Sashe 9
Joy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Matso mata da shi gabanta tayi, kwancewa tayi ta shiga fito da kullin ledodi a kasa buhun kuma ta fito da doya manya guda uku, kallon Fatima da tayi kasake tana kallonta tayi ta ce "kwashe wannan ki kai mana kitchen wannan kuma ta fada tana nuna mata ledodin gabanta ki bud'e robar da muke ajiye kayan abinci ki sassakasu ciki shinkaface da wake, Fatima da mamakin Ummi ya gama kasheta tace "Ummi kasuwa kika je? Ita kanta bata san sanda tambayar ya subuto mata ba ganin dai tunda suke Ummi bata tana zuwa kasuwa ba komai yayanta ke kawowa, komai za'a siya shi yake siyowa dagowa Ummi tayi ta kalleta kafin ta ce "ba kasuwa naje ba." "To ina kike je waya baki wadan nan kayan abincin?" Ta fada a zuciyarta a zahiri kuma ta ce "Oh ai na dauka can kika je na ganki da kayan abinci." Ummi bata amsata ba, sai ci gaba da kokarin kwance ledan shambo da tarugu da take yi ta juye a kwando.
Cefane Ummi ta dawo da shi ba na wasa ba , harda su mai da maggi da busasshen kifi, sai da suka gama Adanawa tsab ta kalli Fatima ta ce "ba na son yayanki yayanki ya san da maganar kayan abinci nan ko da wasa." "To Ummi amm....." "Kinji abunda na fada ko baki ji ba." Sai da ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce "naji Ummi insha Allah bazai ji ba." Murmushi Ummi tayi ta ce "yawwa fateetee ngd,." Fateeteen data fada yasa Joy ta fado mata a rai, cike da dan damuwa ta ce "Ummi yau joy bata zo school." Ummi ta ce "Allah sarki kila ta samu wani uzurine yau din." Fatima ta ce "ummi Joy fa bata fashin makaranta, ni dai ina ji a jikina kamar bata lafiya, tun dazu da na tuno ta gaba na ke faduwa." Ummi ta ce "Assha! To kiyi ta addua, koma menene Allah ya takaita." "Amin Ummi" Fatima ta amsa yana mikewa zuwa kitchen dan ta hada wutar sanwar dare.
Karfe Tara dai dai Al'ameen ya maida keke nape gidan Alhaji bala baka shot, kamar yadda yayi singing sanda zai dauka haka yayi singing da ya mayar bayan alhajin da kan shi ya duba lafiyar keken, yaga babu wata matsala, 3k Al'ameen ya bashi cikin cinikin dubu hudu da dari biyu da yayi, amsa yayi yana washe baki sabanin da da fuskarshi yake murtuk yana jiran yaji da wannne ya dawo dan yanzu kafin shi mutum biyu da suka dawo da kekuna har yanzu gasu nan ana kes, daya ya samu accident gefen keken ya lotsa dayan kuma dubu biyu yakawo sabanin dubu uku da yake a ka'ida idan mutum yayi fitar rana zuwa taran dare zai kawo.
Sallama yayi musu ya tafi bayan yabar alhaji bala na ta bala'i a biya shi ko ya hada su da polie don shi akan kudi babu sani babu sabo ne.
Sai gurin goma saura ya iso gida, a tsakar gida tarad da su, Fatima ta tare shi tare da karbar ledan biredin daya siya musu a hanya.
Ummi ya tsuguna ya gaisar kamar yadda ya saba kullum, ta amsa mishi tana "Alhmdllh yayan Fatima jiki yayi warware dama tunda na dawo Fatima ta ce ka fita aiki nace to jiki ya yi dauki kenan." Murmushi yayi ya ce "eh ummi wlh jiki Alhmdllh." Nan ya zauna Fatima takawo mishi abincin ya ci suna ta hira, gefe daya kuma iska na kadawa hadari na haduwu,
Sai gurin sha daya saura Ummi ta ce su ta shi haka gobe da makaranta, dari takwas din daya rage mai a aljihu ya kwaso duka ya mikawa Ummi, ya ce "Ummi ga wannan ki rike a hannunki a sai wani abin." Kallon shi tayi tana murmushi ta ce "A'a Amintacce ka bar shi kaima ka rike a hannunka kayi hidimar makaranta ni akwai kudi a hannuna kuma a kwai abincin da zamu ci gobe ka fini bukatarsu, Allah yayi albarka." Tana gama fadin haka ta mike ta shiga daki ta turo kofarta don karma ya tsareta da magiya,
Iska da hadarin daya taso gada gadan ne yasa shi sauri ta shi yayi hanyar dakin shi, gaban shi na dokawa wanda shi kadai yasan dalilin haka.
Kamar jira ake yi su ta shi a tsakar gidan, take ruwa ya kece da wani irin karfi mai ban mamaki, kudundunewa yayi cikin bargo bayan ya lafta kaya masu nauyi a jikin shi, kwance yake kawai yana jiran tsammani, amma zuciyar shi cike take fall da tsoro, fatan shi daya kar ciwon shi ya tashi, shiru yayi a kwance yana sauraren sautin ruwa da haka barci barawo ya kwashe shi ba tare da sanin shi kasancewar dama a matukar gajiye yake.
Kusan raba dare akayi ana tsuga ruwa, can cikin barcin shi ya fara jin sauyi a jikin shi, ji yayi wani irin sanyi na ratsa kasusuwan jikin shi, babu abin da yake bukata a lokacin sai dumi, duk da kasancewar a cikin bargo yake a kudundune, dumi yake bukata ba irin dumin bargo ba, sannu a hankali tsigar jikin shi ya fara tashi, kafin daga bisani wani irin feeling ya lullubeshi, rasa Inda zai saka kanshi yasa ya cusa duka hannayenshi cikin wandon shi, ya matse abin shi dake ta mishi wani irin honkoro, yana ambaton innalillahi wainnailai rajiun a zuciya, magani yake son sha , amma har yanzu abin bai kai matakin da Dr ya ce idan ya kai ya hadiyi maganin ba, kuma baya fata ya kai stage din, sai dai fatan shi bata karbu ba, dan cikin abinda baifi minti biyu ba maran shi tayi wani irin kullewan da yasa babu shiri ya yaye bargon ya mike ya nufi jakar nan, ya zaro sachet din maganin shi balla yayi ya jefa a baki kafin ya bi da ruwan buta ya koma ya kwanta yana nunfarfashi.
Da asuba da karfin shi ya tashi ba kamar wancen ranar ba kasancewar bai bari ciwon ya shige shi sosai ba ya sha magani, kamar kullum saida ya kwankwasa masu Ummi kofa kafin ya wuce masallaci, koda ya dawo zama yayi ya gabatar da azkar da sauran addu'o'inshi Inda ya roki Allah ya kawo mishi dauki game da wannan matsalar da kullum kara gaba take yi a gare shi, bayan ya gama kuma ya daura da karatun alkur'ani mai tsarki cikin daddadar sautin kira'ar shi wanda ya karade ko ina na gidan hatta da gidajen makota na kusa, Amira tana daga tsakar gidan su ta na aikace aikacenta tana sauraren shi zuciyarta gari tass.
Seven fourty Fatima ta gama shirinta na schools, sai dai yau ma kamar jiya har ta fito gida babu Joy babu labarinta, jiki a sabule ta k'arasa class, tana fatan Allah yasa ta cimmata a can , sai dai nan ma wayam, haka ta isa sit din su ta zauna jiki a mace.
Yau kan damuwar data shiga yafi na jiya haka kawai jikinta ke bata ba lafiya ba, ta kudiri aniyar zata tambayi David ta ji ko mekefaruwa tun da shi dan uwanta ne bazai rasa sani ba.
Da aka buga break time, ta yi sauri ta isa sit din David da har ya mike yana goya jaka da harshen nasara ta ce "Sannu David." Wani banzar kallo ya mata ya dauke, bata damu ba ita dai fatan ta taji halin da Joy ke ciki ta sake ce ma shi "me yasa Joy bata zo school ba kwana biyu." Share ta yayi kamar bada shi take magana ba bata yi zuciya ba ta sake cewa "ko bata da lafiya ne dan Allah ka gaya min na damun sosai da rashin ganinta?" D'agowa yayi wannan karon ya ce "ha'ahh! Wai ke mayya ce ne? To nima ban sani ba kije gidan su ki duba."daga haka ya fice ya barta tsaye a wurin.
Haka Fatima ta koma gida cikin wani irin yanayi, tana isa kuwa labarin yau ma Joy batta zo school ba ta fara ba ummi da yadda sumayi da David, tausarta Ummi ta yi akan kar ta damu in sha Allah joy tana lafiya ai lafiya ke buya, ta dai ji ne kawai amma ba wai hankali ta ya kwanta ba.
Ranar har Yaya Ameen sai da ya fahimci tana cikin damuwa daya dawo da daddare, shima cikin damuwar yake amma ya danne nashi, koda ya tambayeta damuwarta kin fada ta yi sai hawaye da ta shiga zubarwa sharr! Ummi na jin su bata saka baki ba, don abin na Fatima ya fara wuce makadi da rawa, har kullum bata gajiya da mamakin irin shakuwa da kaunar dake tsakanin Joy da Fatima.
Da kyar Al'ameen ya lallabata ta sanar mashi da damuwar tata, tabe baki bayan ya gama sauraranta, shi bai ga abin damuwa akan wannan ba, hakan yasa bai bama damuwar tata mahimmanci ba, sai ma canza akalar hirar tasu da yayi.
Washegari daya kama friday ma bata sake zani ba still Joy bata je school ba, zuwa yanzu kuwa ta gama yanke shawaran bin abinda zuciyarta keta azalzalanta akai wato zuwa gidan su Joy ...............
Me buƙatar shiga group ya tuntuɓeni ta wannan lambar
09116099486
[12/29, 2:32 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀
*PAGE 8*
ASSALAMU ALAIKUM
KUYI HAƘURI DA JI NA SHIRU DA KUKA YI KWANA BIYU, HAKAN YA FARU NE SABODA WANI DALILI MAI ƘARFI , AMMA YANZU NA DAWO INSHA ALLAH ZAMU ƊORA DAGA INDA MUKA TSAYA, FATAN DAI BAKU MANTA LABARIN AL'AMEEN DA JOY BA KUCI GABA DA BIBIYA AKWAI FAƊAKARWA, WA'AZANTARWA RIKICIN KABILANCI, TARE DA ZAZZAFAN SOYAYYA MAI TAƁA ZUCIYA.