← Book details Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 42

Sashe 40

Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗakin Shaly ta ya da zango kawai ta kwanta tana runtse Idanunta, a hankali ta shiga tunanin ya matsayin tarin waenda babanta ya jefa cikin duniyar kwaya? Meyasa bayan ta san yadda rayuwarsu ke tafiya ba kan daidai ba ne amma ba za ta iya daina wa ba? Ta ya za ta fara hana Pablo allurar penta alhali itama ta riga ta zama addicted to Ice? Har ranta ta fara jin ƙiyayyar yadda mahaifinta ke tafiyar da rayuwar matasa amma ba za ta iya wani abu ba sai ma ta bashi gudummawa ta wani ɓangaren.

Maganan Shaly da Zee ne ya É—an dawo da ita daga tunanin da ya fara addabarta sun riga sun san halin ta za ta iya gama zamanta ma a dakin idan bata yi ra'ayi ba ba zata musu magana ba, hakanan dama yanayinta ba mai wasa da dariya ba ce bare su fahimci abu na damun ranta.

"Zee ni kam baki fahimci Zubash kwanan nan tana cikin damuwa ba?"

Zee ta ce
"Ai tun tafiyar Diva na fahimci ta rage walwala kuma fa yanzu ko yawan zuwa hotels hotels din nan bata yi, na kula har kudin abin da za ta sha bata da shi shiyasa jiya ta sha codein da bata cika so ba"

Diva ta buÉ—e Idanunta tana kallonsu

"Shaly menene matsalarta?"

"Wallahi bamu sani ba amma zan bincika Diva"

Numfashi ta ɗan sauƙe ta koma ta kwanta shiru, sai tayi tsaki kawai ta miƙe tana kiran Skipo.

"Raina a wuya yake ina so a yau ba gobe ba ka binciko min bullet din nan in sauƙe masa zafin kan nan"

Yace
"An gama Diva"

Ficewa tayi daga gidan gabadaya ta koma gida zuwa É—akinta haka ta haÉ—a ice ta shiga sha ko zai rage mata abubuwan da suka fara tarar mata a kai.

Kaman yadda ta umurta a yammacin Skipo ya sanar mata ai yana wani restaurant gashi nan shi da Obafiya sun tsare shi, ficewa tayi daga gidan bata nemi su Shaly ba ma ta É—auki mota ta nufi restaurant da ya ce mata suna nan É—in.

*****

Shehi ne ke driving Ammar na daga gefenshi yau ya shiga BUK yayi lectures Kasancewar ya kwana biyu ba ya gari abubuwan sun ɗan taru a son shi ne ma gobe ya wuce Katsina ya dawo a goben saboda yana so ya fara batun gyaran Gidan sheikh Nasser da tsara yadda zai sauƙa har ya tafi, daga BUK company ya je kai tsaye inda ake shigo musu da kuma fitar da kaya ya nufa ya ɗan yi magana da wani a sirrance kan ya bar wurin ya nufi office na Ammar a chan ya zauna har Ammar ya gama abin da yake suka fito a tare.

"Bari na bika kawai mu wuce gida motan nan zan kira mechanic ya É—auka a nan birkinta ta sake ina zuwa da safe kadan ya saura ban yi hatsari ba"

Dalilin da ya sa ya bishi kenan, a natse yake tukin har ya nufi hanyar gida ma duka sai wani da zai bashi saƙo ya ƙirashi akan komai ya kamallah ga takardun hannunsa.

"Kana ina?"
"Ina dab Majlis restaurant"
"mu haÉ—u a chan kawai"
Ya faɗa yana juya kan motar, dukda gajiyar da yake ji yana son kawo karshen abubuwan da yake bincikowan nan, wanda tabbas idan bai gano ba cikin kankanin lokaci komai zai iya faruwa da companyn bayan ɓacewar makudan kudade.

Kai tsaye chan suka nufa sanye yake da Ox blood jallabiya da jubba da ya zama mahadar jallabiyar don kalar su ɗaya sai dai akwai adon ruwan gold daga jikin riga mai kama da alkyabbar, Ghutra da ya sa a kansa ma mai surkin Ox blood din ne da baƙi sai baƙin Agal da baƙin takalmi.

A natse yayi parking motar suka sauka suka shiga ciki, bayan sun zauna waiter din ya zo sai Ammar ya umurceshi da ya kawo musu coffee, matashin mai sanye da kananun kaya ya zo ya zauna suka gaisa kan ya ɗauki brown envelope din ya ba Shehi, ya karɓa tare da furta
"Jazakallahu khairann"

Matashin yayi murmushi cikin girmamawa ya tashi zai fice Shehi na mishi tayin ma ya tsaya ko coffee da suka yi order ne ya sha ya ce a'a kan ya wuce.

An kawo musu coffee din suna sha Ammar na tambayar shi ko ya kira Na'ima ɗin yace ya ƙira bata yi picking ba kuma ba ya tunanin zai ma sake kiran, Ammar yayi murmushi kawai daidai lokacin suka shiga jin hayaniya...

Duk hankulansu suka mayar kai idanunsa basu sauƙa ko ina ba sai kanta tana sanye da wando dogo baƙi da wani blouse kalar maroon haka jersey vail din kanta ma kalar maroon ne, dab da su suke don za su iya cewa table nasu ne yake kusa da inda suke ɗin, ƙafanta ɗaya na kan kujerar gefen kato kuma jibgegen mutumin da suka zagaye su uku wanda daga kallo ɗaya ma za ka masa ka san cewa ba bahaushe ba ne ga mamakinsu hannu ta ɗaga ta tsinka masa mari.

Sai ga muryarta cikin kaushi da ƙarfi tama cewa
"Kai ne akuyar da ya tsallakemin danga? Kai ne dattin da ka rasa inda zaka yi da ruwa ya kwaso ka sai hanyana? Me ka ƙira kanka ma?..."

Jikinshi na rawa yace
"Babu! Babu komai..."

Kallon Obafiya tayi sai ya kai mishi naushi yana chakumo kwalarsa
"Me kake kiran kanka?"

"Boss...boss da ya kori Diva"

Skip ya sake kai masa naushi a baki
"Kana kara ambatar sunanta sai na zubar maka da hakwara, Shugaba har wasu daga cikin yaran da ba'a taɓa mana su a layi ya taɓa da ikirarin ya riga ya ɓatar da ke yanzu mu ma duk karkashin sa muke"

Wuƙa ta zaro tare da ɗora mishi kan wuyan da Obafiya ya danne Skipo kuma ya riƙe shi gamm suka hana shi motsi
"Bari na sheƙe ka in ga uban me zai faru... Za ka san ka shiga hurumina"

Waiters da kuma securities din wurin ne suka zube suna roƙonta kar ta zubar musu da jinin kowa a wurin ta yi hak'uri don duk sun san labarinta sun kuma sun san bata ɗauruwa.

Lip ta cije ta saukar da kafarta daga kan kujerar tana juya Idanunta a wurin don bata son yawan magiya, idanunta basu sauƙa ko ina ba sai kanshi da shima yake kallonta mamakin fuskarshi ya koma takaici don har ranshi ganinta hakan yana jin ɗaci da takaicin ta amsa sunan diyar musulmi a irin wannan ɓata.

Miƙewa yayi kawai ya sa hannu aljihu ya zaro kudin da bai san nawa ba ya ajiye kan table ɗin ya kalli Ammar
"Mu je"

Miƙewa Ammar yayi suka nufi fita, baya baya ta ɗan yi ta zauna kan table da suka tashi ta kalli Obafiya
"Ku kyaleshi for now! Ku tabbatar duk inda kuka sake ganinshi a birnin Kano ya baƙunci lahira umurni ne"

Baya suka matsa ya fice da gudu, tana Miƙewa ta taka abu, ido ta kai wurin sai ta duka ta ɗauka wallet ce ta maza, buɗe wa tayi Idanunta suka sauka kan ID cards da kuma Atms, sunanshi ta fara gani kan hoton shi na passports, ta kalli kofar da basu jima da fita ba sai ta miƙe ta nufi kofar don har ranta tana son jin ko police sun kira shi batun yarinyar chan? Ko iyayenta sun same ta? Don bata taɓa jin tausayin wani mahaluki a duniya yadda ta ji na yarinyar ba.

Dab motar su ta hange su da sauri ta ƙarasa tana furta

"Excuse me!"

Babu wanda ya juyo a cikinsu Karon farko da bakinta ya furta sunansa

"Sheikhhh!"

Babu zato ba tsammani ta ga ya juyo cikin kaushin murya da tsawa girman idanunsa duka a waje yace

"Whatt??"

Har Ammar sai da ya waigo yana kallonshi don Shehi ba gwanin ɗaga murya haka ba ne, sai ya fahimci ranshi a ɓace irin ɓacin da yana wuya a gani a tattare da shi.

Yadda ya juyo a zabure kuma idanunsa na kallon nata ya sa ta ji ta tsaya chakk ta kasa motsi Karon farko da wani murya ya girgiza zuciyarta don tsawar ya sauƙa har cikin zuciyarta ga idanun da ya tsare ta da su lokaci ɗaya abin ya zo mata bazata.

Tattaro jarumtarta tayi ta hade fuska ta watsa masa harara tamkar Idanunta za su faÉ—i ta shiga furta
"Da ma abin kirki ai bai karɓi kare ba... Idan da ban nemi na taimake ka ba ba za ka min ihu a kai ba.."

Wallet ɗin ta miƙa masa dukda wata zuciyar na cewa ta jefar in ya so ya je ya ɗauka amma bata yi hakan ba sai da ta miƙa mishi.
"Idan ba za ka karɓa ba wallahi cilli zan yi da shi ko ma me a ciki sai dai ya salwanta"
a ranta tana ƙirge don tana kirga uku bai sa hannu ya karɓa ba sai ta yi cilli da shi wallahi dab ta gama uku tana kokarin wullar da shi ya sa hannu sai ta kalleshi suka haɗa idanu ta sakar masa kan ta juya ta bar wurin a fusace laifinta ne da har ta taimake shi ma zai tsaya yana mata tsawa a kai ta yi tsaki ya fi cikin kwando kan su isa gida.

Kanshi ya É—an dafe yana jan tsiririn tsaki kan ya wullawa Ammar key É—in yana nufar seat na mai zaman banza don ba zai iya tukin ba kuma.

"Shehi me ke faruwa ne?"

Tambayar ya zo mishi ne a daidai sadda yake tambayar kansa me nashi ma na jin haushi don ya ganta cikin yanayin da halinta ne kuma dabi'arta? Menene bai san tana yin ba shaye shaye ne ko dabanci? Ko ko ganinta cikin shiga da ta saɓawa shari'a da ma tsarin musulunci?
Me ya sa zai ji haushin da ya kamata a ce uban da ya haifeta shi ya kamata ya ji mata?

Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi....

DAÆŠIN ZAMA BY SEEMAHWRITES
JODA BY SADI-SAKHNA
ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH

*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*

*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*

Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin

Sai a tura shaidar biya ta
09039206763
Chapter 40 · 0% Book details