← Book details Joy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 46

Sashe 40

Joy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuka tayi sosai don a kalla ta kwashe kusan awa guda tana yi, a hankali ta ji kuncin dake zuciyarta na yayewa, ajiyar zuciya ta shiga saukewa akai akai hadi da shessheka, ita kanta baza ta ce ga dalilin kukan nata ba abin da ta sani kawai umarnin zuciyarta take bi, sam! Zuciyarta baza ta iya jurar jin Kalmar Yaya Ameen yana son wata mace ba, balle har a kai ga batun aure, tabbas a duniya tana ganin babu abin da yafi wannan tashin hankali a gareta, a halin yanzu ita kanta bata san meke damunta ba, bata kishi ba domin ita kadai ta tashi gaban iyayenta abin da ta sani kawai soyayya, shiyasa abin da ya faru da ita yau bata san da mai zata kwatantashi ba.

Shigowar Mom ne ya katse tunaninta, da sauri Mom ta k'araso ganin ta a zaune, zama ta yi a kusa da ita ta kai hannu tana tatta6a goshinta zuwa wuyanta,salam! Babu zafi ajiyar zuciya ta sauke tare da godiya da abin bautarsu. Cike da kulawa tace "Princess ya jikin, yaya ki ke ji yanzu, ina ne ke yi ma ki ciwo?" "I'm fine Mom babu in da ke min ciwo, naji sauk'i." "Ok bari na kira miki Papanki ku gaisa tun dazu yake ta kira yana son yaji muryarki." Da d'unbin mamaki a fuskarta ta ce "Papa kuma?" "Yes Ur Papa." Zun6ura baki ta yi ta ce "Ya daina sona yanzu ai." Murmushi Mom ta yi ta ce "Who tell that, a duniya babu abin da Mr James yake kauna sama dake tillon y'arsa,ina tabbatar miki yafi kaunarki fiye da ni dana kawo ki duniya." Ta karashe maganar cike da d'aci a muryarta, amma sam Joy bata fahimci komai ba saboda kakanun shekaru, "Na sani Mom a da Papa yana sona amma cikin yan kwanakin nan ya canza min, abin ya dame ni amma na yi masa uzuri, nasan aiki ne ya sha kan shi." "Of course princess haka ne, jiya ya kammala duk aikin sa ya kaishi kasar Canada, yanzu hankalin sa gaba daya ya waiwayo kan little princess d'in shi, tun safe yake min waya yana neman ki,. Ta kai karshen maganar tana mika mata wayarta da ta yi dialling lambar Papa.

Cike da shauk'in so irinta tsakanin da da mahaifi ta kara wayar a kunnenta tare da cewa; He'll My Papa." "My Joy My everting." Ya amsa mata cike da soyayya, sun Dade Suna waya ta yi mai korafi akan shareta da yake yi kwana biyu hakuri ya bata da cewa shima bai san mai ya same shi ba cikin kwanakin nan, sun dad'e Suna waya kafin su yi sallama.

Mom ta amshi wayarta tana sakin wani shu'umin murmushi wanda ita kad'ai tasan ma'anarsa.......

Ko kunsan ma'anar murmushin Mom, ni da ban sani ba😢

Oum ummeetarh
09116099486
[12/29, 2:47 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀

~FARHAT~

*PAGE 37*

Mikiya Writer's Association

No editing🙏

Washegari a sanyaye Fatima ta gama shirin school, gaba d'aya bata cikin walwala har sai da Ummi ta kula da yanayinta ta tambayeta ko bata da lafiya ne. Al'ameen dake wanki a tsakar gida lokacin da Ummi ke mata magana ya d'ago ya kalleta, tabbas shima ya hangi damuwa da rashin walwala a tare da ita, hakan yasa ya ce mata "Idan baza ki iya zuwa makarantar ba ki barshi kawai gobe Sai ki je" da sauri ta ce "A'a Yaya zan je." Ci gaba ya yi da wankinsa ba tare da ya sake cewa komai ba, sallama ta yi musu ta goya gakarta ta fice.

Da sauri ya dauraye hannayensa ya bi bayanta, girgiza kai Ummi ta yi ba tare da tace komai ba, tasan dama bazai iya barin ta tafi ba sai yaji damuwarta, idan ba haka kuwa a cikin damuwar zai wuni.

Kasancewar ya hada da sassarfa, ita kuma a sanyaye take tafiya yasa ya cimmata a zaure, jin k'arar taku ya sakata saurin juyowa ganin shi yasa ta shagwa6e fuska, a gabanta ya tsaya ya kafeta da ido sannan ya jeho mata tambayar "Meke damunki?" Take ruwan hawaye ya cika mata mata kaurin ido, "shiii!!!." Ya yi mata tare da daura yatsa a lips dinsa ya ce "Kar ki kuskura ki zubar da hawayen nan." Kokarin shanye hawayen ta shiga yi don cika umarnin shi, amma ina sai da su ka zubo.

Ganin haka hankalinsa, ya k'ara tashi, riko hannayenta yayi ya ce "Kin samu wanda zaki sanarwa damuwarki wanda ya fini a duniya ko?" Da sauri ta girgiza kai, ya ce "Oya tell me meke damunki." Cikin shessheka ta ce "Yaya Joy ce." Wani irin yankewa gabanshi ya yi ya fad'i, "Joyyy?" Ya maimaita sunan cikin sigar tambaya, gyada mai kai ta sake yi, cikin tashin hankalin da yake kokarin boyewa ya ce "What happend to her?" "Bata da lafiya ne." Ba karamin jarumta ya yi da bai kai hannu ya dafe heart dinsa ba saboda wani irin fad'uwa da ya yi, cikin wani irin voice da saida Fatima ta d'ago da sauri ta kalle shi ya ce "Mekedamunta." Jim! Fatima ta yi zuciyarta ne ya so shiga rudani, kasancewar ta mai azabar wayo yasa ta yi gaggawar boye yanayinta ta ce "Ji ya ne school ta dinga yin wani abu haka kamar ta sums numfashinta ya dinga sizing idanunta ya juya har saida a ka bata bed rest, kafin Mom d'in ta tazo ta dauketa su ka wuce gida, ni yanzu bansan halin da take ciki ba tun jiya." A sanyaye ya ce "Addu'a zaki ta ya ta da shi na kuka ba Fatima, ki yi mata addu'a Allah ya bata lafiya." Ta gyada kai alamar to, ya ce "Share hawayenki." Babu musu ta share, naira dari ya ciro a aljihunsa ya cika mata tare da cewa; Maza ki wuce kar ki yi latti." Amsa ta yi da hannu biyu ta ce "Nagode Yayana."

Tafiya take tana tariyo abin da ya faru yanzu cike da tarin mamaki, wani irin rauni hadi da damuwa ta hanga karara a tattare da shi, irin wanda ba kasaifai a ka fiye gani a tattare da shi na sai a kan abu mai mahimmanci a gare shi.

Bayan tafiyar Fatima k'asa komawa ya yi yaci gaba da wankinsa, gaba daya jikinsa ya yi san yi kalau, gabansa kuwa har lokacin bai dena faduwa ba, dakinsa ya shigeta ya lalubi kafifarsa ya kwanta a hankali ya lumshe idanunsa da suka canja launi sabida damuwa.

Ya dad'e a haka, ya rasa mai ke masa dad'i a lokacin ya rasa ina zai tsoma zuciyarsa ya ji san yi, tambayar da yake jehowa kansa shine "Meya sameta? Meya faru da ita? Meke damunta." Abinda ya yi ta maimaitawa a ran shi kenan, har bai san iya adadalin lokacin daya 6ata ba, kiran wayar shi ne ya dawo da shi hayyacinsa, Aliyu shine sunan daya bayyana akan fuskar wayar, a matukar sanyaye ya d'aga wayar, magana suka yi na mintuna uku zuwa hudu kafin ya sauke wayar, message ne ya shigo wayar, budewa ya yi, My Meerah ita ce ta yi masa sak'on sai da ya saki murmushi kafin ya bude sakon, kamar kullum sakon Barka da safiya ne da fatan ya ta shi lafiya hadi da zafafan kalaman soyayya, ya kan yi mamakin a ina ta koyi irin wad'an nan kalaman, Sam! Bata jin kunyar fad'a masa kalaman soyayya, ajiyar zuciya ya sauke ko babu komai suna burge shi kuma suna saka shi nishadi a duk lokacin da yake karantawa.

Kwanciya ya ci gaba da yi sai da Ummi ta gaji ta biyo shi d'akin sannan ya samu damar mikewa ya je ya karkare wankin ya yi wanka ya shirya ya tafi school inda daga nan zai zarce wajen kasuwancinsa.

**********

Da sauri Fatima ta karasa sit d'in su, dalilin hango Joy da ta yi zaune, zama ta yi ta shiga tatta6a goshinta zuwa wuyanya at d same time ta na tambayar ta na cewa; Friend ya jikin ki? Meya same ki jiya. Ina ke yi miki ciwo?" Rike hannun Fatima ta yi tana murmushi ta ce "I'm fine Teetee ki bari haka mana." Rau-rau da ido Fatima ta yi ta ce "Hankalina ya ta shi sosai jiya, ban yi zaton zaki zo school yau ba." Dan dariya ta yi ta ce "Matsoraciya naji sauki tun jiya." Daga haka bata sake bata dama sun yi magana akan abinda ya faru jiya ba sai ta canza akalar hirar da gaya mata cewa cikin Wannan month d'in Papanta zai dawo kuma sun dai-daita yanzu ya kula da ita kamar yadda yake yi da, da yake Fatima ta san komai game da tsakaninta da Papanta.

************

Da misalin karfe goma sha daya Maman Amira ta shirya ta shiga wajen Ummi, tun jiya a d'okance take da tazo ta labarta mata abin farincikin dake shirin wanzuwa a tsakanin su.

Gyara zama Maman Amira ta yi bayan sun gama gaisawa da Ummi tare da tambayar lafiyar iyalai harma da d'an ta6a hira, tace "Wai nikam Ummin Fatima ko kin hangi abin da na hango?" Cike da rashin fahimta Ummi tace "Name kenan Maman Amira?" "A game da yaran nan Al'ameen da Amira, sai nake ganin kamar a kwai wata alak'a a tsakanin su." Dariya Ummi ta yi , tace "Maman Amira na dad'e da fahimtar hakan, sai dai rashin tabbaci yasa na bar maganar a zuciyata, don su y'ay'an yau ba'ayi musu katsalandan a irin wannan lamarin, nasan dai komai dad'ewa idan zargina gaskiya ne zasu bayyana kansu, to ashe kema kin kula." Mama da fara'ar fuskarta ta kara fad'ad'a tace "Hmmm na kula Ummi lamarin yaran zamani sai a barsu." Ummi tace "In dai haka be sai muce Alhmdllh! Don wannan abin farin ciki ne." "Kwarai Ummi Fatima zan iya cewa nafi kowa farin ciki da hakan." "A'a fa Maman Aysha, na fiki farin ciki domin kuwa amira diya ce yar albarka duk wacce ta sameta matsayin rusuka ta yi dace." Mama ta amsata da shima "Aminullahi haka." Sun dad'e suna raha kamar na masu shirin zama surukai ba kafin Maman Amira ta yi sallama da Ummi ta tafi............

Oum ummeetarh
09116099486
[12/29, 2:48 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀

~FARHAT~

*PAGE 38*

Mikiya Writer's Association.
Chapter 40 · 0% Book details