← Book details Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 42

Sashe 32

Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari Kasancewar da wuri yake da program din ya shirya tsaff turaren wutan da ya taho da shi na bakhoor by seemah ya turara a jikinshi bayan ya gama shiri cikin shigarsa na ko da yaushe, yau ma white thobe ne ya saka da brown jubba sai ya saka farin Ghutra a kansa tare da baƙin Agal ya saka half cover da ya karbi kafarsa Sossai, bai karya ba sai a chan saboda akwai abubuwa da za su yi organizing kan lokacin lectures din wurin da nisa ga yanayin Abuja don haka da wuri zai fita ya isa akan kari, jakar system kawai ya ɗauka da wayarsa ya fice daga ɗakin yana fitar da ni'imtaccen ƙamshi.

Yana isa parking lot ɗin sai ga drivern jiya da aka haɗa shi da shi ya zo da sauri ya karɓi briefcase din suka tafi wurin mota ya buɗe masa ya shiga ya zaga ya shiga suka fara ficewa daga hotel ɗin.

A natse yake driving irshad din na ɗan kallon tsiririn titin hotel ɗin kaman an ce ya kalli ta gefen ya hangeta sanye da baƙaƙen spotwear na kamfanin Addidas tana jugging a gefen hanyar ido ya zuba mata yana mamaki, ita dai duk wani abu na addini bata ciki, Sossai yake mamakin rayuwarta. Ya tsinci kanshi da yi mata adu'ar shiryuwa kan ya ɗauke kai suka fice daga layin.

******

"Ya Khalil!"

Nana ta kwala kiran sunanshi ganin zai ta da motar, dakata wa yayi ta zo da sauri ta tsaya daga jikin windown tana gaishe shi.

Ya amsa a hankali dukda ya ga kamanninta da Zubaidah Sossai da Sossai amma bai santa ba.

"Sunana Nana Khadija kanwar Zubaidah"

Yayi murmushi
"Oh Allah sarki khadija ya school?"

Ta amsa da
"Alhamdulillah!"

"Wurin Yaya zubaida ka zo?"
Ta tambaya bayan shirun dogon lokaci da ya ɓace cikin tunani.

"Eh Nana amma ta fito ta min gargadi akan in fita harkar ta babu aure gabanta"
Ya karasa cikin wani yanayi, a kan Zubaidah ya bi shawarar aboki ya fara ketere iyakokin ubangiji ya aikata abin da bai taɓa tunanin aikatawa ba dukda tarin laifukan Fatsuma matarsa na banzatar da buƙatunsa kuma ta shiga ta fita mahaifiyarshi ta hana batun karin aure a zamansu, amma daga lokacin da ya san Zubaidah yaji zai iya auren ta a hankali kuma ya fahimci rayuwarta tausayinta ya ninku a ranshi ya ji yana kwadayin cire ta daga wananan baƙin rayuwar, yana sane da irin gwagwarmayar da zai yi da Mamanshi da kuma Fatsuma amma bai damu ba muddin zai sami Zubaidah.

"Abu É—aya nake tunani za ka yi ka mallaki Zubaidah"
Nana ta faÉ—a a hankali tana kallonshi
"Menene wannan É—in?"
"Ke je wurin mahaifinmu ka nemi aurenta"

Dukda tsoro da take ji na tura Khalil har Taraba amma muddin da gaske yana son Zubaidah zai iya zuwa ko China ne soyayya da ma tana cike da sadaukarwa.
"Ki ba ni full Address na yadda zan same shi in Shaa Allah zan je, muddin zan yi nasara kan Zubaidah"

Takarda ta fitar ta rubuta mishi yadda ta haddace bata haddace komai haka ba, rayuwarsu ya wargaje tun daga yaranta a kan idanunsu komai da ba za su taɓa manta wa ba ya faru, a kan idanunsu mahaifinsu ya yafe su ya sallamawa mahaifiyarsu ya zame hannayenshi, a kan idanunsu ya sa almakashi ya yanke alakar da ta haɗasu dukda jininshi da ke yawo a nasu jinin.

Hawayenta ta mayar tana miƙa mishi papern ya karɓa yayi mata godiya kan ta fita ta shiga gidan, abin mamaki ta samu Zubaidah na kuka irin wanda bata taɓa gani ta yi ba! Kuka ne da ke fita daga cikin zuciyarta, a hankali ta ƙarasa wurinta hawayenta na zuba ta dafa ta.

Zubaidah ta É—ago ta kalleta.
"Me ya sa kike kuka Aunty Zubaidah? Mama ce?"
Girgiza kai Zubaidah ta yi sai ta koma ta jinginu da gini tana rufe Idanunta.

"Baba?"
Ta faÉ—a dukda ta san Malam Iro a yanzu ba dai ya sa Zubaidah kuka ba sai dai ma ita ta saka shi aiko Zubaidah ta buÉ—e ido ta zabga mata harara.

Nana ta É—an yi murmushi
"Toh menene kike kuka haka Yaya Zubaidah?"

"Babu Nana! Babu abin da ya faru"
Tana kai nan ta miƙe ta fice daga ɗakin, tana tafiya a hankali jikin ta a matukar sanyaye kanta ƙasa tana ji Wayanta na kira tana kallon sunan Ghali amma ta ƙi picking, saboda ta san hookup ne ya samar mata kuma ba ta cikin mood.

A dakin Shaly ta samu click ɗin nasu Pablo ya tafi kabu kabu, Pascal yana injin bredi, Obafiya gym coach ne saboda gyming ya samu ƙirar da ya zama na hannun daman Diva don kowa ya ganshi sai ya ji shakkarsa bare yana wuri ko kallo Diva ta yi ya san ma'anar, a lokacin Kasancewar yammaci ne shima baya nan. Daga Zee, Shaly sai Skipo.

Ta zauna kawai bata ce komai ba. Skipo ne yace
"Ya ne Zubash? Na ga jikinki duk yayi wani la'asarrr"

Ta É—an sauke Numfashi
"Kawai kewar Diva nake ji wlh ko ya take a chan da bata san kowa ba?"

Zee tace
"Nima wlh ina jin kewarta sossai dukda kin ga ba wani hira take na a zo a gani ba amma Diva mutum ce da in tana wuri spirit dinka sai ya haÉ—u da ita ko baku yi magana ba"

Shaly tace
"Za ta dawo ne soon ku daina damuwa, ba tafiyan ne ni ya tsaya min a rai ba...dalilin Jagaban na tura ta ne ya tsaya min. Anya bakwa ganin akwai wani da abu ta haɗosu da Jagaban kuma ya fi ƙarfinsa yake so ya yi amfani da Diva don lankwasar da shi ba? Suna fa aka rubuta mata a jiki da wuƙa daga kuma ganin saƙon sunan Jagaban ya rasa natsuwarsa"

Zubash ta amsa tana gyara zamanta
"Tabbas na kula da yadda baya da natsuwa a kwanakin nan gabadaya, waye ne kenan? Me kuke tunani zai haÉ—asu haka?"

Shaly tace
"Ban sani ba gaskiya har ita kanta Diva din bata sani ba dukda kokarin bincike da take ita da Pablo da obafiya amma sun kasa gane komai akan mutanen da suka illatata a karshe zagayensu kuma ya kawo su wurin Jagaban"

Skipo ya É—an yi shiru cikin nazari
"Kina nufin Jagaban dinne kenan suke zargi?"

Zee tace
"Me ya sa zai cutar da É—iyarshi?"

Shaly fuskarta na nuna damuwa tace
"Zai iya yin hakan akan business amma ba zai yi da nufin cutarwa ba, kun san yanayin yadda underground war yake ina kyautata zaton ko saboda ya yi framing wani saboda ya karbe kasuwarsa daga sama zai aikata. Don gaskiya idan ba shi ba ban san mai tsauri idon da zai iya taɓa Diva har haka ba"

Magananta ya fi kama hankalinsu don a yanayin zuciyoyinsu Jagaban ya dame su ya shanye, yana da hatsari kwarai fiye da zato kuma yana riƙe ne da baƙar duniyar laifuka masu yawa da ba komai ne suke da masaniya a kai ba, hakan ya sa irin su babu abin da ba za su yi ba don ganin ba'a jijjigasu ba.

Shaye-shayensu suka cigaba da yi suna hira zubash dai tun da aka gama maganar Diva ma bata sake sa baki ba ta ma bugu ne lisss ta kwanta Idanunta a rufe amma har lokacin bata daina jin abin da take ji ba, bata daina jin tasirin kalaman Khalil a zuciyarta ba, bata daina jin tsoron makoma ba, kwakwalwarta kuma bai karɓi ta sauya ko ta chanza ba don ta tabbatar mama ba yarda za tayi ta aurar da ita ba ko ana ha maza ha mata kai ko ita ce ta samu damar auren muddin Nana bata yi ba ba zata tafi ta barta mama ta lalata mata rayuwa ba.

****

"Mama Ya Sheikh ba ya ƙaunata, bana tunanin zai taɓa ƙaunata mama bai fa gane ni ba! Nunawa yayi bai taɓa sanina ba"
Cikin hawaye tayi maganan.

Maman tace
"Laifinki ne Na'ima kina mace me zai kai ki inda yake? Ai shi ya kamata a ce ya zo ya same ki har inda kike, da kin yi shawara da ni wlh ba zan goyin bayan zuwanki office dinshi ba don zub da aji ne."

Karfin kukanta ta ƙara
"Ki daina wannan kukan, kuma zai kiraki ya baki hakuri in Shaa Allah bari zan kira mamartashi, amma gaba ko da wasa kada ki nuna zaƙewa a kansa in ba haka ba za ki sha wahala"

Sam hankalinta bai kwanta ba, idan komai sai Mamanshi ta saka shi in sun yi auren ya zai yi da ita kenan? Dole ta nemawa kanta mafita ba za ta bari ta rasa abin da ta kwallafa rai ba don tana son shi Sossai tana tunanin duk duniya babu wanda ya kaita sonshi.

Mamanta na fita ta janyo Wayanta ta kira wata secondary school friend É—inta da ta san ta haddace kalolin maza iri iri tun daga kananun shekaru, ita ce kawai za ta bata shawarar yadda zata kama zuciyarsa tun kan ta shiga gidan.

Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi....

DAÆŠIN ZAMA BY SEEMAHWRITES
JODA BY SADI-SAKHNA
ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH

*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*

*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*

Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin

Sai a tura shaidar biya ta
09039206763

🖤Gureenjoh🖤

ƘARFE ƊAYA BA YA AMO

✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN
(GUREENJOH)

@Gureenjo on Arewapen
@Gureenjih6763 on Wattpad

ADABI WRITERS ASSOCIATION

#THE TRIO OF TALES
(THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY)

*SHAFI NA ASHIRIN DA HUÆŠU*

Kusan awanni uku da zama cikin conference hall É—in an fara program É—in ne da basu abin kari wanda serve ur self ne ya dibi abin da zai iya ci ya ci ya sha coffee, kan aka soma abin da ya tara su gabadaya vibration na Wayanshi ne ke daukar hankalinsa ganin ba za'a daina kira ba ne ya sa ya fitar ya fara dubawa sai ya yi mamaki.
Chapter 32 · 0% Book details