Sashe 22
Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ku tabbatar duk runtsi baku bar dakin nan ba, ku tabbatar baku dauke idanunku akanta ba, ku kuma tabbatar da duk wani likita ko ma'iakacin asibiti da zai shigo dakin nan kan ya ta'ba ta... ku kula"
Yana kai nan ya fice daga dakin, duk da kallo suka bi shi.
Skipo yace
"Anya jagaban bai da masaniyar abin da ya faru fa diva?"
Pabloo yace
"Ba wannan ba Skipo, ban taɓa ganin tsoro ko shakka akan idanun Jagaban ba sai yau dole akwai abin da ke faruwa da mu bamu sani ba"
Shaly tace
"Idan harkarshi ne to me ya sako Diva? Idan fa da karar kwana da sai dai mu ji labarin mutuwarta"
Duk jikinsu ya yi sanyi kowa ya nemi wuri ya zauna suka zuba mata idanu.
****
"Tun yana ƙarami na fahimci cewa zai iya zama barazana a gareni, na tsani ganin yana numfashi..."
Ya faɗa cikin ɓacin rai jin mummunan labarin cewa Irshad zai shiga company ranar monday bisa tilastawar mahaifinshi ko da awanni kadan ne ya dinga leƙawa yana yi.
Daga ɗaya ɓangaren aka ce
"Toh yanzu ya za'a yi da shi?"
"Zan yi tunani a kai amma na rantse ko da zan tafi tsirara sai na tabbatar Irshad bai yi min shamaki da cikon burina ba. Za ka ji ni!"
Yana kai nan ya katse wayar tare da jefarwa kan kujera cikin nazari da zurfafa tunani.
*****
Fusgota yayi ya dora kan wuyanshi tana ihu tana wurge wurgen kafafu da kai mishi duka bai direta ko ina ba sai wani karamin daki.
"Natsu!"
Ya daka mata tsawa
"Duk rashin kunyarki idan na ga dama zan turmusheki ne kamar cinnaka wallahi, kina cin sa'a J ya hana a aikata miki komai ne da yanzu sai wata ba ke ba!"
Dukunkunewa tayi wuri guda tana hawaye, wani tv ya kunna sai ga Ma'u nan an saka mata bindiga marar kara a goshinta.
Ihu tayi tana kuma rufe baki lokaci guda idanunta duk a waje
"Me...me za ku mata? Don Allah kar ku kasheta kar ku kashe min 'yar uwa!"
Kuka take yi tana rokonsu. Shadow yayi murmushi
"Ba za mu kasheta ba ne kawai idan kin yi abin da muke so"
"Ko menene kuke so wallahi zan yi, zan yi ko menene amma don Allah kar ku kasheta...."
"Ashe kina da wayo"
Wasu uniform ya watso mata kaman na islamiyya
"Tashi ki saka!"
Ta tattara, ya juya ya fita cikin lokaci kankani ta shirya kamar 'yar makaranta.
Ya dawo ya bata school bag
"Ki goya wannan jaka a bayanki kamar 'yar makaranta, ki tabbatar kin natsu ko me zai faru sako ne kawai za ki kai ki dawo karki yiwa kowa magana kuma kar ki bari a yi miki, kika kuskura aka samu akasi haka za ki dawo ki kwashi kwakwalwar yayarki a kasa wallahi"
Kai take gyadawa har ya gama ta goya jakar ta sauke hijabin da ya kai mata gwiwa a kai, ya mata jagora zuwa harabar akwai mota guda daya da wani da yayi shigar bahaushe amma talaka alamun dai acting yake as driver ta shiga baya shadow ya sake ja mata kunne kan suka fice daga gidan.
Duk karfin halinta zuciyarta rawa yake, idanunta cike suke da wani irin tsoro haka matukin ke tafiya cikin garin da ba zata ce ga sunanshi ba kalle kalle take ko zata ga wani signboard tayi kokarin karantawa ko zata fahimci ina suke, ta ya za su kubuta? Ta ina za ta fara neman taimako a yadda suke ta tabbatar tsaff za su iya kashe Ma'u hakan ya sa bata ko motsin kirki cikin motar a hankali suka tsaya inda ake ba da hannu, kasancewar farar glass ce da motar idanunta na ta kalle kalle kaman an ce ta waiga hannun damanta idanunta suka faÉ—a cikin nashi da a lokacin ya É—ago.
Yanayinta bai mishi kama da wacce take cikin natsuwa ba hakan ya sa ya dan tsawaita kallon sai ya ga ta yi sauri ta dukar da kai kuma ya ga sadda bakin driver din ya motsa, idanun ya kawar yana mayarwa kasa a daidai lokacin da wutar ta ba da kalar green suka wuce ta hanyoyi daban daban.
"Tsaya...."
Ya tsinci kanshi da furtawa haka kawai yan jin zuciyarsa bata natsu ba.
Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi....
DAÆŠIN ZAMA BY SEEMAHWRITES
JODA BY SADI-SAKHNA
ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH
*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*
*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*
Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai a tura shaidar biya ta
09039206763
🖤Gureenjoh🖤
ƘARFE ƊAYA BA YA AMO
âœï¸FATIMA MUHAMMAD GURIN
(GUREENJOH)
@Gureenjo on Arewapen
@Gureenjih6763 on Wattpad
ADABI WRITERS ASSOCIATION
#THE TRIO OF TALES
(THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY)
TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne.
GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba.
NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k.
*SHAFI NA SHA BAKWAI*
Ammar da yake driving cikin mamaki ya ce
"Me ya faru?"
"Just turn...mu bi wanchan hanyan yi sauri."
Kaman yadda Irshad ya buƙata haka ya juya da sauri suka bi hanyar, Allah ya taimaka ya hange su ya nunawa Ammar akan ya bi bayan motar haka ya cigaba da binshi har gaban wata makaranta da aka Rubuta Asasul Islam, daga dan nesa Irshad ya dakatar da Ammar idanunsa na kan motar har jidda ta sauka ta shige cikin makarantar.
Sun É—an jima tsaye har driver din ya ja ya bar wurin.
"lafiya kam Shehi?"
Girgiza kai yayi
"Lafiya, mu je"
Juyawa Ammar ya yi ya kallesa
"Haka kawai ka sa muka zo nan?"
"Akwai abin da na yi tunani ne amma kaman ba haka ba ne, mu je kawai"
Ya amsa yana jingina da kujerar idanunsa a lumshe yana tunano fuskar Jiddah especially idanunta da suke cike da wani irin yanayi hade da kwallah.
Haka Ammar ya juya suka nufi gidan Ustaz Abdallah, Irshad ji yake kaman kar su isa, sai lokacin yake jin da ma bai saka wa Maamah ranar akan zai zo nan É—in ba don shi bashi da abin cewa mace.
"Manya-manya babban shehi ko in barka daga nan ne ka ƙarasa ciki kar in kalle maka mata?"
Tsiririn tsaki ya ja ya buÉ—e idanu yana kallon Ammar din.
"Me kake kallona haka? Ka ga ka sauƙa mu isa ciki a yi a kawo maka ita nan da kwana kusa mu ma mu samu mu shige daga cikin nan"
Ya fada cikin zolaya da dariya.
"Ammar ka kiyayeni! da ma na hanaka aure ne?"
"Eh mana baka ji su Abba na cewa shekaru ya kamata a bi ba, daga zaran ka yi nima zan samu na yi na gaji da cin tuwon Maamah idan kai baka gaji ba"
Murmushi kaÉ—an Irshad ya yi bai ce komai ba sai kallon gidan da yake, har ga Allah bai san me zai shiga ya yi ba ko ya ce.
"Ammar ka nema mana iso"
"Ni ne ma na ke son matar kenan"
Kallon please irshad ke mishi, ya sani dama ko kwana zai yi wurin ba lallai ya iya shiga ba muddin shi kaÉ—ai ya zo.
Sauƙa Ammar yayi ya samu mai gadi akan yayi musu iso wurin mai gidan ya ce Shehi ne.
Mai gadi ya wuce ciki chan sai ga shi ya fito yace ya sanar za'a fada mishi yanzu, ba'a jima ba sai ga shi ya fito, kamilallen dattijo ne kuma malami fuska a sake yake yi wa su Irshad da suka fito daga cikin motar maraba, wani irin daadi yake ji na kasancewar Irshad a cikin gidansa da sunan nema da 'yar cikinsa babu abin da ya kai mishi wannan farin ciki ya san Na'imatu ta gama dacen mijin kwarai kuma ta kerewa sa'a.
Iso ya yi musu har babban parlornshi suka gaisa sossai har yake tambayar shehi Uban gidansa don ya kwana biyu ma ba ya Nigeria.
"Sheikh na nan yana maganan shigowa ma kwana kusa in shaa Allah"
"Masha Allah, Allah ya tabbatar"
Daga nan ya miƙe ya wuce ciki, chan aka kawo musu ruwa da snacks da drinks.
Shi dai Irshad gabadaya a takure yake Ammar na ta murmushi don dariya yake bashi wlh kaman me tsoron mata, chan sai gata ta shigo da sallama suka amsa sai dai muryar Ammar ce ta fita shi gogan chan ciki ya amsa sanye take da hijab yadin Mercedes Golden yellow har ƙasa, fara ce kuma kyakkyawa kanta ƙasa ta shigo cikin palorn dan dosanuwa tayi kan kujerar tamkar mai tsoron wani abu.
"Barkanku da zuwa ina yini?"
Ta fada cikin kamillalliyar muryarta, daga jin muryar ka san ma'abociyar karatun alqur'ani ce don su suka iya ba har kalmomin hausa hakkokinsu.
"Barka dai malama Na'imatu kina lafiya?"
"Alhamdulillah"
Ta faÉ—a jin murya É—aya ne ya amsa ya sa ta É—an dago sai suka haÉ—a idanu da Irshad da shi ma a lokacin ne ya kalle ta.
"Ina yini"
Ta gaishe shi, ya amsa chan ƙasa
"Alhamdulillah"
Ammar ya katse shirun da ya biyo baya tana ta wasa da fingers dinta ta ji yana cewa
"Ya fama da school na ji kina Part 3 ko?"
"Alhamdulillah! eh ina Part 3 a nan BUK"
"Wani program kike yi"
Ta amsa
"Arabic and Islamic Studies"
"Masha Allah, ubangiji ya taimaka"
Ta amsa da Ameen ya rabbi.
Irshad ya dan yi shiru kenan dalibarsa ce ma bai san da ita ba, kuma babu yadda za'a ce bata san shi a makarantar ba hakan ya sa introducing kanshi da yayi niyya ma ya fasa.
Miƙewa ya yi.
"Ki gaishe da mutanen gida"
Ya kalli Ammar dake kallonshi baki sake ya juya ya fice daga parlorn a dole Ammar ya yi mata sallama shi ma ya bi bayan shi.
A jikin mota ya same shi
"Shehi wani irin hira ne wannan?"