← Book details Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 42

Sashe 16

Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana nan zaune tana gadinsa kafarta ɗaya take ta karkadawa idanunta sun ƙara girma kuma sun sauya, ta ci sa'a ya ɗaga wata waya mai muhimmanci ya tashi ya fita daga dakin taron, zuruf tayi ta fice itama ta zaga ta kofar da ya fita, ya koma ɗan baya inda babu ƙarar speaker don jin abin da na ɗaya ɓangaren ke cewa, cikin kamalarsa yake fitar da maganan yana nan tsaye hannunsa ɗaya a goye a baya, kaman an ce ya ɗaga idanu sai suka faɗa kanta tana tsaye babu wani tazara tsakaninsu sossai, Dukda ba tarr yake kallonta ba idanunsa sun kusa seconds goma a kanta kan ya fahimci ita ce dama ya raya a ranshi sai ta nemeshi.

Ta cire duka boturan Abayar yana iya kallon wandon jeans da farar rigar da suke ciki, a hankali ya bi hannunta da kallo wuka ne take riƙe da tsirararsa yana walkiya kanta babu ko gyale ko hula gashinta na ɗaure daga tsakiya, idanunsa ya ɗan sauƙar sai kuma ya kawar daga kanta gabaɗaya yana ta'awizi.

Sai ya nufi inda take tun kan ta nufo shi yana sauƙe wayan, dab ita ya tsaya, kamshinshi na gauraye numfashinta, abin da take so da burin gani a cikin idanunsa na tsoro ko shakkarta bata ga ko ɗaya ba sai ma ita da yake shirin karyawa alkadari, wuƙar ta damke tana datse hakorinta hannunta na rawa ba na tsoro ko shakka ba sai na zafin da ya tara na kusan wata guda don samun wannan opportunity na ɗaukar fansa a kansa, sai yayi murmushi mai sauti kaɗan.

"Yau ko ni ko kai!"
Ta faÉ—a a fili cikin wata kalar murya tana kallon cikin idanunsa da nata marasa tsoro.

Idanunsa babu firgici kwata kwata sai ma cewa da yayi cikin natsuwa da sanyi

"Da ma na san za ki zo."

Ya ƙarasa yana sake karantarta, idan bai ce ya ji bakin cikin ganinta a Buge ba yayi ƙarya, matasanmu suna lalata rayuwarsu a banza suna ɓata future ɗinsu yanzu ina amfanin wannan?

Sai kalamanshi suka ƙara tunzura zuciyarta, hannunta ta ɗaga rike da wukar tana nuna shi ko ɗar bai yi ba Dukda ya san tana iya cutar da shi ɗin kawai ita ɗin bata kai ya ji tsoro ko shakkarta ba ne, a lokaci ɗaya wani ɓari na zuciyarsa na mamakin irin karfin halinta, duk rayuwarshi tsawon shekarunshi ba zai ce akwai macen da ke iya sanya idanunta cikin nasa ba tare da zuciyarta ta girgiza ba, a idanun wannan ba ya ganin komai sai zarrah da rashin tsoro, tabbas ta gama kangarewa ko ma babu zuciyar gabaɗaya a ƙirjinta bare idanunsa su firgitata ko su sanya mata kwarjininsa kaman yadda suke sanyawa mata da mazan da za su yi arangama da shi kila kuma saboda bata cikin cikakkiyar hankalinta ne.

Cutarwa na gaske take shirin yi masa.
"Ka san me ka yi min? Ka yi abin da ba zan iya yafe maka ba, ka yi sanadin da nake jin muddin na kyaleka ban amsa sunan DIVA ba, a yadda na zuƙi Para ɗin nan yau ko ni ko kai na sake faɗa..!"

Fakonshi tayi ta kai wuƙar da iyaka zuciyarta na son cutar da shi cuta mafi muni da wani irin niyya da bata taɓa ɗora hakan a kan kowa ba na son dakatar da fitar numfashinsa saboda yanayinshi ƙara tunzura zuciyarta yake zuwa turiri.

********

Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi....

DAÆŠIN ZAMA BY SEEMAHWRITES
JODA BY SADI-SAKHNA
ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH

*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*

*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*

Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin

Sai a tura shaidar biya ta
09039206763

🖤Gureenjoh🖤

ƘARFE ƊAYA BA YA AMO

✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN
(GUREENJOH)

@Gureenjo on Arewapen
@Gureenjih6763 on Wattpad

ADABI WRITERS ASSOCIATION

TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne.

GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba.

NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k.

*SHAFI NA GOMA SHA BIYU*

Cikin hanzari ya riƙe wuƙar wanda take ya yanke hannunsa jini ya shiga zuba, da ƙarfi ya riƙe hakan ya sa ta kasa fusga sai idanunta ta zubawa nashi da suka rine zuciyarta na wani irin bugu da ta rasa na jin daaɗi ne ko na menene?

"Yanzu aka barki sai ki kashe ni?"

Tambayar ya zo mata wani iri ga idanunsan nan masu cike da masifar kwarjinin da bata taɓa ganin irinsu ba tsaye cikin nata kaman da gayya ya zuba mata saboda sanin tasirinsu da kaifin su ga duk mai kallon cikinsu.

"Kana raina abin da Diva za ta iya aikatawa kenan, sake wuƙar ka ga idan ban tsayar da numfashinka ba."

"Baki tsoron haÉ—uwarki da ubangiji a ranar gobe? Baki tsoron abin da zai iya biyowa baya? Wace irin kangarewa zuciyarki tayi da baki tunanin komai sai na zalunci? Kin san makomar ki kuwa da zarar kin kashe rai?"

Jikinta tsuma yake yi Dukda tana jinshi amma ba har chan ciki ba saboda already kwayar da ta sha ya É—auki effect.

Shi kuwa har ga Allah tausayi da wani irin karaya akan tarbiya ne ya rufe shi, menene amfanin wannan rayuwar, motsa wuƙar da ya riƙe ta yi wani irin azabar zafi ya ratsa har kwanyarshi da ya sa ya saki wuƙar ta faɗi ƙasa saboda itama ta saki, saurin duƙawa tayi za ta ɗauka ya sa kafarshi ya taka ta ɗago tana kallonshi.

A karo na biyu ya nufi yi mata nasiha bayan haƙuri da ya kudurta zai bata
"A cikin littafin tirmizi an ibn Abbas (RA) Manzon Allah yace mutumin da aka kashe zai zo da wanda ya kashe shi a ranar alkiyama, wanda aka kashe zai riƙo gashin kai da goshinshi yana janyo shi jiyoyinshi a waje suna zubar da jini har wurin Allah madaukakin sarki zai ce ya Allah ka tambayi wannan me na mishi ya kasheni? Sai dalibai suka ce idan ya tuba fa? Man qatala mu'iminan muta'ammidan.....sai ya ce wannan aya tana Nan ba'a share ta ba ba'a sauya ta ba duk wanda yayi kisan kai da gangan sai ya dauki zunubinsa na har abada.."
Ashe baki tsoron gamuwarki da Allah cikin wannan yanayin?"

Zuciyarta rawa yake da ta rasa dalilin durkushewarsa, kafafunta sanyi ne ke shigar su tamkar wacce aka jefa cikin tsakiyar ƙanƙara sai kuma a hankali kwakwalwarta ke juyawa a saninta bata da imani, Meyasa mere kalaman bakin wannan ke neman rushe duk wani ƙwarinta?

Ya taka da kafarsa É—aya gabanta yana kallon cikin idanunta da tsantsar gaskiya a kan harshensa da ya tafi ya ratsa zuciyarta ya furta

"Idan har don na mareki ne kike neman ɗaukan haƙƙin raina ki rataya a wuyanki ki yi haƙuri! Ina baki haƙuri daga zuciyata bisa kuskuren da na yi..."

Waennan kalmomi guda uku na ki yi haƙuri su suka rusa ta gabaɗaya zuwa ƙasa, hawayen da bata san daga ina ba suka cika kurmin idanunta. Tabbas raɗaɗin abin da yayi mata bai kauce nan take ba domin rauni ma yana da nasa lokacin warkewar amma tabbas ta ji saukin nauyin zuciyarta.

Dayawa É—ora waennan kalamai kan harsunanmu sun yi mana nauyi.

"Shehi!! Shehi!!!"
Muryar Ammar ne ke kiranshi don shirun yayi yawa hakan yasa ya biyo bayansa, sauƙe idanunta tayi bata yi magana ba ta zubawa hannunsa da ke ɗigar jini.

Hannun ya É—an kalla ya É—ago sai suka haÉ—a idanu.

"Leave!"

Ya faɗa a hankali don ba ya so Ammar ya zo ya sameta wurin, duk wani bibiyar rayuwarsa da take yana so ya ƙare anan, ba kaskantar da kai ba ne a wurinshi kalaman da yayi mata yayi hakan ne saboda duk wanda ya san rayuwa ya kuma san duniya ta fuskar ilimi ba ya barin mutane su zama abokan gabansa, ko da ko akwai wanda ke gaba da shi ma zai yi kokarin chanza sa domin ya dawo masoyinsa makiyinka zai iya zama mai matukar amfani har ma ya ceceka daga cikin wani bala'in shiyasa ake son kyautata zato da alaqa da kuma zamantakewa a dabi'ance da kuma addinance.

Ko kan Ammar ya iso ta bar wurin, duƙawa Irshad yayi ya ɗauki wukarta da ta bari nan ya naɗe a hanky ya saka cikin aljihu.

"Innalillahi wainna ilaihi rajiun Irshad! Me zan gani haka? Me ya faru?"

Ammar Yayi maganan yana kamo hannunshi.

"It's an accident ba wani Big deal ba ne in shaa Allah"

Zai yi magana Irshad ya wuce daidai suna zagayowa ta enterance na hall É—in motarta na ficewa daga wurin.

Ammar malam bala ya kira a waya akan su zo su kai Irshad asibiti.

Duk yadda suka so su samu wani bayani ma ko magana daga bakinshi bai ce komai ba kuma sun san ba zai ce É—in ba ne tunda bai faÉ—a ba tun farko. A haka suka yi asibiti aka shiga yi masa dressing na ciwon da kokarin tsayar da jinin.

***

Dukda yadda ta fito cikin rashin sanin yanayin da ta ke ciki hakan bai hanata sake sauƙe idanunta kan jar motar da ta kula yadda take tailing Irshad haka shima yake tailing ɗinta ba, bata damu ba don ta san kila Jagaban ne da wannan aiki don haka da wani irin speed ta isa gida.

Ko da ta shiga parlor baya nan, É—akinshi ta je ta yi knocking...

"Sohana! Lafiya kuwa na ga yanayinki wani iri?"

"Baba ba na ce ka kyale min Irshad na san yadda zan yi da shi ba? Then Meyasa ka tura mutanenka suke bibiyata?"

Da É—an mamaki ya ce
"Ban tura wasu mutane su bibiyeki ba Sohana, tun da kika nuna kin fi son handling situation É—in da kanki na bar zancen"

"Then Meyasa sai ta hanyana suke gane inda Irshad ya nufa?"
Ta faÉ—a da mamaki don ta san babanta ba zai mata karya ba.
Chapter 16 · 0% Book details