Sashe 2
Joy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta sunkuci Jakarta ta goya, saida ta yi tsayuwar minti biyar a bakin get din ganin babu Wanda ya ganta yasa ta juya cikin sauri sauri gudu gudu ta bar bakin get din, dai dai zata shiga wata kwana dake bayan katangar school din taji ance " *JOY JAMES* " da ƙarfi, koda bata juya ba tasan me wannan muryar hakan yasa ta juyo ido huɗu sukayi da juna ta maka mai harara tare da kallon gargaɗi kafin ta juya ta runtuma da gudu, "Joy!! Joy!!" Haka David ya dinga kwala mata kira amma a banza dan bata juyo ba balle ta tsaya, ƙwafa David yayi kafin ya kinkimi jakar shi ya shige cikin school din.
*********
*AL AMEEN* kiran sallan Assalatun farko a kunnen shi saboda sabon da yayi da tashin asuba ko a wani iri hali yake idan har asuba tayi ko da kiran sallah ko babu zai farka, babu laifi yaji sauki sosai amma duk da hakan ciwon bawai ya gama sakin sa bane, lallaɓawa yayi ya mike yana yamutsa fuska alamar ciwo, ya dauki butar shi guda ɗaya dake ɗakin ƙofa ya nufa ya zare sakata tare da buɗe wa, wani sanyi ne ya doke shi wanda yasa yayi saurin rintse ido, danne zuciyar shi yayi ya zuro ƙafafun shi waje, a haka yana mammatse jikin shi ya nufi cikin gidan, tsakar gidan madaidaici ne mai dauke da daki babba guda daya ciki da falo, sai makewayi da madafi dake daga gefe.
Ƙofar ɗakin Ummi ya nufa kamar kullum duk asubar duniya shi yake tashin su, sai da yaji Ummi tayi gyaran murya alamar tana farke, sannan ya lallaɓa ya nufi toilet, ruwa ya kama, ya fito ya daura alwala da sauri sauri ya koma ɗaki yana rawar ɗari, ranar kasa fita sallar asuba yayi yana ji yana gani aka tada sallah a masallacin kusa da gidan su amma bazai iya fita ba domin yana tsoron abin da zaije ya dawo bugu da ƙari kuma dama ba wai ya gama wartsakewa bane, komawa yayi ya kwanta bayan ya idar da sallah, a maimakon tilawar alƙur,ani daya saba yi kullum bayan sallar asuba har gari yayi haske, dalili kuwa, saboda jiya bawai ya samu isasshen barci bane.
Ummi sai da tayi sallarta ta idar kafin ta ƙarasa kan karamin gadon dake uwar ɗakin ta, a tausahe ta kai hannu tana tsashin *FATIMA* Dake barcinta hankali kwance, ware ido fatima tayi akan Ummi, ganin ta buɗe ido yasa Ummi cewa "'ki tashi gari yayi haske, koda ba sallah zakiyi ba ki dauro alwala kizo kiyi arkar ɗinki." tashi tayi tana cewa "to Ummi" ganin ta tsahi yasa ummi komawa taci gaba da azkar ɗinta.
Alwala Fatima ta dauro ta zo ta zauna ta gabatar da azkar da addu'ointa kamar yadda ummu ta sabar mata koda kuwa tana jini ne bata yarda ta barta ta zauna haka kara zube ba .
Bayan ta idar miƙewa tayi taje gaban ummi ta tsuguna tace "ina kwana ummi." sai da ummi ta shafa adduar da take yi sannan ta juyo ta kalli fatima tace "lafiya ƙalau fatima, fatan kin tashi lafiya." ta amasa da "lafiya ƙalau ummi." "To alhamdulillah, maza ki tashi kije ki gaida yayan ki sai kizo ki amshi kuɗi ki sayo gawayi asaka ruwan wanka a dama kunu." "to ummi" fatima ta amsa tana miƙewa
Ɗakin dake zauren gidan ta nufa, tafi matukar mamakin jin yau bata jiyo sautin zazzaƙar muryar yayanata ba, haka dai ta daure tayi sallama abakin ƙofar da mamakinta shiru taji ba amsa kusan sau uku tana sallama taji shiru abinda ba kasafai ya cika faruwa ba, hannu tasa ta dan turo ƙofar dakin ta leƙa don duk atunaninta baya ciki ne, ga mamakinta ta hango shi kwance kan gadon shi ya ƙudundune waje ɗaya cike da mamaki ta juyo ta dawo cikin gidan, ganin yanayinta yasa ummi tambayarta lafiya, cikin dan damuwa tace "ummi me yasa mu yayana yau yake barcin bayan asuba ko bashi da lafiya ne." kallonta ummi tayi kafin tace ""barci kuma? cikin sigar tamaya gyada mata kai fatima tayi ta ƙara da cewa "na leƙa ɗakin shi na ganshi kwance ƙudundune cikin bargo" ɗan jim ummi tayi ita kanta ta cika da mamaki can kuma tace "eh to wata ƙila baiji daɗi bane, bari naje na duba shi ki dauki dari biyu cikin pos ki siyo gawayi ki hura wuta."
Bayan tafiyar fatima tashi ummi tayi taje ta duba Al'ameen, kamar yaddz FATIMA ta fada haka ta same shi, cike da alhini ta ja mishi kofar ta koma cikin gida.
Ko da Fatima ta dawo kitchen ta shige ta hura wuta dakyar ya kama saida ta ɓata lokaci kasancewar gawayin yayi sanyi, tana gamawa ta haɗa wanke wanke, koda ta gama ta samu ruwan baiyi wani zafi ba haka ta zauna tana fofitawa har ummi ta gama lazuminta ta fito ta same ta, ganin haka yasa ummi cewa "har yanzu baki Shiga wankan ba Bintz kinsan yayanayin makarantar Ku basu da sauki idan aka makara fa"
"Wlh ummi gawayin ne jikakke wutan baici sosai." Bude ruwan ummi tayi ganin zai isheta wanna idan ta juye duka yasa tace "je ki dauko bakitin wanka ki juye duka kije kiyi in kin tafi ni da yayanki sai musa muma muyi tunda mu babu Indi zamuje"
Bayan ta juye ruwan, ruwan kunu ummi tasa gani har bakwai ta gota, da kanta ta zauna tana fifita wutan, koda Fatima ta fito wanka ɗaki ta wuce ta ciro kayan makaranta cikin sif a goge tsab, da sauri sauri ta fara shiryawa, cikin farin Riga mai dogon hannu da skirt sky blue sai dai nata dogo ne ya sauka har kaurinta kasancewarta musulma ta daura dankwali tare da madaidaicin hijabi daya rife mata kirjinta, Jakarta ta dauko ta fito tsakar gidan bayan ta saka takalmi da safa, nan ta tarar ummi ta gama dama kunun koko, ganinta yasa ummi cewa yawaa Binta miko robar siga da ledan kulikuli in baki naki ki karya ki tafi, ajiye jakar tayi ta koma ɗaki dauko sugar da kulin ta fito tana zare ido ganin yadda lokaci yaja.
A gurguje tasha kunun bata ma shanye ba saboda da zafi ta ajiye saura ta sunkuci Jakarta, ummi tace "ki dauki nera hamsin a pos." Da Sauri ta shige dakin ta dauko tana fitowa tsakar gida *JOY* na kwada Sallama cikin gurbatacciyar hausarta, dai dai time ɗin kuma Al'ameen ya fito daga dakin shi sanye da singlet fari da dogon wando a jikinshi,turuss joy tayi gabanta na wani irin dokawa da mugun karfi take jikinta ya dau rawa lokacin da idanun Al'ameen ya sarke cikin nata.....
More comment more typing
Me buƙatar shiga group ya tuntuɓeni ta wannan lambar
09116099486
[12/29, 2:19 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀
*BY*
*AYSHA NALADO*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
*LITTAFI NA ƊAYA*
*PAGE 2*
Turusss Joy tayi gabata na wani irin dokawa, take jikinta ya ɗauki rawa lokacin da idanunta ya sarƙe cikin na Al'ameen, wani irin mugun kallo ya shiga jifanta da shi kallon gargaɗi da tsantsagwaron tsana wanda ita kaɗai ke ganin hakan , ta rasa dalili a duk lokacin da idanunta zai haɗu dana yayan Fatima ta kan rasa nutsuwarta, ta kan shiga firgici, da tashin hankali kwarjini yake mata kamar zaki, yanzu ma gani ta yi duk ya cika wajen, zata iya rantsuwa da yesu almasihu bata taɓa ganin murmushi a fuskarshi ba.
Cikin rawar muryar ta ce " good morning Yaya Elameen." Bata yi zaton zai amsa ba don bai cika amsa mata gaisuwa ba, sai dai ga mamakin ta dauke kai yayi daga kallonta ya ce "morning." tare da rabawa ta gefenta ya shige toilet ya turo ƙofa garam.
Daga ita har Fatima da Ummi da kallo suka bishi, bata san ta lula tunani ba sai da ta tsinkayi muryar Ummi na cewa "A'a Joy kece, baki tafi abinki ba kika tsaya biyoma Fatima salon ki ƙara makara, oya maza Ku tafi kar ku tsaya wasa Allah ya tsare." Sallama suka ma Ummi suka fice jikin Joy a sanyaye ko martanin murmushin da Fatima ke sakar mata bata iya mayar mata ba.
Da kallo Ummi ta bisu a ranta ta rasa wannan wani irin haɗuwar jini ne tsakanin Fatima da Joy, ba yadda bata yi ba don ta raba wannan alakar tun abin baiyi nisa ba, amma ina!!! abin ya ci tura tayi dukan tayi faɗan ta daure fuskar amma duk a banza karshe dole ta hakura ta fawwalawa Allah bayan ta gane tsakanin Joy da Fatima hadin Allah ne.
Motsin fitowar Al'ameen daga toilet ne ya dawo da ita hayyacinta, da kallo ta bishi har ya ajiye butar dake hannun shi, ranshi gaba ɗaya a jagule, ga ciwon daya kwana dashi yanzu kuma ga bacin ran ganin arniyar yarinyar nan mai fistari a tsaye a gidan su, tsugunawa yayi a gabanta cike da ladabi yace "Ina kwana Ummi." Amsa mishi tayi cike da kulawa tana nazartar yanayin shi, kwarai ta hango rashin nutsuwa a tattare da shi ga idanun shi ya dan fada, "Tabbas a kwai abin da ke damunshi don banza bata kai zomo kasuwa" ta fada a ranta, mikewa yayi bayan sun gama gaisawa ya nufi hanyar Zaure, murmushi tayi ta Riga ta sani dama bazai taba fada mata damuwarshi ba ita ta haife shi tafi kowa sanin zurfin cikin shi.
Har ya kai bakin Zaure ya ji tace "*AMINTACCE*." Sunan da take Kiran shi da shi kenan a wasu lokutan, zai Iya rantsuwa tunda ya mallaki hankalin kanshi bai taba ji Ummi ta kira sunanshi ba yayan Fatima tafi kiran shi sau da yawa, cak ya tsaya tare da juyowa, kallon juna sukayi cikin ido da sauri ya sauke kan shi ƙasa, a sanyaye tace "Meke damunka." Bai yi mamaki ba don yasan yadda Ummi tasan shi ciki da bai duk yadda taga sauyi a tare da shi sai ta gane.