← Book details Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 42

Sashe 30

Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tasbihi yake yi da yatsun hannunsa dayan hannun na riƙe da waya yana dannawa ya shiga jin sautin takalmi na shiga kunnenshi don sauti ne na takalmi mai tsini da ya haɗu da tiles sai yake ba da ƙarar marar Daaɗin saurare a wurinshi bai ɗaga kai ba Sam.

Ita kuwa kujerar da yayi mata ta samu ta zauna bayan ta tura milk color traveling bag É—inta da ta É—ora mishi kit din Saman hannun gefenta kaÉ—an kafa É—aya ta É—ora kan É—aya tana cigaba da cin chewing gum yana ba da sauti fuskarta na kan waya.

Tsakin da bai san ya fita ba ya É—an yi rashin manners din yayi yawa, ga kamshi da take bazawa tamkar namiji da alama bata da masaniyar ubangiji ya haramta irin wannan kamshi ga mace, saka Turare har ya cike wuri ga mace ba ado ba ne illa kwasarwa kai zunubi saboda duk namijin da ya Shaka har ya burge shi tamkar yayi zina ne da macen alhakin kuma baya kan kowa sai kanta.

Waya aka ƙirashi ya amsa yana ɗago fuskarsa Kasancewar suna saitin juna sai idanunsa suka sauka kan fuskarta, sallamar da yayi ita kuma muryar ya sa ta ɗago ta kalli wurin sai karab suka haɗa idanu...

Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi....

DAÆŠIN ZAMA BY SEEMAHWRITES
JODA BY SADI-SAKHNA
ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH

*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*

*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*

Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin

Sai a tura shaidar biya ta
09039206763

🖤Gureenjoh🖤

ƘARFE ƊAYA BA YA AMO

✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN
(GUREENJOH)

@Gureenjo on Arewapen
@Gureenjih6763 on Wattpad

ADABI WRITERS ASSOCIATION

#THE TRIO OF TALES
(THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY)

TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne.

GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba.

NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k.

*SHAFI NA ASHIRIN DA BIYU*

Kowannensu idanu ya janye a take, Wayanshi ya cigaba da amsawa yayinda ta fitar da nata wayan ta shiga taɓawa dukda ita ba gwanar media ba ce amma zaman shirun ya ishe ta.

For over 30minutes babu wanda ya motsa cikinsu, ganin lokacin magrib yayi ya sa ya miƙe ya tafi ɓangaren masallaci yayi sallah ya sake dawowa same spot ya zauna, har aka yi isha saboda yanayin delayance na jiragenmu suna zaune kan aka fara announcement za su yi boarding, shi ya fara Miƙewa ya ja trolley ɗin shi yayi gaba, sai da ta bari ana final announcement ma kan ta miƙe kamar ba za ta tafi ba ta nufi wurin shigewa ɗin, duba ticket ɗinta aka yi ta wuce zuwa ciki a hankali take duba seat number ɗinta tana zuwa inda yake zaune ta ɗaga kai ta kalli number ɗin abin mamaki ita ce daga ciki jikin Window shi yana daga gefe kuma ya riga ya zauna.

Luggage ɗinta ta ɗora a sama tana jin bai ma isa ta ƙi zama saboda shi ba, dukda yadda take jin wani abu mai kama da nauyi da bata taɓa ji kan kowa ba.

"Excuse me pls!"

Faɗin haka da ta yi ya sa ya ɗaga kai ya kalleta suka haɗa ido sai ta nuna seat na gefenshi wurin zamanta, dole ta yi baya ya miƙe ya fita kan ta shiga shima ya zauna.

Har suka ɗaga babu mai magana, ta kwanta jikin kujerar tana kallon waje shi kuwa karatun alqur'ani yake yi chan ƙasa ƙasa amma muryar na shiga har cikin zuciyarta, tsikar jikinta ke tashi, ta rasa Meyasa take jin amsa kuwwar karatun har cikin kanta dukda ba lallai ma wani ya san yana yin ba amma fessss take ji, karatun ya saukar mata da wata natsuwa da bata san akwai shi a jininta ba, ko da aka kawo musu snacks ma ruwa ta karɓa kawai ta sha tana sake yin lufff shi kam babu abin da ya karɓa.

Sun sauƙa Abuja dare ya ɗan fara ga ruwa da ake ta tsulawa kamar da bakin ƙwarya, kusan kowa ya fita yana zaune bata motsa ba sai da ya miƙe ya ɗauki akwatinshi ya fice itama ta miƙe ta ɗauki nata ta fita.

A terminal ta tsaya tana kallon yadda ruwan ke zuba gashi babu wani taxi, kalle kalle take É—an yi wannan ne karonta na biyu zuwa Abuja din kuma ba wai ta san yanayin garin ba ne dukda ko É—arrrr babu uban da take tsoro ko shakka kawai bata san yadda za ta fara ba ne.

Wayanta ta kalla ta sake duba sunan hotel da Jagaban yayi mata booking akan anan za ta zauna har sai ya ce ta dawo.
Numfashi ta É—an sauke Idanunta na yawo kan mutanen da ake ta É—auka ta É—an lashi lips kaÉ—an kan ta harÉ—e hannu tana tsaye kawai bata gama yanke hukunci ba.

A hankali ta ga wata black Mercedes ta yi parking gabanta sai matukin ya sauko yana rike da lema ya zo inda take cikin girmamawa ya ce

"Madame ko za ki shiga mu rage miki hanya? Kin san nisan dake tsakanin nan da cikin gari kuma taxi sun É—auke saboda ruwa"

Wani irin kallo ta mishi don bata yarda da shi ba, sai glass na motar ɓangaren da yake na baya yayi ƙasa Idanunta suka sauka kan Shehi dake zaune a baya yatsina fuska ta yi.

"Dukda ban nemi taimakonku ba amma mu je!"

Da sauri ya É—auki Luggage É—inta ya sa a baya ta buÉ—e gaba ta shiga don bata jin za ta iya sake zama kusa da wanchan mutumin, haka ya ja ya fara tsula gudu a titin na Abuja a lokacin sheikh ya amsa waya yayi biyar zuwa shidda sai tsaki take ja don an cika mata kunne.

"Ina za mu ajiye ki ma?"

"Grand Cubana hotel, Jabi"
Ta faÉ—a kai tsaye.

"Wow! What a coincidence ai mu ma chan muka nufa"
Baki ta taɓe kaɗan shi kam sheikh bai ma san suna yi ba.

Har zuciyarsa kuma taimakon musulunci ne yayi mata don za ta zama stranded a inda take, hakan ya sa yayi wa drivern umurnin su rage mata hanya zuwa open place da za ta iya samun abin hawa, ganin ta fara fuskar rashin mutunci ya sa ya sauke glass din don ta tabbatar ba cutarta za su yi ba bare ma su cuceta su ce sun cuci wa? Ya ayyana a sadda drivern ke saka mata kayan da shigowarta kamshin ta da yayi ta hawa mishi kai gabadaya zaman flight din ya sake yi mishi sallama, Sam ba ya son kamshi mai ƙarfi irin nata shiyasa lattafas suka zama best perfumes dinshi kamshi ne masu sanyi da natsuwa dukda shima ya kan cika waje musamman na maza ɗin amma nata ya yi over a hancinshi.

Ko da take Faɗin hotel da za ta je bai yi mamaki ba, haka suka cigaba da tafiya shiru yana amsa call sa'i da lokaci har suka isa hotel ɗin, drivern ya sauƙa ya buɗe mishi ko kan ya gama sauƙa ta zagaya ta buɗe booth din ta fitar da akwatinta da kit ɗinta.

Har ta taka baya kaÉ—an kan ta ce
"Thanks"

Ya kalleta kaɗan sai ya gyaɗa kai ta juya ta yi ciki, sunanta kawai ta basu suka bata key a daidai shi ma ya shigo ya faɗi sunanshi suka karbeshi zuwa cikin elevator, tuni an kaita corridor din da room ɗinta yake ta ƙagu kwarai ta ga ta kwanta ga shi yunwa take ji na bala'i don rabonta da abinci tun safe, tana shiga ɗakin ta tura Luggage ɗinta ta faɗi kan gadon rigingine Idanunta rufe.

Bata san adadin lokutan da ta ɗauka ba kan ta miƙe ta fara zame kayan jikinta sai da ta cire tas kan ta nufi toilet tayi wanka, hotel room din ya mata kyau kwarai hotel ne mai matsakaicin tsada amma komai intact har da kayan bacci sabbi fill a Leda bayan towel da su tissue da ake tanadarwa duk wani sabon customer.

ÆŠaure da towel din ta nufi akwatin ta janyo ta buÉ—e me za ta gani? Neat and clean jallabiyoyi ne Kala daban daban a jere ga su Ghutra da jubba har nan a shirye a kuma goge.

Baya ta koma ta zauna dabas fuskarta a kwaɓe!

"Garin ya muka yi exchanging akwati da wanchan mutumin?"
Ta faɗa a bayyane kan ta ja tsaki ta miƙe tsaye ta tafi ta dauki kayan baccinsun farare tass ta sa bai mata yawa ba riga da kuma wando ne free sai ta ɗaura dankwalinta a kanta.

"Allah ya sa bai buÉ—e min akwati ba don wallahi zan iya yi masa rashin mutunci akan akwatin nan abubuwan da ke ciki sun fi karfin karamin kanshi na wa'azi"
A bayyane take maganan cikin sauri.
Dankwalin kawai ta mayar ta É—aura a kayan da ta cire ta zura lofas na hotel din farare ta ja akwatin ta fice daga É—akin kai tsaye reception ta koma don bata san inda yayi ba ma a cikin hotel din.

"Sannu! Akwai wani da muka shigo tare mun yi exchanging Luggage can you please check his room number for me?"

Matar ta fahimci frustration dake muryar Diva ga gajiya don haka ta amsa mata da
"OK ma lemme check"

Ta duba numbern É—akin sai dai ba ta so ta yi gaggawar exposing customer sai ta shiga kiran landline na dakin amma bai É—auka ba sai da Diva ta buga kan desk na gabanta.

"Malama jiranki nake kin bar ni tsaye wata tsiyar zan je in É—auka dakin da sai kin sanar masa? FaÉ—amin numbern in je da kaina kafin ya buÉ—e min akwati!"

Ta É—an firgita kan ta ce
"Sorry ma! It's room 409 block B"
Chapter 30 · 0% Book details