Sashe 4
Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
****
Daga gidan Jagaban bata zauna ba ta yi wa sauran click É—in sallama ta fice, cikin rashin tsoro da sabo da dare ta cigaba da tafiya sai da ta wuce akallah gidaje biyar ta tsaya jikin kofar wani gida da bashi da kyaure, zaure ne kawai a buÉ—e ciki ta shiga ta cigaba da tafiya hannayenta a aljihu tana isa tsakar gidan aka hasketa da toci hannu ta sa ta kare idanunta kan ta lailayo zagi ta buga.
"Wani É—an abu kazan ne wannan?"
"Ubanki ne! Na ce Ubanki ne marar kunya fitsararra, wallahi na gaji na gaji da ganinki cikin gidana kina abin da kika ga dama, rumfar kasuwa ce gidan da za ki fita sadda kika ga dama ki dawo sadda kika ga dama? Ko da shi ke ba laifinki ba ne, laifin Zaliya ce uwaki ba? laifinta ne da ta kasa baki tarbiyar da ta dace"
Ta zuba mishi idanu na seconds.
"Malam Iro na fa sha gargadinka akan idan kana abin ka ka daina saka mahaifiyata a ciki yawwa, yawo kuwa yanzu na fara shi rashin tarbiya ai kura ba zata ce da kare maye ba..."
"Ke Zubaidah!"
Wata murya daga cikin É—aki ta fito tana daka mata tsawa.
"Ashe baki da kunya? Ba mahaifinki ba ne?"
Taɓe baki tayi tana layi kaɗan kadan
"Mahaifina? Allah ya kyauta mijin Asawa ai ba uba ba ne da kanshi ya faÉ—a ya fi a kirga"
"Eh laifina ne a kullum ina ganin laifina tunda na auroki Zaliya kuma na ce na ji na gani zan riƙe miki yaranki, ni Iro ni ne mai laifi..."
Ya tashi ya shige wani É—aki yana cigaba da mita.
"Kin kyauta"
ÆŠakin da ta fito ta juya ta koma.
Wacce aka ƙira da Zubaida ta bi bayan mahaifiyartata ta dage labule ta shige, Maman za ta sake magana kenan ta ji an jefeta da kuɗi da sauri ta ɗauka.
"Ashe da abin arziki kike shine kika tsaya kina ta fitsara tsakar gida. Sai ki samu wuri ki kwanta"
Maman ta faÉ—a fuskarta fesss tana kirga kudaden babu ruwanta da tambayar inda ta samo.
******
Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi....
Ƙarfe ɗaya ba ya amo by Gureenjoh
DaaÉ—in zama by Seemahwrites
Joda by Sadi-sakhna
*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*
*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*
Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai a tura shaidar biya ta
09039206763
🖤Gureenjoh🖤
ƘARFE ƊAYA BA YA AMO
âœï¸FATIMA MUHAMMAD GURIN
(GUREENJOH)
@Gureenjo on Arewapen
@Gureenjih6763 on Wattpad
ADABI WRITERS ASSOCIATION
THE TRIO OF TALES
THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY.
TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne.
GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba.
NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k.
*SHAFI NA UKU*
Ƙarfe Tara da rabi ta farka kaman koyaushe yau ma dai Sallar asuba ya wuce ta dama ɗaiɗaikun ranaku ne take samun sallah kan lokaci amma sai dai tayi daga baya wani sa'in ma ya wuce da haka kenan.
Wanka ta yi ta zo tayi Sallar, wani material da aka yi wa É—inkin garari don a yanke yake ko ta ina ta saka da wando Jean, scarf ne ta É—aura kanta don bata cika barin kanta ba É—ankwali ba muddin zata fita daga cikin É—akinta.
Parlor ta fito ta samu Baba a inda ya saba zama.
"Barka da safiya"
"Sarauniyata kin tashi?"
Kai ta gyaÉ—a.
Yayi murmushi.
"Barka da tashi dama su Pabloo suna chan suna dakonki"
Ta miƙe tsaye
"Bara na karasa, hajjo ta dafomin indomie yadda na saba ci Baaba"
"an gama É—iyar Baba"
Ta fice daga parlorn.
Murmushi ta saki ganinsu duka zaune kan plastic chairs suna jiran fitowarta, Shaly da Obafiya ne suka fara ganin Fitowarta don hankalin Pabloo ya É—auku ne wurin neman jijiyar da zai tsira wa kanshi allurar pentazocine.
"Barka da fitowa Diva"
Ta ƙarasa tsakiyar su suka bata kujera ta zauna tana karbar allurar don taya Pabloo duba jijiya, su ne 'yan uwan da ta buɗi ido ta gani, su ne ƙawayenta kuma su ɗin ne shaƙiƙanta.
Pabloo ta kalla bayan ta gama mishi allurar Penta É—in idanunsa lumshe ta koma ta jinginu da kujerar tunaninta na komawa wani lokaci chan baya.
****
"Pabloo menene wannan?"
Ta yi tambayar ne da zuciya É—aya saboda kwata kwata a lokacin bata haura shekaru bakwai ba, Pabloo É—in kuma zai iya kai wa sha uku zuwa sha huÉ—u kuma a lokacin ma da kanshi yake yi wa kanshi allurar.
"Sunanshi Penta"
"Shi ma Baba na sayar da shi?"
Kai ya gyaÉ—a mata.
"Meyasa kake jin daaÉ—in yi wa kanka allurar bayan na san da zafi? Kuma dama don kawai a bugu aka yin shi?"
Yayi murmushi
"Za ki fahimta ne daga baya sohana amma bana miki Fatan zama É—aya daga cikinmu, ina so ki yi rayuwa mai kyau"
Ta É—an tura baki
"Ka ba ni amsa Meyasa ka ke yiwa kanka wannan allurar?"
"Na fara shi ne saboda Baba ya ce shi ne zai sauƙaƙa min damuwata, shi zai mantar da ni matsalolina kuma da gaskiyar shi tunda na fara bana tunani ko fargabar komai"
"Menene damuwar?"
Ta Yi saurin tambaya.
"Sohana Mahaifiyata ta haifeni ne da wani irin baudadden talakan mutum, talauci irin mai tsananin nan da abin da za'a ci ma wahala yake bare a shayar da ni, suna zama ne a ci yau gobe a kwana da yunwa, a haka kuma ya ƙaro aure ko watanni uku ban rufa ba duk malnutrition ya gama bayyana a siffata, sun yi rigima sossai don ɗan kudin da ya samu ne a gado maimakon ya yi amfani da su wurin gina mu sai ya zaɓi ƙaro aure, ita kuma mahaifiyata ta zuciya sanin irin kangin talaucin da ta juri zama ciki, ganin ba zata iya ba ya sa ta ajiye mishi ni tayi tafiyarta, ba zan ce miki ga yadda na tashi har na shekara bakwai wurin Stepmother na ba, Baaba Salame ta fahimci irin talaucin Baba da rashin makamarshi ne bayan 'yan kudin gadon sun ƙare, ɗawainiyar gidan ya dawo kanta a dole tunda tana sana'a amma fah ko baban kwaryarshi a wulakance, talaucinshi ya ja mishi wani irin raini kuma bashi da bakin magana saboda idan ta bar gidan ma bai san ya zai yi ya ci da mu ba.
Salame macece mai baƙar zuciya da mugunta ban samu wani katabus ba saboda irin abusing ɗina da ta dinga yi, physically, emotionally and mentally na azabtu irin azabar da bana yi wa ko makiyina fata, almajiri ya fi ni gata da kima a gidan uban da haifeni, wata rana ta saka ni wanki sai ta aikeni ban dawo da wuri ba na tsaya wasa a hanya har kudin suka ɓace, tsoron hukuncinta ya hanani komawa tunda ita ke ci da mu da ni da mahaifin nawa shima bashi da say a gidanshi, ko da na tattara courage na koma tayi min dukan da ban yi tunanin zan rayu ba saboda mutuwa ya ratsa idanuna a lokacin, ko da ta kyaleni washegari ta ba ni tallarta yadda ta saba na ƙwai dafaffe a kasuwa wani mai babur ya kaɗe ni.
Hankalina ya tashi ba ciwon kafafu na nake duba ba sai asarar kwan Baaba Salame, ganin irin kukan da nake da halin da na shiga ya sa wasu dattijai suka raka ni gida don yi wa Baaba Salame bayani tunda mai babur É—in ya gudu bai tsaya ba, bayan ta gama jinsu tayi godiya suka tafi suna fita ta fusgo ni ta shiga kirba tana tsine min kaman wacce Allah ya aiko daga ni har mahaifina da na tabbatar yana jinmu tunda ya gama kashe zuciyarsa ba neman yake ba bare ya sa tunanin samu, ta ja ni ta rufe a É—aki kwanana biyu sai ruwa kawai take ba ni wai na ci kwan da na mata asara ba dai abincinta ba, a kwana biyun mutuwa ne kawai ban yi ba Sohana.
Kwana na ukun ta buÉ—e ni na yi furu furu na firgice, ciwon kafafuna basu samu kula ba kudaje ke bi haka ta sake É—ora min tallah a akan idan ban sayar ba yau ma haka zan kwana da yunwa in na ga dama in mata asara.
Nayi kuka na ji na tsani kowa da komai zuciyata ta kitsa min irin muguntar da zan mata, har tunanin buga mata tabarya na yi, nayi tunanin kwarara mata rufan zafi haka dai na gama sake sake na har na sayar na dawo ta ban abincin da bai taka kara ya karya ba, tana shiga É—aki na zuba mata manja a tiles tana fitowa ta shiga wurin wanke-wanke ta zame ta yi mummunan fasa kanta da har aka yi tunanin ta samu brain injury tsoron hukuncin da za'a dauka a kaina ya sa na gudu. Allah ya haÉ—a ni da Jagaban ya É—auke ni tamkar danshi, a wurinshi na samu dukkan kulawa, ya ja ni a jiki inda yake ba ni abinci har sau uku a rana kuma bai saka ni aikin komai kan ya ba ni, shine mutum na farko da ya fara yi min kirki hakan ya sa na ji kome zai faru zan mishi biyayya kuma zan zauna da shi har in gina kaina.
Na shiga matsanancin damuwa da tsoro haka kawai sai in firgita shi ne Jagaban ya fara yi mini wannan allurar da nufin zai sa in manta duk wani damuwana da tsanar da na yiwa iyayena daga haka na saba da shi har ya zama ina iya yi wa kaina da kaina, allurar na rage raɗaɗin ciwo ne (narcotic) musamman ga masu ciwon sikila ko wani ciwon ƙashi mai tsanani... Tun jagaban na yi min a kyauta har ya sakani a sana'ar gyaran machine ina kawo mishi kuɗin shi a lissafe na yawan allurar da nake karɓa.