← Book details Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 42

Sashe 28

Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wallahi wallahi Subai'a idan na miki Allah ya isa sai Allah ya saka min akan yaranki, Allah ya gani kuma shine shaida iya kokari na yi wurin tarbiyatar da yarinyar nan amma ke bata taɓa laifi a idanun ki ba, babu wanda ya isa ya hukuntata a duniyar nan baki ɗaga ido kin kalleshi kin rama mata ba, yanzu yadda take yawo lungu lungu da gungun 'yan daba ashe bai zama miki izina ba? Wallahi ko rantsuwa zan yi babu kaffara Zainab ce ta ɗauki sarkar nan don haka ku fitar na gaji da biyan abinda ban ci ba"

Wacce aka kira Subai'a ta kalli Alhajin tace
"Ai dama abin da kake nema kenan kiris ka daura min alhakin lalacewar Zainab, kun kyauta ke kuma suwaiba in karya kika mata ma ke da Allah. Zainab ke tashi mu tafi"

Ta miƙe tare da jan hannun Zainab din suka fita, Alhj ya tafi da baya kaman zai fadi suwaiba ta tare shi suka zauna.

"Ba damuwa Alhj na hakura da sarkar duk da yana cikin zinari na mai tsada amma ba komai, Allah ya shirya mana ita ya sa ta gane don Allah kar ka É—aga hankalinka"

"Suwaiba na gaji da ganin Subai'a da Zainab a gidan nan na gaji"

"Na sani amma babu ta yadda hannunka zai rube ka yanke ka yar, kana addu'a baka taɓa gajiya ba ka cigaba in Shaa Allah za su chanza"

Ya kalleta
"Kin san dai Ƙarfe ɗaya bai taɓa amo ba dole sai ya haɗu da wani karfen, kina ga Zainab ta cigaba da zama da Subai'a da ta watsar da alhakin tarbiya da Allah ya ɗora mata ta ɗauki soyayya mai muni ta ɗora wa kanta akan yaranta zai bari su shiryu? Ba Za su taɓa shiryu wa ba ina tsoron tambayar Allah akan yaran nan"

Shiru suka yi cikin jimami, tsawon shekarun talatin da wani abu suke rayuwa tare da 'ya'yansu amma duk wanda ya shigo gidan ya san Yaran Suwaiba daban da yaran subai'a, samm bata yarda da abin da zai taɓa su ba, bata yarda ko da wasa sun yi laifi wani lokacin ko a kan Idanunta kuwa za ta mutsuke ta nuna basu yin ba kuma ya sha kenan.

Wannan sakacin ya jefa Zee-zee cikin halin da take ciki har ma take bibiyar Diva dukda kudin mahaifinta, yayi iya kokarinsa har Rehabilitation center ya kai ta Maman taje ta ciro ta, kuma ba ita kaɗai ba har yayyunta biyu duk a watse suke a kan titi babu wanda ya tsaya ya tsinana wa kanshi komai ga yaran Suwaiba har suna iya ɗaga abu da alfaharin nasu ne na ƙashin kansu.

Suna fita Zee za ta fice daga gidan Maman ta riko ta
"Ina kuma za ki je? Meyasa bakya gajiya da janyomin magana ne?"

Kallon yaushe aka fara wannan ta mata kan ta zare hannunta
"Wurin Diva za ni"
Tana kai nan ta yi gaba, a cikinsu duk babu mai daukar abin wani idan ka ga sun yi abu da abin wani to sun lalata ne don Diva bata shiri da ɓarawo bata son sata kwata kwata, basu damu da inda Zee ke samun kudi take saye sayen abubuwan mayenta ba har wani lokacin ma ta sayawa kowa free sanin cewa babanta mai kudin ne ita kuma ta ishe 'yan gidan da dauke dauke duk abin da suka ajiye mai muhimmanci in dai ta gani sai ta dauke shi.

Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi....

DAÆŠIN ZAMA BY SEEMAHWRITES
JODA BY SADI-SAKHNA
ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH

*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*

*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*

Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin

Sai a tura shaidar biya ta
09039206763

🖤Gureenjoh🖤

ƘARFE ƊAYA BA YA AMO

✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN
(GUREENJOH)

@Gureenjo on Arewapen
@Gureenjih6763 on Wattpad

ADABI WRITERS ASSOCIATION

#THE TRIO OF TALES
(THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY)

TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne.

GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba.

NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k.

*SHAFI NA ASHIRIN DA ÆŠAYA*

"Ma'u don Allah ki buÉ—e baki ki ci kin ji?"
Jiddah ta faɗa cikin muryar rarrashi don Ma'u yini guda kenan babu abin da ta yarda ta ci kullum lamarin kara ta'azzara yake, bata san me ya same ta ba amma ko a hirar da ta tsinkayi masu tsaron nasu suna yi ta ji suna magana akan rashin ƙarfin kwakwalwa shi yasa trauma din yayi hitting ɗinta Sossai kuma muddin ba kudi aka kashe a kanta kuma aka haɗa da kwararrun ma'aikatan jinya ba kwakwalwarta na shutting kanshi down a je a je za ta iya faɗuwa ta mutu.

Dukda hankalin jidda a tsanani tashe yake bata daina addu'a da rokon Allah ya hana kalmansu tabbata ba, tun da suka gano lagonta sai suka kashe mata baki, ya zamana bata iya yi musu musu sam, iyakaci saƙo take kaiwa wanda a wani sashe na zuciyarta tana jin har hakan ma bai dace ba kila amfani ake da miyagun kwayoyi ana lalata al'umma, ta tabbatar babu wani abu da za'a fitar daga gidan da kyakyawar nufi don dukkansu mugaye ne, dukkansu babu mai imani ciki.

Kuka kawai jiddah ta shiga yi a wurin cikin rashin makama, ganin irin kukan da take yi yas a Ma'un miƙa hannu ta riƙe nata sai ta dago da sauri, ruwan ta bata ta karɓa ta sha ta shiga bata abinci sai ta ga tana ci, hawaye ke zubarwa jiddah har Asm'aun ta gama cin abincin bata yi ko loma guda ba kuma nasu ne su biyun.

J da yake hakimce cikin kujera yana ɗan juyawa a hankali sanye da wasu bakaƙen kaya ya dauke kai ya kalli shadow
"Wannan kayan idan ta kara sati bata da amfani a yi da ita kudu a tabbatar ta yi nesa da nan a zubar ta bi ruwa"

"An gama J na fahimta"
Ya miƙe ya fice yana duba lokaci, Wayanshi ya zaro ya zubawa sakon kai ido na seconds kan yayi wani murmushi.

"Yaro yaro ne! Yaro bai san wuta ba sai ya taka!"
Mota aka buÉ—e mishi ya shiga suka fice daga arear gabadaya.

****

Shehi ya zama busy kwarai a kwanakin da suka biyo baya, zai iya cewa ma bai taɓa cin karo da kwanaki irin wannan ba ya haɗa stress mai yawa hakan ya sa Sam bashi da wani lokaci, tuni ya manta da wata Na'imatu da ya je ya gani yayin da a gafe su Ammiey ke ta hidimarsu har kuma lokacin Abbiey basu yanke hukunci ba.

Shi kam gabadaya damuwarshi sunan Ammar ya wanku, Abba ya rage fushin da yake yi ba wai suna ganin laifin Abba bane don yana fushi a'a abu da dole kowani uba zai ji babu daaÉ—i abin da idan ya tambaya za'a bashi to me na zamba? Shi kuma Ammar ganin É—an uwanshi ya shiga lamarin Sossai sai ya ja baya ya bar mishi.

A ɓangaren wa'azi sai ya ƙara zafi ya zamana kullum maganan shi kan azzaluman 'yan siyasa da yadda za mu farka mu tsayawa kawunanmu, barazanarshi ga azzaluman sai ya ƙaru shi zai yi ya kwana lafiya amma da zaran ya fita duniya su kuma babu bacci.

Yau yana zaune a office dinshi cikin BUK yana duba wasu takardu ya ji an yi knocking.

Ya amsa sai aka tura kofar aka shigo, bai É—ago ba sai da ya ji shiru kan ya É—ago sai idanunshi suka faÉ—a kanta yadda ya tsare ta da su sai ta rasa natsuwa, bakinta ya shiga rawa ta rasa me za ta ce.

Cikin rashin sanayya yace
"How may I help you?"

Wani dummmmmm kanta yayi, yana nufin bai gane ta ba ne ko yaya? Rawa muryarta ya fara dukda maganan da take so ta yi da kyar tace

"Na'ima ce"

"Na'ima?"
Ya maimaita sunan trying really hard to be polite.

Sai ta juya da sauri ta fice wani irin kunya mai yawa na rufeta, a lokaci ɗaya hawaye ya shiga zubo mata ashe haukanta take, ashe tana nan tana baza hauka bata sani ba ya mance da ita ma, zuciyarta ya shiga ƙuna tun daga ranar da aka ɗarsa mata shi bayan dogon crushing bata samu isashen bacci ba ta zaci ko a waya zai ƙirata amma shiru, ta yi tunanin to kila ya sake zuwa nan ma shiru ta kasa hak'uri da kyar ta yi gaining courage na zuwa ashe rabon tayi kwanan baƙin ciki ne ya kaita.

Shi kam aikin shi ya cigaba da yi yana taɓe baki mata sun sha zuwa mishi haka don sai da ya shata layi mai girman gaske ya buga misali na ban mamaki da wata kan ya shawo matsalar zirga-zirgan su na ba gaira ba dalili da sunan gaisuwa ko wata kyauta(Gift).

Sai da ya gama ya miƙe ya bar makarantar yau ma shi kaɗai ne don haka da kanshi yake driving har Company, office ya wuce yana duba inda suka kwana ganin jiya-e-yau ya sa ranshi matukar ɓaci.

"Meyasa Hisham? Meyasa?"

"Ranka ya dade...."
Hannu ya ɗaga mishi sai ya miƙe tsaye

"A da ina zaton cewa matsala ake samu na ƙirge har kudin su ke ɓacewa amma a yanzu yadda ake tempering aikina ya tabbatar min da cewa da gaske sama da faɗi ake yi da kudaden nan. Ban san amfanin kiran kanku Audit ba muddin za'a samu wani yana lalata duk ayyukanku daga ciki"

Hisham yace
"Ka yi hak'uri Ranka ya dade"
Chapter 28 · 0% Book details