← Book details Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 42

Sashe 18

Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ma'u da ta fi Jidda jin tsoro ta fara kuka, Jidda taje ta na buga kofar amma har suka gaji suka fadi a wurin basu ji motsin komai ko kowa ba, kaman 'yan prison haka suke yashe a ɗakin jiddah maƙale jikin 'yar uwarta.

Sai dare aka kawo musu abinci babu wanda ya motsa har aka ajiye aka fita, Ma'u tace cikin dasashiyar murya.

"Jiddah tashi ki ci abinci, zama da yunwa ba shi ne mafita ba, dole za mu ci ko don mu samu ƙarfin fuskantar abin da zai je ya zo"

"kin san me suka sa a ciki? Ma'u su waye su? Meyasa suka rabo mu da iyayenmu da sunan taimako suka kawo mu nan suka zubar? Me za mu musu? Me ribansu?"
Ta ƙarasa cikin kuka sossai.

Ma'u ta share hawayenta
"Koma menene za mu rayu jiddah, za mu tsere mu koma wurin su inna, ki ci abinci ba za mu mutu basu san halin da muke ciki ba"

Haka suka tura abincin ba don daaɗi ba, wani irin bala'i ne wannan an fita daga mai an faɗa wuta? Bacci ɓarawo ne kawai ya kwashe su, Washegari da safe aka kawo musu abin kari nan ma sun ci har lokacin kaman kace kule su ce chass tsabar firgita duk sun yi zuru zuru.

Sai da rana tayi kan aka zo aka tattare su suka fito wani parlor mai girma da kujera ɗaya jal, duk a ƙasa aka zubar da su suka tattakure musamman su da suka san junansu waenda suka fito daga chediya, manyan maza majiya ƙarfi ne zagaye da parlorn. Chan wani mutumi ya fito bayanshi mata ne wurin huɗu kowacce da wani irin shiga.

Jiddah ta gane ɗaya daga cikinsu itace ta sa hijabi har ƙasa suka yaudari iyayensu suka kawo su nan ba tare da sun san me za su yi ko me rayuwarsu ke ciki ba.

"Waennan su ne daga ƙauyen chediya J"

Ya kallesu da kyau kan ya zauna, a hankali yake pointing da hannu ana ware mishi har ya gama sorting.

"Waennan su za su mayar mana da kuÉ—in mu"
ya nuna su Ma'u da aka kaisu gefe.

"Waennan a yanzu su zama 'yan aike kan idanunsu su sake buɗewa, a zaɓi wasu cikin na farko a rabar kaya sun yi karanci irin wannan wurin manya"

"An gama J"

Ya miƙe ya fita, matan nan ne suka sake tarkata su Ma'u zuwa wani daki mai gadaje kaman na boarding, Jidda ta tashi da gudu za ta bi Ma'u wani ya riƙota ya wullar ta bugu da ƙasa ta sake rushe wa da kuka.

"Me muka muku? Gida muke so gida za mu je ku bar mu mu tafi..!"
Ihu take da kuka ganin ba zata yi shiru ba ya gwabeta sai da tayi karamar suma ta farfado, a wuya suka É—aga ta zuwa wani daki na daban da gadaje irin na boarding, a ciki akwai wata babbar mata É—aya rike da bulala, ita ta zare mata idanu tayi shiru.

"Ba'a mana taurin kai anan don a take za ki karɓi hukunci, ana cewa ku yi za ku yi ku bari za ku bari, ba'a kananun maganganu ko hira mai yawa idan na kama daya daga cikinku da karya min doka za ku ga abin da zan muku."

Kowacce ta maƙale a bonk da aka ajiye ta, har lokacin Jidda kuka take na rashin mafita.

Da dare aka fitar da su don haduwa ake a ci abinci, a lokacin ne Jidda ta ga Ma'u da sauri taje ta riƙe hannunta.

Ma'u ke duba jikin Jiddan cikin diriricewa take cewa
"Babu abin da suka miki? Basu miki komai ba?"
Girgiza kai Jidda tayi ta riƙe ma'un
"basu yi mini komai ba ke fa?"

Ma'u ta girgiza kai amma hawaye na zubo mata, a kwakwalwarta take ganin É—aya daga cikinsu da bayan an shigar da su É—aki aka zo aka fita da ita kusan awa uku aka dawo da ita aka jefar kan gado jikinta duk jini.

A lokacin sauran 'yan matan suka tsorata don abin da iyayensu suka guda ne yake shirin faruwa a kansu É—aya bayan É—aya...

"Ku wuce ku ci abinci"
Ihun da aka yi musu ya sa suka nufi gaban tray É—in da sauri suka zauna suka shiga ci, kowacce da abinda take tunani.

Suna gamawa aka sake raba su sai da Jidda tayi kuka.

Rayuwa ya zama babu daaɗi, duniya ta ishe su sun gaza sakewa yayinda wasu daga cikinsu har sun fara sakewa, akwai mata a gidan dayawa amma kaman sashe sashe ne, na kusa da su suna da wani buɗewar ido, su suka shiga jikinsu Jidda suka zama ƙawaye.

Suna nuna musu gwara su karɓi rayuwar nan kawai don ba za su taɓa fita ba kila har abada.

"Babu wanda ya taɓa tafiya?"
Tambayar Jidda ya zo musu kaman daga sama

ÆŠayar tace
"Babu sai dai gawa, sai kuma idan sayar da ke aka yi"

Jidda ta sake cewa
"Sayarwa? Kaman shanu ko rago?"

Dariya suka yi basu ce komai ba suka fice.

Ma'u ta fashe da kuka.
"Jidda rabon mutuwarmu ne kawai ya rabo mu da chediya, ya zamu yi? Ina za mu sa rayuwarmu?"

Sai da suka ci kuka aka zo aka watsar da su, a daren Ma'u ta ga tashin hankalin da bata taɓa gani ba.

Tana shirin kwanciya aka zo aka É—auketa wata mata ta mata wanka aka shiryata da kyau kan suka ja ta zuwa wani É—aki a cikin gidan.

Matar ta zare mata ido fuskarta babu digon fara'a tace
"Kwanta!"
Kwanciya Ma'u tayi ta buÉ—ata ta yi examining ta tabbatar budurwa ce Dukda fusge fusge da Ma'u ke yi bata kula ta ba sai da ta gama ta bata wani drinks.

"Karɓi ki sha"
A razane tace
"Me..me? Menene?"
"Kin sha ko sai na tsinka miki mari?"
Ƙin sha tayi kan ta gama girgiza kai ta ji sauƙar marin da ya kusa sumar da ita.
"SHA..."
Hannunta na rawa hawaye na zuba mata ta karɓa ta shiga sha tana gamawa bata yi ko minti ɗaya ba ta fara ganin duniyar na juya mata.

A take ta bugu jikinta ya sake matar ta kama dantsen hannunta ta fito da ita tana layi ta jefawa wani bouncer ya É—auketa sai mota ya ja ya fice daga gidan.

Ba'a dawo da ita gidan ba sai Washegari, Jidda ta fito karyawa tana ta neman Ma'u bata ganta ba, idanunta ya sauka kan 'yan É—akinsu da sauri ta nufe su tana tambayar su.

"Ina Ma'u?"

"An fita da ita tun jiya da daddare bata dawo ba"
A firgice Jidda ke cewa
"Ina aka kaita? Ina aka ce taje?"

Kan su yi magana sai ga Ma'u na shigowa kayan jikinta duk jini ne, tana tafiya tamkar za ta kifa saboda layi sam kallo daya za ka mata ka san bata cikin hayyacinta da gudu Jidda ta isa gareta ta riƙeta...

"Me ya sameki Asma'u? Me aka miki? Ina kika fito? Ji...ni?"
Duk ta firgice sai jero tambayoyin da ma wacce take yi wan ba jinta take ba.

"Innalillahi wainna ilaihi rajiun... Asma'u!!"
Ta fashe da wani irin kukan tashin hankali, wani bouncer ne ya zo ya ja ta...

"Ke kina da hankali? Yi mana shiru anan..."
Kan ya ƙarasa ta dankara masa cizo sai da hannunshi ya fashe ta koma wurin Ma'u da ta faɗi ƙasa ta ɗagota tana kuka da jijjiga ta a haukace tana tambayar me ya faru da ita?

Tsinka mata mari taji an yi ta rarumi flower vase ta jefa mishi a fuska sai ga jini a take wurin ya kacame, bulala ya zaro cikin bacin rai ya rufeta da duka ita kuma tana kare Ma'u tana ihun kuka don abin da take ji a ranta ya fi ƙarfin bulalar da ake yi mata...

Hayaniyarsu shi yayi alerming shuwagabannin gidan.

"Kai Shadow! Menene wannan?"

Wanda aka dakawa tsawar ya tsaya da dukanta.

"J, yarinyar nan ce bata da kunya ko kaÉ—an nake so in yi maganinta"

"Asma'u kina ji na? Me aka miki? Me ya sameki Asma'u?"
A zafafe ta juyo suka haÉ—a ido da wanda aka kira J kuma shi ne yayi kason da yake so da su.

Kallonta yake kaman yadda take kallonshi Dukda rashin imanin fuskarshi bata damu ba...

"Ku mayar da mu inda kuka ɗauko mu, ku mayar da mu kauyukanmu azzalumai macuta....Allah ya isa Allah ya isa! Wallahi duk ba zan taɓa yafe muku ba mugaye... Allah yayi ma 'ya'yanku abin da kuka yi wa Asma'u"

Mutumin ya gyaÉ—a kai lallai yarinyar nan na da tsaurin ido.

"Ita ta maka wannan?"
Ya nuna goshin Shadow.

Kai ya gyaÉ—a cikin fushi.
"Ka yi mata hukunci, sannan ka sauƙe haushin kan ita wannan da take yiwa faɗar"

Girgiza kai Jidda ke yi, Shadow yayi murmushi ya ja Ma'u ba tausayi ko imani yayi wani É—aki da ita Jiddah na ihu tana neman taimako da kai mishi duka amma bai daina ba...

Yana shiga ya rufo ƙofar sai jin ihun Ma'u tayi a gigice ta faɗi a wurin zuciyarta na Gaza ɗaukar abin da ke faruwa da 'yar uwarta...

Ina ne nan? Wanene wannan mutumi? Ta ya za mu tseratar da kanmu? Ta ya za mu É—auki mummunan fansa kan waennan azzaluman? Jiddah ke tambayar kanta tana kuka sossai babu me bata amsa, ya fito yana gyara wando kan ya ja Jiddar yana zaginta babu imani.....

********

Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi....

DAÆŠIN ZAMA BY SEEMAHWRITES
JODA BY SADI-SAKHNA
ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH

*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*

*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*

Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin

Sai a tura shaidar biya ta
09039206763

🖤Gureenjoh🖤

ƘARFE ƊAYA BA YA AMO

✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN
(GUREENJOH)

@Gureenjo on Arewapen
@Gureenjih6763 on Wattpad

ADABI WRITERS ASSOCIATION

TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne.

GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba.
Chapter 18 · 0% Book details