← Book details Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 42

Sashe 31

Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana A ne, ginin kuma A na kallon B ne, wanda ke tsaye a corridor din A tsaf zai kalli wanda yake corridor din B, layin kowani block kuma da farkon number ya fara wato dakuna goma ne kowani floor har hawa biyar.

Lift da zai kaita ɓangaren ta hau ta danna 4 ta tsaya tana ɗan bubbuga ƙafa saboda sauri da take kar ya buɗe mata akwati.

Shi kuwa ta bangarenshi shima zama yayi ya É—an huta saukinta ba wani sallah a kanshi, ya cire jubba da rawanin ya bar iya gashin kanshi mai spring asalin na Fulani amma da yake yana É—an tarawa sai ya ba da wani style mai kyau, system dinshi ya É—auko daga jakarta dake daban ya shiga dubawa ya fi awa zaune dukda yunwar da yake ji amma ba zai iya cin komai a lokacin ba sai ya ja waya yayi placing order na tea daga restaurant na hotel din.

Daga nan ya miƙe ya shiga toilet don aikin ba ya mishi yadda yake so sai ya fara da wanka kan ya fito ɗaure da towel a ƙugunshi ginannen jikinshi da bai murde dayawa ba tsaka tsaki na yalƙi, shi ma kayan baccin da suka ajiye sabbi ya saka sai ya nufi akwatin ya buɗe don duba files da yake so yayi amfani da su kan ya kwanta sannan kuma ya fesa turare.

Kasancewar girgida da akwatin yayi Sossai yana buɗewa da yake a kan gado ya ɗora sai ya ji abu ya faɗar masa a ƙafa, tsuguna wa yayi ya ɗauka yana mamakin menene wannan ɗin don bai tuna sa abu haka a jakanshi ba, Yana buɗe karamin envelope ɗin da bai san dashi cikin kayanshi ba wani strong abu ya shige hancinshi da sauri ya yar yana ambaton

"Subhanallah!"

Tari ya É—an fara fuskarsa har ta sauya, idanu ya kai kan akwatin sai ya ga kwata kwata ma babu abin da ya haÉ—a shi da nashi daga ciki ta waje ne dai suke kama da nashi É—in.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un... La haula wala quwwata illah billah"
Abinda yake ta maimatawa kenan.

"Akwatin 'yar daba!"
Ya sake faɗa a zahiri don tabbas nata ne, hannu ya sa ya riƙe waist dinshi bai taɓa tunanin zai rike irin wannan abu ba a rayuwarsa. What sort of nonsense? Ya sake ayyanawa yanzu idan mistakenly wani abu ya faru jakarnan ya buɗe cikin mutane matsayin nashi ai ta gama zubar masa da ƙima nan duniya.

Bai ma gama sanin abin yi ba ya ji ana knocking da ƙarfi, ya kalli kofan kan ya nufi kofar ya buɗe tana tsaye dab har sun kusa cin karo yayi baya.

"Me ya sa za ka chanza min akwati? Me zan yi da akwatinka?"

Kallon ba ki da hankali yayi mata don ta gama raina masa wayo, da ma duk natsuwar da tayi dazu kaman ba ita ba na munafurci ne ya zaci ta fara sauyawa don ya zauna da ita for over 4hours a ranar bai ga tayi faÉ—a da kowa ba, amma ji abin da take ce mishi a kan kayan maye?

"Wannan tambayar daga bakina ya kamata a ji shi, me zan yi da kayan maye? Me zan yi da abin da Allah ya tsinewa? A'uzubillah! Wa'iyazubillah"

Wani abu ne ya daki zuciyarta ranta ya shiga tafasa, É—an kirkin da take mishi tuni ya kau don ya zo inda ba za ta bari ba.

"Wa ya sani kila kana da abin yi da shi? Ai maye shi ya san makwancin maye idan baka sha ta ya ka san menene ciki...."

Ido cikin ido suke kallon juna don ji yayi kaman ya rufeta da duka, shi take kallo take gayawa wannan magana? Shi dai Irshad Omar Al-Noor? Wonderful! Ya ayyana a ranshi kan yayi magana ta ce

"Malam ka dauƙo min akwatina ko ka ba ni hanya in ɗauki abata!"

Matsawa yayi don ba zai ma iya sake cewa komai ba tunda tace shima shaye shayen yake baya so ma wani ya ji su ko cikin baƙin taron su fito su ga yana magana da irin wannan, ciki ta shige ta ga akwatinta a buɗe tana mita tana rufewa har ta gama ta ja abin ta ta fice, nashi ya ja ya shigar ciki yana rufe kofar cikin adu'ar Allah kar ya sake kawo abin da zai haɗa su.

Yana shiga bai zauna ba Wayanshi ya shiga kira ya É—aga ya duba Ammar ne sai yayi picking yana komawa ya zauna har da kishingiÉ—a.

"Ammar!"

"Ya na ji muryarka haka ko ka fara bacci ne na tasheka?"

Tsaki ya ja yana sake Miƙewa zaune wai shi za ta cewa yana shan wani abu! Duk yadda ya so yayi shiru ba ya jin zai iya abokin taya kuka yake nema, sai yace wa Ammar ɗin

"Yau ni aka kalla tsakiyar ido aka ce ina shaye shaye."

Ammar yayi kasake...kan ya ce
"Ban gane ba! Wa zai ganka ya furta hakan? Waye bai san fuskarka ba da zai iya jefanka da wannan maganan? Ko kwarjininka da kamalanka sun fi ƙarfin a yi musu irin wannan suɓutar bakin lallai ko ma waye ne da tsaurin ido yake"

Irshad ya sauke Numfashi
"Mace ce!"
Sai da ya É—an muskuta ya furta
"Wannan 'yar daban!"

"Mace?"
Ammar ya maimaita da tsantsar mamaki, shi karan kanshi wani lokacin Irshad kan mishi kwarjini kai hatta iyayensu suna matukar jin nauyin shi a abubuwa dayawa saboda tarin baiwa da Allah yayi masa har mace ta faÉ—a mishi hakan a cikin ido? Lallai ko wacece bata da kunya kuma fitsararriya ce.

"Wace 'yar daba? Me ya haÉ—a ku haka?"

"Wannan da ta yi sharing hospital room da Daddah"

"Diva!!!"
Ammar Ya faɗa yana Miƙewa daga zaunen da yake mamakinshi na ƙara ninkuwa.

Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi....

DAÆŠIN ZAMA BY SEEMAHWRITES
JODA BY SADI-SAKHNA
ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH

*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*

*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*

Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin

Sai a tura shaidar biya ta
09039206763

🖤Gureenjoh🖤

ƘARFE ƊAYA BA YA AMO

✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN
(GUREENJOH)

@Gureenjo on Arewapen
@Gureenjih6763 on Wattpad

ADABI WRITERS ASSOCIATION

#THE TRIO OF TALES
(THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY)

*SHAFI NA ASHIRIN DA UKU*

Tana tafiya tana mita chan ƙasa har ta shiga ɗakinta, ta ajiye akwatin kan gado tana kokarin buɗewa a fili take furta.

"Allah ya sa in samu an taɓamin abina mai raba mu yana China kan ya karaso sai mun ɗaga Nigeria..."
Don haka kawai take jin wani hasala na buÉ—e mata akwati da yayi har da sanin me a ciki.

Wani zuciyar yace kai Diva kema fah kin buÉ—e nashi, a fili ta sake furta
"Ai dai ban taɓa komai ba Meyasa da ya buɗe ya ga ba nashi ba ne bai yi gaggawar rufe wa yadda na yi ba?"

Tsaki ta ja bayan kuma ta tabbatar da komai na nan sai ta zauna gefen akwatin, wani abu kaman guiltness take ji irin dai wannan feelings na rashin jin daaÉ—i a kama ka kana yin abu marar kyau. Amma Diva ce tuni ta watsar tana furta
"Oho! Ai shi ya so gani don haka shi ta shafa...we move on"

Tana kai nan ta kai akwatin ɓangaren wardrobe ta ajiye shi a haka kan ta dawo tayi ordering chips and chicken saboda tana jin yunwa, Wayanta ta cigaba da dannawa har ma tayi call da su Jagaban da su Obafiya kan aka kawo mata abinci.

Ta ci Sossai ta sha ruwa, kan ta jinginu da jikin gadon bayan ta haÉ—a ice da ta saba sha don zaman da tayi for over 6hrs yau ba tare da ta sha ba ji take har tsikar jikin ta na tashi kanta na wani yammmm, ji take kaman za ta yi hauka don haka enough ta sha abinta kan ta kwanta tuni ta yi bacci.

Shi kam ta ɓangaren sa rufe ido yayi yana tuna abin da ta ce mishi, yana jin Ammar na maimaita Diva dai? Sai ya jefa mishi tambayar

"Me taje yi a Abuja har hotel da kake?"

Baki ya ɗan taɓe kaɗan
"Ina zan sani Ammar? Ni na fara tunanin ko dai yarinyar nan bibiyata take?"

"Saboda ka mareta?"

Sai kuma ya tuna ashe har yau babu wanda ya san sun haÉ—u bayan nan har ta yanke shi a hannu.

"Kila! Kila kuma abu ne ya kawota kaman yadda ya kawo ni but koma menene I'm very sure ba alkhairi ba ne duba da tarin kayan maye da na gani a akwatin chan, ƙasar mu ya zama abin da ya zama to walk freely da irin wanchan abin a Airport from one state to another"

Ammar ya ce
"Allah ya kyauta to ya kiyaye, sai ka saka ido kar ta cutar da kai Shehi irinsu baka sanin me za su aikata don su kashe mutum har lahira ba komai ba ne a wurin su"

Murmushi mai sauti ya É—an yi kan ya ce
"Ammar za mu yi magana da safe I'm sleepy"

Sallama suka yi yana juya maganan Ammar, ai ya san ba shi ba koma waye ba zata kashe ba matukar da zuciya a kirjinta yayi mata nasiha kan kisa, matukar ta san za ta mutu itama ta komawa Allah.

Knocking ake mishi ya miƙe ya je ya buɗe ya karɓi tea dinshi ya dawo ya sha daga nan ya rufe aikin da yake ya je yayi alwala ya zo yayi karatuttukan da ya saba kan bacci tare da adu'o'i da addini ya tanadar kan ya rage hasken ɗakin ya kwanta.
Chapter 31 · 0% Book details