da shiga gabadaya ward din sai tests results din shi su fita, akwai dai side ward"

Shehi ya ce
"Ba komai a kai ta chan din"

Likitan ya gyada kai yayi wa nurses din hannu suka wuce da ita, ya bi bayan su su Ammar ma suka rufa musu baya.

Shehi na sanya kafafunsa ɗakin idanunsa basu sauƙa akan kowa ba sai Diva Without intending to ya cigaba da Kallonta har lokacin tana kwance ido rufe hannayenta bisa cikinta drip makale a ɗaya, gashinta kuma baje a kan pillow. Something about her face made him pause ko cikin bacci fuskar rashin mutuncin nan bai chanza ba, kallon seconds ya yi mata ya ɗauke kai ya mayar ɗayan gadon da ake kokarin kwantar da Daddah don gado biyu ne ɗakin.

Ko a fuska bai nuna alamar sanayya ga Diva ba ya ƙarasa kusa da jaddah ya tsaya daga kanta yana mata sannu, kamshinshi na Asad Elixer da ya haɗa da Art of Arabia I ya cike ɗakin.
Sai a lokacin Ammar ya kai idanunsa kan su Diva da tsantsar mamaki yake kallonta Shaly ce kawai a É—akin zaune gefenta.

Ya kalli Shehi sai dai Shehi ya basu baya ne, bai da tabbacin ya kula da ita.
Me ya same ta haka? Ya tambayi kanshi duk da babu mai bashi amsa.

Likitan da ya shiga duba Daddah ne ya sa ya mayar da hankalinshi kansu, ta gurÉ—e ne a kafa dole aka yi mata duk abin da ya kamata ta sha wahala kam amma tayi dauriya da addu'a, shaly sai kallonsu take yadda duk hankalinsu a tashe kan matar da ta tabbatar kakarsu ce duba da girmanta.

"Sannu Mama"
Likitan ya faÉ—a yana kallonta kan ya kalli su Irshad.
"Za ta huta, ga drugs a je a karɓo ta sha ko zuwa safiya sai a yi hoton bayan a tabbatar babu inda yake da wani matsala kan a sallameta"

Ammar ya karɓi takardar.
"Toh Dr. Mun gode sossai"
A tare da Likitan suka fita ya wuce pharmacy.

Sumayya ma ta fita ta yi don ba za ta iya zama Irshad na wurin ba sai ta fito gaban dakin don ta kira su Maamah.

Shaly ta miƙe ta nufi toilet da ke cikin dakin.
Tana shiga wata nurse na shigowa, kan Diva ta tsaya da tray na magani, a hankali ya É—aga idanunsa ya saukar kansu ta cire drip É—in tayi mata wasu allurai a canular É—in kan ta mayar, garin juyawa ta buge sandar drip din sai da yayi taga taga ita ma ta kusa faÉ—uwa amma ta samu tayi balancing ta juya ta kalli sandar ganin babu abin da yayi ta fice.

Sandar drip din ya zubawa idanu ganin yana rawa da alama ya bar jikin ramin kuma nurse din bata kula da hakan ba, ya bi ruwan da ido har kan hannunta dake kwance akan shafaffen cikinta, zai ɗauke ido ya ga ta motsa hannun ta sauƙar gefenta hakan ya ƙarasa jan IV stand ɗin zai faɗo kanta without thinking twice ya miƙe ko kan karfen ya faɗo mata ya tare, a hankali ya mayar da shi cikin ramin dake jikin gadon ya riƙe igiyar ya gyara da kyau don ta ɗan harɗe shi jikin hannunta.

Just then, diva's fingers twitched.

Idanunta suka É—an buÉ—u a daidai ya kalli fuskarta sai ya kawar da idanu ya bar wurin as if ma bai tsaya kanta ba.

Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi....

DAÆŠIN ZAMA BY SEEMAHWRITES
JODA BY SADI-SAKHNA
ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH

*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*

*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*

Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin

Sai a tura shaidar biya ta
09039206763

🖤Gureenjoh🖤

ƘARFE ƊAYA BA YA AMO

✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN
(GUREENJOH)

@Gureenjo on Arewapen
@Gureenjih6763 on Wattpad

ADABI WRITERS ASSOCIATION

#THE TRIO OF TALES
(THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY)

TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne.

GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba.

NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k.

*SHAFI NA SHA TAKWAS*

Ta jima tsaye cikin makarantar sai da wani ya fito yake tambayar
"wacece ke?"
Kan ta É—an zabura.

"Na ɓace ne yi hak'uri"
Ta faÉ—a cikin rawar murya kan ta fito a lokacin wanchan driver din ya dawo ta shiga motar.

"Kin kyauta da baki ja wa 'yar uwarki kwana a lahira ba"

Bata ce komai ba don duk yadda take tunaninsu sun wuce nan, tun kallon da wanda bata sani ba yayi mata ta ji yana magana ashe akwai earpod kunnenshi, suna fara tafiya ko da motar su ta bayyana ta ji yana magana cikin Hausar da ko fahimta bata yi, sai da ya ce mata zai sauke ta ta shiga wani islamiyya zai tafi amma zai dawo ya dauke ta, ya kara nuna mata Ma'u da bindiga a kai ya gargaÉ—eta kan ta sauka.

Sai a sannan ta fahimci binsu ake duk da tsoron da ya cika ta bata yi gigin yin wani abu ba, ko da ta tsaya cikin makarantar babu abin da bata tuna ba, a yanzu a ranta ba Ma'u kawai take jin tana son taimakawa ba har ma da sauran yaran da suke gidan da kuma waenda za su iya faÉ—awa a gaba, don haka za ta jure za ta tsaya ta ga abin da ubangiji ya tsara don zalunci ba ya tabbata.

Wani wuri da bata sani ba suka tsaya ya mata umurni ta sauka ta shiga ciki gefen dama za ta ga wani gini kawai ta ajiye jakan bayan nan ta fito, duk da yadda zuciyar ta ke bugawa haka ta aikata ta dawo ta shiga ya ja suka bar wurin, duk da bata san garin ba amma hanyar da ya bi da ita daban da wanda ya biyo a zuwa yayi wasu irin zagaye sosai kan suka iso tana shiga da gudu tayi inda ta san za ta samu Ma'u ta kuwa same ta zaune da gudu ta faÉ—a jikinta ta sake fashewa da wani irin kuka mai tsuma rai.

****

Kwance kawai Na'imatu take Idanunta na kallon sama tana jin ta a sama, wai ita ce yau Sheikh Irshad Al-Noor ya tako ya zo zance wurinta? Ita ce mai wannan sa'ar? Yanzu watarana da sunan Mijin ta za'a ƙirashi?

Ƙanƙame pillow tayi tana juyi a kan gadon a fili ta furta
"Ya Allah!"
Har ƙoƙon ranta wani irin farin ciki marar misaltuwa take ciki.

Shigowar mahaifiyarta ne ya sa ta natsu kaɗan, ta miƙe zaune.

"Sannu da shigowa Umma"

"yauwa Na'imatu, ya kuka yi?"
Chapter 23 · 0% Book details