← Book details Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 42

Sashe 5

Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*****

"Diva!"
Shaly ta ƙira sunanta tana taɓa ta ta ɗan yi firgigit tana dawowa daga tunanin da ta tafi, ta sake kallon Pabloo zuciyarta na karta a hankali, a yanzu sana'ar machine yake mai kafa biyu amma duk inda kuɗin ya zo na Jagaban ne ko biyan gidan hayan da ya gina a gefensu da dakuna masu yawa yake accomodating thugs da suke under drug addicts ko kuma ya biya kudin pentazocine da ya zame mishi addiction ƙarfi da yaji.

"Me kike tunani ne haka?"
Ta girgiza kai
"Ga shi Diva maganin damuwan kenan ko ma wace iri ce"
Zee baby ta faɗa tana miƙa mata coke mai sanyi da ta juye codein ciki, karɓa tayi ta kalla kaɗan kan ta kai Bakinta ta shiga sha.

"Zubash fah?"
"Bata shigo ba bai wuce tana chan suna rigima da Mijin Asawanyarta ba"
Kai ta gyaÉ—a

Suna ta hiran su tsakaninsu bata tanka ba bata ce uffan ba har sai da ta bugu sossai aka kawo mata breakfast ta ci sossai saboda yanayin shaye shaye da ke saka jin yunwa, daga nan É—aki ta koma ta zube kan gado sai bacci.

Da misalin ƙarfe uku da 'yan kai wani irin hayaniya ya farkar da ita, tsaki ta ja tana mutsitsike idanunta da suke a lumshe farare da su, bata da aukin kirki sai hatsari, doguwa ce mai matsakaicin jiki, tana da albarkatun sama da ƙasa don shape ɗinta mai kyau ne, bata da ra'ayin maza shiyasa duk wanda ya tinkareta da sunan soyayya ma sai ta zubar masa da jini wannan alkawari ne hakan ya sa kowa ke gudunta, ita ba fara ba ce ba...irin wannan warm golden brown complexion ce, bakinta ya ɗan yi duhu daga ƙasa tsakiya kuma da haske saboda shaye shaye da take yi.

Miƙa ta yi tana ɗan sosa idanunta, ɗakin har lokacin duhu ne dulum kaman ba rana tsaka ba, ta janyo wayanta ta kunna ta ga time kan ta dira daga kan gadon taje ta kunna hasken ɗakin da kaman na wata princess ya bayyana sai dai komai baki da fari ne don kalar da ta fi so baƙi ne...

Toilet ɗinta ta nufa tana zubar da kayakin jikinta a hanya kan ta gama shiga ba komai jikinta tayi wanka Sharp Sharp ta fito da Alwala gefe chan ta nufa akwai sallaya da doguwar riga da ƙimar ta saka ta haɗa sallar azahar da la'asar hakan ya bi jikinta Dukda ba ya mata dadi yawanci in ta bugu sai ta gwamutsa salloli wasu ta rama wasu kuma sun shige daga haka kenan.

Wardrobe ta nufa babu abinda ta ɗaga a kayakin da ta zubar ta saka wani wando dogo da trench coat a kai ya kai mata har gwiwa duk baƙake sai a lokacin ta zame ɗankwalin ɗazu tulin gashinta ya bayyana ta aske har ta gaji ta daina don kwana kaɗan zai dawo har ya fi wanda ta asken, tufkeshi tayi kan ta ɗauki vintage scarf fara ta ɗaura sau ɗaya ta baya ta saki jelar gefe da gefe, wukakenta da duk akwai sunanta jikin kowanne ta ɗauko, daya bakinshi ma ziz-zag ne irin wannan tana so idan ta soki mutum da shi ta zaro da tsokokinshi ya fi bata kwanciyar hankali sai ɗayan plain ne ta saka su jikinta.

Har lokacin gidan na cike da hayaniya da sauri ta nufi kofa ta fito, ba kowa a parlor ta nufi waje, yaran gidanta ne tsaitsaye suna ta hayaniya.

"Wai ya aka yi ne? Me ke going?"
Muryarta da suka ji ya sa suka daddare.

"Barka da fitowa Shugaba!"
Suka hada baki suna miƙa mata gaisuwa.

"Pascal ne aka sokaaa ya kusa warewa chan kiyama amma dai bai ware ba..!"
Obafiya ya faÉ—a cikin yanayin maganansu.

Lokaci ɗaya fuskarta ya chanza, idan kana kaunar ɓata mata rai ka taɓa daya a cikin mutane bakwan nan da suka zama rabin jikinta.
Pablo, Pascal, Skipo, Obafiya, Shaly, Zee da Zubash.

Jar uban chann! kayyasaa...Wasu ƙananun fitsararru ne da wannan gangancin na tarar aradu da ka?"

"Eh shugaba yaran chan sabon titi ne"
Skipo ya faÉ—a a daddare.

"Chan dallah! kun zo kun tsaya kuna menene yaran basu riga sun shiga kogin jini ba? Ku wuce mu je daga Dorayi zuwa Sabon titi kowa bacci dole....."

Fitooo mai ƙarfi ɗaya ya yi daga ciki wani ya ja addaa kan dakali ya ba da ƙiiiiiiiii

"kowa ya zaburo a bar shi ya kawo... Kafin a yi dare akai kwan, Kuma komin lalacewar masa ta fi karfin kashin shanuuu...kowakkwana lafiya shi ya so... Wallahiiii"

Skipo ya zaro mata key ɗin motarta don bata yarda a tukata, da hanzari kusan su goma sha wani abu da suke gidan a lokacin suka chusu cikin SUV baka wuluk ta zagaya ta shiga ɓangaren driver, tun fitowanta mai gadin ya wangale gate don ya san yau ba zaman lafiya yayi mata garaje ma shima kwana zai yi jinya.

Da wani irin reckless driving ta fita, matasan suna ta ihu da kirari rike da adduna da sanduna...

Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi....

*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*

*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*

Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin

Sai a tura shaidar biya ta
09039206763

🖤Gureenjoh🖤

ƘARFE ƊAYA BA YA AMO

✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN
(GUREENJOH)

@Gureenjo on Arewapen
@Gureenjih6763 on Wattpad

ADABI WRITERS ASSOCIATION

TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne.

GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba.

NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k.

*SHAFI NA HUÆŠU*

Kaman yadda ta yi alƙawarin hana kowa zaman lafiya a yankunan haka suka yi, sun zubar da jini har da waenda basu ji ba basu gani ba, sun ja wa mutane dayawa asarar kayan sana'o'insu kuma basu samu yaron da suke nema ba.

Sanda ne maƙale a wuyanta ita ce gaba suna take mata baya har gaban mota ta shiga su ma duk suka ɗuru sai asibiti inda Pascal ɗin ke kwance, nan ma sai da suka yi rigima amma ta hana a taɓa kowa, daga nan bayan sun duba shi suka yi gida.

Magrib ne ta shigo gidan bayan ta yi parking ko oho ta sauƙa, a cikin motar ta bar key ɗin kofar ma bata rufe ba ta nufi cikin parlor, jagaban ta gani zaune yana shan tabar wiwi.

"Baaba"
"Zo nan 'yar baba"
Don niyyar wuce shi ta yi, dawowa da baya tayi ta zauna kan kujera tana harÉ—e kafafu.

"Daga ina kuka fito haka? Ya na ga yanka a hannunki?"
Ta É—aga hannun ta kalla.

"Nima ban san ya aka yi na yanke ba... Chan Dorayi muka yi muka ɗaga musu hankali, Pascal nawa fa suka taɓa!!"

Pascal kusan idan basu yi sa'anni ba to bai wuce ya girme ta da shekara É—aya ba hakan ya sa tana da shakuwa sossai da shi a click É—in nata, bata manta sanadiyar haduwarta da Pascal a nan gidan ne ya zo sayan Tramadol wanda oganninshi suka aike shi a sadda ta tambaye shi shima yana sha? Ce mata yayi

****

"Ban taɓa sha ba amma Oga Sanusi ya ce watarana da kanshi zai ɗandanamin wai yana hana gajiyar aiki. Kin san aikinmu ba na rago ba ne"

Ta yi dariya tare da kallonshi

"To Meyasa kake zuwa gidan bredin aiki ba ka zuwa makaranta?"

"Diva idan ban zo gidan burodin ba ina zan samu kudin da za mu ci abinci da kanwata da mahaifiyata? Babanmu babu ruwanshi da ciyar da mu a gidan ya auri mata sama da biyar kuma kowacce ta ajiye 'ya'ya amma kowani ɗaki su suke ciyar da kansu, tufatar da kawunansu da kuma kula da lafiyarsu har ma da makaranta idan suna so su saka kansu shi ya ce ba'a yi mishi ba yana ƙarami shima ba zai yi wa kowa ba"

A lokacin tausayinshi ne ya kamata a yadda yake magana, ya taɓa ce mata babanshi na da gidajen haya kaman Babanta haka kuma yana da gonaki a kauyuka da gaske baƙar mugunta ce kawai zai sa ya watsar da nashi da uzurin cewa shima nashi uban bai mishi ba alhali shi ba jalihi bane da iliminshi boko da arabi sai dai ɗan aƙida ne..

Bayan kwana biyu da ya dawo sayan Tramadol É—in yake sanar mata ai ya sha kuma yayi aiki sossai ya samu kuÉ—i har kifi soyayye ya sayawa mahaifiyarshi, daga nan rayuwar shi ta lalace daga wannan sanadiyar ya zama addicted to drugs, ya zamana idan bai sha ba baya aikin bredin, idan ta ga mahaifiyarshi da natsuwar ta ta kan tausaya wa rayuwar Pascal amma bata bari ya bayyana ba, tun samuwar click É—inta yake na gaba gaba a dukkan lamuranta sai dai idan faÉ—a bai tashi da Diva ba yana ciki hakan ya sa take kaunarshi tamkar ciki É—aya suka fito.

****

"Shi ne kika bari aka É—auki hotunanki ana yamadidi da su duniya? Bana son kalar bakin da ake yi miki Sohana bana jin daaÉ—i, ba rayuwar nan na so ki yi ba"
Yayi maganar da iyaka gaskiyarsa don yayi iya kokarinsa amma abin da rayuwa ta zaɓa mata kenan karatun ta yi shi iya secondary ta shiga FCE ta fara karatu ya ƙi dadi don ko ɓata mata rai aka yi ta dawo to su Pascal sai sun shiga sun ɗaga hankalin kowa a makarantar bata je ko ina ba aka koreta ita kuma ta ce ta gama karatun tunda ba dole ba ne babu yadda ya iya ya zuba mata idanu.

Jin ya kira asalin sunanta ya sa ta tabbatar da gaske ya shiga yanayin damuwa.

"Kuttt to na rantse da Allah duk gidan jaridar da suka poster ni har suka yi sanadiyar bacin ranka sai na tarwatsa su..!"
Chapter 5 · 0% Book details