← Book details Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 42

Sashe 10

Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zubash ta É—aga idanunta sama cikin kokarin hana nata hawayen kwaranya, kan ta yi magana Mamansu da ke daga kofa kusan tun fara maganganun nasu ta banko ta shigo.

"Wato ciwon ƙara tsirarshi kike kina labgwabewa don karya zuciyar yayarki ku gudu ku bar ni ko? Toh Allah ya kamaki...kina tunanin a banza ne Zubaidar ke kula da ni? Bautar da na yi muku kun yi min ne? Wahalar da na sha daga daukar ciki har zuwa haihuwa da raino wallahi idan kuka gudu duk sai na yi muku Allah ya isa a kanshi don ko nawa kuka ba ni baku biyani ba. Kuna komawa wurin ubanku kuma babu ni babu ku har Abada ko mutuwa na yi Allah ya isa wanda ya zo kan gawata. Munafuka Algunguma"

"Mama ta ya zan fara tsirar ciwo? Mama haka Allah ya ce? Ki daina amfani da kalmar tsinuwa kina dulmiyar da mu Mama, babu inda Allah ya ce a miki biyayya a sabonsa ko ita Yaya Zubaida ta sani kin riga dai kin yi brain washing É—inta ne take biye miki amma wallahi kaso mai girma cikin zunubinta naki ne Mama"

Hannu ta kai za ta kai mata duka Zubaida ta riƙe.
"Kar ki daketa mama"

Yadda tayi magana ya sa maman fusge hannunta.

"Ki cigaba da zama Nana ke faÉ—a miki abin da za ki yi da wanda ba zaki yi ba, idan kika naÉ—e hannu kika dawo kika zauna zan ga uban da za mu ci har mu rayu kuma wallahi ina kan bakana Yasin zan ja muku akan nonona da kuka sha muddin kuka waiwayi marar zuciyar ubanku"
Tana kai nan ta fice fuuuu khadijan ta fashe da marayan kuka yayinda da Zubaida ta saki murmushi, ba yau ne ta fara jin hakan daga Mamansu ba tun kan ta gama mallakar hankalinta take ji, a da idan ta faɗi hakan hankalinta kan tashi damuwa ya shigeta har ta ji zata iya koma menene don cikawa Mamansu burinta na dai a kawo mata kuɗi, amma a yanzu ko ɗarr bata ji ba kuma da ta yi niyyar komawa uban nasu tsaff za ta koma amma ta tsane shi, ta mishi mugun tsanar da bata ji ta taɓa yi wa kowa ciki har Iro da basa haɗa Inuwa.

Ko babu komai shi Malam Iro ya bar su sun zauna karkashin inuwarsa, sau dayawa shi ya zama makari kuma jingina a garesu Dukda bai É—auki ragamar uban gaske a rayuwarsu ba amma ya tare musu wani gibin.

"Khadija ki yi shiru haka kin ga ba lafiya ce da ke ba! Komai zai wuce ne"

"Har yaushe Yaya Zubaida? Har wani lokaci za mu cigaba da irin wannan rayuwar? Me yasa Allah ya ba mu irin waennan iyayen?"

Sai a lokacin zuciyar Zubaida ya karye ta miƙe kawai ta fice don hawa sama ne kawai zai hanata kuka a lokacin kuma tabbas ta shawu ɗin don codein uku ta kwankwaɗe wani nurse ne ya hange ta ya taho
"Me kike yi haka a asibiti?"
Ta kalleshi ta watsar tare da juyawa ta koma É—akin
Khadija sai ganinta tayi ta dawo É—akin ta zauna sai bacci.

Idanu khadija ta zuba mata tana ta kallonta cikin wani irin tausayi da karayar zuciya.

*****

"Kai!"
Mai sayar da kayan ya matso da sauri yana zubewa
"Ranki ya dade"
"HaÉ—omin abin da na saba saye"
Tun ranar da ta zo ta zaɓi turarukan da take so ta tafi bayan kwana biyu ta dawo ya tambayeta waennene ta kikkifa mishi maruka bai sake tambaya ba idan ta zo tana faɗa zai tattaro su ya zube mata a leda ya kai mata har mota.

Wannan karo ma haka aka yi ya gama ta bashi Atm ya zara ta juya ya bi ta har mota ya kai mata.
Ta jima zaune ciki tana shan ice wanda ita fa shi ne kabb ya zama addiction É—inta idan bata sha ba har ciwon kai take, ba ma ta fara tunanin yadda za ta yi rayuwa babu shi, idanunta ne ya kai kan wani ya shakure wuyan karamin yaro mai sayar da pure water yana kokarin dukan shi ta buÉ—e motar ta fita.

Ya ɗaga hannu kenan ya ji an riƙe ta murɗe tare da ture shi yayi tangal tangal yana kallonta.

"Ƙaton banza Ƙaton wofi idan kwanji kake son nunawa ka samu kato mana daidai kai sai ka samu yaro ƙarami ka zalunce shi?"

Miƙewa yayi zai tunkareta wasu kananun ɓarayin kasuwa suka riƙe shi
"Kai malam Wuta gabanka wallahi.... Kiyaye kar ta soye ka gwara ka shafawa kanka lafiya ka bata haƙuri idan ba haka ba...."

"Idan ba haka ba m...."
Ƙulii suka kaiwa bakinshi bai zaci za su dakeshi ba ya riƙe da wuri yana jin gishiri gishiri na jini da ya tarar mishi
"Ka ware ko kuwa?"
Da sauri ya wuce suka fara mata kirari, Ta juya wurin yaron ta bashi dubu biyu tace ya kara jari yayi sana'a.
Yayi mata godiya bata kula shi ba tayi mota waennan Matasa na bayanta su ma sallanarsu tayi suna ta mata kirari har kan ta ja ta fice da wani irin gudu, music na tashi cikin motar, daidai ta zo shan wata kwana motar Malam Bala ma ta sanyo kai Dukda ya yi Horn sossai bai ji alamar wata mota ba ita kuma ba Horn tayi ba kuma gudu take, ta yi wani irin buga musu gefen mota, ƙiiiiiiiii ta jaa wani uban birki a fili ta furta

"Kan uba!!"
Cikin fushi, motar take kallo da ido ta mirror amma don rainin wayo na cikin bai sauƙo ya bata hakuri ba, ranta ne ya ƙarasa ɓaci da wani irin zafin nama ta ɓalle murfin ta fitoo...

Tana kallon yadda gaban motarta ya gurje har danger light ɗinta na gaban ya fashe tayi saurin isa farar motar ta ɓalle murfin, malam Bala da tun da ya ga ita ce yake salati jikinshi na wani irin rawa, Ammar na ƙoƙarin mishi magana sai gani suka yi an janye shi waje, shima malam bala bai gama firgita ba sai da ya ji ta mishi riƙon ɓarayu hannun mata, ta chakumo kwalarsa ta janyosa waje tamkar wani ƙaya ta haɗashi da jikin motar idanunta gabaɗaya a waje suka kara firgita dattijon...

Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi....

DAÆŠIN ZAMA BY SEEMAHWRITES
JODA BY SADI-SAKHNA
ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH

*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*

*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*

Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin

Sai a tura shaidar biya ta
09039206763

🖤Gureenjoh🖤

ƘARFE ƊAYA BA YA AMO

✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN
(GUREENJOH)

@Gureenjo on Arewapen
@Gureenjoh6763 on Wattpad

ADABI WRITERS ASSOCIATION

TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne.

GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba.

NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k.

*BAABI NA TAKWAS*

"Innalillahi wainna ilaihi rajiun..."
Ammar da Imam suka faÉ—a suna balle murfin motar suka fito da hanzari, hill É—inta ta sa ta take masa kafa sai da ta fasa ya saki karar azaba ta tsinka mishi mari tana furta.

"Kai wani irin dakiki ne kana tafiya baka kallon hanya? Ka san Allah yau sai ka gwamnaci kida da karatu tunda ka taɓo DIVA..." Cikin wani kalar murya take magana da ya ƙarasa kaɗa 'yar hanjin shi, ko kan yayi wani motsi ko ɗaya daga cikinsu ya farga suka ji ƙarar ƙarfe....
WUƘA ta zaro tana ƙoƙarin kai mishi yanka ta ji an riƙe hannun, wani irin riƙo da za ta iya cewa ta ji Ƙashin wurin ya motsa.

Tana Juyowa don ganin mai wannan zarrar ta ji sauƙar wani mahaukacin mari da ya sa tayi taga taga gyalen kanta na suncewa gashinta ya zuba a fuskarta, hannun da ya sake murdewa ya Buge wuƙar ƙasa ya ɗora kafarsa kai, ita kuma hannun ta kai kan fuskarta ta riƙe tana kokarin dawo da kanta duniyar mutane.

Ita wani zai yi wa wannan mari?
Ita aka mara a yau?
Lallai duk garin Kano babu zaman lafiya, wani irin É—agowa ta yi Bakinta gefe ya fitar da jini haka idanunta gefen marin ya yi ja.

Idanunsu suka sarƙe yana kallonta cikin wani irin fushi da bai taɓa sani yana da shi ba, sossai ya ji ciwon marin da ta yi wa Malam Bala da zai iya cewa idan bai yi shekaru daidai da su Abba ba kaɗan ne za su fi shi, dattijo mai kirki da kawaici wai wata 'yar kwalta har ta samu zarrar marinshi a karkashinsa?
A haka ma Allah yake ta ambato don da sai ya ɓallata, wani irin tafasa ranshi ke yi har tsokar jikinshi na rawa don ranshi ya kai makura wurin ɓaci kuma shaidan na ƙoƙarin taking over, bai taɓa duka ba don duk kannenshi presence ɗinshi kawai kan saka su natsuwa bare ya ɗaga idanu ya kalli mutum.

Muryarsa da bai iya ɗagawa har chan ba a yanzu sai yayi ƙasa saboda bacin rai, duk su Ammar sun daskare ya kara matsawa, sai ta zama wata 'yar baby a gabansa, bata taɓa jin abin da ya girgiza zuciyarta ba irin idanunsa masu dauke da fushi da bacin rai.

"Ashe bayan dabancin ke É—in mahaukaciya ce? Kai ko mahaukaci ba zai kalli furfurar bawan Allahn nan ya tsinka masa mari ba, ko bai yi jika da ke ba ya haifi ire-irenki dayawa..."

Yadda take kallonshi da idanunta waje kaman har lokacin bata fita daga kaÉ—uwa ba ga shi mutane sun fara taruwa ya É—auke idanu daga kanta ya ce har lokacin wani kyama, haushi da tsanarta ke sake building a ransa.
Chapter 10 · 0% Book details