Sashe 1
Ƙarfe Daya Ba Ya Amo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ƘARFE ƊAYA BA YA AMO
âœï¸FATIMA MUHAMMAD GURIN
(GUREENJOH)
@Gureenjo on Arewapen
@Gureenjih6763 on Wattpad
ADABI WRITERS ASSOCIATION
#THE TRIO OF TALES
(THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY)
TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne.
GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba.
NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k.
*SHAFI NA ÆŠAYA*
*SHIMFIÆŠA*
Farar mota ce mai matsaikacin kuɗi ƙirar lexus ke tafiya cikin natsuwa babu gudu bare rough driving, daga gani matuƙin ba yaro bane ko kuma ya iya kasancewa yaron amma mai tarin sani akan harkar tuki da kuma dokokinta, idan ka tsananta nazari kuwa zaka fahimci ana bin motar a hankali ne saboda wanda ake tuƙawan ba abin wasa ba ne ko na ganganci.
Daga cikin motan mutum huɗu ne, ɓangaren mai zaman banza akwai wani matashin saurayi da ya fi yanayi da ɗalibin neman ilimi, sanye da jumpa mai sauƙin kuɗi har da hula rungume da wasu tarukuce na briefcase, Laptop da sauran gadget.
A baya ɓangaren hagu nan ma wani matashin ne amma da alama zai iya girmewa wanda ke zaune daga gaban a shekaru, fari ne sanye da baƙar Thobe (jallabiya), ya ɗora hular taɓani-ka-ji-hadisi fara a kanshi mai matsaikacin gashi, fuskarshi cike da saje haka kuma hankalinshi gabaɗaya na ga gefenshi da magana mai sanyin amo ke tashi cike da wani irin natsuwa da waenda ke cikin motan ba don sun natsu kuma sun kasa kunne ba babu abin da zai sa su ji me yake cewa.
Mai maganan dake zaune daga ɓangaren dama ya ɗan muskuta, tare da ambaton Allah ya yi shiru tamkar mai nazari sai kuma ya cigaba da magana a hankali.
Duk inda kake neman natsuwa da kamala a kallo ɗaya da zaka yi wa wannan bawan Allah ka same su ka gama, daga yadda yake zaune za ka fahimci dogo ne, yana da matsakaicin jiki amma da alama ƙarfaffe ne, yana da haske fari ne fat, fuskarsa da cikakken gemu wanda da alama ba'a taɓa shi iyakaci gyara, idanunshi sakaye da wasu fararen madubi amma hakan bai hana bayyana natsuwa da zurfinsu ba.
Sanye yake da Grey Thobe ya ɗora baƙar shara sharan alkyabba irin ta Larabawa wanda ake kira (jubba) a kai, kanshi akwai Ghutra(wannan gyalen da aka san Larabawa da ɗora wa a kai mai kalar ja da fari da ya zauna mishi sossai a saman ta kuma akwai Agal (wannan baƙin abu mai yanayi da gammo wanda ke hana Ghutra faɗuwa idan ana iska) agogo mai sauƙi amma tsadar a bayyane take ɗaure a tsintsiyar hannunshi, hannunshi ɗaya jikin motar ɗayan na daga kan kafafunshi yana cigaba da yi wa na gefen magana.
"Ammar ina fatan ka fahimta?"
"Eh Shehi, In shaa Allahu za'a yi komai yadda ka ce"
Kai ya gyaÉ—a kan ya mayar da idanunsa kan titi ya cigaba da azkar cikin natsuwa don shi ma'abocin yawan zikiri da salatin annabi ne hakan ne kan katangeshi da duk wasu surutai marasa dalili.
Wani kalar wawan birki matuƙin motar ya ci. Ammar da yake danna waya ya ɗago da ɗan hanzari.
"Ya dai Malam Bala?"
"Malam Ammar ina ga fa 'yan fashi ne a gabanmun nan, gashi sun rufe hanyar"
Malam Bala ya faÉ—a sai dai ko É—arr dukkansu babu wanda ya ji don ba yau suka saba encountaring irin waennan É—in ba tunda aikinsu ne na kai wa dare wurin wa'azi da karatuttukan Shehi na dare.
Ko kan wani daga cikinsu yayi yunƙuri an fara bubbuga musu glass kuma tuni Matasa har huɗu sun zagaye motar da Malam Bala ya dannawa General lock.
"Ka ga irinta ko Irshad? Sai da na faɗa maka securities are very important to you amma ka ƙi aminta, yanzu idan wani abu ya sameka fa?"
Ammar ya faÉ—a duk tashin hankalinshi na bayyana Dukda adduna ne da sanduna yake hange hannayensu, alamunsu duk sun bayyana tsananin maye da ficewar hayyaci.
Sai a lokacin Shehi da Ammar ke yi wa magana ya buÉ—e idanu ya kalli situation É—in cikin natsuwa.
Ya kalli Ammar
"Rayuwa da mutuwa duk na Allah ne Ammar"
Jarumtakarshi da tsantsar tawali'unshi na sake bayyana tsantsa a kalaman bakinsa.
"Duk da hakan wani sa'in ba mutuwar ce abin tsoro ba wahala ake ji wa"
Ko kan Ammar ya gama rufe baki an bugi glass na gefen Malam balan sai da ya daddatase, innalillahi wainna ilaihi rajiun duk suke maimaitawa, kan su ajiye ma an sake kaiwa glass É—in duka da sandar gora tuni ta tarwatse.
"Kai Tsoho me ya biyo da kai hanyarmu a lokacin farauta?"
Wata kakkauran murya marar daaɗin ji ta faɗa tana haske su da tourch light, maganan su ya sa hankalin Ammar ya ɗan kwanta da alama zaune gari banza ne, 'yan daba masu kwacen waya da sauransu, wayanshi yake kokarin kunnawa ya kira 'yan sanda cikin dabara aka bugi glass ɗin ɓangaren shi ma ya rushe har yana ji mishi ciwo.
"Hasbunallahu wani'imal wakeeel.."
Kalmar da ta fito a bakin Shehi kenan don idan akwai abin da ke zama weakness ɗinshi to cutar da makusancinshi ko masoyinshi, yana ƙoƙarin buɗe kofar ya fita don basu duk abin da suke nema ya ji wata murya ta shiga ratsa kunnuwanshi.
Mace?
Ya raya a ransa yana juya fuskarshi inda sautin Muryar ke fita bayan ya kai idanunsa kadan ya ga time wurin karfe É—aya da wani abu na dare.
"Kaiiiii....wasu ƙananun ƙwarin ne nan?"
Yadda Muryar ta fita babu abin da zai hanaka fahimtar mammallakiyar Muryar a Buge take, kuma cikin wani irin salo na dabanci sai dai zaƙin Muryar bai ɓuya ba sam.
Waenda suke jikin motan ne suka juya gareta suna hasketa idanunsa suka samu nasarar sauƙa a kanta.
Ya subhallah!
Ya ambata a ransa, wani cargo baggy trouser, sai sweeter hoodie mai hula jikinta baƙake, kanta sanye da facing cap da ya rufe rabin fuskarta sai ta ɗora hulan rigan a kan facing cap ɗin, hannunta wani coke ne da ba tantama a surke yake da wani abin.
Abin da ya ɗaga mishi hankali tabarbarewar tarbiyar wannan zamani, mace ta tsinci kanta cikin wannan kazanta ba ƙaramin abu bane ga malamin addini irinshi.
"Ke!"
ÆŠaya daga cikin waenda suka tare su ya faÉ—a yana sa hannu a baki alamun mamaki kan ya cigaba.
"Babawo... ka ga wata gara chan wai da mu take?"
Tsaki ta ja tsiriri ta matso sossai kan ta sa hannunta ta ja hoodie É—in kanta idanunta dake a lumshe cikin maye amma tsaff kanta ya gama É—auke wa don tana cikin hankalinta suka bayyana ta kallesu.
Zare ido É—ayan yayi
"Kaiiiii.... Gayuuuu wallahi DIVA ce..."
Bata ce komai ba wasu gayu huÉ—u da mata uku a bayanta duk cikin shigar da zai tabbatar maka thugs ne, kowa kuma ka bincike shi ba ka rasa mugun makami a tare da shi suka bayyana.
"Ku bar nan...!"
ÆŠaya daga cikin mazan ya faÉ—a cikin kakkausan murya.
"Tuba muke uwar É—aki, ai ja da ke sai É—an wahala ko mai kararren kwana! Allah ya taimaki shugaba..."
Hannu ta ɗaga kaɗan ta nuna musu hanya fuskarta babu digon fara'a ai tuni suka yi gaba don babu ɗan daban da bai san sunan DIVA ba da click ɗinta waenda suke tamkar yayyunta amma kaman bodyguard suke a gareta umurninta suke bi a komai, kuma su ne ƙawayenta abokan hiranta, yana wuya ka ga Diva na magana idan ba da su bakwan nan ba to Babanta... shiga komarta dai dai yake da yanke kauna da rayuwa, ko bata ɗauki mataki ba Jagaban Uban daban gabaɗaya garin Kano shi ne Babanta dole ya farauceka ko ina ne ya yanke maka mummunan hukunci, bare ita kaɗai ta ishi gayya, wargaza taro ce da idan tayi juyi sai an bata wuri Dukda matsayinta na mace wasu kan ƙirata kwaruwa don fitinanta ya fi ƙarfin giwa.
Idanu ta zubawa Malam Bala.
"kai dattijo! ka kiyaye fita a irin wannan lokaci na dare da duk karnuka suke waje, idan yau ka taki sa'ata gobe zan iya wucewa tamkar ban ga me ke faruwa ba...gayun nan kuma...ehh ya nee...ina fata kana fahimta?"
Tana maganan ne cikin wani salo idanunta suna lumshe wa da buÉ—ewa da kansu.
Tsantsar mamaki ya kama su, amma Malam Bala ya daure ya ce
"ÆŠiyata mun gode, amma don Allah da za ki yiwa kanki faÉ—a wannan rayuwar bata kama...."
Muƙuttt haka maganan ya koma tamkar an tura shi jin sauƙar wata kyakyawar WUƘA mai sheki saman maƙogoronshi.
Muryarta ya ƙara kaushi, tana mishi wani jan kallo da har Ammar da Imam sun razana ta ce
"Ko da kuskure ka sake buɗe baki da niyyar min wa'azi sai na tsinke maƙogoronka na rantse da Assamadu!! Naaa daɓa ma wannan wukar na ga gatanka"
Bai yi magana ba hannunshi dake kan stiring ne ke wani irin rawa, tayi tsaki tare da janye wukar ta nuna hanya
"Ware..."
Idanunsu ne suka sarƙe saboda shi mamaki da tsoron Allah duk ya rufeshi, wani ɓangaren tausayi ne, idan yana jin labarin akwai 'yan ta'adda bai san abin ya kai har mace ma ta zama shugaban 'yan dabar ba don daga reaction na waenda suka soma tare su zaka san sunanta ya jijjigasu.
Kallon seconds biyu yayi mata saboda wani irin mamaki na iya dorawa mutum kaman Malam Bala dattijo wuka a makogoro ya rufe shi.