Sashe 21
Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta tattare duka kuzarin da ya saura mata cikin wani irin karfin hali ta mike tana ganin jiri lalube take saboda idanunta sun rufe da jini dake zuba mata daga kanta da goshinta ga ruwa kuma hannunta ya sauka a kan Tire ta ji shi flat alamun sun fashe shi, jikinta babu inda baya rawa haka ta kama motar ta mike hannunta daya na hakarkarinta da azabar ya fi na ko ina tana tafiya cikin layi idan bata nemi taimako ba mutuwa za ta yi.
A lokacin duka rayuwarta ne ke flashing a saman idanunta, wani irin tsoro ne ya mamaye ranta idan ta mutu bata san ta ya za ta fuskanci ubangiji ba, babu abin da ya taba girgizata a rayuwa irin tsoron mutuwa a yanzu kuma dama haka abin yake.
Daga nesa take hangen wutar mota, bata tsaya ba ta cigaba da tafiya cikin wani irin layi da juriya, ƙiiiiiiiii haka motar ta taka wani irin birki bayan ta dan bugeta kadan don matukin ba wai ya kula da ita ba ne, bata fadi ba sai dai jikinta rabi na ga motar, da sauri ta ji karar bude kofa, sai ta ji ana magana amma ba zata ce ga abin da ake cewa ba.
Ta tafi luuuu za ta fadi ta ji an tare ta, ta ji sadda hannun wanda bata sanin ba ya sauka kan wukar hakarkarinta ta ji sautin salati daga nan bata san me kuma ya faru ba ta karasa ficewa hayyacinta.
****
Jingine yake da kujera kafarsa a harde kaman ko da yaushe shigar larabawa ce jikinshi fari sol din jallabiya da yalkinta ya bayyana tsadarsa, golden color din jubba sai gutra fara tass da ya dora a kanshi idanunshi sanye da farar madubi da ya kara masa kyaun zati.
Hannunshi wani takarda ne yana dan dubawa daga gefe yake jin maganan Ammar.
"Ammar ka fahimta mana ba ni da wani interest kan Twins enterprises duk yadda su Abba suke so nayi aiki chan ba zan iya ba abubuwan gabana kadai sun ishe ni"
Ya faÉ—a yana rufe takardar tare da dora idanunsa farare tass kan Ammar.
"Muna bukatar kwakwalwarka a kamfanin nan, kuma field dinka ne harkar kasuwanci amma ban san meyasa kwata kwata baka son alakanta kanka da abin da ya zame mana dole ba, abubuwa dayawa suna faruwa a cikin kamfanin nan yanzu su Abba shekaru sun ja ba komai ne suke iya yi ba abubuwa sun mini yawa a kullum kuma samun ɓace ɓacen kudade ake ba na wasa ba"
ÆŠan hararsa shehi yayi cikin muryarsa mai natsuwa yace
"Duk babu mai iya gano bakin zaren kuma aka ce sai Irshad? Ka daina saka ni magana Ammar ku yi ko ma menene amma ni kam ba zan sa kaina ciki ba"
Yana kai nan ya mike ya nufi shige wa dakinshi, Ammar ya girgiza kai bai san meyasa a duniya idan akwai abin da shehi ba ya mayar da hankali kai su ne dukiya da kuma kadarorin iyayensu.
Dab zai shige Ammar yace
"Ammm Maamah tace gobe ne za mu je gidan su buduruwarka ko?"
Da gayya ya fadi hakan don ya ci nasarar dakatar da shehin ya juyo ya zuba mishi ido bai ce komai ba Ammar ya tuntsire da dariya.
"Kana kallona ba zance zaka je ba?"
Tsaki tsiriri ya ja ya juya kawai ya shige amma fuskarsa a dan sake yana girgiza kai.
Kai tsaye rigar saman ya cire ya fito balcony dinshi ya tsaya idanunsa zube wuri guda wasu abubuwa na zuwar masa kai, ya jima tsaye nan kan ya kai idanunsa kan agogon hannunshi sai ya juya ya koma dakin kai tsaye ya shiga bayi yayi alwala tare da fitowa ya mayar da rigarsa ya nufi kasa don tafiya sallar magrib da dab ake da kira.
****
"Ni kam Shaly kun ji daga uwar dakinku kuwa?"
Jagaban da shigowanshi gidan kenan ya fada don yayi ta kiran layinta baya shiga, bata cika kwana waje ba ko ta kwana to asubar fari zata shigo gidan, haka bata zama inda babu dayansu na awanni dayawa kuma tun jiya da rana bai sanyata ido ba yanzu ana neman magariba bata shigo gidan ba.
Dukkansu suka mike tsaye obafiya yace
"Tun jiya da ta fita bamu ji daga gareta ba jagaban.... Tattaunawar da muke kenan don babu wanda ya samu layinta, mun ta shigowa Hajjo na cewa bata dawo ba....Anya kuwa lafiya?"
A kan fuskarshi suka karanci tashin hankalin da ya fara shiga don idan akwai abin da jagaban ba ya wasa da to Diva ce.
"Me yasa kuka barta ta fita ita kadai? Kun sani tana da makiya dayawa kaman yadda nake da su me amfaninku a tunaninku na haÉ—a ku ne kawai ku zauna zaman banza a gangarta? Maza ku bace duk inda take ku nemomin ita"
Skipo yace
"Diva fa ko ita kadai ce ba abin wargi ba ce, na tabbatar babu abin da aka isa a yi mata don nan gani nan bari ce wallahii"
Tsaki jagaban yayi
Zai yi magana zubash tace
"Kila dai wani business din take yi mai muhimmanci amma nima ban yarda wai don tana ita kadai wani abin zai iya samunta ba"
Jagaban da yayi shiru yana jin zuciyarsa na rawa ya san ko ma menene ba daidai bane don hankalinshi ya ki kwanciya a ranshi yake jin ba kalau ba, zai yi magana cikin fusata ya ji wayanshi na kara.
Zarowa yayi ya daga cikin wani salo ya furta
"Ya nee?"
A take ya zare idanu duka cikin wani kalar murya marar daadin saurare ya furta
"Whatttt?"
Duk sai suka razana wayan hannunshi ne ya nemi faduwa jikinshi har tsuma yake amma ya kasa magana sai sauraron dayan bangaren yake cikin tashin hankali wayar ta zame a hannunsa.
"Jagaban menene! Me ya faru?"
Suke jero mishi, ba su kadai ba hatta da sauran 'yan daban da suke cike da gidan sai da suka matso ya furta
"Sohana!"
Sai ya girgiza kai.....
Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi....
DAÆŠIN ZAMA BY SEEMAHWRITES
JODA BY SADI-SAKHNA
ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH
*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*
*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*
Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai a tura shaidar biya ta
09039206763
🖤Gureenjoh🖤
ƘARFE ƊAYA BA YA AMO
âœï¸FATIMA MUHAMMAD GURIN
(GUREENJOH)
@Gureenjo on Arewapen
@Gureenjih6763 on Wattpad
ADABI WRITERS ASSOCIATION
#THE TRIO OF TALES
(THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY)
TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne.
GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba.
NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k.
*SHAFI NA SHA SHIDDA*
Cikin tashin hankali suka isa asibitin da aka ce musu Diva tana chan tun cikin daren jiya. Kai tsaye Reception suka tsaya suna tambayar wacce aka kawo emergency.
Nurse din ta kallesu tace
"'yan uwan Suhan?"
Shaly ce ta amsa
"Eh, tana ina?"
Gaba ta shige suka bita har É—akin da take kwance, sai da Obafiya ya rike jagaban ya zaunar don jiri ne ya kwashe shi ganinta, likitan dake kanta ne ya kallesu yace
"Kai ne Babanta?"
"Likita me ya sameta? Su wa suka kawota? Garin yaya hakan ya faru?"
Pascal ya shiga jerowa likitan tambayoyi.
"Ni ma ba zan ce ba amma wani ne ya kawota emergency, hasali ma da asuba ya bar nan don sai da aka yi mata aiki aka iya cire wukar da yake hakarkarinta"
Likitan ya amsa yana sanya hannayensa a aljihu.
Ya kara da cewa
"Ku kwantar da hankalinku she's out of danger dukda dai sai mun yi hoto mun tabbatar da wukar bai ta'ba kodarta ba tukun za mu tabbatar amma duk wani physical ciwo mun magance shi har ta farka ma ta ba ni layinku na kira kan ta sake komawa saboda alluran da nayi mata"
Idanunsu duka zube kanta tana sanye da wasu fararen kayan asibiti riga da wando, goshinta bandage ne da ya rufe rabin gashin kanta, a wuyanta akawai ciwuka haka hannayenta, a hankali Shaly ta karasa ta dan d'aga rigarta sai ta runtse idanu bruises ne sossai a shafaffen cikin nata bayan katon bandage da aka rufe inda aka yi mata dinki.
Zubash da zee idanunsu suka cika da kwallah, bacin rai da tashin hankali duk sun bayyana a fuskokin mazan, duk wanda zai iya yiwa Diva haka sun san ba karamin dan daba ba ne kuma babu ta yadda mutum daya zai iya hakan, duk sun tafi tunanin waye ne? Sai dai sun san suna da makiya ko ta wani bangare sun taba yara dayawa, sun gagari duk 'yan dabar zagayen kano.
Har likitan zai fita jagaban yace
"Likita babu wani hint daga wanda ya kawota? Wanene shi? Ta ya kuka karbeta babu hukuma?"
"Shi karan kanshi hukuma ne, kuma gaskiya ya yi kokari don da bai yi gaggawar kawota ba komai ma zai iya faruwa da ita, shi ya tsaya ya biya kudin komai hatta jini da aka kara mata shi ya bayar saboda babu jinin da zai hau da nata a blood bank...."
Ya É—an dakata yace
"Yauwa abu d'aya akwai rubutu da aka yi a bayanta da kaman wuka JJ"
Wani irin mikewa tsaye Jagaban yayi, ya tafi gabas ya dawo yamma da sauri ya nufeta, likitan ya ba shaly umurnin yadda zata dan karkatata, ya bude kafadarta daga sama ga JJ din a zane guda biyu su ma sai da aka dinka don ya shiga sossai.
Gasping Air jagaban yayi ya koma da baya baya ya zauna hannunshi kan bakinshi.
Likitan ya juya ya fita.
Pabloo ne yace
"Jagaban ka dauki wani haske ne kan waenda suka aikata mata hakan"
Shiru yayi na seconds kan ya girgiza kai sai kuma ya mike zuruf ya nufi fita daga dakin sai kuma ya dakata ya waigo ya kalle su.