Sashe 24
Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Umma da ma an ce bashi da magana sossai idan kin ji ya jima yana magana wa'azi ne toh hakan ce dai gaisa wa muka yi É—ayan dan uwanshi ne yayi ta min tambayoyi, umma kina ga zan iya kwanta masa a rai?
Kai Umma ta gyada cikin murmushi
"kwarai da gaske, ai shi duk abinda mahaifiyarsa take so to ba ya ƙi kuma kin ga kin riga da kin gama shiga zuciyarta, mu cigaba a addu'a in Shaa Allah sai ki ga an yi aurenku kuma kun zauna lafiya har Abada"
Murmushi kawai Na'imatu ke yi tana gyada kai har Umman ta tashi ta fita ta barta a duniyar farin ciki da ta tsinci kanta.
****
Irshad na nan zaune bakin gadon Daddah kanshi ma na ga waya ya ji fitowar Shaly, a lokacin ya ji tana magana.
"Diva! Kin farka? Alhamdulillah!"
A ran shi ya raya ashe sun san Allah. Da sauri ta fita kiran nurses bata jima da fita ba ma Ammar ya shigo rike da ledar magani Irshad ya karbi ruwan gora da ya taho da katon din ya zari daya ya bude murfin shi kuma Ammar ya fitar da magungunan ya ɓalla suka bata ta sha.
"Ba na so in yi bacci ban yi sallah ba"
Ta faÉ—a cikin harshen fulatanci.
"Bai kamata ba kam idan za ki iya daurewa Daddah ki zauna har ki yi magrib É—in"
Ta gyada kai.
"In Shaa Allah, Ku tafi ku bar sumayya Shehi na san kana da karatu bai kamata ka bari ba tunda ai Alhamdulillah Allah ya taƙaita"
Hakane kam, kuma basu musa ba yayi mata sallama akan za su dawo Ammar ya kira sumayya daga waje su kuma suka nufi fita, ko idanunsa bai kai ta inda su Diva suke ba a lokacin Nurses sun shigo da likita suna duba ta, Shaly na tsaye daga wurin kafafunta, bata cikin cikakken lafiya ko natsuwa har kuma lokacin kanta na juyawa don haka bata ma sanin su waye da waye ne a dakin don bata wani bude idanu ba.
"Shehi baka yi mamakin ganin Diva kwance magashiyan a dakin nan ba?"
Ammar ya faÉ—a a sadda suke nufan waje don ficewa.
Ya ɗan lashi lip din shi na ƙasa idanunsa na ƙasa yace
"Wacece hakan?"
Shi Ammar ya zaci Shehi ya mantata ne
"Wannan 'yar daban da ta kora mana thugs da suka tare mana hanya kwanaki muna dawowa daga wa'azi? Wannan da ta mari Malam Bala ka rama masan?"
Cikin ko in kula ya ce
"Ooh! Madallah da ta gamu da daidai ita dama ai gaba da gabanta"
"Gaskiya kam a yadda taken nan ban yi tunani za'a iya kai ta ƙasa ba"
Suna shiga mota Shehi ya ce
"Ka daina mamaki, har kasheta sai a yi kuma ta mutu a banza ta je lahira ta yi wa ubangiji bayani muddin wannan abu da ya same ta bai zama mata izina ba"
Shiru Ammar yai yana tunanin dama 'yan daba suna sauyawa ne? A sanin shi ko sun gama tsoron mutuwar kwana kadan ne daga sun samu lafiya za su komawa abin da suka bari su É—ora daga inda suka tsaya.
Gudu Ammar yayi ta yi saboda sun kusa makara, ko da suka zo basu samu shiga cikin gida ba a nan bakin masallaci suka yi alwala suka shige saboda lokaci ya kure, akwai wani limamin don haka Irshad a Layin gaba kawai suka jera ya barwa wanchan din ya ja don yawanci idan baya nan ko sallah bai riskeshi a gida ba Ustaz Khamis ke yi.
Bayan sun idar dole suka shiga gida kan isha saboda Abba da ya kira Ammar, sun samu har lokacin duka mutanen gidan basu dawo ba, daga gidan bikin duk asibiti suka wuce saboda abin da ya faru ya É—aga musu hankali.
Ammar tare da Irshad suka shiga parlorn Abba É—in suna shiga ya jefawa Ammar takardun hannunsa.
"Me wannan Ammar?"
Abbiey da ke tsaye ya ce
"Usman..."
Hannu Abba ya É—aga masa alamun yayi shiru
"Abba..."
Ammar da ya É—auki papers din yana dubawa ya faÉ—a cikin mamaki da kaduwa
"Abba ni? Ni wallahi ban sa hannu a takardar nan ba...me zan yi da makudan kudade haka zuwa personal account da ko suna bai da shi? ba ni ba ne...."
Abba ya daka masa tsawa
"Yi min shiru Ammar ka daina min rantsuwa a kan ƙarya, dama mutum ba ya taba tsallake jarabawar dukiya! Ammar muna ta jimami kullum yadda kudade suke ɓacewa ba dalili ashe kai ne kake abin da kake so? Ka fa san menene cin Amana... Ka san bala'in dake cikin zamba cikin aminci ka rasa waenda zaka ha'inta sai iyayenka? Wannan ba sa hannunka ba ne?"
Hular kansa ya cire yana shafa gashin kanshi ko zai ji iska na shigansa, gabadaya hankalishi a tashe ta yaya? Shi ya san bai taɓa cin amanar company ba ya za'a yi a ce shine yake yin abinda burinshi a gano inda matsalar take? Meyasa zai ha'inci iyayensa?
Irshad ne ya kama hannun Abba ya zaunar da shi ya taka ya dauko ruwa ya zo ya miƙa masa, ba musu ya sha don haki yake tsabar yadda yake kidime Sam ba ya so zarginsu ya tabbata ta ya zai cigaba da kallon Ɗan uwansa?
Irshad yace
"Abba don Allah ka natsu, ka yi hak'uri...Ka daina maganganu cikin fushi hakan ba daidai ba ne, babu ta yadda Ammar zai yi zalunci ko ha'inci, babu ta yadda Ammar zai fara cin amanar Twins enterprises"
"Irshad shi yasa nake so yayi min bayanin saka hannun nan da kuma me yake yi da kudade haka?"
Abbiey ya ce
"Usman ka ƙi saurarata ne kawai amma na tabbatar kaima zuciyarka bata amince da cewa Ammar zai aikata abu haka ba, ka bashi dama yayi magana cikin natsuwa ba faɗa ba"
Abbiey yace
"Ammar zo ka zauna"
Kaman wanda aka jefar haka ya zauna kan kujerar, babu abin da ya kai sharri ko ƙazafi zafi, bai san taya komai ya faru ba, bai san me signing dinshi ke yi wurin ba, bai san ina kudin da aka fitar ya shiga ba Meyasa shi ne zai amsa tuhumar?
"Abbiey, Abba wallahil Azeem ban san daga ina wannan ya fito ba kuma ko kusa ba ni da alaka da waennan papers din... Ban san ta yadda signature na ya hau kai ba."
Irshad yace
"Na yarda Ammar, na san ba za ka taɓa aikata abu makamancin hakan ba! Abbiey mu bi abin nan cikin natsuwa in Shaa Allah za mu gano bakin zaren"
Abbiey yace
"Haka ne, Nima na tabbatar ba za ka yi hakan ba Abbanku ne ya dauka da zafi amma hakan ba ya cikin tarbiyarku ya sani kaman yadda Nima na sani"
Ammar zai yi magana Uncle Ishaq ya shigo.
"Na zaci kuna Asibiti me kuke yi a gida? Ba dai maganan da muka gama ba ne Yaya Usman ka sake tasarwa?"
Abbiey ya ce
"Shi ne Ishaq, amma ya kare in Shaa Allah idan mun yi isha za mu wuce asibitin kuma don Allah maganan nan ya tsaya a tsakaninmu babu amfanin kowa ya sani"
Irshad ya miƙe ya kama hannun Ammar yana tattare takardun suka fice ba tare da sun ce komai ba.
Sashenshi suka yi a parlor suka zauna Shehi na bin takardun da kallo, duk yadda ba ya son shigar da kanshi kamfanin ya zama dole a gareshi ya shiga.
"Ko ma menene da gayya aka yi, Ammar ka kwantar da hankalinka tunda ka sani mun sani baka da masaniya a kan wannan, komai zai daidaita in Shaa Allah with time"
Numfashi ya sauke yana shafa fuskarsa a hankali yace
"Me yasa sai ni Shehi? Me yasa sai ni za su shafawa kashin kaza?"
"Ko ma menene dalilinsu ubangiji ya fi su kar ka tsawwalawa kanka"
Sun jima sosai suna tattauna wa akan issuen don har signature Ammar yayi tayi a paper suna comparing da wanchan babu maraba, basu gano bakin zaren ba har isha yayi suka fita suka yi sallah, suna fitowa jama'ar gidan na dawowa Goggo hindatu ce aka bari wurin Daddah din don ta ce duk su dawo su huta da safe za su koma.
Abba da Abbiey kuma a lokacin suka wuce, Irshad na da wa'azi don haka shi da malam Bala da kuma Imam suka wuce don Ammar ba ya cikin mood da zai iya zuwa, Ammiey ce ta kira shi yana kokarin nufan Sashenshi.
"Ammar idan ka gama abin da kake yi ina son ganinka mana"
Ya amsa da Toh kan ya wuce.
Bayan yayi wanka ya sauya zuwa kananun kaya ya fito ya nufi sashen Ammie din, ya same ta a parlor tana zaune, dab kafafunta ya zauna
"Ammie barka da dare"
"Barka dai Ammar, Na ji labarin kun samu zuwa gidansu Na'imatu ko?"
Kai ya gyada
"eh mun je Ammie"
"Ya na ganka wani iri? Akwai matsala ne?"
"Akwai Ammie ki taya ni da addu'a kawai"
"Me ya faru? Wace iriyar matsala ce da za ta fitar da kai natsuwarka haka?"
"Ammie kar ki damu kawai adu'arku muke bukata"
"Sai dai mu ƙara Ammar amma kullum kuna cikinta, Allah ya yaye koma menene"
Yadda tayi maganan da sanyi sai ya kirkiro murmushi
"Ammie Na'imatu tana da natsuwa, hankali da tarbiya bata da wani abin kushewa sosai kuma suka dace da Shehi don bata da rawar kai, shi ma bai kushe ta ba"
Murmushi mai kyau Ammie ta yi na jin daadi lallai lokacin auren Shehi ya yi, zuciyarta fess tayi sallama da Ammar bayan sun sake maganar kadan ya fita.
Washegari da safe Irshad bai tafi BUK ba, hasali ma class din ya mayar 2-4 saboda daga asibiti company zai je a yau É—in.
Cikin fara sol ɗin thobe ya shirya, farin har tana daukar idanu, yana tsaye gaban mirror ya dauki turarukansa masu kamshin natsuwa ya feshe jikinsa da su kan ya dauki golden colour ɗin jubba ya ɗora a kai, ya dauki Ghutra dinshi gogagge fari sol ya ɗora a kanshi kan ya saka bakin Agal, agogo baƙi na fata ya ɗaura tsintsiyar hannunsa, ya saka wani zoben azurfa mai bakin dutse sosai yayi kyau kaman ko yaushe.