← Book details Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 42

Sashe 39

Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Scrolling yayi biyu uku sai ya sake ganin wa'azin a duet wani matashi na kawo ayyukan da yayi ya rubuta daga sama BASHIR DANTANI DA KA SAURARI MALAM
Wa'azin na playing kwaltan da yayi commisioning a satin chan ruwa ɗaya aka yi mai karfi ya kwashe shi har ya fara rami rami, daga nan videon makarantun da ya ce ya kawo tsarin free education har da ikirarin ya kashe makudan kudade kan uniform da zai rabar kyauta sai aka hasko makarantun babu board, babu benchuna babu dai duk abin bukata na karatu yara na zazzaune a ƙasa suna karatu, aka sake hasko asibitoci babu gyara babu kayan aiki da wasu kauyuka da suke fama da rashin tsaro gomnati ta nuna ko-in-kula yana shiga comment dai da ya fi dubu biyu zagi ne da tsintuwa ake mishi wasu na cewa ya gama kenan babu shi ba zuwa senate har wasu na kawo shawarar a tilasta Irshad shiga siyasa ya zama gomna dukda ya nuna baya ra'ayin siyasa kila shi zai tallafawa ƙasar.

Ranshi idan yayi dubu ya ɓaci, Wayanshi ya fidda yana jin dole komai ya zo karshe wannan gaskiya da Irshad ke ikirarin yana faɗa sai dai ya cigaba da faɗarta a lahira. Kira yayi na seconds goma sha biyar kan ya ce
"Za ka ga saƙo"

Daga haka ya katse wayar yana jefar da na hannunshi ya koma ya kwanta kan kujerar dake juyawa da shi idanunshi a rufe.

****

"Pablo fa? Ni sai nake ga kaman bashi da lafiya don tun na dawo na kula yanayinshi ya chanza Sossai"

Diva tayi tambayar tana juya Idanunta a kansu ganin bata ganshi ba kaman yadda jiya ma bai yini da su ba.

"Bai shigo ba fa"

"Ya kamata ku duba shi ai!"

Bata gama rufe baki ba Skipo ya miƙe ya fice ita kuma ta zauna.

"Shugaba ya kamata fah ki ce wani abu kan wanchan banza gajan, me za'a yi masa?"

Tace
"Ya ma sunan shi?"

"Bullet"
Zubash ta faÉ—a tana kashe Sigarin da take sha

Ta Yi dariya
"Paskal ka duba inda za ka same shi daga yanzu zuwa gobe zai san ya shigo territory É—in Diva har yana ikirarin shine shugaban wannan kwaltan"

Shaly tace
"Laifin Obafiya ne da bai tarwatsa shege tun kan ki dawo ba"

"Kin san Jagaban ya hana mu duk wani motsi ya ce babu ruwanshi idan wani abu ya faru a yanzu"

"kar ku damu da kaina zan ganshi in yi maganinshi duk inda ya shiga cikin wannan birni"

Dawowar Skipo ya hana kowa magana yace
"Pablo fah ba lafiya Diva!"

Duk Miƙewa suka yi tana tambayar
"Me ya same shi?"

Basu jira amsar shi ba ma suka wuce zuwa gidan sun yi mamakin yadda suka sameshi tuni Diva ta koma ta É—auko mota Obafiya ya dauke shi zuwa motan suka bar unguwar zuwa asibiti.

An karɓeshi amma bayan tsawon lokaci Likitan yana fito yana kallonsu
"Lafiya Dr?"

Diva tayi tambayar har ranta tana jin tashin hankali don bata son komai ya sami dayansu tana kaunarsu tamkar jininta.

"Patient da kuka kawo ba za mu iya yi mishi komai ba"

"Why? Meyasa alhali ba ya cikin hayyacinshi?"

"Na sani yana sume, kai tsaye zan iya ce muku ya kamu da cutar da ake kira Nerve damage jiyoyinsa sun yi damage duk wani hanyar da za mu bi don basa taimako ba zai yiwu ba don mun nema mun rasa sun ɓace"

"innalillahi wainna ilaihi raji'un"
Yadda suka hada baki suka faÉ—a sai da Likitan ya sake kallonsu yana jin dariya na shirin taso masa ba na mugunta ba sai don tsantsar mamaki ji yadda suke ambaton Allah.

"A matsayinka na likita na san akwai hanyoyin da za ka iya bi don taimakonsa don Allah ka taimaka ka sake duba shi kar mu rasa shi"

Diva ta faÉ—a hawaye na cika Idanunta a Karon farko.

Da gangan ya zo ya ce musu ba yadda za su yi dukda hakan ne babu wani jijiya da za'a samu lafiyayye a jikinshi duk sun lalace amma ba shi ya hana suka taimaka masa numfashinsa ya dawo daidai ba, yayi hakan ne don ya tsorata su akan bayanin da zai musu in anjima akan illar Penta da suka gama gane abinda ya kashe duka jijiyoyin Pablo kenan har ya fara haddasa ruɓewar tsokokinsa.

"Ina zuwa"
Ya faÉ—a yana komawa don ba zai yarda su san da gayya ya tsorata su ba tsaff sai su illatasa a yadda hankalinsu ya tashi.

*****

Shi kam Shehi na haurawa shirin azahar yayi bayan sun gabatar ya dawo yayi bacci bai tashi ba sai la'asar yayi sallah kan ya dawo cikin gida ya fara da shiga sashen Daddah ya gaishe ta ya jima nan har ya ba Mufida Atm akan Malam Bala ya kaisu shopping su sayi abin da suke bukata as tsaraba, manyan kuma a wurin yayi musu transferm kudi masu tsoka su Goggo hindatu na ta godiya don yana da wannan kyauta a kai a kai.

Daga nan wurin Maamah yayi suka gaisa ta mishi godiya kudin da ta gani yayi murmushi kawai, sai ya nufi wurin Ammiey karshe sun taɓa hira ya kuma ci sa'a bata kawo mishi zancen Wanchan yarinyar da ya mance layin ta a inbox don Ammar ya tura mishi tun jiya.

Daga nan ya dawo ya shirya ya fita sallar magrib bayan nan ne ya yamutsa hazo da wa'azin da yayi don ya sosawa mutane ne inda yake musu ƙaiƙayi, bayan isha kuma ya nufi parlorn Abbiey da ya san a chan zai same su da Abba ya ci sa'a kuwa suna nan zaune har da uncle Ishaq da ya fara mishi tsiyar yana mantawa da su saboda shi gidanshi a jikin gidan ne ta waje kuma Shehi gaskiya bai cika shiga ba ribibinshi na dayawa sai in sun haɗu cikin gida a gaisa. Haƙuri ya bashi kan ya zauna suka shiga gaisuwa cikin tsanaki.

Ya sanar da Abbiey batun zuwan Sheikh Nasser duk sun yi murna Abba yace
"Ai to dole a É—aga batun zuwa neman auren nan sai Ubangidanka ya iso a yi da shi Irshad"

Abbiey ma yayi na'am don wannan aikinshi shine uba ga Shehi.

Sun taɓa hira kan ya bar su ya wuce sashenshi yana tunanin da gaske fa suke auren nan dai shi suke shirin dole sai yayi. Layin yarinyar ya zubawa idanu na seconds kan kuma ya sa hannu yayi copying ya mayar calls ya ƙira.

Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi....

DAÆŠIN ZAMA BY SEEMAHWRITES
JODA BY SADI-SAKHNA
ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH

*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*

*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*

Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin

Sai a tura shaidar biya ta
09039206763

🖤Gureenjoh🖤

ƘARFE ƊAYA BA YA AMO

✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN
(GUREENJOH)

@Gureenjo on Arewapen
@Gureenjih6763 on Wattpad

ADABI WRITERS ASSOCIATION

#THE TRIO OF TALES
(THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY)

*SHAFI NA ASHIRIN DA TARA*

"Na san duk kun san da cewa allurar pentazocine ba'a yi ta don bugarwa ba, allura ce mai ƙarfi ta rage raɗaɗin ciwo sannan dole ana amfani da ita ne bisa umurnin likita kuma a asibiti, don rage raɗaɗi da zafin ciwo mai tsanani misali bayan tiyata ko wasu manyan raunuka, saboda tana iya haifar da jaraba da sauran matsaloli ya sa bai kamata a yi amfani da ita gaba-gaɗi ba tare da umurnin likita ba. Wannan patient da kuka kawo yana cikin abin da yake fuskanta na daga cikin manyan hatsarinta."

Duk sun sani duk sun san Pablo is addicted to penta, irin addiction da zai iya yin hauka idan ya ɗauki awwani masu tsawo bai yi ba haka kuma duk inda zai samu jijiya yi yake idan zai yi a wuri ɗaya sau goma muddin jijiyar bai ɓace ba a wurin zai cigaba amma basu taɓa sanin illarta ta kai haka ba.

"Likita zai iya warkewa ko? Jijiyon da ka ce sun ɓace har suna haifar da ruɓewar tsokokinsa duk za su dawo daidai?"
Diva ta tambaya muryarta na bayyana damuwarta don tabbas hankalinta ya tashi.

Likitan ya dubeta yace
"Abu na farko da za'a fara shine dakatar da shi daga wannan allurar saboda lalacewar bata yi tsanani har chan ba za mu ɗora shi kan wasu magunguna da zai murmure a hankali bayan watanni amma muddin bai daina ba zai zama ya ƙarasa lalata jijiyoyin nashi na har abada"

Hankalinsu ya É—an kwanta har ma Diva ta sa a ranta dole ya daina ko da zai koma wani abin buguwar ba damuwa ba ne tunda duk suna yi din sai dai kowa da abin da ya fi so ne amma dole ya bar penta.

Sun bar Pascal ne asibitin suka koma gida ko da ta yi wa Jagaban bayanin yadda abubuwan suka faru tayi mamakin rashin ganin kololuwar damuwa a tattare da shi har kaman ta yi shiru sai ta ce

"Baba"
Ya kalleta
"Ina so bayan an sallami Pablo daga asibiti ko da ya zo neman penta kar ka sayar masa"

"Meyasa?"
Yadda yayi tambayar sai da ya sakata É—an tsayar da Idanunta kansa
"yanzu fa na gama maka bayani Baba idan bai daina ba komai zai iya faruwa da shi gaba, tsokokinsa ruɓewa za su yi Baba"

"Sohana ba zan miki ƙarya ba muddin ya kawo kudinsa yana so sayar masa zan yi, ni sana'ata ce hanyar samun kudina kenan"

Mamaki tsantsa ya bayyana a fuskar Diva.
"Na zaci da ni da su Pablo duk ka daukemu É—aya ne, idan ni ce na zama addicted to penta har yana neman rayuwata za ka cigaba da ba ni?"

"Sohana sana'ata ce ba damuwa ko rashin damuwa ba, muddin shi ya kawo kudi yana so zan sayar masa abin da ya fi muhimmanci kudina ne"

Wani irin abu da bata taɓa ji kan Baban ba ke taso mata, a hankali hawaye suka cika Idanunta amma bata bari sun yi tasiri ba ta haɗiye ta miƙe kawai ta fice daga gidan gabadaya ya bita da kallo a fili yayi dariya

"Hmmm Sohana har yanzu ke yarinyar ce, har yanzu da sauranki a sanin Underground world"
Chapter 39 · 0% Book details