← Book details Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 42

Sashe 17

Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ko kuma su ma wani abin daban suke bibiya dangane da shi ba, idan dai har kin fahimci shi suke bibiya ina zaton su ma da nasu 'yar tsamar da shi"

Kai ta gyaɗa kawai ta juya ta nufi ɗakinta, a yadda ta ke ta tsaya ƙasan shower babu abin da ta cire saboda yadda take jin wani kunci a ranta, kaɗaici ya ziyarci jikinta Dukda tana zagaye da mutane amma ganin shadows take yi musu basu da wani impact a rayuwarta...

Ko da ta fito bata ji daidai ba sai da ta bugu iya buguwa kan ta zube sai bacci kuma.

***

Zubash ce zaune É—aure da towel bayan ta fito wanka tana gyara jikinta, matashin saurayin mai ji da kuÉ—i ya zuba mata idanu.

"Kina da kyau"

Ta kalleshi ta madubi ta san tatsuniyar gizo dai ba ta wuce ta ƙoki don haka ta ce.

"Na sani"

Yayi murmushi
"kowani irin magana kina da amsar ta"

"hakan ce daidai da ma"

"Zuby wlh tallahi da za ki amince da na aureki"

"ko?"
Ta faÉ—a tana sanya kayanta.

"Da gaske nake yi komai kike so zan yi miki shi muddin za ki killacemin kanki ki zama matata wallahi ba zan kama ki da laifukanki na baya ba"

Hannun da ta miƙo masa ya riƙe ya ja ta ta zauna gabansa suka zubawa juna idanu

"Sallameni Khalil in wuce, aure ne kake so ka je ka nemi wata ban shirya aure yanzu ba"

Ta faɗa tana Miƙewa, a kalaman ta ya jiyo zafin ƙasan zuciyarta daga furucin.

Zai kara magana ta juya kawai ta fice.

Yana da account number É—inta don haka yayi mata transfer É—in kudi masu kauri.

Da kafa take ta tafiya hawaye na zuba mata duk dakiyar zuciyarta bata jin za ta iya danne hawayen.

"Rayuwar da Mama ta zaɓa min kenan kuma shi zan yi har sai ta fahimci kuskurenta, ba zan taɓa tafiya in bar Nana ta faɗa irin halin da na faɗa ba..."

Hawayen ta share ta tari machine zuwa gidan Jagaban, jin Diva bata available suka baje a wurin suna lido da shaye shayensu ana ta shiga da fice na sayan kwayoyi da sauransu.

Wani irin jiniya ne ya karade unguwar kan ma kowa ya motsa a gidan wasu jami'ai suka fara shigowa da gudu gudu.

Babu wanda ya tsorata ko ya firgita har sai da suka shiga cikin parlor suna bincike, abunsun bai taɓa kai wa nan ba kuma sun tsatsare su da bindigu manya a hannayensu.

"Ina shugabanku?"

Biggy ya ce
"Baya nan"

"Ƙarya ne! An tabbatar mana yana cikin gidan nan ko ku fito da shi ko mu shiga mu fiddo shi da kanmu"

ÆŠayan ya faÉ—a, babu wanda ya sake magana suka nufi dakunan gidan suna tura murfin farko, na Diva suka buÉ—e mutum uku suka shiga suka kunna haske ta bayyana a gabansu...

********

Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi....

DAÆŠIN ZAMA BY SEEMAHWRITES
JODA BY SADI-SAKHNA
ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH

*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*

*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*

Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin

Sai a tura shaidar biya ta
09039206763

🖤Gureenjoh🖤

ƘARFE ƊAYA BA YA AMO

✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN
(GUREENJOH)

@Gureenjo on Arewapen
@Gureenjih6763 on Wattpad

ADABI WRITERS ASSOCIATION

TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne.

GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba.

NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k.

*SHAFI NA GOMA SHA UKU*

KAUYEN CHEDIYA
KARAMAR HUKUMAR TSAFE
ZAMFARA STATE
NIGERIA

Duƙunkune suke a ƙasan gadon su rai huɗu ƙarar harbe-harbe da ya karade garin shi ya saka suka dunkule tamkar kifin gwangwani wuri guda ko motsin kirki babu mai kataɓus na yi.

"Inna fitsa..."
Da hanzari mahaifinta ya sa hannu ya danne mata baki, da hannu wacce ta kira da Innar tayi mata alama da ta yi a wurin jikinta na rawa ta saki fitsarin haka har gari yayi haske tarrr suna cikin wannan yanayi sai da suka ji motsin mutane kan suka fito jiki duk gajiya.

Hawaye Inna da Baba suke share wa har yaushe wannan fargaba zai bar su? Har yaushe za su kwanta a kan gadajensu su yi bacci cikin salama?

Babu mai iya cewa uhmm ko uhmm inna ta kama yanmmatan da duk suke ɗigar fitsari ta musu wanka, a lokacin Baba yayi alwala ya gabatar da sallah cikin kuka da roƙon ubangiji na ganin karshen musibun da suke fama da shi a kauyen na 'yan bindiga.

Bayan sun yi wanka suka yi sallah inna ta fara kokarin haÉ—a wutar da za ta dama musu kunu.

Baba kuma wani kullin leda ya saka a gabanshi yana aikin kallo zuciyarshi babu abin da bata raya wa.

"Atika! Yau ne fa muka yi da mutanen nan"

Inna da ta gama É—ora ruwan zafin ta dawo ta zauna kan wani dutse gabanshi idanunta na kan yanmatan guda biyu da babbar bata haura 16 ba karamar ce za ta yi goma sha uku zuwa sha hudu ta ce

"Malam ko za mu mayar musu da tallafinsu, ni dama tun chan hankalina bai kama ba wallahi sai in ga kaman duk wuya duk tsanani gwara a ce suna a gabanmu"

Ya girgiza kai
"kin san lamarin mu ƙara ta'azzara yake Atika, gomnati babu ruwansu azzaluman nan a kan idon iyaye suke haikewa yara kananu wallahi ba zan iya jurar ganin abin ya zo kan 'ya'yana ba, ko babu komai sun yi alƙawarin saka su makaranta kuma su ma za su samu rayuwa mai kyau ba kaman mu anan ba"

Numfashi ta sauƙe hawaye na zuraro mata, rayuwar da suke ciki ya tsananta, babu sakewar zuwa gona ko kasuwa, makarantu a rufe ana fargabar tura yara, idan kana so ka yi ko noma ne sai ka je ka yi yarjejeniya da su rabi da kwatar abin da za ka shuka nasu ne kwata ne naka shi ma a wulakance za su bar maka.

Rayuwa duk inda suka juya babu daaÉ—i a kauyen, wani abu da mutanen mu kuwa gani suke nan ne gidansu nan ne marayarsu, nan É—in ne dolensu duk wuya duk tsanani ba za su iya barin garin ba.

Sallama da aka doka a kyauren gidan ne ya dawo da dukkansu tunanin da suka shiga.

Baba ya amsa wasu mata biyu sanye da hijabai har ƙasa suka shigo cikin fara'a suka shiga gaisawa da jajen abin da suka samu na Shigowar 'yan bindiga jiya kauyen.

"Idan ba matsala za mu wuce yanzu saboda kar su san da zuwanmu"

Hakane ko baƙo ne ya shigo gari akwai awannin da idan ya haura zai iya shiga cikin hatsarin kidnapping don waennan mutane suna da idanu da kunnuwa cikin gari.

"Ma'u, Jidda yehe hose kare mun un dillah, Allah Lamido renu mun wanne mun barka"
(Ku je ku É—auko kayanku ku zo ku tafi, Allah ya tsare ya kiyayeku duk inda za ku shiga yayi muku albarka)

Miƙewa suka yi jiki a sanyaye zuwa ɗakin su kowacce ta ɗauko 'yan tsommokaranta cikin ɗankwali.

"Inna... Tafiya za mu yi mu bar ku?"
Jidda ta faÉ—a sai kuka, Innar ma kuka take amma da gaskiyar malam barin kauyen nan shi ya fi musu alkhairi.

Rako su suka yi har jikin wata coaster ashe ba su kadai ba ne 'yan mata sun yi sha biyar kowacce da kayanta a É—ankwali suma suka bi ayari suka hau suka zauna a tare suna rungume juna.

Haka sai da suka haÉ—u tass kan bayin Allahn nan suka yi musu sallama suka fice da yaran daga garin.

Tafiya iya tafiya suka yi, da suka yi nisa dai an tsaya an ba su pure water da bredi amma daga Ma'u har jiddah kowacce na rike ne da nata.

Ita Jidda ji take a ranta cewa wannan tafiya ba daidai ba ne, duk nan iyayensu sun ba da su ne don su yi rayuwa mai kyau ba kaman na kauyensu ba amma tana jin uneasness akan tafiyar, mutanen sun ce daga wata ƙungiya ne na malamai da suka kafa don taimakon irin yaran garuruwan da zaman lafiya yayi musu karanci, za su yi karatu kuma za'a koya musu sana'ar hannu da har za su iya dogaro da kansu, za su na zuwa gida duk bayan wata uku, har form sun cike.

Jidda ta É—aga idanunta ta kalli garin da suka shiga da bata sanshi ba, ta dai san akwai tarin mutane kwarai, akwai kasuwanci na ta tafiya, akwai hayaniya sossai anan ma sun tafi sossai kan suka isa wani gidan sama a cikin wani unguwa dake lungu sossai.

"Ku sauƙo"
Matar da ta zago ɓangaren su ta faɗa suka fara fita ɗaya bayan ɗaya har suka kare su goma sha takwas.

"Mu je"
Wasu maza na daga bayansu matan sun shige gaba har kofar gate ɗin suka buga aka buɗe ganinsu ya sa mutanen suka matsa suka shige ciki, Jidda na bin halittar da bata taɓa ganin irin sa ba da ido, sun fi yanayi da yadda ake fasalta samudawa ga tsawo ga kwanji, bouncers ne da ke gadin gidan, gate uku suka wuce da irin waennan mutane kan suka shiga cikin matsatsen gidan, mata ne kusan duka suna ta hada hada, abin da ya fara buga zuciyar su Jiddah ganin yadda yan mata ke ta shaye shaye.

Ma'u ta damke hannun jiddah jikinsu na rawa.

Wani mutum ne ya zo ya lissafa su kan ya raba su gida biyar Allah ya taimaki su Ma'u ba'a raba su ba aka nuna musu inda za su shiga, suna shiga dakunan duk aka bi aka rurrufe da kwado hakan ya sake tsinka su.
Chapter 17 · 0% Book details