Sashe 38
Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ka yi wa Allah Ammar ka daina haÉ—ani da 'yar daban chan, wanda aka yiyyi a baya ma ya isa"
Ammar yayi dariya
"Gaskiya mutane basu da adalci, ai ko da gami kurna ta fi magarya zaƙi hanyar jirgi kuma daban da ta mota me zai hadaka da wanchan yarinyar da shaye shaye ya zama jininta, zubar da jinin mutane ya zama ado a wurinta kuma rayuwar titi ya zama duniyarta?"
Irshad ya É—an sauke Numfashi ya ce
"Ni karan kaina ina mamaki Ammar, ko kusa ko alama ba na jin wani ɗabi'a ko halayyarta yayi kamanceceniya da rayuwata bare har a alaƙantata da ni, bayan musulmi da nake ita ma kuma take amsa wannan sunan."
Ammar ya ce
"kawai so aka yi a ɓata maka suna da ita, har ma na yi zargin ko an biyata ne musamman don ta lalata maka mutuncin da miliyoyin al'umma suke kallonka da shi"
*"Ka san mene? Ka fita a sabgata tun ban nuna maka kalolin rashin darajata ba don yanzu ka gama faɗa ba ni da mutunci, kuma a rashin sanin mutuncin kamewar ban ga abin marmari da zan bibiya a rayuwarka ba, kudi kuma sun yi kadan su sa na ɓata lokacina a kanka idan ma zargi kake to tun maza ka daina! A baya ma na bibiyeka ne saboda in ɗau fansar abin da ka min kuma mun gyarota idan ba kana son na janye ma hakurar da nayi ba ne ka daina nuna min fuskarka a tawa don babu abin burgewa a rayuwarka wurin DIVA"*
Kalamanta da suka dawo mishi kai kenan kaman yanzu take jero su gareshi cikin gargadi da kaushin murya, ido ya ɗan runtse yana hango yadda Idanunta da suke lumshewa da maye suke ƙara girma da raguwa cikin nashi da sauri kuma ya buɗe idanun yana ambaton Allah tare da riƙe goshinsa.
Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi....
DAÆŠIN ZAMA BY SEEMAHWRITES
JODA BY SADI-SAKHNA
ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH
*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*
*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*
Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai a tura shaidar biya ta
09039206763
🖤Gureenjoh🖤
ƘARFE ƊAYA BA YA AMO
âœï¸FATIMA MUHAMMAD GURIN
(GUREENJOH)
@Gureenjo on Arewapen
@Gureenjih6763 on Wattpad
ADABI WRITERS ASSOCIATION
#THE TRIO OF TALES
(THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY)
*SHAFI NA ASHIRIN DA TAKWAS*
"Ya dai?"
Ammar ya tambaya yana É—an kallonshi while driving.
Ya saki goshin yana zubawa titi idanu ya furta
"Babu, gajiya ce kawai"
Babu wanda ya sake magana cikinsu har suka isa gida, kusan mutanen gidan sun fito yi mishi maraba don suna da wannan É—abi'ar a gidan idan wani yayi tafiya ranar da zai iso za su fito duka su jira saukarshi daga mota a yi maraba kan a barshi ya je ya shirya ya kuma bibiyi iyaye yayi gaisuwa da fatan samunsu lafiya.
Yanzu ma sun yi murnar ganinsa Sossai, cike da kaunar ahalinshi yake amsa sannu da dawowa da suke mishi tuni Mufida da sumayya sun ja trolley dinshi da jakar system sun nufi sashenshi kan ya gama ya nufi sashen ma sun fito, cikin natsuwa ya shiga sashen dake ta fidda kamshi ya san aikin kannenshi ne bisa umurnin Maamah don har abinci gashi an jere mishi.
A natse ya haura samanshi, ya wuce parlorn zuwa bedroom É—in shi da sallama kan lips É—in sa sai yake jin kaman ya shekara ba ya gidan yayi kewar Kano Sossai ashe bai farga ba.
Rage kayan jikinshi yayi don ba ya jin zai fita wajen ma sai azahar, farin dogon wando na yadi da farar shirt ya saka, shirt din irin mai roba da ke kama jiki ne don haka ya fitar da kirarsa gabadaya wuyan kuma V line ne mai guntun hannu, bayan ya feshe jikinshi da turarukansa masu sanyin kamshi ya nufi parlorn ƙasa a chan ya zauna ya karya don tun jiya sai a lokacin yake sa wani abu bakinshi.
Yana cikin cin abincin ne Imam ya shigo bai takura masa ba sai ya zauna a parlor har ya gama ya zo ya samesa yana zama hurairah na shigowa da gudu ya dauketa ya sakata kan cinyarsa yana shafa gashinta.
"Ya hurayr kaif haluki? Istaqtu ilayki..."
Ya furta da murmushi don da ma ba hausa yake yi wa kuliyar ba kuma jin yaren take tsaf na larabci
"Hurayr kina lafiya? Na yi kewarki"
Imam yayi murmushi yana miƙa gaisuwa Shehi na cigaba da shafa kuliyar suka gaisa, nan Shehi ya fara tambayar sa abubuwan da suka faru ba ya nan wani Imam din ne zai tuna ya faɗa masa wani kuma zai tambaya sun jima suna magana kan ya tafi, shi kuma Shehi ya haura sama yana ɗan sa hannu cikin gashin kansa da ya ji yana bukatar ragewa don ya fara damunsa, system ya janyo ya shiga inda ya tsaya da batun companyn Abbiey shawarar Sheikh Nasser ya bi sai gashi ya fara ɗaukar haske cikin kankanin lokaci.
****
Khalil ne tsaye kofar gidan da aka yi mishi kwatance sallama yake yi cikin É—aga murya har aka amsa, bai jima yana tsaye ba wani yaro ya fito
"Yaro ina neman Malam Sule ne"
"Yana ciki"
"Ka ce mishi yana da baƙo"
Komawa yaron yayi chan sai gashi ya dawo
"Wai ka shigo"
Bin bayan yaron yayi zuwa ciki yana kallon gidan ganin yadda yake nan a rushe rabi da kwata daki daya ne na taɓo wanda aka rufe bakin da buhu daga gefen bishiyar tsada ya ga wani dattijo da wahala da talauci suka bayyana jikinshi zaune kan wani kujera.
Tsugunawa yayi
"Baba ina yini?"
"Lafiya yaro, ka zo lafiya?"
"Alhamdulillah baba"
Sai yayi shiru ya rasa me zai ce ya zubawa almajirin dake dibo ruwa daga rijiyar gidan yana zubawa a randar dake gefen É—akin.
"Sai dai ban sheda ka ba yaro"
Numfashi ya sauƙe kaɗan yace
"Sunana Khalil na zo daga Kano ne"
"Wai wai wai ashe daga nesa kake yaro sannu da zuwa! Kai Usmanu kawo masa ruwa"
"A'a Baba ai ba ma yau na zo ba tun jiya ne, da ma na zo ne kan maganan 'yarka Zubaidah"
Tuni jikin wannan dattijo ya fara rawa cikin rawar murya yace
"'yata? Ƴata Zubaidah?"
"Kwarai kuwa Baba..."
Sai dattijon ya fashe da kuka mai tsuma, kukan da ya É—aga hankalin Khalil.
****
"Ranka ya dade akwai matsala fah!"
"Matsala? Meyasa za ka kiramin matsala?"
"Ranka ya dade wannan yaro ya fa fara shirin bankaÉ—oka idan ma bai bankado din ba kenan don bincike ne ke shigar da shi cikin wani binciken"
Da hanzari ya miƙe tsaye ya fara jeka ka dawo zufa na karyo mishi.
"Dole a yi wani abu! Dole a yi wani abu..."
Ya maimaita ya kai sau hudu kan ya katse wayan"
*****
Fadar gomnati, zaune yake yana nazari idanunshi na kan fai-fain videon da aka mishi playing na wa'azin Irshad na bayan magrib da ya dawo a ranar wa'azi ne da ya É—aga masa hankali.
Musamman a lokacin da Irshad ya kalli camera ya ce
"Wannan saƙo ne zuwa ga kai shugaba marar adalci mai mantawa da Allah...
Ya kai shugaba! Ka tuna cewa kujerar da kake kai ba za ta bi ka kabari ba. Duk ikon da kake da shi a yau amana ce daga Allah, ba mallakarka ba ce.
Idan kana neman ci gaba da mulki saboda hidimar al'umma da adalci, Allah Ya taimake ka. Amma idan kana neman zarcewa ne saboda son mulki, girman kai, ko tsoron rasa iko, to ka tuna cewa ranar da za ka tsaya gaban Allah ba za ka zo da jami'an tsaro, kuÉ—i, ko mukamai ba.
Manzon Allah ï·º ya ce:
"Kowannenku makiyayi ne, kuma za a tambaye shi game da abin da aka ba shi amana."
Shugaba ba sarki ne a kan bayin Allah ba, bawa ne da Allah Ya ɗora wa nauyin jama'a. Hawaye na maraya, kukan al'umma, yunwar talaka, da zaluncin da aka yi wa mabukata ba sa ɓacewa a wajen Allah.
Ka ji tsoron ranar da mulki zai ƙare, amma hisabi bai ƙare ba. Ka ji tsoron ranar da waɗanda ka zalunta za su karɓi hakkinsu a gabanka. A ranar ba kuɗi za su amfana ba, ba iko ba, sai ayyukan ƙwarai.
Ka tuna: mutane na iya tsoronka a duniya, amma kai ma kana ƙarƙashin ikon Allah. Wanda Ya ba ka mulki zai iya ƙwace shi a lokacin da bai zo maka a zato ba.
Saboda haka, ka yi adalci. Ka guji zalunci. Ka tuna cewa shugabanci ibada ce idan an yi shi da gaskiya, amma babban nauyi ne idan aka mayar da shi hanyar son kai da tauye haƙƙin mutane"
Masallacin yayi tsit babu tsoro ko shakku ya cigaba da jan hankalin mutane akan tashi tsaye su kwatarwa kansu 'yanci daga azzaluman shuwagabanni daga ƙarshe ya rufe da adu'a
"Allah Ya shiryar da shugabanninmu zuwa ga adalci, ya kare al'ummar annabi Muhammad (SAW) daga zalunci, Ya sa mu kasance cikin masu tsoronSa da kiyaye dokokinsa Ameen"
Kalaman sun zo wa Bashir dantani ta fuskoki biyu, dukda wani zuciyar na cewa ba da shi yake ba amma saboda ya san kanshi sai yake jin kaman da shi yake kai tsaye, ji yake kaman zai iya faduwa a yadda Irshad ke nusar da mutane da jan hankalinsu kai har sunanshi yaji yana amsa kuwwa da muryar Irshad na cewa mutane da shi yake kar su zaɓe shi.
Scrolling yake yana duba comment section na wa'azin, wasu na tamabaya kan batun Diva ya dawo bai ce komai ba, wasu na kiran wasu daga cikin azzaluman shuwagabanni suna cewa ya kamata a saka musu don idan wa'azin nan bai shige su ba tabbas sun rasa imani.