← Book details Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 42

Sashe 20

Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Nana! Baki yi bacci ba?"
"Ban yi ba ke nake jira"
"Lafiya kam? Akwai wanda ya taɓa ki ne? Ke ba zan je makarantarkun nan in ja wa duka ma'aikata da daliban kunne ba kuwa akan taɓaki?"

"A'a yaya Zubaida kar ki sa a koreni don Allah ina tsaka da paper, ba ma makaranta ba ne ina so mu yi magana ne Yaya"
Zubaida ta zauna tana kallonta.

"Ina jinki"
"ÆŠazu wani ya zo neman izinin iso gidan nan"
Murmushi me kyau da ba kasafai ake gani ba a fuskar Zubaidar ta saki.

"Alhamdulillah zan aurar da ke hankalina sai ya fi kwanciya Nana"
Nana ta girgiza kai tana jin zuciyarta babu daaÉ—i.
"Ba a kaina ba ne akan ki ne. Sunanshi Khalil yana da kyaun hali da natsuwa gashi kyakyawa mai rufin asiri, Don Allah yaya Zubaida ki aureshi"
Miƙewa tayi tsaye ranta na ɓaci
"Khalil ya zo gidan nan?"
Ta gyaÉ—a kai tana fitar da wayanta don kiran Ghali ta san babu mai kawoshi gidansu sai Ghali za ta mishi rashin mutunci kan ta isa ga shi Khalil É—in a gobe ba sai jibi ba.

"Yaya Zubaidah Don Allah"
Nana ta riƙe hannunta.

"Ya suka yi da Mama?"
Bayani ta mata Zubaida ta sauƙe wayan tare da wani numfashin baƙin ciki.

"Ko na yi niyya ba zata bari ba shiyasa ma ba zan yi ba Nana, da dai ke ce zan tsaya kai da fata wurin ganin kin samu ingantaccen rayuwa ta hanyar aure da hayayyafa amma waennan kalaman ba sa cikin rayuwar Zubaida! Mama ba zata taɓa bari ba Dukda a yanzu ba don tsoronta ba ne zai hanani kawai ba zan yin ba ne. Ki yi bacci kina da paper gobe"
Tana kai nan ta kwanta tare da juyawa Nanar baya don É—aki É—aya suke.

Shi dai Khalil Allah yana jin son Zubaida har jininshi, kuma abin da ya gani na Red flags daga mahaifiyarta ba shi zai sa ya ji ya fasa aurenta ba.

*****

Yana zaune gaban Maamah yana shan Kunun gyaÉ—a da farar Safiyar don Dutse za shi, a natse yake sha har ya gama yayi hamdala Maamah ta saki murmushi.

"Da ma ina son Magana da kai Shehi"
Ya gyara zama yana bata dukkanin natsuwarsa.

"Ammie ta kawo min ƙararka"

Ya san kwanan zancen, idanunsa na zube kan bandage na hannunshi da yake nan fresh ta ce

"Maamah na so zuwa amma ban samu lokaci ba ne"

"Ya kamata ka samu ka je ɗin Shehi, kai ne babba duk ƙannenka mazan har Ammar ka tare musu hanya, Ammie kullum tana cikin damuwar rashin auren nan naka don mata dayawa an kawo ka ce ba haka ba kai ka ƙi fitar da naka har yaushe za mu cigaba da zuba ido uhmm?"

Ya sauƙe numfashi kaɗan yana ɗan cizan labbanshi.
"Ku yi haƙuri zan je"

Maamah da ta sanshi sarai ta ce
"Ba ni rana, muddin ka bani ranar zuwa na yarda zaka je É—in amma kalaman zan je basu da tabbas a wurinka"

Ya É—an murmusa kadan
"Ko sunday ne sai mu je da Ammar"

Kai ta gyaÉ—a
"Allah ya taimaka, yanzu za ku wuce dutsen ne?"
Ya miƙe a natse yana gyara Ghutra ɗin kanshi ya sake dan rufe fuskarsa..

"In shaa Allah"
"Toh Allah ya tsare ya kiyaye ya dawo da ku lafiya"
Ya amsa da Ameen yana ficewa.

Malam Bala da Imam suna jiranshi don Ammar yana company yau dama ba koyaushe ba ne suke tare shima yana aiki ne.

Don haka mota kawai ya shiga suka bar gidan suka É—auki hanyar Dutse.

Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi....

DAÆŠIN ZAMA BY SEEMAHWRITES
JODA BY SADI-SAKHNA
ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH

*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*

*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*

Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin

Sai a tura shaidar biya ta
09039206763

🖤Gureenjoh🖤

ƘARFE ƊAYA BA YA AMO

✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN
(GUREENJOH)

@Gureenjo on Arewapen
@Gureenjih6763 on Wattpad

ADABI WRITERS ASSOCIATION

#THE TRIO OF TALES
(THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY)

TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne.

GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba.

NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k.

*SHAFI NA SHA BIYAR*

Kwananta biyu da Æ´ar uwarta amma ba za ta ce ga halin da Ma'u take ciki ba, wanka sai ta kama hannunta ta kaita har bayi tayi mata, hatta ruwa wannan sai ta bata ta sha idan bata bata ba to ko kwana za su yi Ma'u ba zata tambayi ruwa ba.

Hankalin Jidda ba'a karamin tashe yake ba tayi kuka har kaman ba gobe tayi ta rokon su akan su kai mata ma'u ko asibiti ne amma babu wanda ma ya kulata bare su nuna sun san da su take.

Yau ta fitar da ma'u harabar gidan inda iyakacinsu nan ne, akwai masu wanki akwai masu shaye shaye akwai masu hira, kusa da su wata ta zo ta zauna Jiddah da tayi wani irin zuru zuru ta kalleta hawaye na cika mata idanu tace

"Don Allah har sai yaushe ne za su bar mu mu tafi? Babu wani da zai iya kiran hukuma a cecemu? Iyayenmu na chan a tunaninsu sun sama mana rayuwa mai kyau ashe rami suka haka suka binne mu ba tare da sun sani ba..."

Yarinyar ta sauƙe numfashi tana dafa kafadan jidda tace
"Da haka za ki saba amma bana tunanin hukuma za su iya aiki akan waennan azzaluman, ta wani bangare ma zan iya cewa bakinsu daya da manyan, kin ga gidan nan ban san shekara nawa yayi yana existing ba amma ni a karan kaina shekaruna shidda, idan kin ga kin fita an sayar da ke ne ko an yi safararki zuwa wani ƙasa da babu yadda za ki yi zama dole, za'a turaki aikatau ko ma zinace zinace, babu yadda kika iya jidda gwara ki saki jiki Ma'u kuma Allah ya bata lafiya don wasu dayawa sun shiga irin wannan trauma amma da kansu suke overcoming har ma su yi adopting wannan rayuwa da muka tsinci kanmu"

Jidda da zuciyarta yake bugawa da karfin gaske tace
"idan iyayenmu sun neme mu fah?"

"Na gayamiki ba ta yadda za ki sadu da iyayenki jiddah, su karan kansu basu san ta inda za su fara nemanku ba komai da aka yi fake ne"

Hawaye ne ya shiga zubowa jiddah tana kallon Ma'u dake zaune kawai kaman wacce aka dasa idanunta wuri guda ba uhm ba uhm uhm.
"Akwai Allah in shaa Allahu za mu fita, in Allah ya so ya yarda rayuwarmu ba zai tagayyara ba"

Ta karasa da kuka, tana jin labari ana safarar mutane, tana jin labarin irin waennan duniya na karkashin kasa amma bata taba sanin da gaske suna nan cikin al'ummarmu ba, suna amfani da 'ya'yan wasu don biyawa kawunansu bukatu, suna zaluntar iyaye su yi musu shigo shigo ba zurfi su yi musu illah mafi muni a rayuwa.

"Ke!"
Ta É—aga kai ta kalli Shadow
"tashi mu je!"
"Ina?"
Ba tsoro tayi tambayar don ta ci alwashin ba zata taba jin tsoro ko shakkarsu ba, duk kuma wanda yayi mata a cikinsu za ta rama sai dai su kasheta.

"Kin tashi ko sai na saɓeki a kafaɗa?"
"Allah ya tsari jikina ya hadu da kazantaccen jikinka..."
Ya kai hannu da niyyar marinta tayi saurin mikewa tsaye ba zato ta ji....

****

Iska ne mai karfi ake na alamun ruwa zai iya saukowa any moment, kasancewar farkon shigar daminar ce ba kowa ke da tabbacin zuwan ruwan ba hakan ya sa wasu dayawa basu yanke al'amuransu ba, kaman da wasa ruwan kuwa ya zo da karfinshi wanda tun yamma ya fara zuba har tsakar dare bai daina marka-marka ba.

A daidai lokacin Diva tana zaune cikin motarta hankalinta na ga jikin mirror din motar kofan motar a bude yake duk jikinta kuma na ta waje wani hayaki take busawa tana sake nazarin motar.

Tun arangamarta da sheikh ta lura da motar amma bata taba zaton ita motar ke bibiya ba sai a kwanakin nan biyu bayan ta manta ma da wani sheikh da wa'azinshi.

Tana so ta fahimci me suke so da ita hakan ya sa ta biyo hanyar da ta tabbatar babu wani motsi na jama'a ga kasancewar ruwa ko ina tsitt ko wani mahaluki na gidansa yana bacci.

Ta kusa mintuna goma a haka kan ta sauka ta nufi motar, sai suka yi saurin kunnawa suka yi baya in ta matsa gaba sai su yi baya, wani irin bacin rai take ciki idan zaka yi abu da ita kayi kawai bata son rufa rufa ko wani kumbiya kumbiya, rai a bace ta dawo motar ta zauna tana kokarin yi wa motar key sai ta tsaya chakkk, hannu ta kai za ta dora kan wukarta ta ji an saka igiya ba zato an shake mata wuya daga seat din baya, wani azababben zafi na shigewar makami na ratsa har kwakwalta daga kasan hakarkarinta da alama wuka ne suka soka mata kuma ba karamin shiga yayi ba.

Kokawa suka fara duk yadda ta so ta ma rike igiyar abin ya ci tura har sai da ta kusa suma suka saki sama sama ta ji an janyeta waje kusan mutum hudu ne suka shiga dukanta da kafa da hannu, gabadaya ta jiggata ta fice a hayyacinta, da kyar suka barta ganin tana aman jini, cikin azaba ta runtse ido jin sun juyata sun sa wuka suna wani zane daga kafadarta daga nan suka juya suka tafi suka barta anan yashe ruwa na zuba mata chab chab chab.
Chapter 20 · 0% Book details